Showing 204001 words to 207000 words out of 230725 words
ajiye saman tebur. Shi kuwa dakinsa ya shige, har ta kammala jera kayan abincin da ruwa bai fito ba. Can kuma ba jimawa sai gashinan, daga shi sai jallabiyar maroon. Ko ba'a faɗa ba wanka ya yi don ƙamshi kawai ke tashi a jikinsa. Kauda kanta ta yi tana mamakin ma kunyarsa da ta ke ji, ta yarda dai mazan ma suna suka tara don Hussein wani kwarjini yake mata. Tana zuba abincin amma a jikinta ta ke jin ya cika ta da ido yana kallonta, gaba ɗaya sai ta rasa sukuni. Ta saci kallonsa, ita ɗin kuwa ya ke kallon babu ƙakƙautawa. Ta gama zubamishi ta ajiye a gabansa, tana shirin zuba nata ya damke hannunta. Kallonsa ta yi. Murmushi ya sakarmata.
"Wannan ya yimin yawa. Zo mu ci tare."
Ya fadi yana matso da kujera daf da shi.
"Seat." Ya fadi a hankali yana dubanta ƙasa-ƙasa. Ba musu ta zagayo ta zauna, ganin jikinsu na gogar juna ne yasa ta yunkurin ja da baya, hannu ya sa da sauri ya saƙalo ƙugun.
"Why?" Ya furta kamar mai raɗa a saitin kunnen. Ta yi ƙasa da kai ba ta ce uffan ba. Ganin haka ya saketa ya soma cin abincin yana haɗawa da sanyamata a baki. Ramlat dai ta ga ta kanta, duk wannan yunƙurin da alwashin da ta ci sai ta neme su ta rasa. Ita har wani shakka-shakkarsa ma ta ji tana yi. Bayan sun ci ya ba ta umarnin ɗauko ledojin da ya shigo da su, ta bude, kaza ce sai lemuka. Ya ja plate ya ajiye, nan ta bude kazar ta zuba, lemukan kuwa ta kai firij don akwai wani a ajiye. Koda ta dawo nan ma ya dage sai dai ya ba ta, ta gaji da wannan abin don haka ta ɗan yi kicin-kicin da fuska. Murmushi ya yi.
"Oh, ashe fa kin ce ba zaman da ki ka shirya yi da ni ba kenan ko? Sorry."
Ta ɗan harareshi da wasa, ya shafi fuskar.
"Ko me kika yi, kyau ya ke min."
Haka suka ƙarasa ci yana ta jan ta da hira. Falon ya koma ya zauna bayan ya wanke hannu ya kuma rage hasken fitilu. Ta kammala gyara wurin, sauran abincin ta sanya a firij. Niyyarta ta shige ɗaki ta kwanta amma kaifin idanunsa ya hana ta aikata hakan, dole ta dawo ta zauna.
Hankalinta ya rabu biyu, tana kallon talabijin, yayinda Hussein ke afkin kallonta. Ta gaji ta juyo fuskarta na nuna alamun gajiya.
"Me nayi don Allah?"
Yanda ta marairaice sai ta sanya shi ƴar dariya. Hannu ya miƙamata. Ɗan harararsa ta yi.
"Gulma ce fa ba na so Heart."
Ta basar.
"Wace gulma kuma?"
Hannunta ya kamo ya murza cikinnasa.
"Har yanzu ba ki tabbatar da babu ƙiyayya tsakanina da ke ba? To a tunaninki tun ma farko, don me na aureki?"
Ta rasa amsar ba shi, ita dai gani ta ke kawai rainin hankali ne yasa shi aurenta. Yanzu kuwa ya gama wanke kansa.
"Tunanin me kike ne? Na shayar da ke mamaki ko? Ni yanzu damuwata kamar ma ke ce ba kya sona."
Ta kalleshi, ya wani yamutse fuska shi a dole damuwa. Hannunta ya kai saman fuskarsa. Ta lumshe idanu sadda ya shafa tun daga sumarsa har ya gangaro saman karan hancinsa, yana tafiyar da hannun tana jin wani zuum a gangar jikinta. Hannunta ta ke kokarin ɗaukewa amma ba ta da wannan kuzarin. Tana ji ya maida yatsunta bakinsa, ya bi su ɗaya bayan ɗaya ya sumbata.
"Faɗamin meyasa ba kya sona? Tsakani da Allah nasan muna da kyau. Haka Allah Ya haliccemu kuma mun godemasa. Ba fa yabon kai ba."
Ta maze ta yi gyaran murya kafin ta amsa.
"Ka ɗauka kyau shi ke sanyawa a so mutum?"
Ya shafi sumar kai yana murmushi da dubanta idanun a lumshe kamar mai gyangyaɗi.
"Kin ɗauka bansan rashin ra'ayin hakan ne ya bambanta ki da sauran matan da ke sona ba?"
Baki buɗe ta ke kallonsa don ita mamaki ma ya ba ta. Ya yi ƴar dariya ya gyara zama sosai ya fuskanci talabijin ya matso gareta sosai. Daga yanayin nutsuwarsa ta fahimci ko me yake shirin cewa mai ma'ana ne.
I just published "BABI NA SITTIN DA ƊAYA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1023106863?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=bdvKCKOC3LLp5bowO1ooPkj4NyQWwtoNnAonSsHZp24WzPeGm2lKyYgVyvV%2Bh9gt6e1Oc%2BZqkJMVkFlQ2xAQQ3P60IL2qqoNgqvumrfhTuosHta7gVySLHczdgg1%2Fq97
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
61)
"A rayuwata, kar ki yi mamakin cewa ban taɓa soyayya ba. Ban yi ba tun ma kafin zuwan Zeenat, balle a bayanta."
Ta dubeshi, dama idanunsa na kanta, sai ya yi murmushi ya riƙo hannunta ya damƙe cikin nasa yana murzawa a hankali kafin ya ɗora.
"Sadda Allah Ya soma haɗa ni da ke, mun haɗu ne lokacin bana cikin nutsuwata sakamakon ɓacin ran wata hatsaniya da muka yi da Zeenat, ban ji komai a kanki ba sai sadda na ƙara cin karo da ke a ma'aikatar Revenue da muka je tax payment. A hankali a hankali haɗuwarmu kan zo akai - akai, tun bana daukarki da wani muhimmanci har ban san yanda aka yi na soma kula da lamuranki ba. Na soma jinki kamar wata ƴar uwata. Ba ki ƙara burgeni ba sai haɗuwarmu a A&Z da kika nunawa duniya da ma Zeenat, akwai soyayya tsakaninmu. Duk a matan da suke bibiyata da sunan so, babu wacce ta taɓa rainawa Zeenat hankali kamar ke."
Suka yi murmushin tuna ranar kafin ya ɗora.
"Tun daga wannan ranar na ji ina son kusancinnamu ya fi haka, na dinga hasashen da ace gaskiya ne muna soyayyar ya kenan? Wane yunƙuri Zeenat za ta yi? Duk fa da cewar a sannan ina ɗan shakkarta, hakan bai hana ni tunaninki ba. Dangantakarku da Hisham ya ƙara ƙarfin shaƙuwarmu. Da tafiya ta yi tafiya, na fahimci ba wai kawai burgeni kike ba, kaunarki nake dagaske. Akwai ranar da na ji Zeenat na waya da Chairman tana kyakyata dariyar mugunta. Maganarki suke yi akan ya ci gaba da yin duk yanda zai yi ya aureki, za ta ba shi kyauta ta musamman idan hakan ta kasance. A lokacin har jaddada masa ta dinga yi kan ya yi amfani da masu gidan rana, sai kuma ga Hisham ya zo min da batun aurenki da Chairman. Bayan tsananin kishin da naji yana neman zautar da ni, sai na dinga ayyanawa a zuciyata ashe dagaske ƙarfin dukiya na saurin rinjayar zuƙata. Ban yi zaton kina daga cikin kwaɗayayyun mata ba, sai gashinan lokaci guda kin ban mamaki. Daga lokacin kuma tunanina ya sauya a kanki."
Ramlat jin haka ta bude baki za ta yi magana ya yi saurin dakatar da ita ta hanyar ɗora yatsansa ba bakin. Murya a tausashe ya ce.
"Yi shiru please, labari ne fa nake ba ki, ki bari na kai ƙarshe."
Ta gyaɗa kai sai dai tuni idanunta sun cicciko, ta kasa kunne tana sauraronsa.
"Baki ba zai iya misalta maki ɗumbin damuwar da zancen aurenki da mutuminnan ya jefa ni ba. Na rasa walwalata, ke kaɗai nake ganin za ki mayemin gurbin ƴan uwana da ban san su ba, ina da su ko bani da su, ba zan tuna ba. Sai gashinan lokaci guda wani can zai rushemin hakan. A sannan har kwanciya nayi a asibiti, aka tabbatar da cewa damuwa ce. Na rage tunani. Bayan na farfaɗo na kasa samun sukuni da walwala, ban yi ƙasa a gwuiwa ba sai da na nemi gidan Baba Dakta, naje a matsayin manemin aurenki."
Da mamaki ta tsuramasa idanu baki a sake, hawayen da ta ke dannewa tun ɗazun suka zubo. Ya yi murmushi gami da sa yatsa ya sharemata.
"Kar ki yi mamakin ta yanda aka yi na san Baba Dakta. A hirarrakin da mukan yi da Hisham, yakan sanyamin shi a ciki don ya cemin ma a wurinsa ya soma neman auren Aisha kafin ya sada shi da Kawunnanku. Yanda na fahimta, banda ma makwafci kuma amini ga mahaifinku, kun daukeshi tamkar mahaifin. Kuna girmamashi sosai kamar yanda ya ke kula da ku. Sau ɗaya na taɓa yiwa Hisham rakiya gidansa, a wata ziyarar gaisuwar Juma'a da ya yi. Yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa nake ganin girman Hisham, mutum ne mai son sada zumunci musamman ranakun juma'a, wataran yakan ɗauke ni muje tare, wataran kuwa shi da matarsa suke zuwa. Wasu lokutan kuma uzuri kan hana ni zuwa. Ko Hisham bai san na je gidan Baba Dakta ba, ya sa aka kai ni falon saukar baƙi, daga bisani ya fito muka gaisa. Na yi mamaki sosai da ya shaida ni alhalin sau ɗaya muka ga juna. Bayan mun gaisa sai na rasa ta inda zan fara, karshe ya dube ni da kyau ya ce na saki jiki da shi, na daukeshi kamar Uba, kar nayi shakkar komai na fadamasa meke tafe da ni. Wannan yasa nan take na ji kaunar mutumin nan. Zuciyata ta samu nutsuwa na fayyacemasa cewa na zo neman iznin aurenki ne. Ya gama saurarona, a karshe har ya yimin tambayar ko dama muna soyayya da sauransu. Duka na ba shi labarin gaskiyar yanayin alaƙata da ke. A karshe ya yimin yar nasiha game da hakuri da kuma fawwalawa Ubangiji komai, ya sanarmin cewa an riga da an yi maki miji don magana yanzu ma ta je ga Kawunnanki kuma sun karɓi mijinnaki da hannu bibbiyu. Ya bani hakuri ya kuma ce na ci gaba da addu'a duk abinda Allah Ya yi na sa a raina shi ne mafi alheri. Ba haka na so ba, amma na ji sauƙi daga radadin da naji akan batun an miki miji da farko saboda Baba Dakta mutum ne wanda ya iya kalamai masu nutsar da zuciya da kwakwalwa. Anan ne na nemi alfarma a wajensa kan yanda muka yi maganar ya zama tsakanin ni da shi. Murmushi ya yi ya nunamin kar na sami damuwa."
Ramlat kallon Hussein kawai ta ke yi, so da kaunarsa na ƙara samun matsuguni a kwakwalwarta da ma dukkan wasu sassa na jikinta. Shima idanun ya ƙuramata na sakanni kafin a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ɗan murza hannunta ya ɗora.
"Ramlat, na ci wuya a ƴan tsakaninnan, daga lokacin da na gane ina matuƙar sonki har zuwa sadda ake rikice-rikicen aurenki da Chairman. Ban ƙara samun walwalwa ba. Komai kika ga ina yi maki wala da farin ciki ko akasinsa, kawai yi nake. Idan na yi tunanin zan rasa ki sai na ji hatta da ke din ma haushinki nake ji. Babban dalilin da ya hana na kasa faɗamaki a lokacin, ban gama haƙiƙancewa kina sona din ba ne ko kuwa kawai tausayina kike. Sannan ni mutum ne mai burin duk matar da nake so, na nunamata son a aikace. Ya fi armashi akan mu tsaya muna ta maida martanin kalamai ta waya da zahiri. Ke yanzu abin ma bai fi burgeki ba?"
Ta sunkuyar da kai tana murmushi. Ya ɗora zancen.
"Kinsan wani abu? Nayi mamaki iyaka da na ji labarin ke ce silar haɗuwata da ɗan uwana, mamaki bai ƙara kashe ni ba sai da na ji labarin a sanadiyyata aka harbe ki. Sosai abin fa ya taɓa ni ya dakarmin zuciya. Wannan ne yasa na ƙara ƙullatar Zeenat. A lokacin kuma na kara ji a jikina babu wani abu da zan iya sakamaki duk wata sadaukarwa da ki ka yi gareni face na maidaki karshen ikona kuma mallakina. A bakin Hisham na soma jin labarin duk wani faɗi tashi da ki ka yi kafin aurenki da Hilal, har ma bayan aurenki da Aliyu. Kinsan me? Sai na tsinci kaina da wani mugun farin ciki, tausayi da ma soyayyarki a zuciyata, amma ban nunawa Hisham ba asalima haushi na dinga ba shi har ya yi fushi ni kuwa na haye mota na wuce na yi maki siyayya na dawo. Bana duba Ramlat, amma a lokacin haka kawai na dinga ji a raina da yardar Allah za ki zama mallakina. Musamman da Hisham ya ba ni tabbacin ba kya son Chairman kuma su Hajiya ma ba sonsa su ke yi ba. Abin dai daga Kawunnanki ne. Wannan ne ya sanya ni cikin annashuwa. Kinga wancan aurennaki, ke ki ka yi kiɗa da rawarki, wannan karon kuwa tunda har yan uwanki ma ba sa ta Chairman, to fa abun zai zo da sauki. Na ci gaba da addu'a da miƙawa Ubangiji kukana har zuwa lokacin da na ji labarin fasa aurenki da Chairman. Sai kuma ga wanj Baban Hanif na neman yimin shigar sauri. Sai dai ban sha wahala da shi ba saboda takanas Baba Dakta ya neme ni ta waya lokacin muna Adamawa ya ce idan har dagaske nake to shi kam hankalinsa ya fi nutsuwa da ni, bai kuma tunkareni ba sai da ya ji ta bakin Hajiyarmu. Bai fadamin dalilin da yasa aka bar maganar Baban Hanif ba, ya dai bani damar na turo magabatana tunda har kin bar masa wuƙa da nama, to shi kuma ya zaɓamaki ni a matsayin mijin aure. Na ji dadin lamarin sosai. Anan ne muka yi shawara da iyayena, ba ɓata lokaci muka taho Kano tare da ɗan uwana da Kawu Adamu. Aka shige gaba aka yi duk abinda ya dace. Kin ji dukkan abinda ya faru."
Ta gyada kai tana murmushi, ya saki hannunta ya miƙe, kayan kallo ya shiga kashewa kafin ta ga ya soma rage fitilun falon bayan ya tabbatar kofar falon a rufe ta ke gam! Ganin haka sai ta mike ta tayashi da rufe kofar fita na kicin da kuma kashe fitilun da rufe kofar kicin din gaba ɗaya. Koda ta juyo sai suka ci karo, ya yi saurin riƙota. Goshinsu haɗe wuri guda kowannensu na maida numfashi, za ta zame ya yi saurin riƙeta da kyau. A hankali kuma ya ja baya.
"Ban gama ba ki labari ba, ki yi shirin kwanciya ki zo, ina jiranki."
Daga haka ya yi gaba tana kallo ya buɗe ƙofar ɗakinsa ya shiga. Ta sauke ajiyar zuciya, ba ta daina murmushi ba kamar yanda ba ta gaji da jin wannan daddaɗan labarin da ya ke ba ta ba. Ta tuna Kawu Bello da ya ce dama Hussein din ya taɓa neman aurenta wurin Baba Dakta bai samu ba sai a wannan karon. Da wannan tunanin cike da wata iriyar kasala ta ƙarasa ɗakinta. Sai da ta ƙara wanka don ƙamshin da ta ji Hussein yana yi sai ta ke ji kamar ita banda wari ba abinda ke fita daga jikinta. Loko da saƙo duka sai da ta bi ta wanke kafin kuma ta fito ta goge jiki ta shiga mulka turaruka masu kamshi kala-kala. A ƙarshe ta fiddo wata doguwar riga mai hawa farare ƙal ta sanya, ta ɗora hula da ya rufemata gashinta. Duban kanta ta ke yi a madubi, rigar ta ciki da kaɗan ta wuce gwuiwarta sai top din da ta ketare zuwa ƙaurinta. Girgiza kai ta yi, a haka ma kwarjini Hussein ke mata ina ga kuma ta isa gabansa a haka? Da saurinta ta karasa wardrobe ta fiddo zani. Ido ta fiddo waje kirjinta ya harba jin hannuwansa zagaye a ƙugunta.
"Kin yi kyau, shi ne ki ke kokarin rufemin abinda Allah Ya halarta min gani?"
Ta lumshe idanu, kunya sosai ta ke ji, ta kasa kataɓus. Juyo da ita ya yi suka fuskanci juna. Har lokacin ta kasa buɗe idanun. Kallon fuskarta kawai ya ke yi yana jin sanyi a zuciyarsa. A ƙasan ransa banda hamdala babu abinda ya ke yiwa Ubangijinsa. Jin shirun ya yi yawa ne ta bude idanunta ta dubeshi. Ganin idanunsa har sannan a kanta suke sai ta yi azamar ja baya ta cire jikinta daga nashi.
"Ki yi alwala." Ya juya ya koma ɗakinsa, ta sauke ajiyar zuciya. Hussein zai kasheta da kala-kalan soyayyarsa. Jikinta ya yi sanyi da ta tuna ba ta da sallah, daga yanayin Hussein ba sauki. Sai kawai ta ji ya ba ta tausayi. Ta kashe fitilu ta rufe kofar, tana tafe tana tuna aurenta da Aliyu, ranar da aka kawota sam ba ta da walwala ko misƙala zarra, wannan karon kam Allah kadai Yasan yanda ta ke jin zuciyarta musamman idan ta tuna yan uwanta da ma abokan arziki duk suna son aurenta da Hussein. Wannan ma abin ta ƙara godewa Allah ne. Fatanta Allah Ya basu zaman lafiya da iyali nagari.
Yana saman darduma, ga dukkan alamu sallah ya idar, ba ta shiga dakin ba tun da aka kawo ta sai lokacin. Sosai ya burgeta. Dardumar da ta ga ya shimfida sai ma ya ba ta dariya ta danne. Ganin ta koma gefen gado ta zauna ya sanya bayan kammala addu'arsa ya dubeta.
"Sallah fa?"
Ta kalleshi ta sunkuyar da kai, daga yanayinta ya gane cewa ba maganarsa. Don haka ya mike kawai ya yi nafilarsa ya yi addua, tare suka shafa ya miƙe.
"Taho mu kwanta na ƙarasa ba ki labari."
Yana fadin hakan ne yana nufar makunnin fitilun dakin, kashesu ya yi gami da kai hannu ya kunna na gefen gadon. Hasken ba yawa, kwanciya ya wuce zai yi kai tsaye.
"Ɗan tsaya." Ta dakatar da shi, ya ja ya tsaya kawai yana kallonta. Abin rufar ta ja ta kakkaɓe gadon ta gyara zaman filon kafin ta dube shi da murmushi.
"Bismillah."
Ya kwanta itama ta kwanta, fitilar ya kashe. Ɗakin ya yi shiru na wani lokaci, numfashinsu na gauraya wuri guda kowanne na shaƙar daddaɗan ƙamshin jikin ɗan uwansa. Ya kai hannu ya zame hular kanta, yana shafa kitsonta, ta lumshe idanu. Ya soma magana.
"Heart, kin yi zaton ba sonki nake ba, kamar ma dai kawai zan aureki ne. Ba ki san cewa Hussein ya soma sonki tun kan ki soma sonsa ba."
Duk da cewa babu haske sai da ta zaro ido. Kunya ta sanya ta runtse idanunta. Dama ya san tana sonsa?
Shi kuwa jin ta yi shiru sai ya kai hannu saman fuskarta, murmushi ya yi mai sauti.
"Kar fa ki yi mamaki, na sani. Sai dai ba karamin nishaɗantuwa na dinga yi idan naga kin yi narai-narai kina son yin kuka duk a tunaninki na bana sonki. Sai Hisham wanda yake sanya ni nishaɗi idan ya sauya fuska yana tayaki yaƙi. Kuma yasan sarai ina sonki amma na nunamasa nifa a'a."
Hannunta ya kai saman kirjinsa. Ta nutsu tana jin yanda ya ke bugu da ƙarfi.
"Kamar yanda kike jin zuciyata na bugawa a kowane daƙiƙa, wallahi Ramlat haka nake jin