Showing 96001 words to 99000 words out of 230725 words

Chapter 33 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1073

hadadden gayen da ta gani tare da Ramlat ke tafarfasa zuciyarta, ta ji wani sanyi jin da ta yi  Salma ta ambaceshi da Hilal, wato shi ne dai wanda Ramlat ta gujewa aurensa.

'Marar rabo.' Ta fadi a ƙasan ranta, a fili kuwa murmushi ta yi tana wani ƙwarkwasa a sonta ta burge Hilal.

"Bamu jima da zuwa ba, ashe kina nan kina tsinkar fure.  Ki ce shiyasa ki ka ƙi sauraron Oga. Kina da zazzafa a hannu."

Kalaman Halima wanda da biyu ta yi, ya kara baƙantawa Salma rai, ta karasa ga Hilal a zafafe. Ita kuwa Ramlat kallon ba ki kyautamin ba ta watsawa Halima ta yi gaba, Ummi ta rarumi dankwalin ta bi uwarta a guje tana kiran ta ɗauramata.

  Salma kuwa ta dubi Hilal cike da bakin ciki.

"Yaya kar dai ka cemin ka dawo a karo na biyu zawarcin Ramlat? Duk abinda ta aikata gareka ka mance?"

Daure fuska ya yi yana kallon yarinyar da duka-duka ba ta dade da daina yoyon majina ba, a cewarsa.

"Ke, yaushe muka soma ƴar haka da ke? Sa'anki ne ni?"

Ta ƙara turɓune fuska, zarginta dai ya tabbata. Tasan idan ta kara magana to zai iya yi mata duk abinda ya so, wannan ne dalilinta na juyawa fuu ta ja hannun Halima su bar wurin a fusace. Ta kuma rantse babu mai dakatar da ita daga faɗawa su Anti Fa'iza da Murja, ko ba komai ta hanyarsu saƙon zai fi saurin isa kunnen iyayen Hilal waɗanda suka rantse ko bayan ransu basu yarda da aurensa da Ramlat ba koda hakan akwai yiwuwarsa. Wannan rantsuwa ce da umarni da suka faru tun Ramlat na gidan Aliyu, tun sadda ta fusata zuƙatan iyayensa.

  A ɓangaren Ramlat dakyar ta samu ta maido walwalarta sai dai ko yaya ta waiga ta hangi Halima manne da Salma sai ta ji wata irin faɗuwar gaba, a bakin Naja'atu Azare take jin ashe sun san juna tun suna B.U.K.  Jin hakan bai ƙare ta da komai ba sai ƙarin fargaba.

Ana kammala dinner, Ango Hisham ya wuce da Amaryarsa gida don dama sai da aka kai ta sannan aka taho Dinner. Daren ranar baccin Ramlat rabi da rabi ne, tunaninta me zai biyo baya don ta tabbatar dole Salma ta sanarwa Halima wani abin da ya danganci rayuwarta ta baya, tana ganin kiran Hilal da text dinsa akan yana so su yi magana koda ta mintuna ne amman ta ƙi ɗagawa, a ƙarshe ma ta kashe wayar gaba daya.

  "I am sorry Hilal." Ta furta a fili yayinda wasu zafafan hawaye suka zubomata ta ɗaukesu da tafin hannu.

***
Ta shiga ofis dinsu da sallama tana mai duban abokan aikinta.

"Yau dai Hajiya Ramlat kin so makara."

Ta yi murmushi tana duban Salihu mai wannan furucin, ko kusa ba ta son jaye-jayen wasa hakan yasa ta wucewa bayan ta gaida kowa ta zauna a mazauninta. Matan ta duba da mazan da suka halarci daurin aure ta yi musu godiya da fatan Allah Ya kara dankon zumunci daga nan ta maida hankali ga wani aiki da Oga Ɗalhatu ya ba ta tun wancan satin.

Ta dukufa wurin aiki, Ofis ya cika irin cikar da ta tsana, wato ƴan wasu ofishin su shigo nasu domin hira, wannan yasa tunda ta sunkuyar da kanta ta wasu rubuce-rubucenta a computer ba ta ɗago ba, kamar yanda ta daure fuska kamar ba ta taɓa dariya ba musamman ganin har da Oga Ahmad wanda ke kokarin sanyata a hirar tana ƙi. Babban abinda ke ba ta mamaki wasu cikin matan ma da aurensu amma yanda suka zage kamar ba auren a kansu. Kamar da wasa ta ji Halima ta zage tana bada labarin da nan take ya sanyata gumi duk kuwa da irin sanyin Ac da ke kaɗawa a ɗakin.

"Toh ai yanzu zamanin ne ya sauya. Soyayyar da ƙarfi da yaji ma kwatarta ake yi Oga. Sai na tuno da labarin wata da aka bani, ranar da aka kai ta ta nemi kashe Angon saboda ba ta sonsa, aikuwa ya saketa ta auri zaɓinta amma fa ta ci gidansu. Duka, zagi ba wanda ba ta sha ba. A karshe dai yanzu sun rabu, ta na nan kuma ta dawo tana bin shi saurayinnata na farko kamar jela, kai ka ce karyar da ta hango ƙashi, nema take ƙarfi da yaji sai ya aureta."

Buɗar bakin Oga Ahmad ya ce.

"Ai wallahi ta yi kaɗan don ubanta! Wannan ma an yi ƴar iskar gaske. Au sai da ta ga rayuwa za ta dawomin?"

"Ni kuma da ni ne, zan aureta ko don na koyamata hankali. Sai na sa ta raina kanta fiye da yanda wancan na farkon ya rainata."

Fadin Salihu kenan har da cire hula hira ta yi dadi.

Abin sai ya koma kamar muhawara, wannan ya kawo nashi, waccan ta kawo. Halima ta saci kallon Ramlat yanda nan take ta fice hayyacinta, ta kauda kai tana wani irin murmushi, ji take kamar nan duniya ba ta taɓa samun farin ciki da walwala kamar ta ranar ba.

Zaman ofis din ya gagareta, ta tabbatar idan ta ci gaba da zaman to fa ruɗun da ta shiga zai bayyana kowa ya gane. Tsalam ta mike gami da daukar jakarta, hannunta har rawa yake ta zura takalminta da ta cire don kafafun su huta kai tsaye ta nufi hanyar fita.

"Ah, Ramlat ina za ki je kuma? Da sauran lokaci fa a tashi."

Fadin Halima kamar ta daka tsallen murna, Ramlat ta juya ta watsamata wani banzan kallo ita kuwa ta murmusa gami da kashemata ido ɗaya. Wannan ya kara ba Ramlat tabbacin da gayya ta yi. Tana sane ta yi mata abinda ta yi din.

  "Ba ta ko saurari kiran da wasu cikin ofishin ke mata ba, ta bude kofa ta fice. A hanyar baranda suka ci karo da Ogansu Ɗalhatu. Ya dubi agogo, sauran bai fi mintuna talatin ba a tashi.

"Ramlat, tafiya? Lafiya kuwa?"

Ta dubeshi dakyar, ba don ya zamto shugaba ba a gareta, za ta iya giftashi kawai ta wuce don yanda ta ke jin kanta. Yaƙe ta yi.

"A yimin afuwa Oga don Allah, ban jin dadi dauriya nake."

Cike da tausayawa ya ce.

"Assha, sannu. Allah Ya ba ki lafiya. Ko dai na sanya a kaiki?"

Ta girgiza kai.

"A'a zan iya tafiya ba komai. Nagode."

Zai kara magana tuni ta giftashi ta wuce da sassarfa. Sai dai tun kafin ta karasa ga motarta, hawaye sun wankemata fuska, hannu na rawa dakyar ta iya bude ƙofar motar ta shiga. Kuka sosai ta ci fuskarta cikin mayafi, dakyar ta iya dauriyar share fuska ta yi ribas ta fita.

  Rabin tuƙin yinsa take yi ba'a nutse ba. Abinda ta ke gudu ya faru, a hankali abinda ta shuka ya soma fitar da tsirrai, tana tsoron ya fidda ƴaƴan da zasu nuuna har nata ƴaƴan su samu rabonsu. Tun ba'a je ko'ina ba, komai ya soma bayyana. A yanzun da tsoro ya shigeta, tana ji a ranta za ta iya barin aikinta idan har hakan zai tseratar da mutuncinta da na yaranta a idon duniya. Za ta killace kanta a gida.

'Kin manta cewa watan watarana dama sai rana makamancin wannan ya zo? A gidan a tunaninki kin tsira?'

Ta hau gyada kai kamar ƙadangaruwa  kamar mai ganin zuciyarta a fili.

"Zan tsira, yarana ba zai shafesu ba tunda ba su da laifi! Ni mai laifin a yimin kowane irin zagi zan jure!"

Tana maganar a fusace ita daya a mota, ba ta yi aune ba ta kai dab da dab da wata mota, duk kokarin ganin ta ci burki hakan ya faskara har sai da ta daki bayan motarsa. Masu salati na yi hakanan masu fadin kai! Kai! Suma suna nasu.

Luguden da zuciyarta ke yi ya ƙaru, ɓacin ranta ya ninka na farko. Ta kasa koda motsi, ta kasa fitowa balle ta je ta ba mai shi hakuri ta nemi gafararsa.

'Da ka san damuwar da ke cikin zuciyata, da ka yimin uzuri kamar irin wanda na taɓa samu a wajen wani...'

Ta kasa ƙarasa zancen zucinta ganin wacce ta fito daga mazaunin kusa da direba. Shakka babu fuskar ba ranar ne farkon ganinta da ita ba. Fuskar da ta zo har ofishinsu.

  "Isa da taƙama za ki nunamana?! Kin yiwa motata illa kin zauna kin hakimce ko gezau? Ke ƴar gidan uba wace ce?!"

Sanin da ta yi ita din mai laifi ce yasa ta fitowa daga nata motar, har lokacin akwai hawaye a fuskarta. Wannan hargagin na Hajiya Zeenatu bai dameta ba kamar yanda sanyo ubanta ciki ya yi mata zafi, ko ba komai shirunta ya jazamata.

  "Kiyi hakuri don Allah." Ta fadi tana haɗiyar yawu, damuwar da ke ranta ma ya isheta. Kowa ya yi mata caa akan ba ta kyauta ba yayinda Hajiya Zeenatu ta dage akan lallai sai ta raina kanta, sai ta biya ɓarnar da ta yi mata.  

Ramlat kallonta kawai ta ke sakaka, ita ta ma rasa me za ta ce da ita. Hakuri kawai ta ke bata don ba ta jin yin faɗan musamman a yanzun da ta ke jin tsanar kanta har cikin ranta.

Basu yi aune ba sai jin ƙarar murfin mota suka yi, hankalinsu ya kai gun. Kowa kallonsa yake har ya ƙaraso yayinda Ramlat ta ji bugun zuciyarta ya ƙaru, ba ta taɓa zaton wani abu zai ƙara sa ta ganshi ba. Yanzun kan ta yi amannar ba zai kyaleta ba sai ta biya ɓarnar da ta yi musu, ko ba komai yanzun zai ce da gayya take mishi ta'adi.

Shi kuwa koda ya ƙaraso kallonta ya yi na ƴan sakanni, kallon sani ya yi mata, kallon na ganeki. Ta kauda kai shima ya kawar, kallon da ya kai Hajiya wuya, ta daga hannu da nufin marin Ramlat, caraf ya riƙe hannun. Jama'a aka saki baki don diramar ma tafiya yanda ya kamata, an baza baki da hanci, go slow kam sun haɗa, masu zagi na yi, masu tsayuwa kallo suna nasu aikin.

Hajiya ta dubeshi a fusace.

"Ita yar iskar ina ce za ta tsaya tana ƙaremaka kallo?! Dama nasan ai da biyu ta bugi motar! Na ganeta! Ba ita ce wannan marar kunyar ba ta Revenue? Za ki san ki taɓoni!"

Daga haka ta fisge hannunta ta yi gaba, Ramlat na hawaye ta ke kallonsa. Bakinta ya yi nauyi, dakyar ta motsa.

"Ka yi hakuri. Wallahi ba da gangan na aikata ba."

"Ba komai." Ya fadi ƙasa-ƙasa, daga nan bai ce uffan ba ya wuce ya shiga mota ya ja suka bar wurin. Itama motarta ta shiga tana ji wasu na fadin.

"Ke kam Allah Ya so ki da rahmarSa. Tab!"

Wasu kuwa cewa suke.

"Ina rahmar? Ba ku ji me Hajiyar ke fadi ba? Da alama ta san ma'aikatar yarinyar, za kuwa ta yi mata sanadin barin aiki."

Ita dai Ramlat wacce kanta ke bala'in sarawa, ta ja motarta dakyar ta bar wurin.

Koda ta isa gida, Hajiya ta tambayeta abinda ya faru ganin yanda ta yi kaca-kaca, idanunta jage-jage da hawaye. Ba ta ɓoyewa Hajiyar komai ba. Ranta ya ɓaci.

"Ai ga irinta nan! Ga irin ABINDA AKE GUDU nan Ramlat! Shekara nawa da wucewar abu, yanzu gashinan yana bibiyarki. Ita kuwa wannan Hajiyar a zatonki za ta kyaleki ki ƙara taka ma'aikatarku? Uhm, Allah Ya kyauta."

Daga nan Hajiya ta yi shiru tana huci, ta tausayawa Ramlat amma fa haushinta ba ta da matakin dauka, ba ta da abin yi don kuwa Ramlatun ce ta fara ɓatawa kanta suna. Har Ramlat ta yi ɗaki ba ta ce mata uffan ba.

Ta kudurce a ranta za ta bar aiki, sai dai kuma ta ya za ta dinga wasu cikin hidindimunta har ta taimakawa gida da yaranta?

Ta mirgina saman gadon gami da lumshe ido. Can kuma ta buɗe su cikin zurfin tunani. Ya yi daidai da dawowar yara daga islamiyya, gaba daya suka shigo ɗakinta suna mata sannu da zuwa. Tana murmushi ta mike zaune.

"Kun dawo?"

"Eh, yau Affan bacci ya yi ta yi a aji." Cewar Ansar, Affan kuwa ya yi lamo jikinta, ta shafi kan yaron tana murmushi.

"Wai haka?"

Ya gyada kai, bai iya ƙarya ba ko don tsoro. Suka cikata da surutu, dakyar ta korasu su wuce chanja kaya.

Aliyu ya faɗomata a rai, mutumin da ya bar duniya bayan ya yi kyakkyawar shahada, shi ne ake jefamata bakar magana ake yayata abinda ta aikata dominsa?

'Ko me ya faru, laifinki ne.' Ta shiga gyada kai tana gaskata sashi na zuciyarta dake tunasar da ita hakan. Shakka babu laifinta ne. Dakyar ta samu ta shafe babin a kwakwalwarta ta mike ta shiga wanka. Ta san ƙaryarta ta iya barin aiki saboda Hajiya Zeenatu. Addu'a ya fiyemata komai. Shi ne makamin kowane mumini.

***
"Aikin banza! Kaima ai kallonta ka tsaya yi! Akan wane dalili?"

Hajiya Zeenatu ke wannan kalamin, tun dawowarsu gida duk inda ya saka ƙafa sai ta bishi da zafafan kalamanta na zargi. Idanunsa suka kaɗa, zai shiga wanka ta nufi kofar banɗakin.

"Wankan me za ka yi? Wato ba ka ga girman laifin da ka aikata ba ko? Shi ne har za ka shiga wanka?! Wallahi ka jawowa yarinyarnan! Sai nayi mata sanadin aiki! Sai na wulakanta ta!"

"Daga ranar da kika sanya aka koreta aiki, ki kwana da sanin da kaina zan dauketa aiki a Office dina!"

Cak! Ta tsaya,ta kasa kwakkwaran motsi, dakyar ta iya haɗiye yawun da ya tararmata a baki. Cikin tsananin mamakin kalamansa ta ke dubansa. Wannan ba Hussein din da ta saba juyawa ba ne, bai yi mata kama da wanda zai ɗauki wargi ba. Kalamanta ba su ƙara kashemata jiki sun jefata ruɗu ba sai da ta ƙara tsintar muryarsa.

"Yes Zeenat! Ina miki rantsuwa da Allah daga ranar da kika yi kuskuren raba yarinyarnan da aikinta sai ta dawo aiki a ƙarƙashina! Idan kishi na kisa, ya kashe ki! Haba! Wannan wane irin masifa ne! Wane irin takunkumi ne? Kin hana mace ko ɗaya aiki a gidanki, kin hana na yi aiki da mace a ofis! Babu dama ki ga mace ta kirani ko ta yimin magana ta media sai ki ɗau zargin duniya ki aza a kaina! I'm fed up! Nifa ba yaro bane!"

Daga nan ya gifta ya shige banɗaki gami da banko ƙofar har sai da ta tsorata. Gumi ke tsiyaya daga saman fuskarta duk da Ac dake gudu a dakin. Safa da marwa ta shiga yi gami da kwance ɗankwalinta, akwai babbar matsala! Akwai abinda ke shirin faruwa.

'Ko ita ce yarinyar da Gora ya gargadeni a kai?'

Ta fadi a kasan ranta, shekarun baya da suka gabata, Gora ya gargaɗeta akan abinda zai iya afkuwa muddin ba ta kula da lamarinta da Hussein ba. Ya tabbatarmata ita ce za ta zamo silar rushewar kowane aiki. Wannan ne dalilin da har gobe ta ƙi jinin kowa ya raɓarmata Hussein. Namiji daya tamkar da dubu a rayuwarta. A kansa ta aikata abinda acewarta shaiɗan ba zai iya ba.

"Dole na dauki mataki!" Ta furta a fili kafin ta fice daga dakinsa zuwa nata a gigice.I just published "BABI NA TALATIN" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/5Py5Xl04Mab


🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

*_Rufaida Umar_*

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

30)

Wannan abu da ya faru, sai ya ƙara ragewa Ramlat walwalarta a Ofis. Tambayar duniya ƴan ofis din sun yi amma ta nunamusu ba komai. Tsakaninta da Halima gaisuwa kawai, daga nan ba ta kara bari wani abin ya shiga tsakaninsu. Ga Halimar hakan ba karamin dadi ya yi mata ba, ko ba komai ta samu wani makami wanda yake ganin a koyaushe za ta iya rushe Ramlat din da shi. Wannan girma da ƙimarta da ake gani a daina.

***
  Bayan sati daya da auren A'isha, ranar Lahadi misalin karfe uku na rana, Ramlat ta shirya cikin riga da skirt na leshinta ja, ya yi mata kyau sosai, fuskarnan banda hoda ba abinda ta shafamata, sai gidan A'isha. Nan ma sai da A'ishar ta yi ta roƙonta akan ta zo. Abin ita har mamaki ya ba ta, yarinyar da basu fiye ɗasawa ba, raini ya shiga tsakaninsu, yau ita ke nemanta? Murmushi ta yi, aure ba karamin gyarawa mutum zama yake ba. Kodayake me akai da maza ma?

Ɗan sahu ta hau zuwa gidan A'isha,   su Ummi tun safe Muhibbat ta zo ta ɗaukesu don halartar taronsu na Zuri'a.

***

   Kai tsaye ta shiga cikin falon da sallamarta, A'isha ta amsa tana mai fitowa daga kicin cike da zumuɗi da jin dadi.

"Kai Maman Affan, wai sai yanzu? Wallahi kamata ya yi ki zo tun safe ki wuni."

Harara ta ɗan watsamata tana murmushi.

"Ko? Ga babbar kobo, to ban iya wannan katoɓarar ba."

Dariya A'isha ta yi, ita kuwa Ramlat sai bibiyarta take da kallo yanda ta yi fresh ta yi ɓulɓul abinta tsaf.

"Toh don Allah ku din ne ba wanda na ƙara gani a gidannan, nasan shirye-shiryen auren Yaya ma zai iya ɓoyeku amma ai ba hujja ba ce."

Taɓe baki Ramlat ta yi tana mai ajiye jakarta.

"Ke ni rabani, ba wani shiri da nake yiwa bikinnan. Inace dai mijinki ba ya nan?"

Ta tambaya sadda ta dakata da yaye mayafinta da take shirin yi. Girgiza kai A'isha ta yi.

"Ya fita amma ba jimawa zai dawo, abokinsa ne zai zo  shi ne ya fita yin cefane. Ni wallahi naji dadin zuwanki, ko ba komai za ki taimaka mu shirya daddaɗan abinci."

Ramlat ta ji inama ba ta zo ba. Ba taya girkin ne matsalarta ba, ba ta so Hisham din yana gida ba ne. Dakyar A'isha ta samu ta lallaɓata ta zauna. Ba jimawa kuwa sai ga Hisham. Shi kansa ya ji dadin ganin Ramlat, mutum ne mai barkwanci don ko kadan bai tsaya wani kunya ko ƙumbiya-ƙumbiya ba. Itama ganin haka ta ɗan saki jikinta, daki ya shige su kuwa suka nufi kicin suka shiga aiki, Ramlat na mitar inama ba ta zo ba. Ita dai A'isha ba ta iya magana ba don tasan yanzun sai ta fadi abinda zai sa ta bar gidan ba shiri. Sai da suka yi la'asar suka faɗa kicin.

Fried rice suka yi wanda ya sha hanta.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login