Showing 213001 words to 216000 words out of 230725 words

Chapter 72 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1083

hannunku."

Ba yau suka saba jin Gora na kiran sunayen dazuka ba da sunan wurin da zai yi aiki, don Gora har Sambisa ya ce musu ya shiga yin wani aiki kuma sun yi imanin hakan. Da wannan irin farin cikin Hajiya Zeenatu ta ce.

"Ina mai maka albishir da kyautar sabon gida muddin kwalliya ta biya kuɗin sabulu."

'Makira, me zan yi da gidanki? An fadamaki ni talaka ne? A banza nake aikinnan ban mallaki kadarori ba?'

Abinda ya ce kenan a ƙasan ransa yayinda a fili kuma ya kyakyace da dariya shi a lallai ya yi farin ciki da jin wannan kyauta. Haka itama Hajiya Batool ta mishi alƙawarin mota.

"Ai kun ƙara ƙarfafa gwuiwana wajen yi maku aikin da ya dace! Ku tashi kawai ku je! Gobe ku dawo ku ji sakamako!"

Da haka suka yi mishi sallama suka tafi ransu wasai, su na fita ya mike ya cire babbar rigarsa ya kwashi jakar kudaden ya yi ciki. Nan ya ba yaronsa umarnin duk wanda ya zo kawai a sallameshi a ce ba ya nan. Yaron kasancewar ya san komai kuma tare ma za su yi tafiyar ya sa bayan ya tabbatar da ɓacewar su Zeenatu a layin ya rufe ƙofar sosai yanda ba wanda zai ce Gora na nan.

Shi kuwa Gora da shigarsa ya hau shiri don dama ya haɗa kayansa kaf a ƙatuwar jaka. Ya shige wanka ya gyara jikinsa don jinsa ya ke ya zama Alhaji, ya sauya kaya. Sai a sannan yaron ya shigo, shima gyara jikinnasa ya yi, suka ajiye maganar barin garin cikin daren yau ba gobe ba ransu fari ƙal kamar takarda.

***
"Taheer mutuwa ka ke so na yi? Da wanne zan ji? Da ciwon da ke cin raina ko kuwa da yanda ka ƙi kwantar da hankalinka ka samu lafiya?"

Taheer a wahalce cikin jin zafin kirji ya waigo a hankali ya zubawa mahaifinnasa idanu. Duk da ramar da ya yi  ba ya jin zai fahimci halin da ya ke ciki adalilin soyayyar Hafsat. Ya lumshe idanu bayan ya kauda kai daga duban Modibbo, babban damuwarsa halin da Hafsat ke ciki, wayarta ba ya shiga, ya tabbatar tana can duk abinda ta ke yi hankalinta na kansa, balle kuma shi.

"Ku bani abinda nake so, Abba kai ne ka lalata komai, kai ke da alhakin gyarawa. Ka sani, ba za su taɓa ba ni Hafsat ba, ba zan taɓa samunta ba muddin ba ka nemi gafararsu ba. Abba ka yi kuskure, ka biyewa son zuciyarka wurin nuna ƙiyayya ga ƴan uwanka da kuma abinda suka haifa. Yanzu mene ne ribarka? Kowa a dangi na maka kallo da wannan abin. Abba ka nemi gafararsu tun lokaci bai ƙuremaka ba. Tun kana da sauran numfashinka a doron ƙasa."

Kawu Modibbo da ya yi shiru kai a ƙasa yana sauraronsa jiki a sanyaye ya rasa me zai ce, ba wai nadamar ce bai yi ba, sai dai tunanin ko da wane idon zai dubi bayin Allahn nan har ya ce su yafemasa ya ke. Tun ma kafin wannan ranar ya san kalar rashin mutuncin Hussein idan aka taɓo iyayensa, balle kuma yanzu da Hajiya Zeenatu ta gama kunce masa zani a kasuwa. Kowa ya san da sa hannunsa a lamarin Hussein din. Sai dai kuma kunyar duniya ba ta kai ta lahira ba ranar da Ubangiji zai tsayar da shi da hisabi. Gwara ya tattara ya koam Adamawa gaba daya da iyalinsa ya nemi gafararsu kuma ya faɗi komai a  gabansu. Da wannan kudurin ya rarrashi ɗan nasa tare da nunamasa komai zai zo karshe don za su je Adamawa. Jin dadin wannan kadai sai da yasa Taheer zama maimakon a farko da ba ya iya tashi sai an taimaka masa. Har abinci ya ci sosai, wannan ya faranta ran iyayen.

***
ADAMAWA.

A kwanaki ukun nan, kowa ya ga Hussein da Ramlat ya san ba karamin walwala su ke ciki ba ga wata iriyar shaƙuwa da soyayyar junansu. A kuma ranar ne, Hajiya Binta da Rasheed suka dawo daga Katsina inda ta ziyarci yan uwanta. A washegari kuma za ta juya ta koma Saudiya tare da ɗannata.

Rasheed ba Hausar kirki sai kame-kame yayinda ita kuma Ramlat ba larabci don haka sai kawai suka juye harshe zuwa English suka ci gaba da hira. Abinci lafiyayye ta yi musu shi da abokinnasa, sai da ta ajiye komai kafin ta ba su wuri tana kauda kai daga kallon da Hussein ke jifanta da shi yana ji kamar ya haɗiyeta don kauna.

Ta kwanta rigingine saman gadon, kewar yaranta ta ke ji wannan ta sa ta kiran Hajiya. Bayan gaisuwa Hajiya ta haɗa ta da su. Hira sosai ta dinga yi da yaran, wannan na warce waya, wannan na sako baki yana magana kamar yanda ta fahimta. Dariya sosai suka dinga sanyata jin dagaske su dai so su ke ta dawo Kano ta dinga kai su makaranta a mota. Sai ma a lokacin ta tuna da motarta, yanzun ta san sai dai Hajiya ta ajiye su dinga amfani da shi koda wata matsalar za ta taso da waccan.

"Kinga gajen hakurin Yayanku ko? Sai da ya sauwakewa Bilkisu ya ji dadi."

Gabanta ya fadi jin abinda Hajiya ta ce.

"Kamar ya Hajiya? Me ya kuma haɗasu?"

"Uhm, wai gidan Amaryar ta je ta ja ta da fada har da kokarin dukanta, wannan ya fusata shi. Yanzu dai Kawunnanku sun ce tunda ya dauki zafi a kyaleshi kar a tursasa mishi sai ya maido ta, nan gaba itama watakila ta yi hankali. Yarannasa su na hannun Amarya."

Ramlat sam ba ta ji dadi ba, ko ya ya halin mutum ya ke, saki wani abu ne mai zafi. Cike da jimami ta ce.

"Allah Ya kyauta, Allah Ya daidaita lamuransu idan da alheri."

"Ameen."

Hajiya ta amsa, kamar koyaushe, nasiha mai ratsa jiki ta ƙara yi mata akan riƙe amanar miji da kuma kyautatamasa. Ta kara nusar da ita game da ibada musamman a watan Ramadan da ke ƙara kusantowa don bai fi saura wata guda da ƴan kwanaki ba.

"Allah Yay maku albarka, Ya ji ƙan Abbanku."

Ramlat ta amsa zuciyarta a raunane musamman tunanowa da Abbanta da ta yi, har suka yi sallama ba ta dawo daidai ba. A hankali kuma ta kwanta sosai ta juyawa ƙofa baya. Kewar Abbanta ta ke ji, ta tabbatar da ace yau yana raye zai yi matuƙar alfahari da aurenta na biyu, zai kuma ji dadi. Burinsa da kuma farin cikinsa bai wuce nata ba, ya ci alwashi a kanta a bayan aurenta da Aliyu wanda ya zamemata ƘARFEN ƘAFA, da kansa kuma ya janye sakamakon tsantsar kauna da tausayin da yake mata. Mutuwa ba ta barin wani don wani ya ji dadi. A hankali ta sauke ajiyar zuciya, ba ta san hawaye ta ke ba sai da ta ji tattausan tafin hannun Hussein yana sharemata su. Da sauri ta juyo sai dai babu damar matsawa sakamakon hannunsa ɗaya da ke tokare a gefenta a saman gadon. Ido ya ƙuramata fuskarsa na nuna alamun ba dadi.

"Habibty, meke damunki har ki ke hawaye?"

Ta girgiza kai ta sunkuyar tana murmushi.

"Ba komai, waya muka yi da Hajiya, addu'ar da ta yimin ta sa na tuno Abbana. Shi ne kewarsa ta kama ni."

Ya kamo haɓarta ya ɗago suka kalli juna.

"Kiyi hakuri, dukkanmu muna da wannan tabon na rashin iyaye duk da cewa kaso kusan ɗari, mun samu kulawar da ta dace a wurin Dada wanda ko su ne sai haka. Haka Allah ke tsarinSa a rayuwa, dukkan mai rai mamaci. Allah Ya gafartamusu."

Ta amsa da amin tana mai jin karfin gwuiwa. Ya bita da wani irin kallo yana murmushi, ta yi azamar jan rigarta tana harararsa. Mikewa ya yi ya taɓe baki.

"Wane dare ne jemage bai gani ba?"

"Daren mutuwarsa."

Ta amsa, ya yi dariya, har ya dawo da baya sai kuma ya jinjina kai ya kama hanya yana fadin.

"Ki fito ku yi sallama zai wuce."

Jin haka ta mike ta maida hijab din da ta cire, fitowa ta yi har Rasheed din ya miƙe tsaye don haka suka yi sallama don ta san ba lallai su kara haɗuwa ba tunda a yau sha biyun dare zasu wuce Airport.

***
Bayan sallar isha'i ta shiga suka yi sallama da Hajiya Binta. Mata mai kirki, haka ta sanya ta a ɗaka ta ba ta shawarwarin da za su amfaneta a zamantakewa. Kafin ta yi mata kyautar miski mai kyau marar sirki. Ta yi godiya sosai. Koda ta fito ɗakin Hafsat ta faɗa jin yanda kwanaki biyu ba ta jin ɗuriyarta. A kwance ta isketa yatsarta na dama rike da Counter tana dannawa a hankali. Shigowar Ramlat bai sa ta ɗago ba balle ta san da wanzuwarta a ɗakin. Zama ta yi gefen gadon, hakan ya ankarar da ita, tausayinta ya kamata. Yanzun Dada ta gama faɗan sauyawarta, ta kuma san dalilin tunda Hussein ya faɗamata. Hafsat ta mike zaune da sauri tana goge hawayen saman fuskarta.

"Adda Amal, sannu da zuwa. Yanzu ki ka zo?"

Ramlat ta gyara zama sosai ta dubeta.

"Hafsat kar ki zama marar hakuri da juriya a lamarin soyayya. Ki zama mai hakuri. Kin san illar saɓawa iyaye kuwa?  Na taɓa shiga makamancin halin da ki ka tsinci kanki ciki a baya. Na kuma san yanda ki ke ji, kina jin kamar ba za ki iya rayuwa babu Taheer ba, kina jin numfashinki zai iya ɗaukewa muddin ki ka rasa Taheer matsayin miji ko? Kamar su Dada da Yayyanki ba su yi maki adalci ba."

Hafsat ta kwantar da kai saman cinyar Ramlat, sai kawai ta fashe da kuka ta soma magana.

"Adda Amal wallahi hakane, na sani Mahaifinsa mai laifi ne a wurin su, amma shi me ya yi musu da za su yanke alaƙata da shi? Dada da bakinta ta yabeshi a ɗan  zaman da ya  yi tare da mu, ta fada ta ƙara, bai ɗauki halin mahaifinsa ba balle na mamansa, Hamma AlHassan ma haka. Hamma Hussein bai zauna da shi sosai ba da na tabbatar zai gamsu da kyawawan ɗabi'un Taheer. Adda Amal sanadin aurena da Taheer zai iya sanyawa su shirya. Babban damuwata Hamma Hussein ya kwace wayata, Rasheeda ta kirani ta wayar Dada tana kuka ta shaidamin yana asibiti kwance ba lafiya."

Hafsat na kaiwa nan ta mike zaune, ita Ramlat kallonta kawai ta ke tana fidda hawayen tuna baya, itama dama haka ta kafe? Amma ba za ta taɓa bari Hafsat ta yi irin nata ba.

"Adda Amal kimin alfarma ki ban wayarki, sau daya kawai zan kirashi, daga haka ba zan kara ba. Wallahi kawai gaisawa zamu yi na kuma roƙeshi mu ci gaba da addu'a. Har abada ba na fatan na bijirewa iyayena da yan uwana."

Ramlat ta yi jim, tana tunanin anya kuwa idan ta yi hakan ba matsala? Sai dai kuma irin magiya da nacin Hafsat ya sa ta miƙamata wayarta. Kasa fita ta yi daga dakin ta jira har Hafsat ta kammala wayar, Ramlat banda kallon ƙofa ba abinda ta ke yi. Tsoronta kar Dada ta faɗo ɗakin don ta san abu ne mai matsanancin wahala Hussein ko AlHassan su shigo ɗakin.

Da murmushi ta dubi Ramlat.

"Adda Amal."

Sai ta rungumeta don farin ciki can kuma ta saketa.

"Cemin ya yi za su zo nan da kwanaki kalilan har Babansa, zai zo neman gafarar Dada da su Hamma."

Sosai itama Ramlat ta ji dadin hakan. Ta rike hannunta.

"Toh kinga ni, don Allah ki saki ranki, kinga Dada kin jefa ta a damuwa. Ta ce ko ganin idon baƙuwarku ba kya yi, ba ki san ki danne zuciyarki da abinda ke cikinta ba. Jefa iyaye cikin damuwa masifa ce a garemu. Kuma ina mai ba ki shawara ki dage da nemawa kanki zaɓin Allah, ki rabu da biyewa son zuciya wurin dagewa akan zaɓinki."

Hafsat wacce tuni ranta ya yi fari sumul ta gyada kai.

"In sha Allah Addata. Ina godiya sosai. Sai dai Adda ba ki ban labarin da ki ka ce."

Ramlat ta murmusa.

"Kar ki damu, ai ana tare."

"Da'iman kuwa da yardar Allah." Fadin Hafsat, suka dara kafin Ramlat ta fice  ita kuwa bandaki ta shiga ta wanke fuskarta. Ramlat na sallama da Dada sai ga Hafsat din, sosai ta yi mamakin walwalarta, ta karasa ta fda jikin Dadar tana neman gafararta cike da shagwaɓa. Murmushi Dada kawai ta yi gami da jinjinawa Ramlatun. Ta tabbatar aikinta ne.

***
A ɓangarenta kuwa, ganin fitilu a kashe ya ba ta mamaki matuƙa, ita dai ta san ba ta kashe ba. Haka ta ci gaba da tafiya a hankali har ta kai ga makunnin, kafin ta kunna ya riga ta. Ta juyo ta dubeshi, kafin ta kai duba ga cikin falon. Baki da hanci kawai ta saki tana dubansa ta kuma maida duba ga abinda idanunta ke gani.




I just published "BABI NA SITTIN DA HUƊU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1028701620?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=0Ip%2BQlXDoaoxyM7eqonDyl6cCNMjLR7b13cfWz0PO6rluIvQeUuu1jHeHigNXBE4IV%2Fm159PS%2BDsIeqGDHiIXMY5fTO3p4OINuf3vYe6Dx12trWJCYsK2knobbhhwa9y





🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

64)


_*Assalamu alaikum yan uwa Barkanmu da wannan lokaci. Ku yi hakuri kun sha jira, da yardar Allah kiris*_

Wani ƙaton enlargement ne na ɗaya cikin hotunanta da ya ke da su, ta karkace kai tana murmushi har fararen haƙoranta sun fito, sai wani ƙaton kwali da ba za ta iya cewa ga abinda ke ciki ba sai kuwa akwatuna jere reras har guda sha biyu. Ta kai dubansa gareshi, murmushi ya ke sakarmata sosai. A hankali ya matso ya kama hannunta suka karasa cikin falon. Wani ƙaramin kati mai adon heart da fulawoyi ne ya soma daukar hankalinta don haka ta sa hannu ta ɗauka ta bude.

_*From the moment I first laid eyes on you, I knew you were a perfect match for me. I love everything about you Heart.*_

Ta juyo ta dubeshi, yana tsaye kawai hannuwansa cikin aljihun wando yana zubamata murmushi. Da ido ya mata nuni akan ta ci gaba da buɗewa. Ba musu ta kai durkusa ta kai hannu ta bude wani karamin gida na zobe, ai kuwa zoben ne mai matukar sheƙi, ya fi mata kama da na azurfa. Ya yi masifar burgeta, idanunta ya ƙara kaiwa saman wani kwalin karami da aka ɗaure bakinsa da igiya mai ƙyalli, ta bude, ganin mukullin mota kawai sai ta ɗago ta dubeshi, idanunta nan da nan suka cicciko da kwalla. Ta ajiye kafin ya taimaka mata da bude akwatinan, kaya ne maƙil, kowanne da set dinsa. Yanda dai ku ka san lefe irin na budurwar yarinya don wannan ma ya fi na budurwar kyau da tsari. Ko iyaka haka aka tsaya a na budurwa sai sam barka. Laces, atamfofi, mayafai, shadda, yadika, abayoyi da dukkan sauran kayayyakin shafa da sarƙoƙi ba abinda ba'a haɗa ba. Wannan ya bata tabbacin ba yau ya soma haɗawar ba. Bayan sun mayar da komai ta dubeshi, tuni hawayen da ta ke dannewa sun zubo. Ya kai hannu da sauri ya ɗaukemata su. Ba ta bar kallonsa ba ta soma magana.

"Allah Ya saka da dumbin alheri, na.."

Ya kai yatsa saman lebbanta.

"Shii...Ba kalar godiyarnan nake so, buƙatar fin haka nake. Kar ki manta kuma haƙƙi ne na maki sutura da ma duk abinda bai fi ƙarfina ba wanda zai farantamaki. Kin cancanci fiye da haka."

Ya ƙarashe gami da ɗagamata gira. Kunyar ta nema ta rasa, kawai sai ta juyo gaba ɗaya ta rungumeshi har bayansa na jingina da kujerar. Ya kuwa ba ta kyakkyawan mazauni a kirjinsa, kafin kuma kiɗa ya sauya salo.

***
KANO..

Wutar da ta tashi a wani gida dake unguwar ya sa mutane duk suka fito, cikin dare ne da misalin karfe biyu da mintoci. Banda salati da kokarin kashewa ba abinda ake yi. Da yawa suna aikin kashe ta amma fadi suke don kawa kar wutar ta haɗa da nsu gidajen ne amma banda haka dama sun gaji da Maigidan, bokancin da ya ke yi musu a unguwa yana tare matasa abin ya ɓaci.

Gora kuwa yana daga ciki banda ihu da neman agaji ba abinda ya ke yi, ya rasa ta inda aka yi wuta ta soma cin gidansa, babban abinda ya ƙara haukata shi neman jakar kudadensa da ya yi ya rasa, ga yaronsa ba ya nan. Wannan ya ɗan ankarar da shi cewa cin amanarsa ya yi. Nan fa ya haukace, tun akwai hanyar ficewa har ya zamana ya rasa ta inda zai bi ya tserar da rayuwarsa daga halaka. Haka dai kafin mutane su yi nasarar tsayar da wutarnan, Gora rai ya yi hali.

A ɓangaren yaronsa kuwa har da shi cikin masu kokarin kashe wuta kamar gaske, har ya tafi sai ya yi tunanin gwara ya tsaya ya tabbatar da mutuwar Gora kafin ya gudu, idan kuwa har aka yi rashin sa'a ya tsira, to ya tabbatar duk inda ya shiga a duniya ba zai tsira daga ta'addancin Gora ba. Ganin an fito da Gora a mace ya sanya ya ji wani sanyi a ruhinsa, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya hau mashin dinsa ya wuce can filin makaranta inda abokinsa Jabir da suke kira da Jabson ke jiransa su wuce. Yana zuwa suka cafke su na dariya. Nan ya ba shi labarin komai, ya dubeshi da kyau.

"Jakar fa?"

Jabson ya yi wani malalacin murmushi gami da mishi nuni da aji. Ya bubbuga kafadarsa suka dara kafin ya shige gaba zuwa ajin, sai dai shigar ya yi daidai da sokamishi wuƙa a baya ta ɓullo ta ciki, Jabson ne. Sai da ya tabbatar ya kashe shi har lahira sannan ya ɗauki jakar ya tsallakeshi. Mashin dinsa ya haye ya bar wurin a miliyan. Shi da garin Kano kuma sai nan da wasu shekaru.

  Misalin ƙarfe sha biyu na rana, labarin ƙonewar Gora da tsintar gawar yaronsa ɗan aikensa Salmanu, ya karaɗe unguwar. Ko'ina maganarsu ake yi, ga Jabir abokin Salmanun da aka nema sama ko ƙasa aka rasa. Dama almajirai ne, wannan yasa aka shiga tunanin ko sace Jabir din aka yi bayan kashe Salmanu. Daidai sadda ake wannan hargitsin, motar Hajiya Zeenatu ta tsaya. Tun kafin su fito cikinsu ya ɗuri ruwa ganin yanda gidan Gora ya zama kango lokaci guda.

"Ke Zeenatu, anya gidan ne?"

Hajiya Zeenatu ta kasa amsawa Hajiya Batool, kokari ta yi kawai ta yi parking suka fito, yaran almajirai na ciki su na ta  ɗage-ɗage ko za su yi tsintuwa. Daga ƙasan bishiya wasu samari suka hangosu. Ɗayan ya ce.

"Waɗannan su ne na goma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login