Showing 63001 words to 66000 words out of 230725 words

Chapter 22 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1062

dukkan wata gaɓa ta jikinta.

"Zan wuce." Ta fadi ganin duk inda ta bi sai ya bi ya kare. Ba zato ya rungumeta tsam a jikinsa. Ba ta da kuzarin kwace jikinta. Ita kanta hakan ta fi buƙata. Wasu hawayen ta shiga fitarwa, ya dinga shafa gadon bayanta yana bata hakuri.

"Ki yi hakuri, nayi laifi ba zan kara ba,  ke ce kin kasa fahimtar cewa babu ce ta ke cina. Idan ba ki rufamin asiri ba wa zai rufamin? Duk fa kudin da nake samu akanki yake ƙarewa. Bashi na ci wanda ake barazanar kai ni ƙara kotu, Baby idan ba ta hanyar dukiyarki ba, wurin wa zan je? Wa zai rufamin asiri?"

Hakan da ya fadi sai ya kashe jikinta. Ta ɗago kai tana kallonsa.

"Shi ne za ka kwata da ƙarfi, meyasa ba ka yimin bayani yanda zan fahimta ba? Dukana fa ka yi Sweet Aliy, duka fa? Ina soyayyar da..."

Bai ba ta damar ƙarasawa ba  ya haɗe bakunansu wuri guda. Karshe ma suka koma cikin dakin zance ya sauya.

***
  Tun daga wannan ranar sai komai ya wuce, zamansu ya dawo lafiya kalau. Hajiya ta mata aiken jar miya kaya guda. Taimako daya da Allah Ya mata, Aliyu yasa an gyaramusu wutar nepa kuma ko yaya zai wuya rana ta fito ta faɗi ba'a kawo ba, wanna ya bata damar saka miyar a fridge. Idan ta dawo makaranta sai dai ta dumama. Wataran kuwa ba ta amfani da shi, sai dai ta yi tuwo da miya ko kuma jellof.

Rayuwar sai sam barka, samun Aliyu yana ƙara ja baya. Har ta rage damuwar shaye-shayensa. Yanzun ta fi maida hankali ga tilawar Alkur'ani da kuma addu'a kamar yanda Abba ya tunasar da ita, sai take jin ta wata daban.

  Satinta uku bayan sun kammala gwajin aji ta soma amai da ciwon kai. Tashin farko da likita ya aunata ya tabbatar tana dauke da juna biyu. Wannan karon Aliyu bai yi wani ɗoki ba, a hanya ma jimamin yanda rayuwar za ta yi mishi tsada yake.

"Ga kudin makarantarki, ga cefanen gida kuma yanzu ga ciki."

"Allah zai rufa asiri."
Abinda ta iya cewa kenan, tana jin sadda ya ja tsaki, ita kuwa tunani ne ya ɗarsu a ranta. Ko dai sana'a za ta soma gwadawa ne tunda akwai kudin sadakinta yana nan ba ta taɓa ba,ta ba Abba ajiya, dakyar ya karɓa a lokacin don cewa ya yi babu abin hannun Aliyu da zai riƙe.
'To wace ma sana'a tunda ba wuta ake samu ba?' Wani bangare na zuciyarta ya tunasar da ita. Ta kudurta za ta yi shawara da Amrah ta ji.

***
"Kuɗinki suna nan ina juyamaki Ramlatu, fadamin me kike don ki yi da su?"

Kalaman Abban suka yi mata dadi a zuciya, iyaye ta yarda iyayen ne. Ba su da buri sai na ci gaban ƴaƴansu. Cike da murna ta sanarmishi sana'a dama take tunanin yi, don ragewa Aliyu wani nauyin."

Abba daga bangarensa ya yi murmushi, ya ji labarin tana da juna biyu daga bakin Hajiya.

"Hakan nada kyau Ramlatu, kar ki zama mai yawan roƙon miji hakan na zubda girma kuma ya jawo raini. Sai dai a yanzun wace sana'a kike ganin za ki yi?"

Ta kara gyara riƙon wayar, kai tsaye ta yi amfani da shawarar Amrah tace

"So nake koda kayan kamshi na girki da kuma yaji na dinga yi ina sanyawa a robobi."

"Kina ganin makwaftanki zasu siya?"

Ta yi shiru, tun zuwanta unguwar ba ta shiga gida kowa ba adalilin Aliyun da ya hana, kuma bai bada fuskar da wani a makwaftan zai shiga gidansa ba. Sau daya wata Maman Nawal gida mai kallonsu, ta gwada shigowa bayan tafiyarta ya nuna baya son gulma, ba ta kara gigin barin wata ta shigo ba. Suma kuwa suka shareta.

"Kin yi shiru."

Fadin Abba. Ta sauke ajiyar zuciya.

"Abba ban taɓa shiga makwaftana ba, ba ya so."

Abba daga can ya yi shiru, sai kuma ya amsa.

"Kinga Ramlatu, ki maida hankali ga karatunki, In Sha Allah zan daukemishi nauyin biyan kudin makarantarki. Sana'a ba zai yiwu ki yi ba saboda ba kya shiga makwafta kuma ba ki ɗaukesu ƴan uwa ba, don haka ba zasu siya kayanki ba. Sannan hakan ba rayuwa ba ce, ko hakan kika  gani muna yi da makwaftanmu?"

Ta girgiza kai ta ce.

"A'a Abba."

"To ki daina, ki nusar da shi hakkin makwafta da ya rataya a wuyanku. Zan ci gaba da juyamaki kudinki Ramlatu, na budemaki  acc. Allah Ya yi musu albarka."

So da kaunar Abbanta suka ƙara ratsata. Kunya sosai ta ji, ita ta kasa bin abinda yake so, gahinan yana tayata son abinda take so da ganin ta zauna a gidan aurenta. Godiya da addu'a ta shiga jerowa har sai da Abba ya katse kiran. Ta jima tana tunanin rashin kyautatawar da ta yi ga iyayenta, a hankali ta shafi cikinta.

'Shima zai iya zuwa duniya ya bijirewa umarninki, ya za ki ji?'

Ta sunkuyar da kai ta yi shiru, ranta duk babu dadi.

  "Allah Ka yafemin." A furta a fili. Hawaye kam sun zamemata kamar abin ado a fuska.

***
  Ta dauka zai yi faɗa ko kuma ransa ya ɓaci, sai ta ga akasin hakan, murna sosai ya hau yi har da rungumeta.

"Allah Ya karawa Abbanmu arziki. Kai naji dadi."

Murmushi ta yi, Aliyu kenan mai abin mamaki. Wato dai ji ya yi dagaske an taimaka mishi an daukemishi nauyi. Ita da ya bari ma ta yi karatun hakan ma ya yi mata dadi.

"Amin." Ta amsa a fili.

"Af ke Muhibbat da aure zata yi."

Ya fadi cikin nuna halin ko'in kula. Jikinta ya ɗan yi sanyi.

"Dagaske? Yaushe ne bikin?"

Taɓe baki ya yi.

"Gashinan dai ki karanta, ita ta ban ta ce na kawomaki don Allah. Wai ta so zuwa amma ba lokaci, za dai ta zo kawomaki anko."

Ta karba ta bude ta karanta. Engineer Kabir Ishaq Sodangi, sunan mahaifinsa ba ɓoyayye bane don ya rike mukamai da dama a gwamnati.
"Allah Ya nunamana. Na tayata murna."

Cike da zolaya ya kashemata ido daya.

"Ko? Kina murna ta rabu da Aliyunki. Ya zama naki ke kaɗai."

Hararar zolaya ga watsamishi, ya yi dariya.

"Yauwa ta karbi lambarki ma, za ta kira. Ai kuma kinsan me? Wallahi har gobe yarinyarnan tana mutuwar sona. Da na bata fuska sai ta ce na maidota ɗakinta."

Maimakon maganar da ba ta haushi sai ta hau dariya, idan mace irin Muhibbat ta rabu da Aliyu, me za ta dawo ta yi mishi?

Ya ɗan hade gira.

"Ke wallahi Baby ban da aika-aikar da kika yi, zan fa iya rantsemaki Muhibbat ta fi ki sona. Kawai dai ita din ba ƴar daba ba ce. Ba ta iya barazana da kisa ba."

Dariyarta ta dauke dif, sai lokacin ya shiga yin tasa yana kara jan ta.

"Kai Baby kema fa shu'umar kanki ce. Na dai fada ne kawai, amma ban taɓa zaton za ki iya aikatawa ba. Taɓ! Har na hango idon wannan Hilal din a lokacin? Ni da mujiya."

Ya kara bushewa da dariya. Ita kuwa sai sannan ma ta tuna da wani Hilal a duniya, ko wane hali yake ciki a yanzu? Oho.

Ta daure fuska.

"Please bana son irin haka. Bana so."

Ya taɓe baki.

"Nayi shiru toh kada ina bacci ki hau ruwan cikina da wuƙa."

Haushi da bakin ciki ya sa ta miƙewa za ta bar mishi falon, ya kuwa fisgota ta dawo jikinsa. Nan da nan kuma ya san yanda ya yi aka bar zancen gaba daya.

***
"Haba Hajiya! Meyasa za ku dinga kula lamuran yarinyarnan yanzu?! Har yaushe? Har yaushe ne? Kuna tsammanin hakan da ku ke yi shi zai ankarar da ita ta ce kuskurenta? Don Allah Hajiya ku cire hannunku a kanta. A gabana fa kika bada miya aka kai mata, yanzu kuma tunanin yi mata snacks kike? Ina mijinnata? Har soyayyar ta gushe? Har soyayyar ta tafi?!"

Munir ke wannan faɗan kamar zai ari baki, wancan karon ma dannewa kawai ya yi. Hajiya a sanyaye take dubansa.

"Muniru?" Jin maganar Abba duk suka juya, sam basu ankara da shigowarsa falon ba. Ya ƙaraso ya zauna.
 
 
 


I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/ptlD4eEPhab




🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

20)

"Idan ba mu ja ta a jiki ba wa zai ja ta? So kake mu bar yarinya ciwon zuciya ko hawan jini ya kama ta? Ai hannunka bai taɓa ruɓewa ka yanke ka yarr ba, duk lalacewar Ramlatu, dole mu amsa sunan mahaifanta. Hakazalika duk yanda ka kai da tureta daga dukkan abinda ya shafi rayuwarka, ƴar uwarka ce. Yau ko babu ranmu kai ne uba kuma uwa garesu. A sanadin sharewar da kake cewa mu yi mata, kasan illar da hakan kan iya jawowa? Kasan illar kaɗaici da zama da damuwa a ƙwaƙwalwa kuwa? A'a Muniru, kar ka soma. Fushi da riƙo ba zai kaimu ko'ina ba, ba ka kaini fushi ba, amman gashinan a inda nake ganin zan iya na kasa. Ramlatu tamu ce, kamar yanda muka haifeku, haka muka haifeta. Ban maka lallai ka yi zumunci da ita ba kai da iyalinka, sai dai ka sani, ba ka isa ka cire jininta daga naka ba. Allah Ya riga ya haɗaku matsayin ƴan uwa."

Abba ya ci gaba da kora bayanai da nasiha har sai da Munir ya ji dama bai shigo gidan ba, da ba zai ji batun kai ma Ramlat snacks ba har ya yi magana. Hakanan ya ba Abban hakuri aka bar zancen ba don kuma ya ji a ransa zai iya yafewa Ramlatun ba.

***
  Kanta ya dauki chaji sakamakon jarrabawar da zasu fara na zangon farko a aji daya na jami'a. Tattara litattafan ta yi ta watsar gefe gami da kwanciya saman three-sitter har da lumshe ido. Garin an tashi da hazo da sanyi hakan yasa ta rufe ko'ina ta kuma sanya jibgegiyar rigar sanyi da safa. Lokacin karfe uku da mintuna na rana sai ka rantse biyar din yamma ne. Aliyu bai dawo ba hakan ya bata damar ƙin yin abinci, indomie kawai ta dafa ta ci abinta da zummar sai yamma ta girkamusu tuwo.

Wayarta ce ta dauki ƙara, ta ja guntun tsaki don ba kaɗan baccin ya soma yi mata dadi ba. Ganin baƙuwar lamba kamar ba za ta ɗaga ba, sai kuma ta ɗaga.

"Assalamu alaikum."

Muryar ba za ta taɓa gushemata ba, ta santa tun mamallakiyarta na matsayin da take a yanzun, wato matar Aliyu. (Muhibbat ce)

"Waalaikumussalam."

"Amarya gani a ƙofar gidanki."

Haka kawai Ramlat ta ji gabanta ya faɗi. Tunawar da ta yi da batun kawomata iv da Aliyu yace za ta yi sai ta ɗan sami nutsuwa.

"Toh ganinan zuwa."

Daga haka ta ɗauki ɗankwalinta da ya ɗan zame ta ɗaura ta fita.

Tsaye ta ganta, suka yiwa juna murmushi. Hanya ta bata ta shigo.
 
  A falo suka yada zango. Bayan an gaisa ne ta mike ta kawomata ruwa da lemu mai sanyi.

Muhibbat kam gidan take bi da kallo tana jin zuciyarta na son karyewa. Idan ta ce babu burbushin son Aliyu a ranta, ta yaudari kanta. Soyayya ta mishi da zuciya daya tun yarintarta har girma, sai dai kuma ta samu wanda ya fiyemata shi alheri.

"Ga ruwa."

Maganar Ramlat ya katse tunaninta, ta basar da murmushi ta dauka, pure water ne marar sanyi sai dai sanyin gari da ya shafeshi.

Ga Ramlat, duk ta kasa sakewa, laifukan da ta yi mata kawai ke yawo a kwakwalwarta.

Muhibbat din ce ma ta daure ta shiga jan ta da hirar karatu, a hankali kuma suka soma sakin jiki da juna. Abin mamaki hira sosai har da tuntsira dariya. Kiran sallar La'asar ce ta katse hirar. Suka mike gaba daya suka yi alwala. Bayan sun idar ne Muhibbat ta soma haramar tafiya don bata kaunar haɗuwa da Maigidan. Ba yanda Ramlat ba ta yi ba akan ta jira ta yi girki amma ina!

Har bakin gate ta rakota, tana son ta ce mata ta yi hakuri ta yafemata dukkan laifukan da ta yi mata a baya, sai dai kunya da jin nauyi yasa ba ta san ta inda za ta fara ba. Zaman yini kawai da suka yi ta fahimci kyawawan halayen Muhibbat din. Tun ma ran gini dai tun ran zane, da wata ce ko kofar gidanta ba za ta tsaya ba balle har ta shigo. Gaisuwar mutunci ba zai haɗa su ba har abada.

"Nagode sosai, In sha Allah zan zo. A gaidamin su Mama don Allah."

Haka ta iya furtawa, murmushi Muhibbat ta yi.

"Zasu ji sosai. Nima a gaidamin Yayannawa."

Daga haka ta fice, ita kuma ta rufe ƙofar ta koma ciki. Katin auren ta dauko ta ƙara karantawa, duka-duka ma sati uku kaɗai ya yi saura bikin.

"Allah Yasa zamu gani."

Ta furta a fili.

***
  Ƙarfe tara ta wuce, goma ta buga ta tsere ta bar sha daya, babu alamun shigowar Aliyu. Tsoro ya soma kamata, wayarta ta duba akwai ƴan chanji. A gaggauce ta danna mishi kira. Maimakon muryarsa, sai ta ji muryar mace a gefe guda kuwa ƙarar ƙiɗa ne da hargowar matasa. Kasa gasƙata abinda kunnuwanta suka jiyemata ta yi, ta fi kyautata zaton hayaniyar mata da mazan wurin ne ke shiga kunnuwanta. Don haka a gaggauce ta kara fadin.

"Aliyu? Kana ina ne?" Shiru ya ɗan biyo baya sai ta ji hayaniyar ta ɗan ragu. Muryar dai ta ɗazun ce ta ƙara amsa kuwwa cikin kunnuwa da kwakwalwarta.

"Baby ko? Babynki na nan karkashin kulawata, kar ki damu yau girkina ne. Zuwa gobe i promise you zan maidomaki abinki. Goodnight."

Ta bude baki da zummar surfawa matar bala'i ta ji an katse. Hannunta har rawa yake wurin ƙara dialing. Wannan karon gaba ɗaya ma kashe wayar aka yi. Rasa meke mata daɗi ta yi, ta kasa tantance a duniya take, duniya irin na mutanen da ta saba rayuwa da su, ko kuwa dai wata duniyar ce daban.

"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Aliyu? Kuma da mace?"

Ta furta gami da dafe cikinta wanda ya ɗan murɗa, ta tabbatar banda Allah ne kaɗai Mai iko akan uwa da abinda ke cikinta, babu abinda zai hana cikinta zubewa a lokacin jin irin yanda yake murɗi.

"Aliyu?" Dagaske ta kasa gaskatawa, zumbur kuma sai ta mike ta zura hijabi saman rigar da wandon baccinta, har ta murɗa ƙofar ta fito zuwa barandar gidan, ta tsaya cak. Iska da sanyin da ke busowa ya ci ace ɗan Adam ya nemi mafaka cikin bargo, banda Ramlat wacce bai sa ta daina zufa ba.

Hawaye take fitarwa mai zafi, a hankali kuma ta juya ta rufe ƙofar falon. Nan bakin ƙofar ta zauna ta dunƙule wuri ɗaya ba ta ko damu da sanyin tiles ba dake ratsa dukkan wata gaɓa ta jikinta. Kuka sosai take yi. Duk a zatonta iyakarsa shaye-shayen, ashe a munanan aikin da yake yi har da neman mata?

  *"Ramlatu addu'a, karatun Alkur'ani, su ne babban makaman kowane bawa da kike gani. Ki rike su ba da wasa ba."*

Ta tuna kalaman Abbanta. Zumbur ta mike ta shiga ɗakinta, alwala ta ɗora ta fito ta yi nafila. Ta jima cikin Sujjuda tana kaiwa Allah kukanta kafin ta yi sallama ta shiga karatun Alkur'ani.  Tana yi tana hawaye. Komai na dawomata daki-daki, tun daga batun aurenta da Hilal har yanda ta bijirewa iyayenta akan zaɓinta.

*"Ke yarinya ce Ramla, ba ki san abinda ubanki ya hangomaki ba. Na taɓa ganin shaiɗaniyar zuciya irin taki da ba ta san Annabi ya faku ba? Wannan taurin kai irin naki Allah Ya miki magani."*

Kalaman Tsohuwa Hajja ya dawomata tiryan-tiryan. Wani sabon kukan ta kece da shi, shakka babu gaskiya Hajja ta faɗa. Yanzu tun ba a je ko'ina ba ta na ta fuskantar matsaloli da dama.

*"Kina shiga haƙƙin aurena, kar ki manta kema mace ce."*

Ta runtse idanu tana jin kamar a sannan take karanta saƙon da Muhibbat ta taɓa rubutomata a baya. Wanda ba ta mancewa har ƙararta ta kai ga Aliyu, ranar ta tabbatar sai da ya ci mutuncinta duk a dalilinta.

"Zunubaina masu yawa ne, Allah ina neman gafararKa."

Ta furta a hankali, a daddafe ta ci gaba da karatun sannan ta sallame ta yi addu'a mai yawa. Neman gafara ne da kuma roƙawa mijinta shiriya da kuma tsari daga dukkan munanan ayyuka.

Ranar yanda ta ga dare haka ta ga rana, waya ta dauka ta dannawa Amrah kira sai kuma ta katse kiran. Me za ta ce? Bayan koma mene ita ce sila.

A hankali ta shiga tuna dukkan rikicin da aka yi akan aurenta, wani rashin kunya, taurin kai, kafiya, babu irin wanda ba ta tuna ba.

'Ba zan taɓa ganin laifinku ba.'

Ta fadi a ƙasan ranta.

*"Ba ina alfahari ba My Future, sai dai wallahi wallahi, na fi dukkan wani namiji da ba muharraminki ba sonki. Ki dawo Ramlatun da na sani a baya, please and please ki maido Hilal cikin zuciyarki."*

Ta runtse ido gami da yin istigfari, wannan tunanin ba amfanin da zai mata, dukkan inda dai Hilal yake tana mishi fatan alheri a rayuwa.  Aliyu wani bangare ne na jiki da zuciyarta, sonsa halitta ne da ba ta isa ta yayewa kanta ba.

***
  WASHEGARI

Kishi mai tsanani cike taf zuciyarta sa'ilin da ta yi ido hudu da shi a falon, har lokacin shaiɗaniyar muryar matar bai bar amsa kuwwa a kanta ba. Ta kauda kai kamar ba ta ganshi ba ta nufi hanyar fita zuwa makaranta ba tare da tunanin cin wani abu ba matsayinta na mai juna biyu.

Hannu ya sanya ya tare ƙofar. Ta ɗago idanunta da suka rine tsabar ɓacin rai. Ba kuma za ta ce tsana ba, don ba ta tunanin akwai ɓurɓushinsa. Kokari take ma ta ɗorawa zuciyar amma abin ya ci tura. Bata da ikon hakan.

"Malam matsa na wuce."

Ya ƙi motsi illa dai ya ƙafeta da mayatattun idanunsa dake kashemata dukkan wata gaɓa a jikinta.

"Ki yi hakuri, ina mai haɗaki da Allah. Wallahi ba'a hayyacina nake ba. Kafin na taho sai da na yiwa Zee dukan da ba za ta kara marmarin kallona ba balle .."

"Ban tambayeka komai ba, nidai kawai ka matsamin na wuce ina da jarrabawa. Don Allah ka matsa."

Ta ƙarashe wani takaici na tahomata, kuka take son yi dakyar ta iya danneshi.

Ganin dagaske ba za ta saurareshi ba sai kawai ya matsa a sanyaye,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login