Showing 207001 words to 210000 words out of 230725 words

Chapter 70 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1087

sonki a kowane dakika. Kwakwalwata ba ta taɓa samun hutu daga tunaninki ba, kar ki ƙara ji a ranki cewa zaman doya da manja zamu yi. Kar ki ƙara sanya wa a ranki wannan bawan Allahn ba ya sonki. Kinji?"

"Uhm." Ta faɗi a hankali, hakan yasa shi janyota ba shiri ya shiga aikamata saƙonnin da suka birkita tunaninta har ta shagala itama wurin maida martani. Nan fa ta ruɗa Hussein, ita kuwa shawarwarin yayyunta da su Amrah ke yawo a  kwakwalwarta.

_*"Kar ki wasa da kowacce dama, kar fa ki manta Hussein bai san soyayya ba sai a kanki. Don haka ki saki jikinki ki rike mijinki da hannu bibbiyu."*_

Ta tuno kalaman Maman Twins.

***
  WASHEGARI....

Tana jin sadda ya maida kanta saman filo madadin a farko da yake a saman kirjinsa, ya gyaramata ya ƙara rufe ta da tattausan bargon sannan ya miƙe. Murmushi ta yi ta buɗe idanu, banɗaki ya buɗe ya shiga, nan ya fahimci Asuba ce. Ta kai hannu a hankali ta shafi makwancinsa, so da kaunarsa marar adadi na kara ninkuwa a zuciya da gangar jikinta. Idan ta tuna manyan kalamai da kuma yanayin ruɗewar da ya yi duk a kanta, Hussein kuka na hawaye ne kawai bai mata ba, ya yi wani furucin da dole ya ba ta tausayi a sannan wato inama a kanta ya soma aure. Jin motsin fitowarsa bai sa ta rufe idanunta ba saboda fitilun ɗakin a kashe suke. Ganin yana laluben makunni yasa ta saurin rufe idon. Kimtsawa ya yi ya fice masallaci a gaggauce don ya so ya makara.

Tana jin fitarsa ta kunne bedside lamp ta mike zaune rungume da bargo, murmushi take kamar wata sabuwar kamu, ta gaji da murmusawar ta koma ta kwanta bayan ta kashe fitilar.  Har Hussein ya dawo ya hau gadon ya jawota jiki, idanunta ƙirr. A hankali kuma wani sabon daddaɗan bacci ya soma fisgarta.

Ita ta riga shi farkawa wuraren karfe bakwai da rabi na safe, miƙewa ta yi ta nufi dakinta. Kai tsaye brush ta soma sannan ta faɗa wanka tana ji kamar an mata albishir da gidan Aljanna. Ba ta da wani sauran buri mai yawa a yanzu face na ta kyautatawa mijinta hakanan da addu'ar Allah Ya rayamata yaranta, Ya ja kwanan Hajiyarta mai sonta.

Koda ta fito shiryawa ta yi cikin doguwar rigar atamfar da ta matse daga sama, ƙasan kuwa ya buɗe amma ba sosai ba. Ta yi kyau musamman ma kwalliyar da ta yiwa fuskarta. Sai da ta shafa turare a gaggauce kafin ta fito da zummar shiga kicin. Sai dai ƙarar wayarta ya katse hanzarinta, ganin sunan Hafsat ta ɗaga. Suka gaisa.

"Dama kira nayi na ji ko kun tashi. Ganinan zan kawomaku abin kari."

"Toh Hafsat, sai kin karaso."

Daga haka ta ajiye wayar, ba jimawa aka kwankwasa ƙofar. Buɗewa kawai ta yi don ta san Hafsat ce. Suka yiwa juna murmushi. Ta karaso ta ajiye kayan hannunta saman tebur. Duk yanda ta so akan ta tsaya su yi ƴar hira amma ina ta ƙi.

"Rufamin asiri Adda Amal, zan dawo anjima dai in sha Allahu. Ban shiryawa faɗan Hamma Hussein ba."

Dariya ma ta ba Ramlat, suka yi sallama ta tafi. Ciki ta koma don ta ga ko ya farka. Tsaye ta iske shi daga shi sai gajeran wando sai kuwa tawul yana faman goge sumar kansa. Sunkuyar da kai ta yi gami da kokarin fita. Caraf ya damƙo hannunta.

"Dodo na zama?"

Ta girgiza kai tana murmushi ba tare data juyo ba. Dawo da ita baya ya yi, ta kasa kallonsa. Karshe ta wayance da gaidashi. Maimakon ya amsa sai ya sumbaci kuncinta.

"Kin yi kyau sosai."

"Na gode." Ta furta a hankali.

"Tunda ba za'a taya ni ba, a zauna a jira na kammala."

Ba musu ta karasa gefen gadon ta zauna, ganin ya juyamata baya yana kallon madubi yasa ta ɗago kai tana ƙarewa mijinta kallo da irin baiwa da ni'imar da Allah Ya mishi na kyawun sura. A fakaice yana kallonta, dariya ma ta dinga ba shi, satar kallon na mene alhalin shi ɗin nata ne halak malak? Har ya kammala da gaban madubin ya juyo bai bar murmushi ba, ganin ya juyo kuwa ta yi saurin kauda kai. Ƙananun kaya ya fiddo ya sanya. Ya koma gaban madubin ya fesa turare, a ranta ayyanawa take son ƙamshi irin na Hussein ko mace sai haka.
Kafin ma ya tunkarota ta mike, suka dubi juna kowanne da abinda ya ke saƙawa a ransa. Ta sunkuyar da kai.

"Barka da Asuba, fatan ka tashi lafiya?"

Ya kama hannunta ya jawota ya sa a jikinsa sosai.

"Lafiya na tashi, ina fatan kema haka?"

Suka kwashi ƴan sakanni kafin ya hau yi mata raɗa a kunne, kunya ta sa ta tureshi tana murmushi.

"Mene hakan wai?" Ta faɗi kamar za ta yi kuka. Ya taɓe baki.

"Gulma ce bana so."

Hararar wasa ta mishi ta juya da sauri ya kuwa bi bayanta yana fadin.

"Ni kike wa wannan kallon?"

Ganin dai kokarin cafketa ya ke yasa ta juyo tana dariya.

"Don Allah ka yi hakuri, na tuba."

Ya shafi sumar kansa kawai ya yi gaba zuwa tsakiyar falon.

"Nan za ki kawomin mu ci, bana son can."

Ta amsa da toh kafin ta yi gaba yana binta da kallo kamar za ta gudu ta bar shi. Sai da suka kammala karyawa tsaf sannan ya bata umarnin saka mayafi su je gaida Dada. Ɗakinta ta koma, dama ba nisa mayafin ya yi ba, ta gyara zamansa sosai ta zura flatshoe. Koda suka kama hanya, hannunta ya lalubo ya kama ya murza har sai da ta lumshe ido ba ta yarda ta kalleshi ba. Ɗan matsowa ya yi har kafaɗunsu na gogan juna.

"Wai ni bakin tsiwar naki mutuwa ya yi? Ko na lalubo amsar a daren jiya?"

Ta tsaya cak ta shiga kokarin zame hannunta a nashi, ya kara damƙewa yana dariya.

"Wallahi sai na ɗaga ki cak mu shiga har wajen Dada. Kin san zan iya ko?"

Dole ta hakura ganin akwai ma'aikata a farfajiyar gidan ta kuma tsorata don ta san halinsa dagasken yake.

Dada ta yi farin ciki matuƙa da ganinsu, ita kuwa Ramlat wacce ta samu dakyar ya saki hannunta, kunya sosai ta ke ji don ma Allah Ya taimaka baƙi duk sun watse, wasu yau da Asuba suka wuce.

Anan wurin Dadar ya bar ta ya fice wurin AlHassan.

***
KANO...

*DA SAURAN RINA A KABA..!*




I just published "BABI NA SITTIN DA BIYU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1024183736?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=kerlmbTD11RJIZ1OU3cjRAuaKiLriOJD0fY0ly4CVNRLiEciXy1qh%2BgcHslN3fAHkmM%2BuxbSZlMyLFyekdT2BAKcap35wfLbDInDLU%2Bf6jBwfeAcG9qlXUARTAIfqHS%2B




🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

62)

*Assalamu alaikum masoya Karfen Kafa. Ina mai ba ku hakurin jinkirin da ake samu kafin posting. Ku yi hakuri pls. In sha Allah aski ya zo dab gaban goshi.* 🥰



Hajiya Batool ta zabga uban tagumi tana kallon Aminiyarta, ba ta san ta inda za ta fara magance mata matsalarta ba alhalin ita kanta yanzu cikinsa ta ke. Gaba daya ɗanta ya kwashi matarsa sun bar garin sun koma Abuja da zama. Waya ta kira sai ya ga dama yake ɗagawa balle a kai ga aike. Komai na rayuwa ya sauyamata, kasuwancin ya ja baya babu albarka ciki.

Hajiya Zeenatu wacce ta gama kai wa bango da shirun Batool, ta kundumar ashar da faɗin.

"Wannan wane irin wulakanci ne Batool, na kawomaki kukana ina neman mafita shi ne tsabar wulaƙanci ki ka shareni ki ka maida ni wata banza?! Hussein ne fa, kin fi kowa sanin yanda nake son Hussein amma har na gama ba ki labarin cin kashin da ya yimin gaban yan uwansa ki kasa  jajantamin?!"

Tana maganar tana faɗa rai a ɓace. Hajiya Batool ta sauke ajiyar zuciya.

"Me zan maki? Wane irin nusarwa ce ban maki ba don Allah? Amma ke makahon son yaron nan ya sanya ba kya ji ba kya gani, ai gashinan ya nunamaki shi na zamani ne!"

Hajiya Zeenatu ta yi kwafa, ba abinda ya faɗomata a rai sai cin mutuncin da ya yi mata a farkon haɗuwarsu, da gaskiyar Batool da ta ce makahon so ya rufe idanunta. Ta sauke ajiyar zuciya.

"Naji, koma me ya faru, ina da hannu a ciki. Amma kuma kin san ba zan zauna haka ba ko? Kin san sai na rama? Ki tashi mu shirya mu leka wurin Gora. Mene a ciki? Zan durkusa na ba shi hakurin laifin da na yi mishi idan ya so ya samarmana mafita."

Hajiya Batool ta yi shiru, itama fa yanzun tana da bukatar hanyar da za ta bi a karkato da hankalin ɗanta gareta, ta kuma amince idan ya dawo ko wacece ya aura idan har hakan zai yiwa Fa'iza ciwo. Abinda ma ta lura da shi, itama kanta Fa'iza tama tsubbace-tsubbacenta shi ne dalilin da yasa ta fi karfinta. Sauke ajiyar zuciya ta yi, ta tuna kowacece Fa'iza, dama tun can ƴan  gidansu ba wata cikakkiyar tarbiyya ce da su ba, ganin irin arzikin da ubanta ke da shi matsayinsa na tsohon minista ya sanya tun ɗanta bai wani ba soyayyar da Fa'izar ke mishi muhimmanci ba, har sai da ta yi yanda ta yi ta tursasashi. Yanzun gashinan tana girbar abinda ta shuka.

"Na yarda muje. Idan ma bai sauraremu ba, za yiwa Mariama waya mu wuce Nijar kawai. Na fi yarda da aikin buzayennan ma."

Da wannan suka shirya suka fice wurin Gora.

***
ADAMAWA..

Dada ta dubi Ramlat cikin nutsuwa ta ce.

"Kinga abin Allah ko? Ba ya kyale azzalumi, shiyasa duk abinda aka dage da kai kuka gareShi, watarana zai shuɗe ya zama tarihi. Ba wanda ya fi ban mamaki a lamarin sai ɗan uwana Modibbo, ban yi tsammanin ƙiyayyar ta kai har haka ba, amma ina nan inda nake, shiru ma magana ce. Allah ne zai maganinsa don nikam ban isa nayi ba. Ba na jin wannan karon zan iya yafemishi wannan zaluncin da ya yimin ni da yarana. Duk yanda zan so na ji alaƙarsa da matarnan, zan jira har zuwa lokacin da zai kawo kansa garemu."

Hafsat da ke zaune itama sai ta ji jikinta ya kara sanyi, wayarta ta kara kalla, wani saƙon ne na Taheer ya kara faɗowa, duka dai ban hakuri ne da nuni da yake mata cewar laifin wani ba ya shafar wani. Kalaman soyayya zafafa ya ke jifanta da su, ta yarda so ba karya ba ne, tana son Taheer sosai, duk da son ta ke mishi bai kai wanda shi ya ke mata ba, amma dole za ta sanyawa zuciyarta dangana. Ta san babu ta yanda aurensu zai yiwu. A hankali ta mike ta zame daga falon ta shige ɗaki, hawaye ne ya tahomata sai dai dole ta haɗiyeshi. A yanda ta ke da zafi, ba ta yi zaton soyayyar Taheer zai russunar da ita har haka ba har ma ta ji inama ɗan wani gidan ne daban ba gidan Kawun ba.

Ɓangaren Ramlat itama haka ta koma sashinta cike da tunane-tunane, ta kara ganin girma da ƙimar uwar mijinnata. Tabbas mahakurci mawadaci. Kai tsaye ta shiga gyaran duk inda bai ba ta ba, sai da ta tabbatar gidan ya kimtsu babu sauran dauɗa da kayan datti a kicin sannan ta kara gyara jikinta ta shirya cikin doguwar riga ƴar kanti milk mai adon duwatsu. Sam ba shi da nauyi. Ta feshe ko'ina na jikinta da turare. Saman doguwar kujera ta shimfide ta zurawa ƙaton enlargement na hoton mijinta idanu. Murmushi sosai ta shiga yi tana tuna kalamansa da ma saƙonni da dama waɗanda ya isarmata a daren jiya. A hankali ta lumshe idanunta wani farin ciki na mamayeta, wani lokacin ta kan ji kamar mafarki, wai yau ita ce a garin masoyinta kuma matsayin matarsa. Ta jima cikin tunani kafin wani bacci mai dadi ya kwasheta.

Ya jima da shigowa gidan, sai dai yana sashen Dada su na tattauna. Koda ya karaso gidan, ya isketa tana bacci murmushi kawai ya yi, ciki ya karasa ya rage suturar jikinsa ya ɗan watsa ruwa don ba laifi garin ana ɗan zafi. Gajeran wando three-quarter ya sanya da yar shirt marar hannu, gaba daya ƙirarsa ta bayyana muraran.  Koda ya fito ya ci karo da Hafsat da ke faman sallama amma gwanartasa ba ta ji ba. Kofar ya bude ya sanya yatsa a bakinsa yana mata alamar ta yi shiru, murmushi kawai Hafsat ta yi hango dalilin, Adda Amal ke bacci. Hanya ya ba ta ta karasa kan tebur ta ajiye kwandon abincin ta juya ta fice ya rufe ƙofar a hankali. Cikin falon ya dawo ya zauna saman kujerar da ke fuskantarta, waya ya ke amsawa da Hisham sai dai rabin hankalinnasa yana ga Ramlatun yayinda ya ke kallon sauka da hawan numfashinta. Harma da yanda rigar ta fiddo surarta fa yi mata kyau.  Wani lokacin kuma ya maida kai ga ƙawatacciyar fuskarta da kallon ke sanya shi nishaɗi.

A jikinta ta ji ana kallonta, a hankali ta soma kikkifta idanu kafin ta budesu kaɗan, ganinsa zaune yana kallonta ya sa ta ware duka dara-daran idanun kafin ta mike zaune ba shiri. Kunya ta sa ta mikewa sum-sum don ta shiga ɗaki ta ƙara wanko bakinta, sai dai tana zuwa gefensa ya yi azamar riƙota ta faɗo cinyarsa ta zaune ɗabas. Ta sunkuyar da kai yayinda shi kuwa wayar yake amsawa amma hannunsa guda ya kasa tsayuwa wuri guda, karshe ma zancen kasa fita ya yi yanda ya dace sakamakon fuskarsa da ya tura a ƙasan wuyanta yana shaƙar ƙamshin jikinta. Hisham ko fahimta ya yi ko mene? Kawai sai ji ya yi wayar ta ɗauke don haka ya kalli wayar sai kuma ya ajiye a gefe yana murmushi, ita kuwa Ramlat da gaba ɗaya ta rufe idanunta numfashinta na hawa da sauka da sauri, ta kara yunkurin miƙewa. Ya riketa sosai.

"Wai ina za ki je? Ba ki yi missing ɗina ba."

Kai ta girgiza ta kasa magana. Ya bi bakin da kallo kafin ya dubi idanu da ta bude a yanzun.

"Kin daina magana ko me? Wani abu ki ke ci?"

Ya maida dubansa ga bakin da take ƙara damtsewa.

Girgiza kai ta yi alamar aa, tana kokarin tashi sai ya ƙara riketa ya yi murmushi.

"Oh na fahimta, wato daga bacci kika tashi ba kya son ki yi magana naji wari ko?"

Kunya da takaicinsa ta ji har ba ta san sadda ta watsamasa harara ba. Ya kara murmusawa.

"Na nawa kuma?"

Ta waro ido.

"Me kake nufi?"

Ba ta san sadda ta yi furucin ba sai kuma ta yi saurin rufe bakin ta mike a guje ta yi daki ta bar Hussein da yi mata dariya. Koda ta wanke baki da fuskar sai kunya ta hanata fitowa falon, ta samu gefen gado ta zauna ta na mai jin haushin kanta. Yanzu dariyar ma da ya yi watakila don ya shaƙi warin bakinta ne. Tana nan zaune ya shigo, fuska ta ɗan haɗe ita a dole kar ya yi mata dariya. Hannu ya miƙamata yana murmushi. Ta kasa miƙamasa nata, sai shi ne ya gaji ya ja kamo hannunta ya miƙar da ita ta faɗo jikinsa har tana take masa kafafu da lausassun tafukan kafafunta. Goshinsu haɗe wuri guda, ta kankame rigarsa don ji ta ke kamar za su zube.

"Ko ba ki wanke ba ni ban ji komai ba."

"Uhmm."Abinda ta ce kenan, amma ita dai ta san ko yaya mutum ya yi bacci to fa sai a hankali.

"Wai idan na riƙe ki me kike ji? Sai naga kina kanne idanu."

Wayyo kunya, ta buɗe idanun tarr ta dubeshi da harara, murmushi ya yi don dama kwayoyin idanun yake son gani.

"Kai ka ga haka."

Daga nan ta zame jikinta ta yi falon ya bi ta a baya. Haushin kanta ma ta ji.

Tana zama ya zauna a gefenta, ta matsa, ya matso. Ta dubeshi, ya sakarmata murmushi. Kafin ta yi yunkurin mikewa ya kamata sosai, ya shiga aikamata da sakonni daban-daban wanda dolenta ta russuna. Sai da ya gaji don kansa ya matseta a jikinsa yana maida numfashi. Lalubo kunnenta ya yi bayan ya zagayeshi da harshensa ya shiga yi mata magana a tausashe.

"Na fi ki mance kaina idan muna tare. Na fi ki rawar jiki da mazari. Kar ki damu da duk abinda Hussein ya fadi ko kuma zai fada, haka nake, ina son tsokana ko don na yi dariya. Ina sonki sosai, ina kaunarki."

Murmushi tayi kafin ta kara shigewa jikinsa, ya kuwa ba ta kyakkyawan mazauni. Sun ɗan jima a haka kafin su mike zaune.

"Yunwa fa nake ji." Ya fadi, ta mike, ita kanta yunwar ta ke ji don tuni abincin safe ya narke.

Sai da ta soma zuba mishi, tana kokarin zuba wani ya hanata.

"Ba fa na son muna raba plate. Ki fahimta please."

Ta gyada kai.

"Zan kiyaye."

Daga nan ta dauki cokali ta matsa suka soma ci. Bayan sun kammala ta tattare komai ta kai inda ya dace. Koda ta dawo shi tuni ya yi daki, alwalar sallar la'asar ya yi. Ya dube ta.

"Bari na wuce masallaci."

Ta amsa da toh da yi mishi kyakkyawan addu'a sannan ya fice ita kuma ta kara miƙe ƙafa don har sannan ba ta samu tsarki ba. Ta sani sai a gobe za ta samu don ita mutum ce mai ƙidaya kwanakin al'adarta. Hakan na taimakawa kwarai wajen sanin lokacin farawa da kammalawa na kowane wata. Wannan yasa a wayarta ta ke da App mai suna FLO, tana lissafe da kwanakin farawa da kammalawar period dinta.

Tana nan zaune ya shigo amma fuskarsa ba kamar yanda ya fita ba, gaba daya a ɗaure. Ya karaso ya zauna  bai ko kalleta ba. Ta ji gabanta ya fadi.

"Sannu da dawowa."

Kai kawai ya gyadamata, hakan ya ba ta tabbacin ba lafiya ba. Shi kuwa a hanyar dawowarsa ce ya biya wurin Dada, Hafsat ya tarar kadai a falon tana amsa wayar Taheer har tana ba shi shawarar ya gwada zuwa neman aurenta hannun yayyunnata. Wannan ne ya fusatashi, ya kuma kirata da marar zuciya da ba ta tausayin Dadarsu. Ya kammala fatattakarta ya kwace wayar sannan ya shigo.

Ramlat gaba daya ta ji damuwa da sauyawarsa don haka ta yi shahadar miƙewa ta karasa kusa da shi ta zauna. Ta daure ta kamo hannunsa ba tare da ta yarda ta kalleshi ba ta ce.

"Ka yi hakuri, ko me aka yi maka, ka zama mai hakuri don Allah."

Shi kuwa kallonta ya ke kawai.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login