Showing 75001 words to 78000 words out of 230725 words

Chapter 26 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1066

fuskar da fitilar bayan ya riƙe a hannu.

"Lafiya?"

Ta matsa kadan.

"Kalau, ina kake nufin zuwa?"

Wani murmushi ya yi.

"Au fita ma a bokon naku akwai ƙa'idarta ko? Toh zance zan je. Akwai magana?"

Ta daure fuska.

"Babu, amma ka sani duk abinda kake yimin a gidannan, Allah Zai min sakayya. Ka auro dubu ma Aliyu, sai dai ka sani, duk radda ka yi aure toh babu Ramlat a gidannan."

Ya yi dariya sai kuma ya ja tsaki.

"Ke kika san wannan. Idan kuma sakin a hannunki yake sai mu gani. Kin dai zabi boko yanzu akan kowane hidima na gidanki ko? Sai ki ci gaba."

Daga haka ya gifta ya wuceta yana mai ɗaga wayarsa da ta addabeshi da ƙara.

"Hey Zee, ganinan tafe yi hakuri."

Zee din da ya ambata sai da ta ji kirjinta ya buga, wani zafi zuciyarta ke mata. Zee dai shaiɗaniyar da ta taɓa kwana da mijinta?

Ramlat ta kasa nutsuwa, sai kuma ta ga da gaskiyar Aliyun, ita ce ta sauya a tafiyar zamansu, wato dai sauyin maimakon ya jawomata martaba da kyautatawa daga Aliyun, sai abinda yake mata ya ƙaru.

'Yanzu ke Aliyu ma ya yi aure wannan ba abin kunya ne gareki ba? Abin a yi maki dariya?'
Wani ɓangare na zuciyarta ta ankarar da ita.

Karatun da ba ta iya ƙarasawa ba kenan, tattare takardun ta shiga yi ta maida jaka, ta dauki Ummi suka nufi daki. Bacci ya gagareta kamar yanda nutsuwa ta kauracemata. Ta rasa ina za ta sa ranta ta ji dadi, waya ta ciro ta shiga kokarin kiran Aliyun, ya yi ringing har ya katse bai ɗaga ba.

***
A lokacin shi kuwa yana tare da su G Baba da su Zee ana banke-banken hayaƙi da shafa jikin ƴan mata. Zee na kusa da shi kamar ta koma jikinsa. A duniya tana son Aliyu, ta kuma lura ba ta samun damarsa sai idan yana cikin ɓacin rai da ta gida, abinda ta karanta kenan. Don haka yanda ya dinga biyemata suna faranta ran juna da soyayya irin ta shan minti abin ba karamin dadi ya yi mata ba.

_*"Duk sadda kika samu dama, ki yi yanda ki ka yi ya kusanceki. Koda ciki bai shiga ba, ki mishi karyar kina dauke da cikinsa, duk yanda zai yi akan ki zubar, ki nuna ba ki shirya hakan ba sai dai ya aureki"*_

Kalaman ƙawarta Nancy suka faɗomata a rai. Ta tabbatar yau din ce damarta. Tana kallon sadda wayarsa ke faman hasken kira, da kanta ta dinga katse kiran. A karshe ma ta kashe wayar gaba daya.

'Sorry Babyn Aliy, yau ma nawa ne. Wancan karon koda ban yi nasara ba, wannan karon zan yi.'

Fadin Zee wacce take faman ɗurawa Aliyu lemu wanda ta sanya kwayoyin da shi kansa sun fi karfinsa.

G Baba ya kalleta suka kashewa juna ido gami da ƴar dariya. Wannan shi ne burinsa, zai fi so ma Aliyun ya kusanceta, ko ba komai yana tare da bakin cikin Aliyun yanda bai taɓa kwanciya da wata mace ba a harkar Bariki. Kusan ma ba wannan a gabansa, bar shi da abinda ba za'a rasa ba. So yake ya kashe bakin fariya da jin kai a wannan fagen irin na Aliyu.
***
Sanyin Asuba da na gari ne ya farkar da Ramlat, ta bude idanunta ganin hasken fitila tar a kansu shaidar an kawo wuta ma cikin daren amma bacci ɓarawo bai sa ta ankara ba. Fanka kam tun shigowar sanyi ta daina kunnawa. Ta miƙe ta sauko bayan ta gyarawa Ummi lulluɓin da ta yi mata da bargo. Alwala ta soma t gabatar da sallar Asuba.
Cike da fatan ya kasance Aliyu ya dawo gidan ta fita zuwa dakinsa, gwuiwa a sake ta ja ƙofar ganin bai dawo gidan ba. Kasa komawa dakin ta yi ta zauna a falon. Wuraren bakwai kukan Ummi ya fargar da ita daga tunanin da ta afka, ta mike ta daukota.

Abin mamaki da tashin hankalin, har sha biyu na rana babu Aliyu ba labarinsa. Ta kasa nutsuwa, ta kira wayar kuma ya fi sau talatin ba ta shiga. Jikinta kuma sai ya yi bala'in sanyi. Tsoro da fargaba suka shige ta. Ta goye Ummi tana jijjigata ba don ta yi bacci ba.

Bugun da ta ji a bakin ƙaton kyaurensu shi ya maidota hayyacinta. Da sauri ta shige daki ta fiddo muƙulli ta yafa gyale ta nufi kofar.

"Waye?" Ta tambaya da tsoron amsar da za'a bata.

"Ni ne Idi direban Alƙali."

Ta san waye Idi don sadda ta je yawon arba'in na Ummi, Justice da kansa ya sanya Idin ya maidota gida. Kamar yanda ta san Alƙalin mahaifin Muhibbat, amma tsabar rudewa ma ta manta ko waye.

"Banganeba." Ta fadi kamar ta yi kuka. Ya hau dogon bayani ta bude kofar a karshe.

"Cewa aka yi na zo na kaiki asibitin Malam, maigidanki ne suka yi hatsari daren jiya. Amma jikin da sauki."

"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Toh, to ganinan."

Ta fadi tana jin kuka na tahomata, ta juya kamar za ta koma gidan sai kuma ta ce.

"Ai zan iya zuwa a haka ko?"

Tsabar rudewa ma ta rasa da wanda ya cancanta ta yi shawara. Idi ya kauda kai cike da tausayawa.

'Allah wadarannaka ya lalace, banda ma aure aure ne, me mace kamila irin wannan za ta yi da yaron da ya kusa mutuwa a hanyar dawowa daga saɓon Allah?' Fadin Idi kenan a ƙasan ransa don ya ɗan tsinkayi fadan da iyayen maza ke yi game da abinda suka tsinta daga bakin yan sandan da suka kawosu asibitin.

"Kiyi hakuri." Shi ne abinda ya iya fada. Ta koma ciki don kanta ta sanya hijabi ta fito ba ta ko dauki waya ba, silifas din amfaninta na gida ne a kafarta.

***
A Emergency ta iske mutan gidan su Aliyu ciki har da Abulle a gefe tana ta kuka da salati. Ta karasa kawai ta durkusa gaban iyaye mazan wadanda su ne mafi kusa da inda take.

"Lafiya kalau Ramlatu, sai hakuri kin ji? Kar ki damu jikin ba wani rauni ya samu sosai ba."

Wannan shi ne jawabin Malam gareta. Ta gyada kai tana dauke hawayen fuskarta. Sai da ta je wurin Abulle sannan take jin abinda ya faru cikin ɓarin zance irin na Abullen.

"Yanzu yaronnan sai da ya jawomin abin kunya abin magana a gidannan? Fisabilillah wannan wane irin bakin ciki ne ace wai a motar mace ka yi hatsari kuma likitoci sun auna sun tabbatar ma ba a hayyacinka kake ba, ka sha kwayoyin da suka fitar da kai hayyaci? Ke yanzu haka kike zaune da shi ba ya kwana a gida shi ne ban isa ki fadamin ba? Yanzu da ko rubutu ne da rokon Allah ba sai na saka a shiga yi mishi ba?

Wani kallo take yiwa Abulle wanda kai tsaye za ka kirashi da harara, ita kanta ba ta san sadda ta yi din ba, ga mamakin Amaryar Malam dake kallon wannan dirama, Abulle ta kauda kai gami da fadin Allah Ya kyauta ba tare da ta nemi maida baƙa da hayayyakowa Ramlatun ba yanda ta saba yiwa duk wanda ya yi mata ba daidai ba.

Ramlat ta kauda kai, jikinta har wani tsuma yake, bakin ciki da takaici ne suka tararmata. Da ta san abinda akai kenan da ba ta zo asibitin ba. Likita ya tabbatar za'a iya sallamarsa da dare don ba wata buguwa ya yi ba Banda buguwar kai da ya jawomasa nannauyan baccin fita hayyaci. Fatansu kawai ya farfaɗo cikin hayyacinsa.

"Ita yarinyar fa?" Tambayar da Justice ya yi ya maido Ramlat hayyacinta, kunya ta dabaibaiyeta, hawaye take kanta a ƙasa, jiri take ji tana daga zaune wanda ta tabbatar da a tsaye take zubewa itama za ta yi.

"Af, an samu an kira wani nata kuwa?"

Fadin Likitan.

"Tukunna dai, bamu santa ba. Sai dai ko idan ta farfaɗo a tambayeta."

Likita ya jinjina kai.

"Da sauki jikinta, karaya ce kafa da hannu sai rauni a goshi, mun yi mata dressing, ba dai ta dawo hayyacinta ba tukunna amma muna da ran itama lafiya don ba ta sha abinda yaronku ya sha ba."

Kowannensu kunya ta kamashi, Malam har hawaye ya share cike da bakin cikin kasancewar Aliyu ɓatacce. Addu'a yake mishi ba dare ba rana akan Allah Ya shiryamasa shi.

Gaba daya mazan suka tafi, duk yanda Abulle ta so a kyaleta har ya farfaɗo suka ƙi, haka suka tasa uwarsu a gaba da zummar da yamma zasu dawo, Amarya da Ramlat kadai aka bari.

Kuka take bayan ta kwance goyon Ummi ta mikawa Amarya yanda ta bukata, ta janyo hijabin ta rufe fuskarta, Aliyun ma ba bukatar ganinsa take ba, takaicinta ya tafi ga abin kunyar da ya jazamusu. Idan ta tuna da mace aka ganshi wacce ba ma muharramarsa ba ya fi komai baƙanta zuciyarta. Ta ƙara gane ba ta yi sa'ar aure ba, miƙewa ta yi ta nufi hanyar fita.

"Ina za ki je?" Fadin Amarya wacce ita kanta zaman ya isheta.

Ta dubeta da jajayen idanunta tana jan majina.

"Waje zan ɗan fita yanzu zan dawo."

Amarya ta gyada kai, yau kam ta ji tausayin yarinyar a ranta. Ramlat ta fita tana jan ƙafa har waje, tafiya kawai take cikin tafkeken asibitin na Malam tana zagaye, kuka take, kuka kamar wata taɓaɓɓiya tana ambaton Allah. Ba ta ko damu da idanun jama'a ba, ƙasan wata bishiya da aka saka kujeru ta samu ta zauna, hawaye take fitarwa tana jin wani kaɗaici a ranta. Kamar ta yi wani babban rashi alhalin ita din tana da gata, tana da iyaye da kuma yan uwa.

"Abinda kuke jiyemin kenan?" Ta fadi a fili tana sheshsheka. Jikinta har rawa yake, so da kaunar yan uwanta ke ratsa dukkan gaɓɓanta. Idanunta ya kai ga wasu ma'aurata kuma inyamurai zaune a can gefe guda. Meatpie da lemu suke sha, mijin na rike da yarinyar a cinyarsa, matar kuwa ciki ne da ita haihuwa ko yau ko gobe. Har suka kammala suka mike, yana rike da jakarta da kuma hannun ɗiyarsu da bata wuce shekaru biyar ba.

Kallon ƙurillah take musu har sai da suka kalleta ta ankara ta sauke idanunta. Tana ji suna cewa watakila mutuwa aka yi mata ba ta ko ɗago ba. Ta jima a wurin kanta na sarawa zuciyarta na tashi, ba ta samu sauƙin kirjinta ba sai da ta matsa can gefe ta yi amai, wata baiwar Allah na mata sannu har da siyo ruwa ta bata ta sha. Godiya ta yi sannan ta kama hanya ta koma da tunanin Ummi kada ta farka.

Ai kuwa Amarya ta gani a waje sai jijjiga Ummi take tana kalle-kallen inda za ta hangota. Tana hangota ta hau fadan inda ta tafi ta bar yarinya na kuka. Karɓarta kawai ta yi ta bata hakuri, wuri suka samu suka zauna ta sanyata a hijabi ta hau bata mama.
"Ai bai farka ba har yanzu, nima gajiya nayi da ganin tashin hankali na fito. Wani aka kawo kamar ma ƙafarsa ta ruɓe don kamar an daddatsata abin tausayi.

Gyada kai Ramlat ta yi ta kauda kai.

"Sai fa hakuri Ramlatu, zama da irin Aliyu sai hakuri. Kinga da yanzu kina can gidanki hankalinki kwance amma to, tunda mai afkuwa ta riga ta afku ba yanda aka iya sai hakuri."

Murmushi mai ciwo Ramlat ta yi, tasan dama suna da labarin aurenta da Hilal da kuma abinda ta aikata, sun jima suna yadamata habaicin da ta san iyakar gaskiyarsu ce. Nadama da dana sani suka ƙara tararmata.

"Ramlatu?"

Ta ɗago kai jin murya kamar ta Dakta. Shi ɗin ne kuwa ga dalibai a bayansa, dama yakan zo asibitin sai dai ba koyaushe ba.

Ta miƙe da mamakin yanda aka yi ya ganeta, durkusawa ta yi ta gaidashi ya amsa.

"Me kike yi anan?"

Za ta yi magana kuka ya ci ƙarfinta, Amarya ce ta fadamasa Aliyu ne ya yi hatsari yana ciki.

"Ya Salam, bari na karasa. Ki yi hakuri, ki bar kukan."
Ta gyada kai sannan ya wuce. Tsoron kada ya ji abinda ke damun Aliyu ya fadawa Abbanta mai fama da kansa ya sa ta miƙewa zumbur har Ummi na kokarin suɓucewa daga hannunta sakamakon gefen hijabinta da ta take ba ta ko lura ba.

"Miƙota." Fadin Amarya. Ba musu ta miƙa ta ta bishi ciki, ta iskeshi tsaye wurin likitan da ta gane shi ya karɓi Aliyu.

"Baba Dakta." Ta kira sunan, ya dubeta.

"Ina zuwa Ramlatu." Ta gyada kai ta ja baya kadan. Jikinta rawa yake ga wani dumi da ya dauka. Ta haɗiyi miyau har ya kammala ya nufota.

"Na ji duk abinda ke faruwa, Allah Ya ba shi lafiya."

Ta amsa da wani matsanancin kunya, kanta ta sadda kasa hawaye na ɗiga jikin hijabin nata.

"Abba, don Allah kar ka fadamasa, bai da lafiya. Kar ya ƙara tada hankalinsa, ni ce silar duk abinda ya faru gareni, don Allah a bar ni na yi kukana ni kadai. Baba Dakta ka rufamin asiri kar ka bari su sani. Abinda na shuka nake girba."

A raunane ta ƙarashe, tausayinta ya kamashi. Ya ja numfashi.

"Ba zan fadamasa ba Ramlatu kinji? Kema muna miki fatan komai ya zo karshe. Kema ba ki da lafiya ko?"
Ya fadi ganin yanda take rawar sanyi, ta dubeshi.

"Bansan me nake ji ba."

Ya kama hannunta suka nufi wurin likitocin.

"Dr Amina."

Ya kira sunan daya ciki, ta mike cik da girmamawa ta ƙaraso, umarni ya bata akan ta dubamasa jikinta. Ba musu ta kama hannun Ramlatun cike da kulawa suka shiga wani dan daki.

Duk abinda ya kamata a biya na Ramlatu, Baba Dakta da kansa ya biya. Hutu take buƙata sakamakon juna biyun dake jikinta. Baba Dakta ya jinjina lamarin, hatta Amarya ta yi mamaki ta kuma yi addu'ar Allah Ya raba lafiya.

Cikin ikon Allah bacci wahalalle ya yi awon gaba da ita bayan an bata lafiyayyan abinci ta ci. Daki ne a wadace, ga Ac a kunne. Amarya itama abincin ta ci ta kwantar da Ummu gefen Ramlatun ganin ta yi bacci. A waya ta sanar da Malam ya kirata idan sun shigo don tana wurin Ramlatu wacce ake yiwa ƙarin ruwa. Tana so ta ce juna biyu ne da ita amma ta bar wa cikinta sai sun zo din.

***I just published "BABI NA ASHIRIN DA HUDU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/TmTSyIbktab


🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

*_Rufaida Umar_*

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

24)

"Ka ji tsoron Allah, da ace kai din mai hankali ne da dogon tsinkaye, wannan lamari da ya afku kadai zai sa ka gane son da Allah ke maka da bai ɗauki ranka a hanyar saɓonSa ba. Me kake nema a duniya haka Ali? Meyasa ka fita zakkah cikin iyalina? Idan wannan bai isheka ishara ba ban ga kuma abinda zai sa ka nutsu ka yi hankali da lamarin rayuwa ba."

Malam na kaiwa nan ya ja jiki ya bar dakin gami da bin bayan ƴan uwansa, Abulle ba ta ce uffan ba don jikinta wannan karon itama ya yi sanyi, har kuka ta yi tana ƙaƙaba laifin ɓatancin Aliyu a kanta.

   Aliyu ya lumshe idanunsa ya bude yana duban mutan ɗakin, Abulle ce sai Atine uwargidan Malam sai kuwa kannensa mata sannan ƙalilan daga samarin gidansu.  Kalaman Malam sun taɓa zuciyarsa, jikinsa ya yi sanyi. Bai taɓa dauka zai rayu ba, kusan ma duk abinda ya afku ba'a hayyacinsa yake ba. Ya ji dai sadda Zee ta ja hannunsa akan ya zo ya mayar da shi gida tunda ba zai iya jan mashin dinsa ba. Yana gani bibbiyu ya bi bayanta zuwa motarta.

"Tana ina?"

Ya yi maganar a fili.

"Wa? Ramlatu? Tana can itama ta samu bacci, tana dauke da juna biyu amma abincin kirki ba ta iya maida hankali wurin ci ba?"

Abulle ke wannan dogon jawabin da ba shi ya nema ba. Gabansa ya fadi, yanzun ne ya tuna da Ramlat. Da wace fuska za ta kalli abinda ya aikata? Me za ta ce? Kuma ciki ne da ita?

A zuciyarsa yake wannan tattaunawar kafin hankalinsa ya ɗauku kan hirar da ta ji Amarya da Abulle nayi bayan ficewar kannensa.

"Ai yarinyar ƴar mace ce, uban ma ba'a san inda yake ba wai haka naji su Alhaji na fada. Ba kiga uwa ba, an sha kwalliyar gwala-gwalai da alama dai akwai arziki. Maimakon a ga ta yiwa yarinyar fada ko ta nuna jin kunyar abinda ɗiyar ta aikata, sai kawai ta nemi ma yin faɗa akan dalilin ita yarinyar na yin tuƙin dare. Har da cewa meyasa ba ta kira Direba ya tuƙa ta ba. Sai da ta sa aka sallami diyarta ta biya komai da aka bukata ta fice da ita wai sauya asibiti zasu yi."

Salati sosai Abulle ta shiga yi jin wannan bayani, Aliyu kam yana daga kwance kansa ke sarawa da wani irin sarawa wanda yasan dalilinsa. Kwanakin da ya yi bai sha sigari bane ke son tambayarsa.

***

"Girma kake ƙarawa Zakina, ga matarka yanzu wani cikin ne gareta, don Allah don sonka da Annabi s.a.w ka daina wannan shaye-shayen. Ba amfanin da yake maka. Don Allah Zakina idan ma kana aikata zina itama ka daina kar fushin Allah Ya sa.."

Riko hannun Abulle ya yi dake faman kuka.

"Zan daina, zan daina My granny."

"Yaushe za ka daina? Da ace Allah Ya dauki ranka yanzu, me za ka je ka ce? Ta wane hanya ka mutu?"

Gabansa ya fadi, ya haɗiyi miyau maƙwat. Jikinsa ya kara yin sanyi kwatankwacin yanda nasihar iyayensa maza ya jefasa. Jinjina kai ya yi.

"Zan daina."

Ya fadi a can ƙasan maƙoshi karo na biyu.

"Na fi so naji ka ce ka daina akan za ka daina. Za ka daina na nufin ba lallai ba, kuma akwai sauran lokaci, amma ka daina shi ne ka aiwatar kuma ba za ka ƙara ba."

Ya lumshe idanu ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login