Showing 66001 words to 69000 words out of 230725 words
ta fice daga gidan ta kyaleshi.
Ita kanta ta yi mamakin yanda ya kwantar da kai har yake kokarin kare kansa, Aliyun da bai fiye damuwa da kafa hujjar da mutum zai yarda da shi ba. Shi dai idan ya aiwatar to ya aiwatar. Amma a lamuranta, ba haka abin yake ba.
***
"Wai ke meke damunki ne? Ina fa lura da ke kamar ba'a hayyacinki kike ba. Anya kuwa kin rubuta abinda ya dace?"
Tambayar Amrah ta katse tunaninta. Ta yi murmushin yaƙe.
"Ba komai,kawai yanayin jikina ne, jiri nake ji idan ban nemi abu na sanyawa cikina ba akwai matsala."
Jin haka Amrah ta mike da sauri.
"Zama bai ganmu ba Maman Baby, tashi muje."
Ba musu ta mike suka nufi wurin siyar da abinci. Amrah na son ƙara tambayarta dalilin damuwarta sai dai ba ta san ta ya za ta fara ba.
*"Ƴar uwarki ce, ki yi hakuri da dukkan abinda ya faru tsakaninku. Yanda ta mana laifi, kema ta yi maki. Ki dinga kokarin bata shawara a dukkanin tafiyarku. Allah Ya maki albarka keda iyayenki, Ya fiddomaki miji da zai riƙe ki bisa amana."*
Ta tuno alfarmar da Abba ya nemi ta yi mishi akan Ramlat satin da ya wuce. Ita kuwa koda Abban bai nema ba, ta yi amannar ba ta da Aminiyar da ta fi kauna sama da Ramlat din, komai za ta ɗaukeshi ba komai ba. Kuma koyaushe za ta kasance tare da ita koda ace Aliyu zai mata zagin uwa uba. Bai isa ya rabata da Ramsy ba.
"Amrah ina cikin damuwar Aliyu."
Muryar Ramlat din ta katsemata dogon tunanin da ta faɗa, a gaggauce ta dubeta.
"Fadamin damuwarki Ramlat. Me ya yi maki wannan karon?"
Shiru ya biyo baya har suka karasa suka nemi mazauni, Amrah ta yiwa waiter magana ta fadi abinda zai kawomusu sannan ta kara dubanta dakyau. Kafin ma ta kai ga magana Ramlat ta soma, kaf ta bata labarin abinda ya faru gami da fadin.
"Rabuwa da Aliyu shi ya fiyemin alheri Amrah. Sai yanzu na hango abinda ku ke hangomin. Ba zan iya rayuwa da shi haka ba. Amrah na yi kuskure, na yi nadamar abinda na aikata. Ya zan yi? Ya zan yi da jinin Aliyu dake tattare da ni? Yan uwan Aliyu babu mai sona, abin mamaki wacce na zaci za ta fi kowa ƙina da guduna, ita ce har da zuwa ta kawomin katin gayyatar aurenta har ta zauna mu yi hira da dariya. Ina alhakin Muhibbat zai bar ni? Ina hakkin iyayena zai bar ni na ji dadin zaman aure? Na gaji, zan roƙi Aliyu ya sakeni na yi biyayya ga iyayena."
Wani murmushi Amrah ta yi, a ranta tasan karya ne Ramlat ta iya rabuwa da Aliyun. Ta danne tausayin da ya ke tasomata.
"Tun ran gini tun ran zane Ramsy."
Ramlat ta gyada kai tana sharce majina.
"Na yarda, hakane na yarda. Ko mene ni na jazawa kaina. Amma bansan Aliyu mashayi bane, bansan kuma yana zina.."
"Astagfirullah, kin tabbatar ya aikata zinar? Kina da shaida? A'a Ramsy, kar ki bari shaidan ya yi wasa da hankalinki. Ba'a yankewa mutum hukunci haka, hukuncin ma na zina kai tsaye. Ke ba ki san tuggun mata ba? Ki dai kwantar da hankali ki ji me zai ce. Sannan sakin da kike kirawa kanki, kinsan wanda za ki ƙara aura? Kin manta da cikin jikinki? Ai wannan kadai ma ya isa duk wani mai miki kallon kin bijirewa iyaye ya yi maki uzuri. Yanzu da ace..."
Ta yi shiru har sai da aka ajiye musu plate din fried rice da chicken da kuma lemu da ruwa aka bar wurin sannan ta ci gaba.
"Ba wanda zai so ki haifi shege. Komai lalacewar abu gwara kin haihu ƙarƙashin inuwar aure. Ya fiyemaki sutura. Nasan ba ki ci komai ba daga yanayinki, mu ci abincin ma yi maganar daga baya."
Ba musu suka yi bismillah, Amrah na satar kallonta cike da tausayi ganin yanda take kai loma, sai da ta cinye tas kafin ta dauki ruwa ta kora. Daga bisani ta soma shan lemun.
"Ko za ki ƙara?" Fadin Amrah tana dubanta.
Girgiza kai ta yi ta harareta da wasa.
"Haba dai, kamar wata jaka?"
Taɓe baki Amrah ta yi.
"Har kin tunamin da Smally, ci ba ƙiba."
Suka yi dariya, nan kuma aka shiga tuna rayuwar sakandire. Wasu sun yi aure wasu kuwa suna dan ganin gilmawarsu a B.U.K musamman mazan. Wasu kuwa basu samu sun shiga ba.
Bayan sun kammala suka nufi aji, anan ne Amrah ta bata shawarwari gami da kara nunamata illar yanke hukunci cikin fushi. A hankali kuma ta ji zuciyarta ta yi fes, ta kara godewa Allah da samun Aminiya irin Amrah.
***
Sun kai wurin sati suna fushi da juna don tun yana ba ta hakuri yana lallaɓata har ya watsar. Karshe kuma suka shirya don har ankon Muhibbat ya siyamata.
Allah Ya taimaketa lokacin sun kammala jarrabawa, wannan ya bata damar shirin biki a nutse. Rana daya kawai za ta je, ranar yini. Amman hakan bai hanata fargaba ba, gani take yi kamar idan ta je habaici da zagi kawai za ta kwasa ta dawo.
Ranar yinin tun karfe daya ta shirya. Anko ta sanya an mata ɗinkin doguwar riga yanda ba za ta takura ɗan cikinta ba. Ta yi kwalliya sosai abinta.
"Wannan kwalliya haka, duk murnar ce?"
Fadin Aliyu cike da zolaya, ta harareshi ya yi dariya.
"Ai ni na dauketa matsayin ƴar uwa, wallahi ko yau ta so dawowa ɗakinta, ina marhaba."
Dariya sosai ya yi sa'ilin da ya ke kokarin rufe ƙyauren ita kuma tana tsaye jikin mashin tana jiransa. Mota dama tuni ya siyar da abarsa.
"Dakyau Mrs Aliyu, amma dai ban yarda ya kai zuci ba. Irinku ai ba'a yi maku kishiya, wataran ƙurmus za'a wayi gari kun ƙone mijin da kishiyar."
Turus ta yi tana dubansa idanunta nan da nan suka cika da kwalla.
"Bana so Aliyu, bana son irin wannan wasan. Dadin abin ma kai ne babban shaiɗanin da ka yi sanadin mutuwar aure."
Ya daure fuska tamau.
"Ni kike gayawa magana?"
Kamar ta ce an fada din, sai kuma ta haɗiye ta kara daure fuskarta ta kauda kai.
"Wallahi sai dai ki taho ke ɗaya, na fasa kai kin. Aikin banza kawai! Har wuyanki ya kai ki yi kirana da shaiɗani? Duk shaiɗancina na kai ki? Mai saɓawa iyaye kawai."
Cikin jin masifa da takaici ta kara magana.
"Oho dai, dadin abin dai na shirya da iyayena, kuma idan fitsari abin banza ne kaza ma..."
Wani bahagon mari ya ɗauketa da shi wanda ya yi sanadin raguwar gudun numfashinta.
"Kai! Haba Ranka Ya dade, wa ke dukan matarsa haka?"
Faɗin wani dattijo yana mai jan kekensa ya tsaya ganin abinda ya faru. Wani banzan kallo Aliyu ya watsamasa.
"Ina ruwanka? Matarka ko tawa? Dallah can wuce!"
Ya fadi cike da tsawa, kafin ya haye mashin dinsa har yana tunkuɗeta ya soma kokarin tashinsa yana fadin baƙa.
"Ni akwai macen da ta isa ta zageni na kyaleta? Wallahi babu don uwarta."
"Aliyu ba uwata kake zagi ba wallahi sai dai uwar.."
A zuciye ya sauko daga saman mashin din ya kara kai mata naushi a baki. Wani ihu ta kwarara wanda ya janyo hankalin matasan dake can gefe suna kallonsu. Da sauri suka taho, yana kokarin kai mata bugu aka rirriƙeshi. Ashar yake musu yana kiran su sakeshi tunda ba matarsu bace.
"Kai dallah ba ma san hauka! Matarka jakarka ce da za ka kamata da irin wannan duka? Wallahi yanzu sai mu miƙa ka hukuma!"
Fadin wani matashi cikin muryar dabanci. Aliyu ya ɗan sha jinin jikinsa, ita kuwa jiki na rawa ta bi shawarar wani matashi da ya ce ta shige makwafta. Da gudu-gudu ta faɗa makwaftan kuwa.
Matar na zaune tana tsifar kai sai ganin mace ta yi a kanta.
"Innalillahi, baiwar Allah daga ina?"
Ramlat ta durkusa tana kuka ga wani kunya da ya addabeta. Wannan ne karon farko da ta shigo gidan.
"Makwafciyarki ce, matar Aliyu. Don Allah kimin rai ki bari na zauna kafin ya tafi, wallahi kasheni zai yi, yana waje maza sun rikeshi."
Matar ta yi shiru da mamaki, ashe dai dagaske ne da mijinta kwanaki ya ce ya ji ihunta har ya kwankwasa Aliyu ya nemi zaginsa.
"Toh, shigo."
Ta fadi tana jan ɗankwali ta rufe gashinta, Ramlat ta bi bayanta zuwa falon. Ba laifi falon mai kyau, sai dai daga gani ba wani karfi garesu can ba.
Ruwa ta daukomata ta ajiye. Ba ta iya sha ba, sam ba ta cikin hayyacinta. Jikinta har lokacin rawa yake. Kallo ɗaya matar ta gane ciki ne da ita. Tausayinta ya kamata.
"Kiyi hakuri."
Ramlat dai kuka take ta kasa cewa komai.
***
A waje kuwa dakyar aka raba Aliyu fada wannan matashin da ya nemi zaginsa, ya buga mashin ya kara gaba.
Yaron matar da bai fi shekaru goma sha uku ba, ya shiga gidan da sallama.
Matar ta amsa.
"Ya wuce?"
Fadin Ramlat. Yaron ya gyada kai.
"Eh, yanzu ya tafi."
Zumbur ta mike ta dubi matar.
"Nagode sosai, nima tafiya zan yi."
Gyada kai kawai ta yi don ita ta kasa magana, ko sunan Ramlat din ba ta sani ba. Har Ramlat ta kai ƙofa ta biyota.
"Baiwar Allah."
Ta juyo ta kalleta.
Jakarta da ta bari ta miƙa mata gami da fadin .
"Sunana Jamila amma ana kirana Maman Anas. Ya sunanki?"
Ta karbi jakar.
"Ramlat."
Gyada kai Maman Anas ta yi.
"Don Allah Ramlat kar ki yanke hukunci cikin fushi, komai ya yi zafi maganinsa Allah, kinji?"
Murmushin yaƙe ta yi ta amsa da toh gami da godiya. Tana fita ta sauya hanya saboda kunya,mutanen wurin sai nunota ake yi. Hawaye take dakyar take ganin gabanta, kai tsaye ta tari abin hawa zuwa unguwar Yakasai gidan Hajja.
I just published "BABI NA ASHIRIN DA ƊAYA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/K6spRvSBkab
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
*_Rufaida Umar_*
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
21)
"Yanzu na dai yaji kika yi?" Hajja ta fadi tana jin kamar ta tashi ta kara rufeta da sabon duka. Ramlat ta kalleta.
"Haba Hajja, duka fa? Duka a waje har sai da aka kwaceni. Kiyi hakuri amma nidai ba zan koma ba."
"Ku ne yaran yanzu! Babu yanda ba'a yi da ku akan ku yi hakuri ku bi zaɓin iyayenku amma sai ku tiƙe lallai sai abinda ranku ke zo. Ku lallai sai kun nunamana kun yi boko, koda dai wasunku ma ba bokon hakanan suke wannan tsiyar. Gashinan auren bai je ko'ina ba kin fara yawon dakan yaji.
Ba bakin magana dai Ramlat, miƙewa ta yi ta shige ƙuryar ɗakin Hajja din ta yi kwanciyarta zuciyar na raɗaɗi. Har lokacin zafin marin da Aliyu ya yi mata ba ta bar jinsa ba. Shikenan kowace mace na zaune gidan aure da daraja da ƙimarta, ita nata ya zube a idanun Aliyu? Da ace yana gani ai ba zai ɗaga hannu ya bugeta ba. Biki kam ta fasa zuwa ko za'a mutu.
Tun tana jin sababin da Hajja ke yi har ta bar jiyowa, baccin wahala ya yi awon gaba da ita.
***
YAMMACI
Munir da iyalinsa ne suka yada zango wurin Hajja, daga gidan su Bilkisun suke shi ne suka ga dacewar su leƙo. Hira ta yi hira har Hajja ta gangaro kan Ramlat.
"Ramlat kuma?"
Fadin Munir cike da mamaki, Bilkisu ta ƙara buɗe kunnuwanta da son jin abinda ke faruwa. Hajja idanu sun rufe balle Munir din, sun mance matsayin Bilkisu wurin Hilal balle kuma a wurinsu. Komai da ya faru ta kwararo mishi, miƙewa ya yi zumbur ya faɗa ɗakin.
Bacci take tsakaninta da Allah, ba ta yi aune ba ta ji an kai mata wawan bugu a ƙafa. A firgice ta farka gami da salati.
Kallonsa take kirjinta na wani irin lugude, babu wannan ƙauna da tausayin na ƴan uwantaka a kwayar idanunnasa.
"Tashi ki bar gidannan tun ban ɓaɓɓallaki ba!"
Abinda ya ce kenan. Idanunta suka cicciko da kwalla tuni hawayen suka soma zuba.
"Yaya Munir.."
"Yimin shiru! Ni ba Yayanki bane, You have no right to call me Yaya! Kin maida mutane shashashai wadanda basu san me suke yi ba! Kin zaɓi Aliyu akan uban kowa yanzu kuma kin koma yawo bin gidajen dangi kina ɓatawa zuri'armu suna. Ba ki isa ba! Wallahi Ramlatu kin yi mugun kaɗan! Wato kin ga kin kasa kashe iyayenmu da baƙin cikinki, shi ne kika taho wurin tsoffinmu ki hallakamana su. Ai ke Ramla da ƴar halal ce ta gasken, ko kasheki Aliyu zai yi ba za ki kallemu ba balle ki kawomana kokenki. Daga yau na miki iyaka da mu, idan su iyayennamu sun kasa fadamaki cewa ke Annoba ce a garemu, toh yau ni Muniru na fada. Ki fita hanyarmu da zuri'armu. Wallahi bama sonki mun tsaneki! Ko mayya kike ya ci ace zuwa yanzu kurwar da kika ci a danginnan ya isheki."
Ta kasa kwakkwaran motsi, daga yanda numfashinta ke bugu ta tabbatar ba mafarki bane. Wane irin tsana Munir ya yi gareta? Bude baki ta yi amma ta kasa furta komai, a hankali ta zame ta sauko daga gadon ƙarfen Hajja ta lalubi ɗankwalinta da mayafi da kuma jaka, jikinta har rawa yake tsabar wani irin ɓacin rai. Ita kuwa dagaske ko Aliyu zai dinga yanka namanta gunduwa-gunduwa ba za ta kara zuwa ta kai ƙararsa ba. Ba ta son koda kallon Munir don ganinsa take kamar wani bare a wurinta yanda yake dubanta a yanzun. A gaggauce ba ta ko tsaya sallah ba ta fito falon ya biyo bayanta.
"Ke ina za ki je? Muniru korarmin ita ka yi? Ina kuma kake son ta faɗa?"
Fadin Hajja tana miƙewa tsaye a rikice, Bilkisu ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya wani azababben dadi yana yawo daga kai har kafafunta tana ji kamar ta yi tsalle ta rungume mijinta. Burinta ta ga Ramlat a wulaƙance fiye da yanda ta yiwa ɗan uwanta.
'Kaɗan ma kenan!'
Ta faɗi a ƙasan ranta, Ramlat kuwa ba ta ko lura da ita ba, ba ta tsaya amsa kiran da Hajja ke faman kwalamata ba, ta zura takalminta ta bar gidan.
A hanya har tuntuɓe take yi tsabar sauri da tunani har ba ta kula da abinda ke gabanta. Haka har ta iso titi tunanin kalaman Munir ke mata yawo a kwanya.
Wani wawan burki da aka ci, gami da salatin da jama'a suka ɗauka ya ankarar da ita dalilinta ne. Ta hau titi ba ta sani ba, ta hau ba'a hayyaci ba har mota na shirin ɗauke ta. Ta tsaya cak, mai motar wani dattijo, ya fito ya dinga surfamata ruwan masifa. Abu daya ta dauka a ciki, kalmar da ya yi amfani da ita.
"Ba ki da hankali!" Wannan kaɗai ya tsaya a kwakwalwarta. Tana hawaye ta gyada kai.
"Eh ban da hankali. Ka yi hakuri, ka yi hakuri." Abinda ta iya faɗi kenan kafin kuma ta tsinci kanta da ƙarasawa wurinsa ta durkusa.
"Don Allah Baba ka yi hakuri. Wallahi banda hankali ka taimaka ka kaini asibiti."
Kowa kuma sai ya tsaya kallonta, kallon taɓaɓɓiya, ita kuwa kuka take, kukan da take jin har ta mutu ba za ta daina ba. Kukan dana sani, kukan nadama.
'Bijirewa iyayenki ne ya jawomaki.'
Wani bangare na zuciyarta ke mata tuni.
"Ke mene haka? Tashi ki tafi na yafemaki. Allah Ya kiyaye gaba."
Dattijon ya samu kansa da faɗa don abin kuma mamaki ya koma ba shi. Ta miƙe cikin bin umarninsa har da godiya ta ja gefen titi ta tsaya. So take ta tari abin hawa da zai maidata inda ta fito, gidan Aliyu. Gidan da a yanzu Muniru ya tabbatar mata nan kaɗai ne gatanta. Dakyar ta iya ɗaga yatsa ta tsaida napep har sannan idanun wadanda aka yi abin gabansu suna kanta. Ta fadi sunan unguwa ta hau ba ta ko tsaya ciniki ba.
Ɗan sahun har da saita madubi yana kallonta, kuka take yi babu makari (hannu ko gefen mayafi), ba ta damu a ganta ba. Ba ta da zaɓi akan ko ɗaya. Nadama ce tsantsa da dana sani.
"Bansan zai jawomin baƙin jini har haka ba, a lokacin giyar soyayya ce ta kwasheni. Ban san haka zan koma ba. Ramlat nada gata ta kowane bangare, iyayena ba su rageni da komai ba. Amma na kasa yi musu biyayya akan abinda bai taka kara ya karya ba, wannan wane irin sakamako ne? Ni na dawo haka?"
A fili take zancen, ko kuma zantuka. Mai adaidaita sahu tun yana tsoro da yi mata kallon taɓaɓɓiya har ya gane kamar damuwa ce da ɓacin rai ya jawomata komai. Tausayinta ya kamashi, kamar ya ce dama duk wanda bai bi iyayensa ba, rayuwa za ta zo mishi a baibai, sai kuma ya ja bakinsa ya yi shiru.
Dakyar ya samu ta mishi kwatancen inda za ta sauka, ta ciro dari biyar ta mikamasa babu batun karɓar chanji. A farko ta yi niyyar shiga gidan Maman Anas, sai kuma kalaman Munir suka tunzurata ta bude gidan Aliyu ta shiga.
Mashin dinsa yana nan kuma inji a kunne shaidar ya dawo, tana shiga falon hayakin sigari da ƙamshin shisha ya karaɗe hancinta, ko mutum dakyar kake iya hangowa a falon. Ba ta yi mishi magana ba, shima bai mata ba sai ido da ya bi ta da shi har ta shige ɗaki.
Bai taɓa zaton dawowarta a ranar ba, wannan ya ɗan kashemasa jiki. Yana son Ramlatu, abinda ya sanyawa ransa shine ba ta iya magana ba. Shi kuma ba ya son raini, idan shi ya fadamata, ya isa ne. Ita kuwa ba ta isa ta fadamasa ya kyale ba.
***
Sallolin da suke kanta ta biya, zama ta yi tana lazimi har aka kira Magriba ta ɗora da shi. A hankali yunwa ta addabeta, ta fito falon. Hayaƙin ya tafi sosai, sai ta kula da labulayen da ya ɗaga, gami da ware fanka. Kai tsaye kicin ta shiga, Allah Ya taimaka tana da miya don haka taliya fara kawai ta dafa ta dumama miyar. Nan ma koda ta fito ba ya falon, ɗakinta ta wuce, ta dawo ta dauki ruwa ta koma ta kulle da muƙulli.
Tana cika cikinta ta jawo wayarta da zummar kashewa. Karo ta ci da sunan Muhibbat na yawo saman screen din da alamar message. Budewa ta yi ta soma karantawa.
*Assalamu alaikum matar yayana. Naji shiru ba ki zo ba, Yaya ya cemin ba ki jin dadi. Ba haka na so ba dai, amman ba komai. Allah Ya saukeki lafiya. Nagode sosai."*
Wasu hawaye suka zubomata saman ƙuncinta, Muhibbat su ne irin matan