Showing 21001 words to 24000 words out of 230725 words

Chapter 8 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1039

ɗan waken da take kokarin zubamusu bayan ta ɗibarwa Affan nashi ya ja gefe. Harararta ta yi.

"Me kuma za ki cemin bayan kin maidani wata banza don kawai ina nunamaki abinda ya dace."

Hannunta ta riko tana dubanta.

"Kiyi hakuri, wallahi duk ba haka bane. Amrah yanzu ke a tunaninki da wane ido zan kalli Hilal na ba shi dama a karo na biyu bayan ni ce ummul aba'isin duk wani abu da ya faru a baya? Ko kin manta ba da Hilal kadai zan zauna ba? Akwai matarsa kuma akwai danginsa da babu ranar da zan goge bakin fentin da na yiwa kaina a idanunsu? So kike na bar wa ƴaƴan da zan haifa da shi abin gori? Yanzun ma wadannan din da ya na ƙare? Kin fi kowa sanin abinda ya faru, kuma kin fi kowa sanina Amrah. Da ace zan iya auren Hilal, da tuni yanzun wani labarin ake banda wannan. Amma bakin alƙalami ya bushe, zan iya yin aure ga kowane mutum a doron ƙasa banda Hilal. To balle ma auren babu shi a gabana yanzu, na gwammace na zauna na kula da yarana. Hakan zai fiyemin komai dadi."

Tausayinta sosai ya kama Amrah, har ba ta san sadda hawaye ya zubomata ba, ita kanta uwar gayyar sai jin ɗuminsa ta yi saman kuncinta. Ta kuwa shiga yi ba kakkautawa.

"Na cuci rayuwata Amrah, na cutar da mutane da dama wanda har gobe ban bar dana saninsa ba. Amrah har gobe ina tunanin bakin cikina ne sanadin mutuwar Abbana duk kuwa da irin rabuwa ta salama da amincin da muka yi. Ƴan uwana ba sa fahimtana, har gobe suna min kallon mai laifi a idanunsu. Ya zan yi ne wai?"

Nan fa suka shiga kukan har Affan wanda ganin Mominsa na kuka shima ya shiga yi. Dakyar suka rarrashi kansu sakamakon ƙarar da Affan yake da kuka yana rirriƙe Ramlat. Komai da komai ya shiga dawowa kwanyarta, daga lokacin da ta saki jiki suka soma gudanar da soyayya mai karfi tsakaninta da Aliyu, daga lokacin ne komai ya faro asali wanda har gobe ta kasa goge *BAƘIN FENTIn* a zuƙatan masoyanta.

***
   *BAƘIN FENTI*

_*Komai yana da sila, komai da mafarinsa. Duk abinda bawa bai ɗora kan turba mai kyau da tsari ba, mafi yawan lokuta ƙarshensa nadama ne! Koda ace a haka kaddarar ta zo masa.*_

"Wai Ramsy me kike ne? Ki fito kina ɓata lokaci."

Muryar Amrah kenan sa'ilin da ta ke kokarin shigowa dakin. Zuwa yanzu ta kai matakin da ba ta jin za ta ɓoyewa kowa a duniya sonta ga Aliyu. Wannan tasa ko bayan shigowar Amrah ba ta fasa amsa wayar a nutse ba ba ta ko damu da kallo da murmushin Amrah ba.

"Kai wannan Hilal, shi ba ya  jin kudinsa ko? Daga Malaysia mutum ya kira a yi ta wayar fin sa'i biyu? To nidai don Allah ya kyalemin ke ai daya, idan ba haka ba wallahi zamu yi lattin."

Ba ta da niyyar ba ta amsa, ta fahimci ba ta gane wanda suke wayar ba, ko ma ta ce ba ta sanshi ba.

Daga dayan gefen Aliyu wanda ke zaune a falon Muhibbat yayinda ita kuwa ke kicin tana shiryamusu abincin rana ya ɗan hade fuska kamar tana kallonsa.

"Baby waye Hilal? Baby ashe ban Kai darajar da har yanzu za ki iya sanar da mutane ni din kike so ba ba wani banza ba? Watanni goma da soyayyarmu wanda ya fi karfin na wadanda suka kwashe shekaru goma suna yi shine har yanzu ban samu karɓuwa ba? Sai anjima."

Ya katse wayar gaba daya yana fitar da huci.  Fitowarta kenan daga kicin, ta ji dukkan abinda yake fadi, sai dai ta yi kamar ba ta ji ba. Ranta na ƙuna kamar koyaushe, ta haɗiye kwallar dake barazanar tona abinda ke ranta. Ganin ya ɗan kalleta ya kauda kai ya ja tsaki ya sanya ta kakalo murmushi ta nufi inda yake zaune a darare.

"Yaya na kammala girkin."

Ya yi mata kallon sakara. Ta sauke kwayar idanunta, a duniya idan da abinda ta tsana ya biyo bayan kallon wulakancin da Aliyu ke mata a lokuta da dama.

"Sai aka ce miki yunwa nake ji? Ga jaki kin ajiye? Mtsww!"

Ya ja dogon kafin ya mike tsaye ya sa kafa ya ture Centre Table a zuciye har yana kifewa, ɗan flower vase din dake kanta na ado shine ya fashe. Bai ko waiwaya ba ya sa kai ya fice daga gidan. Ta zubawa ɓarnar da ya yi mata ido, ko ba komai kudi aka sa aka siyamata. Ba abinda ta nema ta rasa na ƙawata gida wanda iyayenta basu yi mata ba, yayyunta maza kuwa ba wanda bai ba ta gudummuwarsa ba duk kuwa da irin tsanar da suka yiwa Aliyu. Kuka sosai ta shiga yi tana tattarawa, Aliyu bai damu da ita ba. Ta hakikance ba ya sonta, ba kuma ya tausayinta. Ita kullum ke kwana da tashi da bakin cikinsa, ga so da tausayinsa wanda ke sanyawa ta ɓoye aibunsa a idon danginsu har a gaban Abulle wacce koyaushe cikin sanyamusu albarka take. Burin Abulle ta ga ɗa ko ƴarsu sai dai har a sannan Allah bai ba ta ciki ba. Ba kuma ta zargin Aliyu da komai.

"Allah ga mijina, Allah Kai ke shiryawa, Allah Ka shiryamin shi. Ka karkato da hankalinsa gareni." Ta furta a fili tana mai daga hannu gami da kuka, sannan ta shafe fuskarta ta ci gaba da tsince ɓarnar da ya yi.

 
    A gefen Ramlat hankalinta idan ya yi dubu to ya tashi, hawaye take tana kara dialing lambarsa sai dai amsa daya ce, a kashe. Wannan ya tashi hankalin Amrah. Ta dubeta a gigice gami da dafa kafaɗarta.

"Ke, meyafaru da Hilal din? Me yace maki? Mun shiga uku."

Ambaton Hilal da ta ƙara ya farkar da Ramlat. Ta buge hannunta a saman kafaɗarta ta hau masifa.

"Hilal Hilal! To hell with him! Haba! Sai kiramin Hilal kike, a sanadinsa kin sa Aliyu ya yi fushi da ni! Ya kashe wayarsa bansan kuma me zai aikata ba! Dole ne zuwa walimar?! Ba zan je ba! Nace ba zan je ba ko za ki kaini dole?! Wallahi zuwanki bai min rana ba! Ni ki tafi kawai ki rabu da ni!"

Yanda take rufe ido tana zuba masifa iyakar gaskiyarta shi ya fi komai ba Amrah mamaki.

"Aliyu kuma? Waye hakan? Yanzu akan wani banza Aliyu kike min masifa?"

Ai kiran Aliyu da banza shi ya kara tunzura Ramlat. Ta nuna ta da yatsa.

"Kin yi na farko ya zama na karshe Amrah don wallahi ba don ina ganin mutuncinki ba sai na gasamaki abinda zai miki zafi a rai! Aliyu ya fi karfin ki kiramin shi da banza! Kika kara kuma Allah Ya isa! Ba zan je walimar ba ki tafi ki kyaleni! Aliyu shi nake so kuma da iznin Allah shi kadai ne mijina anan duniya!"

Daga nan ta juya a fusace ta soma cire kayanta tana tsaki. Amrah ranta ya dinga suya har bata san sadda ta shiga hawaye ba.

"Akan wani Aliyu kikemin Allah Ya isa? Idan kin kara ganina a gidanku kimin abinda ya fi haka."

Daga haka ta juya ta fice. Allah Ya taimaka Hajiya na wurin Abba, A'isha kuwa kallon cartoon  da take a tashar Spacetoon ya dauke hankalinta.

Ita kuwa Ramlat ko a kanta, tashin hankalinta fushin Aliyu. Ta kwanta lamo tana fitar da hawaye, text ta shiga aikamasa kashi kashi.

_*Sweet na tuba don Allah Ka yafemin. Sweet fushinka barazana ne ga lafiyata. Wallahi sweet kai kadai nake so, Kar ka manta na san da zaman Hilal din amma nake sonka."

_*Wallahi Sweet Aliy zuciyata za ta buga. Wallahi har fada muka yi da Amrah a kanka. Ka yafemin. Wallahi don ba ka yanda na ci mutuncinta ba.*_

_*Sweet Aliy har walimar ban je ba saboda kai. Na kasa samun nutsuwa. Sweet Aliy ka yafemin ka bude wayata. Na maka alkawarin fadawa kowa kai nake so. Ka ji? Kuka fa nake. Kaina ma ciwo yake*_

Haka ta yi ta rubuta malamai kashi-kashi tana aikawa sai dai duk ba ya tafiya adalilin wayarsa a kashe. Ta kuwa ci gaba da rusa kuka, dakyar ta samu ta mike ta yi alwalar la'asar ta shiga sallah. Tun tana cikin sallar ta ji wayarta na kara, sallamewa kawai ta yi ba ta ko ida ba ta nufi wayar a guje. Ganin mai kiran ya sa ta ɗagawa da sauri ba tare da ta jira ya ce ba, ta ce.

"Sweet Aliy ka yafemin don Allah, na tuba wallahi ba zan ƙara ba."

"Zan yafemaki Baby amma sai kin fito na ganki. Ina nan bayan layinku. Ba zan iya bacci ba idan ban sanyaki a ido ba."

Wani dadi ta ji a ranta,

"Yanzu zan zo Sweet, ban minti biyar."

Sallar da ba ta yi ba kenan ta bar shi a sai ta dawo, nan da nan ta shafa hoda ta sanya lip gloss, kayan zuwa walimar da ta cire su ta mayar. Ta ja mayafinta, sai da ta kama kofa za ta fice daga dakin ta ji faduwar gaba, me Amrah ta ce ga su Hajiya kafin ta fita?

'Ko me ta faɗa ita ta sani, ke dai kar ki ƙara laifi wurin Aliyu.'

Wani bangare na zuciyarta ya ba ta shawarar da nan take ta dauka. A hankali ta fito tana ɗaga labulen da ya raba dakunansu da falon, babu kowa sai A'isha da ta gaji da kallonta tana bacci. Hamdala ta yi ta fice da sauri.
Tun kafin ta karasa a hangoshi tsaye gaban mashin ɗinsa. Ya haɗe cikin shadda kalar sararin samaniya, babu hula a kansa sai dai ya yi kyau kwarai a idanunta. Kirjinta har wani bugu yake tsabar so da kaunarsa. Shima ya zubamata ido yana ji kamar ya saceta su gudu.

"Ba ki kyautamin ba."

Ya furta yana dubanta da shanyayyun idanunsa. Ta yi narai-narai da idanunta.
"Ka yi hakuri don Allah."

"Banda wannan, na hakura ai tun kallon farko da na miki na mance dukkan damuwata. Sai dai ba ki kyautamin da kika yiwa Aminiyarmu wulakancin da kika faɗa ba."

Sai a sannan ta tuna da ta yi laifi, ta jinjina kai.

"Haushi ta bani, banza fa ta kiraka." Ta fadi cike da wauta.

Ya ji ciwon kalmar sai dai ya yi murmushi. Har a ransa ya ji haushin Amrah na kiransa da banza.

"Kiyi hakuri, a kanki komai zan dauka zan kuma shanye muddin za ki zama rabona. Idan dai kina don farin cikina ku shirya a yau ba gobe ba."

Ta shiga gyada kai.

"Zamu shirya, zan je har gidansu na ba ta hakuri amma yau ba ta nan ta tafi walimar da na fadamaka zamu je dazun. Idan muka hadu a makaranta gobe zan bata hakuri ka ji? Ka yi hakuri don Allah Sweet Aliy."

Ya dan lumshe idanunsa yana murmushi, murmushin da ke ƙara tafiya da imaninta.

"Ya isa, shikenan ya wuce. Allah Ya kaimu goben. Da ban ganki ba, ba zan iya bacci ba."

Wani sanyi da dadi suka lulluɓe zuciyarta. Nan da nan kuma suka shantake da hirar soyayya kamar kar su rabu. Sai dab da karfe shida suka rabu, ba ta iya tafiya ba sai da ta ga tafiyarsa sannan ta juya cike da annashuwa ta koma gida.

"Sai yanzu ku ka dawo? Kun so ku yi dare." Abinda Hajiya ta fadi kenan, sai ta ji kaunar Amrah a ranta, wato dai ba ta sanarmata rigimarsu ba.

"Eh Hajiya, ki yi hakuri."

Hajiyar ta gyada kai tana kallon yanda ƴar ke zuba uban fara'a kamar wacce aka yiwa albishir da aljannah. Gudun kada Hajiyar ta watsamata tambayar da za ta kasa amsawa game da walimar, ya sanya ta saurin shigewa daki gami da faɗawa kam gado tana murmushi, Aliyu shi ne komai nata a yanzu, ba kuma ta jin har abada za ta bar shi ko me za'a yi, kuma ko me zai faru. Tunawa ta yi da sallar la'asar, da sauri ta mike ta faɗa banɗaki ta kara dauro alwala sannan ta tayar da sallar kusan ma a sallar banda murmushi da addu'ar Allah Ya sa ta zama matar Aliyu ba abinda take.

       ***
Muhibbat tun tana zuba idon ganinsa ya dawo gidan har ta gaji, ragowar abinci ranar ta juye ta miƙawa wasu makwaftansu marayu suka yi ta godiya.  Tasan ko ta bar shi Aliyu ba zai taɓa ci ba don a cewarsa ba ya son kwantai. Ba ta gaji ba ta ɗora sanwar dare, tuwon semo ta yi da miyar danyen kuɓewa, a gefe kuma ta yi farfesun kifi sai kunun aya. Komai ta jera inda ya kamata ta faɗa wanka, tana fitowa ta haɗe cikin doguwar riga ƴar kanti mai ɗankwali. Ko ba ado ita din kyakkyawa ce, hakan dai bai hanata daukar kwalliyar ba. Ta fesa turare ta fito falon tana addu'a cike da tsoron yanda zai shigo gidan. Fatanta kar ya shigo a maake kamar yanda ya saba. Jin karar mashin dinsa ya kara kaɗa hanjin cikinta. Ta miƙe da sauri ta bude kofa, a kan idonta ya yi parking ya shigo. Ta yi mamakin ganinsa cike da walwala. Itama sai ta saki fuska.

"Sannu da zuwa." Ya riko ƙugunta yana murmushi kafin ya kai mata sumba a kumatu.

"Yauwa Matar."

Ta rufe kofar suka karasa falon zuciyarta kamar ta fito ta taka rawa tsabar farin ciki duk kuwa da tasan silar farin ciki nasa. Ramlat ce! Ganinta ya je ya yi hakan yasa shi sakarmata fuska sai dai hakan bai dakusar da nata jin dadin ba. Murmushin Aliyu da dariyarsa ma kadai abin so ne a wurinta.

Ta taimaka ya yi wanka, ga mamakinta sosai ya ci abinci har suna hirar abinda ya shafi danginsu. Ga duk wanda ya ga Muhibbat ya san tana cike da farin ciki. A karshe ma ya ja hannunta suka shige ɗaka.

Tun da ya soma sarrafata yake kiranta da suna Baby, wani sa'in ya ce Ramlat sai kuma ya ce oh i an sorry na manta. Har ya yi ya gama ba ta fasa fitar da hawaye na baƙin ciki, ta waiga ta dubeshi yana baccinsa hankali kwance, miƙewa ta yi ta tsarkake jikinta ta fito zuwa ɗakinta. Nafila ta yi ta zauna tana addu'a tana kuka. Sau da dama takan ji kishin Ramlat, sau da dama kuma takan ji ko ma mene Aliyu ne ya ba da fuskar da komai ke faruwa. Sai ta dinga kallon wasu abubuwan ba laifin ita Ramlat din bace. Ta gaji da kukan ta dau Kur'ani ta karanta sannan ta haye gadon ɗakinta sai bacci.

Da asuba koda ta mike ta yi alwala ta shiga tashinsa. Wayar da yake ta tsaida ta.

"Baby ki tashi mana ki sallah, ban san wannan baccin fa. Uhum? Ina magana kina min magagin bacci ko?"

Kasa ƙarasawa ciki ta yi da sauri ta maida kofar ta rufe ta koma ɗakinta cikin hawaye. Mutumin da sai ya ga dama yake tashi salla idan ta tashe shi, shi ne har ya iya tayar da wata yin ibadar. Abinda bai taɓa yi gareta ba kenan, koda dai lokuta da dama ita keda kokarin tashi salla ta tayar da shi.

Wannan karon kasa zubda hawayen ma ta yi ta haɗiye abinta.

    ***
_*Alhamdulillah, your future husband is back. I can't wait to see you. Love you.*_

Saƙon da ya shigo wayarta misalin bakwai na safe kenan, sa'ilin da take shirin fita makaranta, saƙon da ta tabbatar na Hilal ne. Wani makokon bakin ciki ya turnuƙe zuciyarta har ba ta san sadda ta ja tsaki ba. Sai me idan ya dawo? Ba dai za'a yi mata dole a auren wanda yanzun ta tsana ba. Haka ta kammala saka uniform ranta na suya, ba don Sweet Aliyunta zai kira ba da ta kashe wayar gaba daya ta bar ta a gida. Sai dai duk sadda ta samu dama takan ɓoye a banɗakin makaranta ko cikin aji idan ba malami ta kirashi su gaisa.

"Ke kuma lafiya kike cin magani? Hala ba ki da labarin dawowar mutuminki?"

Hajiya ke zancen cikin murmushi don tun jiya Munir ke fadamata Hilal ya dawo.  A dole Ramlat ta ƙaƙalo murmushi bayan ta haɗiye dankali da kwai da ta sanya a bakinta.
"Yanzu da safe yake fadamin."

Ta kai duba ga agogon fatar dake daure a hannunta tana mai miƙewa.

"Hajiya zan yi latti muna da test. Sai na dawo.". Daga haka a gurguje ta fice Hajiyar na mata addu'a sai dai tana dan nazarin yarinyar da yanda ta ga kamar ba a walwala da zuwan Hilal din. Fatanta kar abinda take tsoro ya tabbata.https://my.w.tt/ub8deMQ0g9


🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

09)

    Tun shigarta ajin ta hango Amrah ta sauya wurin zama daga kujera mafi kusa da ita zuwa can ɓarin hagunta, ba ta yi mamaki ba don dama duk sadda saɓani ya haɗasu sai an gane a ajin ko don sauya wurin zama. Ba ta yi gigin zuwa inda take ba ganin malaminsu ya taho. Sai dai kusan rabin hankalinta yana gareta, a yanzun ta gane kurenta sosai, Amrah yar uwa kuma Aminiya tun suna yara bai kamata ace ta yi mata hakan ba. Yanzun ta fi koyaushe bukarta kasancewarta abokiyar shawarar da suke haƙowa su binne ba tare da kowa ya ji ba. Sai dai a ranta tana da yaƙinin muddin ba za ta bata goyon baya game da sheƙar da ta sauya ba, komai ma ya biyo baya ba matsalarata bace. At her age, Babu wani ko wata da za ta bari ya tauyemata ƴancinta.
Test har biyu suka yi, da na Economics da Commerce, bai bata wuya sosai ba, ko ba komai tana da basira daidai gwargwado sannan ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba wurin karatu bisa shawara sanyin idaniyarta.

Ana tashi break ajin duk an fita sai ita sai kuma Amrah da ta maida hankali ga kwafar note. Wurinta ta nufa kai tsaye, ko ba ta ɗago ba ta san ita ce, takaici ya kamata. Nan da nan kalaman da ta jefata da su suka dawomata, wasu hawaye ta ji sun soma wanke mata fuska.

"Ko ba amintaka tsakaninmu Ramlat, zan ci darajar kaunar da nake miki kamar ƴar uwata ta ciki ɗaya. Akan namiji kika zageni kika wulakantani tamkar ba ki sanni ba. To ni kuwa me za ki cemin? Tsayuwarki ba ta da amfani don yanzun babu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login