Showing 18001 words to 21000 words out of 230725 words
ɗayar ta mike ta nufi kicin. Toh kawai Ramla ta ce tana mai ƙarewa gidan kallo lokaci guda tana kara jinjina arzikin mijin Muhibbat.
'Kin manta itama daidai gwargwado suna da rufin asiri?' Wani ɓangare na zuciyarta ta tunatar da ita wacece Muhibbat.
_*Mahaifinta Justice AbdulRazak Buba, tsohon alƙali ne a wata babbar kotu ta ƙasa. Ƴan asalin garin Kano ne gaba da bayansu, duk a zuriar Marigayi Malam Buba shi ne fitaccen mai arziki wanda sunansa ya shahara har wasu a zuri'ar kan ara su yafa. Babban family house ne wanda kusan duk ana tare wuri guda. Muhibbat ita kadai ce ɗiyarsa mace wacce yake so kuma yake matukar ji da ita. Ita ce kuma wacce kaddarar aure ya faɗa mata wanda a yanzun ya zama tarihi.*_
Ƙamshin turaren da ya mamaye falon ne ya ankarar da ita zuwan Muhibbat. Ta ɗago kai tana dubanta lokaci guda suka sakarwa juna murmushi mai nuni da tsantsar kauna da farin cikin ganin juna. A gefe guda kuwa kamanninta da ALIYU take ƙara gani zahiran wanda har Muhibbat kan rikiɗemata zuwa kamannin Affan wanda ke matukar kama da mahaifinnasa.
Fara ce mai matsakaicin tsawo, tana da siririn jiki sai dai ba mai muni ba. Gashinta luf-luf ya kwanta har saman goshinta. Mace ce mai hakuri kuma mai yawan fara'a. Ba ta daukar lamura da zafi. Cikar kamala dai Muhibbat ta kai, jaruma ce har gobe a idanun Ramlat, yayinda bata fasa yiwa kanta kallon zalamammiya kuma mai laifi a idanun Muhibbat ba.
"Kai Madam, kinga yanda kike ƙara mulmulewa kuwa? Anya nan gaba za ki nuna kin san mu?"
Muhibbat ke wannan kalamin sa'ilin da take zama da kamo hannun Affan, lokaci guda tana ƙarewa Ramlat kallo cikin dariya.
Harararta ta yi da wasa gami da jan guntun tsaki.
"Kin ji wata magana, ina hutu a wurina nida koyaushe ina hanyar Ofis? Hutu ai sai ku Hajiyoyi."
Suka dara.
"Ba ki kyauta ba, shi ne kika bar Ummina da Ansar a gida? Wannan autan na ƙagu ki yi aure a mishi ƙanwa ko ƙani mu ga ta autantaka."
Taɓe baki Ramlat ta yi sa'ilin da take kurɓar ruwan da aka ajiyemata.
"Ke kika san wannan, ni kam ai na rufe babin aure har abada."
Jiki a sanyaye Muhibbat take dubanta.
"Kar ma ki fara wannan tunanin, shi aure lokaci ne. Idan ya zo ko bakya so sai mun wanke ki mun kaiki. Kuma da yardar Allah ma kina so za'a yi shi. Duka-duka ashirin da nawa kike?"
Murmushi mai ciwo Ramlat ta yi, ta basar da zancen ta hanyar janyo jakarta.
"Kar ki dameni da wannan zancen, ni karɓi wannan."
Ta miƙa mata envelope da ta ciro, ɗaya na kamu da yini ne da za'a yi a Meena Event Centre yayinda ɗaya na dinner party ne da ango ya shirya a Marhaba.
"Allah Sarki mai sunan Mamana za'a fada kwaryar manya, toh Allah Yasa zamu gani. Ya kawo na ƴan baya. Ko Affan?"
Ta ƙarashe gami da rungume Affan wanda tuni ya sake yana dariya. Murmushi Ramla ta yi, zuwa yanzu masu neman ta yi aure dariya ma suke ba ta wasu lokutan.
"Akwai fa taro da za'a yi na family, har jikoki gaba daya. Ba ki da labari?"
Ta girgiza kai.
"Ba wanda ya fadamin, to wa zai fada?"
Harararta Muhibbat ta yi,
"Ai dole a fada ko don yarannan. Ina jin nan da sati biyu zasu gudanar. Zan biyo mu tafi tare da yarana."
"Toh." Shine kawai abinda Ramlat ta ce, ba ta wani jima sosai ba ta mike. Duk yanda Muhibbat ta so ta tsaya ta ci abinci ta nuna akwai wuraren da za ta je kan ta koma gida. Dole Muhibbat ta cika Affan da kayan zaƙi kala-kala ta takomata har farfajiyar gidan suka rabu. A hanya tana tafe tana tunaninta. So da kauna tsantsa idan an ajiye na ƴan uwantaka a gefe, Muhibbat ta nunawa Aliyu. A yanzun sai soyayyar ta koma kan yaransa. Har ta tsayar da adaidaita suka yi cinikin unguwar Gaida ba ta bar tuna tarin laifuffukan da ta aikata ga Muhibbat din ba.
***
*Son Zuciya*
Zaune take ta zuba uban tagumi ta yi shiru, kai ta ɗaga tana kallon ƙaton enlargement na hotonta da Aliyu. A ƙasa an rubuta sunansu. Aliyu Abdussalam Buba da Muhibbat Abdulrazak Buba. Za ta iya cewa ita ke son shi, son da take mishi ya hanata ganin aibunsa.
Tun suna yara suke shakkar haɗa inuwa da shi, don ko kusa ba ya wasa da su. Mutum ne wanda ya fita zakka a zuri'arsu, don kuwa a iya saninsu Aliyu giya ce da kwaya kawai za'a ce yana sha su ƙaryata. Ya soma shaye-shaye a ɓoye ba tare da sanin mutan gida ba. Hakan ya samo asali ne daga manyan ɓatattun yaran masu kuɗi da yake abota da su a sakandire, Innarsa Amina bafulatanar Gombe, mace mai hakuri wacce ba'a taɓa yin kace nace da ita ba duk kuwa da tarin facaloli da kuma kishiyoyinta biyu da take tare da su. Aliyu ɗa na fari a wurinta hakan yasa koda wasa ba ta sakewa da shi. Kusan rayuwarsa ya yi ta ne a hannun kakarsa Abulle matar Marigayi Malam Buba. Da wuya ka ganshi cikin gidan Mahaifinsa Abdussalam sai dai sashin Abulle wacce ta dauki son duniya ta ɗora akan Aliyu. Wannan tasa a duka yaran Malam Abdussalam, Aliyu ne kadai ke makarantar manyan masu kuɗi irin na yaran Justice bisa jajircewarsa akan shi ba zai yi makarantar da za'a rainashi ba. A sannan sai da Mahaifinsa ya ji kamar ya mishi duka don shi mutum ne mai zuciyar nema da kuma son kyautata iyalinsa da daidai karfinsa. Yana aiki a ma'aikatar ilimi ta gwamnati. Mahaifiyar Aliyu ita ce matarsa ta biyu. Yana sonta da kuma tausayamata ganin ita kadai ce ya auro daga nesa.
Abulle ce ta dage Justice ya mayar da Aliyu makarantar yaransa, wannan abu ba ƙaramin bakin jini ya janyo wa Aliyu wurin iyalan Justice ba idan ka cire Muhibbat da ke jin kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha don dadi.
A hankali bayan sun tasa, ta tattara ta koma gidan Abulle da zama itama kawai don ta dinga sanya Aliyu a idanunta. Ranar farko da ta soma ganinsa a makaranta yana shaye shaye da abokansa, ranar ta gigita. Za ta gudu ya kamata ya fallamata mari dama da hagu akan yanda ta gani ta binne a nan kar ta sake ta fadawa wani ko wata a gida. Wannan ta sa ta kama bakin dole. Abin mamaki soyayyar da take mishi bata ragu ba sai ma tausayi da yake ba ta. Kewarta da yayyunta suka yi har ma da iyayenta ta sa Justice da kansa ya zo ya lallaɓa Abulle dakyar ya tafi da ita. Abulle ta rantse kaf a jikokinta Aliyu da Muhibbat ne ƴan gaban goshinta.
Aliyu na aji na biyu a jami'a kowa ya fahimci mummunan ɗabi'ar da ya faɗa na shaye-shaye, karatun ma ba ya bar maida hankali, kullum yana daki yana bacci. Taro kuwa na family an yi akan Aliyu ya fi a kirga, Innarsa kan shiga daki ta yi kuka son ranta. Shi kadai namiji da Allah Ya bata sai kannensa mata uku, sai dai ya zamemata wani tambari wanda ake faƙewa da shi a ci mutuncinta. Mahaifinsa kuwa ya ce sam ba zai yarda ba sai dai yaronsa ya koma gabansa. Wannan ne silar komawarsa gidansu.
Duk wannan bai sa Muhibbat ta fasa so da tausayin Aliyu ba, takan rufe kanta a daki ta ci kuka ta kuma bishi da kyakkyawar addu'a akan Allah Ya shiryeshi.
Rayuwa ta yiwa Aliyu zafi yakan ji kamar ya yi hauka duk ranar da Babansa ya kulleshi a ɗaka ya hanashi fita ko nan da can. Makaranta dama ba labarinta don tun ranar da aka rabashi da gidan Abulle ya zuciya ya ce ya fasa karatun gaba daya. Ranar da ya ɓalle ya fice daga gidan, bai koma ba sai da ya yi mankas. A ranar Innarsa ta yanke jiki ta fadi. Tun daga wannan rana ba ta ƙara lafiya ba. Ciwon Innarsa ya sanyaya jikinsa kadan, duk da a ganinsa matar sam ba ta damu da shi ba hakan bai mantar da shi matsayinta wurinsa ba.
Bayan farfadowarta ya daukar mata alkawarin ya dainawa, ba ta ce mishi uffan ba har ya fice. A hankali kuma ya dinga ɓoye munanan halayyarsa, ya maida turare abin fesawarsa, ba ya taba yarda ya zauna na awanni da yan uwansa gudun kar a ga sauyawar leɓɓansa adalilin shan taba. Sai dai ya zama masifaffen karfi da yaji, ya daina ragawa duk wata mace da za ta gasawa Innarsa magana. Akwai ranar da ya kusan yiwa Amaryar babansa duka duk don ta zagi Inna a fakaice. Wannan ya fusata Baban ya ce ya bar mishi gidansa. Zuciya irin ta Aliyu ya sanyashi haɗa komai nasa ya koma gidan Abulle. Ba abinda ya boyemata har da karin gishiri, nan kuwa ta tara meeting ta gargadi kowa akan takurawa Aliyu da ake.
"Duk wanda ba zai bi shi da Addu'a ba kar ya zageshi ya kara bin duniya. Kai kuma Abdussalamu ba ka isa ka rabashi da gidan ubansa ba. Ko yau yaro ya ga dama zai je. Don kunga an samu ya soma gyaruwa shikenan kuma sai ku kara sanyashi ya bi duniya? Ke kuma Amarya ki ci gaba, idan dai za ki ci gaba da gasawa Amina magana, yaron nan ba zai fasa kirɓarki ba. Shashasha."
Nan yaran suka shiga ba ta hakuri gami da nunamata kuskuren Aliyu cikin sanyi. Aliyu ya ba Amarya hakuri aka ce ya ci gaba da zama anan gidan Abulle. Bayan watsewar surukan da jikoki, Abulle ta nemi shawarar ta yanda za'a inganta rayuwar yaron tunda ya ƙi boko. Nan take Justice ya kawo shawarar a dorashi kan kasuwanci. Ba musu kowa ya yi na'am. Justice da kansa ya dauki nauyin budewa Aliyu shago da komai. Nan kuwa Abulle ta yi ta sanyamasa albarka daga nan aka tattauna batun auren yanmatan da suka isa aure a zuri'ar da zarar sun kammala Sakandire don a sannan suna ajin karshe. Budar bakin Abulle ta ce.
"Banda Muhibbat, na yi mata miji."
Kalamanta sai da yasa kirjin Justice bugawa, tsoransa kar ya zamana abinda yake gudu ne zai afku. Duk yanda suka so jin waye mijin Muhibbat ta ƙi basu fuska. Asalima goronta ta hau tauna ta ce su mike su bata wuri ta sallame su. Jiki ba kwari dai Justice ya tafi.
Ita kuwa Abulle tun wani dare da ta kama Muhibbat na kallon hoton Aliyu tana kuka ta ci alwashin sai ta auramata shi. Ba ta bari ta ganta ba ta juya ta ci gaba da baccinta cike da farin ciki da tausayin yarinyar.
Cikin luɗufin Allah zaman kasuwa ya karɓi Aliyu, dakyar yake ajiye wasu kudaden don shi da za'a bar shi ya yi facaka zai fi son hakan. Bai fasa shaye-shayensa ba sai dai ya fi yi da dare wanda daga ya sha ya ɗan yi tamɓelansa zai ɓige da bacci. Taba kuwa ko a kasuwa zuƙarta yake don zuwa lokacin bai dauketa abar tashin hankali ba. A wannan lokacin ne kuma Inna ta tashi lafiya kalau, daga baccin rana ta gamu da ajalinta, ta rasu. Mutuwarta ta girgiza jama'ar gidan musamman kishiyoyinta wadanda suka cika da dana sanin zaman gaba da hassadar da suka yi da ita. Batun mijinta kuwa ba'a magana, Abdussalam ya shiga tashin hankali marar misaltawa. A gefen Aliyu da yaran Innar mata suma ba'a magana.
"Ka ji tsoron Allah." Shi ne abinda Innar ta fi yawan fadamasa a kalamanta masu tsawo, sai a sannan ya san yana son mahaifiyarsa halinta na banzatar da lamuransa kawai ya tsana. Yan uwanta daga Gombe duk sun zo. Mutuwar Inna ya karawa Abulle da Muhibbat tausayi da son Aliyu.
Suna kammala Sakandire magabata suka yiwa Muhibbat caa akan ta fiddo da miji, ita kuwa ta kasa zaɓen ko ɗaya saboda Aliyu.
Aka yi sa'a koda Abulle ta tari Aliyu da zancen Muhibbat don jin ta bakinsa sai ta ga ya hau murmushi, nan take ya nuna ya amince don dama ya jima da sanin yarinyar na sonsa. A cewarsa ko ba komai zai ƙara martaba a idon duniya kasancewar mahaifinta wani ne kuma ɗan uwan mahaifinsa.
Tashi ɗaya kowa ya ce bai yarda da auren ba, Justice dai ya yi alkunya ya yi shiru, daidai da mahaifin Aliyu bai amince a ba Aliyu auren Muhibbat ba. Ita kuwa Abulle ta rantse ko bayan ranta aka ƙi aurawa Aliyu Muhibbat ba ta yafewa yaranta ba. Kuma bakinta sai ya bi su, wannan ya tashi hankulansu, a dole suka amince.
Justice ya yi mamakin murnar da Muhibbat ta nuna. A gefe guda Mamarta Saudatu na cika da batsewa.
"Dama kina sonsa?" Ta riga Justice jefamata tambaya, ta kara sunkuyar da kai tana murmushi kafin ta mike a guje ta nufi daki. Saudatu ta dubi Justice dake hamdala da alama abin ya mishi dadi.
"Kana nufin ka amince da auren yaron da ya fitini kowa a dangi da ɗiyarka kamila?"
Yayi murmushi.
"Allah Ke shiryawa, kuma Ya shirya Aliyu sai dai a ci gaba da yi mishi addu'a. Farin cikin Muhibbat ya fiyemin komai, fargabana kar ya kasance ba ta sonsa. Tunda har tana sonsa shikenan, Allah Ya tabbatar da alheri. Ba zan ƙi bin umarnin Mahaifiyata ba."
"Tabɗijam!"
Abinda Mama ta furta kenan. Rigima sosai ta tayar akan lallai sai dai a fasa auren, karshe Justice ya zuciya ya fita harkarta, har yaji ta yi da ta gaji ta dawo ɗakinta. Abulle ta rantse ba don darajar ta haifomata sanyin idaniyarta Muhibbat da sauran jikoki ba da sai ta saka an saketa. A dole ta dangana aka yi auren Aliyu da Muhibbat wanda alokacin ya yi nisa da son Ramlat.
Muhibbat ta sauke ajiyar zuciya, ta kara maimaita sunan Ramlat da mijinta yake yawan kiranta da shi a shimfiɗa. Hannu ta sanya ta dauke hawayenta. Kauna da son Aliyu abu ne da ta fara tun ba ta mallaki hankalin kanta ba. Ba kuma ta jin za ta daina. Addu'a za ta dage da yi har Allah Ya fidda Ramlat daga ran mijinta. Ba ta santa ba ko a hoto, ta dai santa a bakin mijinta. Takan yi mamakin yanda Ramla ke aminta su yi waya da mijin aure har cikin dare. Ta rasa gane SON ZUCIYA ne ko kuwa a'a?
Fatanta Allah Ya karkato hankalinsa gareta su ci gaba da rayuwa kamar yanda suka fara a farko.
***
*DAWOWA 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
08)
_*Dawowa Labari*_
A kofar gidan Amrah ɗan sahu ya ajiye Ramlat. Ta biyashi tana mai kama hannun Affan wanda duk ya ɓata kayansa da cakulet suka fara knocking. Aka bude, harararta Amrah ta yi.
"Sai yanzu ko? Yinin kenan?"
Ramlat na dariya ta juya.
"Shikenan, bari mu juya daga nan." Da sauri ta kama hannunta ta maidota baya suna dariya.
"Ni ban ce ba, yi hakuri."
Suka shiga ciki suka zauna, nan take sanarmata sai da ta biya gidan Muhibbat.
"Allah Sarki Muhibbat, matarnan akwai kirki wallahi. Ba ruwanta, kinsan babu ranar da ba za ta turomin gaisuwar juma'a ba."
Murmushi Ramlat ta yi.
"Ai wannan daban take cikin mutane ma. Allah dai Ya bamu ikon yin zumuncin mu ma."
Amrah ta amsa da Amin. Ramlat ta shiga waige-waige.
"Ke ina ƴata wai? Tun da kika ce min kun dawo ita nake son ganin yanda ta girma."
"Tana wurin Mama na kai mata yaye. Abinda ya ban mamaki ko ciwon nono ban yi ba."
Ramlat ta dara.
"Kika sani ko wani cikin ya shiga? Tsarabar Lagos?"
"Allah Yasa. Ai nikam ina so wallahi."
Ba ta yi mamakin kalaman Aminiyarta ba don tun bayan aurenta sai da ta shekara biyar ba ta samu ciki ba sai yanzun. Mijinta Ɗahiru ya ce ba ita babu planning sai ta yi biyu.
"Allah Ya kawo mai albarka toh. Nidai yanzu yunwa nake ji."
Miƙewa suka yi a tare zuwa kicin Amrah na fadin.
"Mutuminki ɗan wake nayi niyyar yi kuwa, na haɗa komai ki dora ruwa idan ya tafasa ki yi sakin bari na yanka mahaɗin."
"To da ban zo ba fa?"
Amrah ta yi dariya.
"Ai kuma tunda kin zo din magana ta kare. Yi hakuri ki taimaka ban jin dadin jikin."
Haka ta soma sakin ɗan waken tana yi suna hira.
"Ni kuwa ina Hilal?"
Tambayar Amrah ta tunasar da ita yanda suka yi a kwanakin baya, text ya yi mata akan ta sanyamishi rana da lokaci ya zo su tattauna abu mai muhimmanci sai dai ba ta yi karambanin ba shi amsa ba, daga ranar kuma bai ƙara nemanta ba.
"Kamar ban kyauta masa ba, amma a wurina hakan ne daidai."
"Me kika yi mishi?" Jin abinda Amrah ta ce yasa ta fahimci zancen zucin ya fito fili, nan ta bata labarin yanda suka yi. Ajiye wuƙar hannunta ta yi ta juyo da mamaki ƙarara saman fuskarta tana dubanta.
"Meyasa kike yiwa kanki irin wannan gangancin?"
Cikin rashin fahimta ta ɗan dubeta.
"Wane gangancin kuma?"
Haushi da takaici ya kusan kashe Amrah anan tsaye.
"Tambaya kike Ramsy? Ko kin manta na tunamaki waye Hilal? For all abinda ya faru bai sa ya juyamaki baya ba, bai kuma sa ya bar sonki ba, don me yanzu kin samu damar gyara laifukanki kike kokarin juyamasa baya? Allah Kike son yiwa butulci?"
Murmushi mai ciwo Ramlat ta yi, ba ta ce komai ba ta juya ta ci gaba da sakin ɗan wake, sanin hali na idan ta ga dama ba za ta ce uffan ba yasa Amrah itama ta ci gaba da aiki sai dai ta kumbura kiris ya rage ta fashe. Dama sun saba irin haka tun yarinta.
Ita kuwa sai da ta kammala ta wanke hannu ta jira ya dahu ta kwashe ba ta ko tsaya tambayar inda filas yake ba ta dauko. Sai da za ta zuba ne Amrah ta dakatar da ita.
"Wannan na Daddy ne." Tana nufin mijinta, murmushi Ramlat ta yi don tasan ƙawarta ta shaƙa, ta fice daga kicin rike da plastic din da Amrah ta yanka kayan cin dan waken. Sai da ta soyamusu manja sannan ta fito itama. A falon suna zaune sannan ne Ramlat ta dubeta a nutse.
"Tsaya don Allah ki saurareni."
Amrah ta dakatar da zuba