Showing 210001 words to 213000 words out of 230725 words

Chapter 71 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1040

A hankali yanayinsa ya soma sauyawa, ɓacin ransa ya ragu sosai, ba abinda ya ke ji sai matukar kaunar kasancewa da matarsa kuma halaliyarsa. Ita kuwa dagaske bacin ransa ne ya taɓa ta, ba ta kaunar ganinsa a yanayi irin hakan.

"Toh ya isa, ko su kike ki jefani yanayin da ba za ki iya magancemin ba?"

Sai ta ji gaba daya ya ba ta kunya, ta dan harareshi da wasa tana mai zame hannunta cikinnasa, ya yi murmushi ya zauna sosai yana fuskantarta.

"Yarinyar ce naga alamun ba ta ji, ta yi zurfi a soyayya da wancan yaron."

Ramlat duka ba ta fahimci me ya ke son cewa ba, ta tsuramasa idanu cike da neman ƙarin bayani.

"Hafsat."

Ya fadi kai tsaye, nan ta fahimci komai, ta san da soyayyar Taheer ɗan Modibbo da ita  Hafsat din, tausayinsu ya kamata, ta tabbatar laifin Babansa ya shafi soyayyartasu.

"Ka yi hakuri."

Haka kawai ta iya cewa don ta tabbata idan ta fadi wata kalmar bayan hakan, zai iya hucewa a kanta.

Da wannan ta samu suka share  zancen inda ya shiga yi mata bayanin ya soma neman aiki. Ta bishi da addua da fatan alheri.

***
KANO

Taheer a fusace ya shiga sashin Hajja Fatouma mahaifiyarsa. Tana kallon yanayin fuskarsa ta ji zuciyarta ta taɓu, tun sadda ta fahimci irin son da ya ke yiwa ɗiyar Dada ta san akwai matsala. Kaf cikin yaranta ta fi sonsa, ko don kasancewarsa namiji na farko a ɗakinta? Ba ta da masaniya, to haka ma daga bangaren Modibbo, duk wani tsaurinsa yakan sassauta akan lamarin Taheer. A yanzun da shi kansa Modibbo kunyar kansa da kansa ya ke ji, ya kuma kasa samun sukuni ko ƙanƙani game da lamuran su Hussein, ta tabbatar ba zai iya komai ba don su ba mahaukata ba me da za su ɗauki ƴarsu su ba Taheer duk da irin abinda ubansa ya shukamusu.

Maimakon Taheer ya zauna, sai ya durkusa ya kama ƙafarta, ga mamakinta hawaye ya ke.

"Hajjata zan iya mutuwa wallahi, kirjina zafi kawai ya ke yi. Ina son Hafsat, bana jin zan iya rayuwa idan babu ita. A yau Hamma Hussein ya kira wayata ya yimin gargadi kan na rabu da ita. Ba zan iya ba Hajjata, ba zan iya ba mutuwa zan yi. Na kasa sukuni tun da muka yi waya da shi, ji nake kamar na shirya gobe na wuce Adamawa."

Ta girgiza kai tana sharemasa hawaye da hannunta, ita kanta nata idanun ne suka cicciko da kwalla.

"Karatun naka fa wanda saura kiris ka kammala? Kar ka kara cewa za ka wuce Adamawa a yanayin nan a muke ciki, ba za su taɓa kallonka ba. Ba za ka yi wata ƙima ko daraja a wajensu ba saboda tun ran gini tun ran zane. Mahaifinka ne silar komai, a yanzun da girmanmu ya gama faɗuwa a gabansu gaba ɗaya, ba na jin ko karen gidansu zai ragamaka idan ku ka ci karo."

Ya numfasa yana jin ciwon gaskiyar da Hajjarsa ke fadi, don ɗacinsa har a maƙwagoro ya ke ji. Ya haɗiyi zazzafan miyau ya dubeta da jajayen idanunsa.

"Idan har dagaske Abban ya yi nadama, meyasa ba zai taka da kansa ya je ya samu Dada da su Hamma ya ba su hakuri ba? Idan mutuwa ta daukeshi a wannan yanayin fa? Shi ne silar lalacewar komai, don haka ya je ya gyara. Na fadamaku, idan na rasa Hafsat ba zan rayu ba. Ita ce numfashina."

Daga haka ya mike ya fice yana tangaɗi sakamakon jirin da ke kwasarsa, bai kai ga ficewa daga ɗakin ba ya zube warwas a bakin ƙofa. Wani ihu da salati Hajja Fatouma ta yi a lokaci guda wanda ya jawo hankalin mutan gidan har shi kansa Modibbo da ya samu zazzaɓi ya lafamasa ya ɗan fara gyangyadi. Ba karamin gigicewa ya yi da ganin shalelan nasa a yanayinnan ba, tuni ya nemi zazzabin ya rasa balle ciwon kai, nan da nan aka kwashi Taheer sai asibiti.

***
Tun zamansu a gabansa, ya haɗe fuska kamar bai taɓa dariya ba. Ba abinda ke mishi yawo a idanu sai irin cakumar da Hajiya Zeenatun ta yi mishi a haɗuwarsu ta ƙarshe kafin wannan. Yanzun tsabar makirci ita ce gabansa har tana kuka da neman gafararsa. Ya yi wani shu'umin murmushi mai nuni da cewa sai ya rama. Kwanaki can ya yi mata aikin da bai yi tsammanin za ta warke da wuri har haka ba, don haka zai mata wanda kaf dukiyar da ta ke taƙama da shi sai ya tarwatse.

"Shikenan, na ji ya wuce. Sai dai ina mai gargadinki akan kar ki kara yin gangancin da ki ka yi gareni a baya."

Hajiya Zeenatu ta kalli Hajiya Batool suka sauke ajiyar zuciya kusan a tare kafin su dubeshi da fara'a.

"Ranka ya dade Gora, ba zan kara ba ko giyar wake na sha saboda na ga abinda na gani bayan na kaurace maka."

'Kaɗan kika gani, yanzun za ki ga fiye da hakan. Gora ba ya yafiya, ba ya mance sharri.' Abinda ya fadi kenan a ƙasan ransa daga nan ya ɗan bubbuga ƙasa kamar gaske, can ya dago ya dubi yanda duk suka kwalalo idanuwansa da fatar duk ta tattare saboda girma ya ja, a ransa ya ce tsoffin banza kawai. A fili kuwa ya yi wata arniyar dariya wanda gaba daya hankalinsu ya kwanta.

"Ai wannan auren ba inda zai je, zan miki aikin da shi yaron da kansa zai tattaro ya dawo wajenki, ita kuma yarinyar zan mata aikin da za ta shiga bariki ya daina ganinta da daraja. Hakan ya yi?"

Wata dariya Hajiya Zeenat suka sanya har da tafawa ita da Hajiya Batool.

"Gora mai gayya mai aiki! Shiyasa duk inda naje sai na dawo gareka nake ganin daidai a lamuran rayuwata (Allah Ya ganar da masu hali irin naki). Hakan ya yimin daidai, dama nafi tunanin kamun kan yarinyar ne ya rinjayi Hussein ban da haka ban ga wani kyau a tattare da ita ba. Na ba ka wuƙa da nama."

Ya yi dariya.

"Hajjaju kenan, sai dai wani hanzari ba gudu ba, aiki ne mai tsauri domin sai na haɗa da tattaunawa da Sarkin bakaƙen aljanu, kinga kenan sai an yi zubar jini na dabba da jaririn mutum kafin a cimma yiwuwar aiki. Don haka aikin zai kama miliyan biyar."

Hajiya Batool ta kalleshi a hargitse kafin ta dubi Hajiya Zeenatu, ta ga alamar ko a jikinta. Asalima ba ta sani ba, yanda Hajiya Zeenatu ke ji a yanzu ko don ta dauki fansa, za ta iya kashe ko nawa ne domin hankalin Hussein ya karkato gareta karo na biyu kuma wanda ta ke fatan ya zama na mutu ka raba.

"Na shirya, na shirya ba da koda duk abinda na mallaka ne muddin Hussein zai dawo gareni."

Gora ya ji kamar ya daka tsalle, shakka babu ya samu kudaden nan zai gudu ne ya bar garin a nemeshi a rasa, dama har yau shi kansa bai san asalinsa ba, daga almajiranci ne ya zama gawurtaccen Bokan Mata. Zai sauya ƙasar gaba ɗaya ya je ya kama wata sana'ar mai kauri. A fili kuwa cikin dakiya ba tare da ya nunamata komai ba ya amsa.

"Shikenan, sai na jiki."

Daga nan ya karkata ga Hajiya Batool, itama dai Miliyan Biyu ya nema, nan da nan ta hau zufa sai dai shaiɗan wanda ya kaɗamata ganga da kuma taimakon zigar Hajiya Zeenatu ta yarda ta kuma amince za ya san abin yi. Da wannan suka rabu akan nan da kwanaki uku za su dawo su damƙa masa kudaden da ya bukata.

A ɓangaren Hajiya Zeenatu, ta yanke siyar da A&Z ga wani hamshaƙin matashin ɗan kasuwa wanda ya jima yana muradin wajen yana son ya ƙara ƙawatashi ya haɗa da filinsa da ke a gefen wajen ya gina Park na wasan manya da yara ma. Amma fir a lokacin ta ƙi yarda bisa shawarar Hussein da ya ce ba hannunsa idan ta yi hakan. Yanzu kuwa ta shiryawa hakan. Dama a yanzun shagonta na siyar da gwala-gwalai da manyan fashion ya ja baya don ta jima ba ta fita Dubai siyayya ba hakanan ba wani balance na kirki Manajan wurin ke kawomata ba. A ranta ta kudurta siyar da shagon ta bude babban boutique na kayan jarirai da na yara.

***
"Damuwa ce ta ke neman illata tunanin yaron, sai kuma yunwa da ke dawainiya da shi wanda ya haddasa masa jiri. Muna tsoron kamuwarsa da hawan jini, don haka don Allah Baba a yiwa yaronnan abinda ya ke so."

Wannan bayanin na Likita ya kara ɗaga hankalin Modibbo. Gumi ya shiga tsastsafowa daga goshinsa. Yan da labarin komai daga bakin Uwargidansa, yana da labarin cewa soyayyar Hafsatun Dada ke dawainiya da kwakwalwar Taheer. Bai san kuma ta inda zai soma magancewa ɗansa matsala ba don shi da kansa kunyar zuri'ar Dada ya ke ji. Ga yan uwansa sun juyamasa baya, kowa ya yi tirr da baƙar zuciya irinnasa da ba ta iya yafiya ba alhalin ma tun asali ba abinda Amina da Aminu suka aikata garesu, bisa tunzurawar Innarsu ce ta sa suka tsangwamesu. Haka ya amsawa Likita da cewar zai bincika damuwar Taheer sannan ya mike ya fita. Su Anti Amarya da ke tsaye suka zubamasa idanu har ya shiga ɗakin da aka kwantar da Taheer. Bacci ya ke sosai, ya zauna gefen gadon ya tsuramasa ido.

"Ta ina zan soma yi maka maganin matsalarka alhalin nima ina da tarin laifuka a wurin bayin Allahnnan? Ka yafemin, ka bar ni na soma zuwa na gyara nawa ɓarnar kafin a yi maganarka."

Ya furta cikin harshen fulatanci, shi kadai ya ke zancensa don Taheer bai ma san yana yi ba, a karshe ya mike babu kuzari ya fice daga asibitin gaba daya ba tare da ya cewa matansa da yaransa dake wurin komai ba.

***
ADAMAWA...

Wankan da ta yi na musamman ne a daren ranar talata, ba don komai ba sai don sanin da ta yi Hussein babu alamar sassauci a ƙwayar idanunsa. Ya lura da sallolin da ta yi a ranar, wannan ya sanya ya ke faman rawar ƙafa. Koda ya fita, zuma ta dauka ta sha sosai bayan ta wuni a ranar tana kama ruwa da ruwan ɗumi. Idan da sabo har ta saba don zai wuya ka ga Ramlatu na amfani da ruwan sanyi a wannan wuri.

Kayan baccin ma da ta sa na musamman ne, riga da dogon wanda marasa nauyi. Rigar mai hannun vest sai top dinta mai dogon hannu. Babu wani underwear da ta sanya a ciki. Ta tabbatar daga kallo ɗaya Hussein ɗinta ba zai iya dauke kansa ba. Duk da Top din rigar da ta ɗora hakan bai hana komai bayyana ba. Ta ƙara mulke jikinta da turare, sai da ta kammala ta tabbatar babu inda ba ya tashin ƙamshi a jikinta sannan ta fito falon inda ya ke zaune ya maida hankali ga danna Laptop, AlHassan yake aikawa credentials dinsa ta email kamar yanda ya buƙata. Koda rashin haske a falon, hakan bai sa hasken tv gaza haskakamasa ita ba. Ya nemi nutsuwarsa na ƴan sakanni amma ina! Sun yi hannun riga, kawai sai ya tsinci hannunsa da rawa, ba don Allah Yasa ya kammala aikawa ba to shakka babu zai haɗa da shirme. Har ta karaso ta zauna a nesa da shi kaɗan bai iya ɗauke kai ba, ba tare da ya tunanin saƙon ya je ko bai je ba, ya kashe Laptop din kawai ya rufe. Mikewa ya yi ya kashe tv, sannan ya karaso, lalubo inda ta ke kawai ya yi ya ja ta jikinsa. A haka ya karasa dakin da ita.

***
WASHEGARI..




I just published "BABI NA SITTIN DA UKU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1026513798?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=zZAfOdew2I80pQK%2B2VbvDQ7XLS4cczmz2oO62oVfO8o7sJbUSeKCeiRU7BICDOiu5Jd2MMKmIVdOPNPwwdQQ7sH8y4fVopayPcwrbHPyKEry%2FHqkikgjsm5msqZ9wmV%2B




🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

63)


A hankali ta ji ana masa susa a cikin kunne. Ta buɗe idanun tarr tana dubansa, ga dukkan alamu alwala ya yi.

"A tashi a yi sallah."

Ta gyaɗa kai tana sakar mishi murmushi, miƙar da ta yi ya sanya shi kaucewa da ɗan sauri-sauri  ya fice daga ɗakin gudun maimaici. Ta mike tsaye ta shiga bandaki, can kuma ta fito bayan ta wanke baki ta kuma  ɗora alwala. Dolenta ta koma ɗakinta ta ɗauki zani da hijab, anan ta shimfida darduma ta yi sallar, sai da ta yi addu'a mai tsawo tana roƙarwa mijinta dukkan wata rahma da alheri kafin ta gangara ga iyayenta da kuma yaranta. A karshe ta kara nemawa Aliyu da Kakarsa gafarar Ubangiji da ma dukkan musulmai, wannan ya zamemata kamar farillah duk bayan kowace sallah.

Tana ninke hijabin tana murmushin tuna daren jiya, a karon kanta ta gama saddaƙarwa son da Hussein ke mata ya ninka ya kara ninka wanda ta ke mishi. Wasu kalaman ma da ya dinga furtawa, ita da kanta idan ta tuno jin kunya ta ke, amma ta san da yake shi din namiji ne, ko a yanzun zai iya maimaitawa. Sai kuma ta yi ƴar dariya kaɗan, ita kaɗai ta san me ta tuna. A ƙasan zuciyarta ta furta kalmar hamdala. Ta shagala cikin tunani don tuni ta kammala ninke hijabin ta koma kan zanin da ta ɗora. Ba ta ji shigowarsa ba, sai jinsa da ta yi ya jawota jikinsa ta baya, ya ɗora wuya saman kafaɗarta.

"Good morning."

Ya faɗi da muryarsa da ke hargitsata. Ta lumshe idanu tana tuna irin laushin da sumar kansa ke da shi sadda ta yi mishi riƙo son ranta.

"Ina kwana, fatan an tashi lafiya?"

"Idan na ce ban tashi lafiya ba, na yi karya. Na samu farin cikin da ban taɓa tsintar kaina cikinsa ba, na kuma  yi baccin da ɓata lokaci ne tsayawa misalta daɗinsa. Kece rayuwata Ramlat, na yarda ba zan iya rayuwa da kowace mace a bayanki ba. Ba alƙawari nake daukar maki ba, kamar yanda ba da alfahari nake faɗin haka ba, abu ne da nake ji a jinin jikina. Yanayi ne da na tabbatar ke za ki fahimta. Ina miki son da babu rabuwa. A shirye nake da yi maki dukkan abinda zai faranta ranki. A yau ni Hussein na ba ki wuƙa da nama, ki yanka iyakar yanda ki ka ya yi maki, ki faɗamin burinki a duniya, da yardar Allah koda ya fi ƙarfina zan ƙoƙarta yi maki shi. Ban san farin cikin da ke cikin auren budurwa ba, amma ina da yaƙinin ba za su kai min ke ba."

Ya na maganar yana kai hannunsa duk inda ya so. Ta gama shagaltuwa da wani irin sonsa, tana ji a yanzu haka numfashinta na shige da fita ne da so da kaunar Hussein, ba ta san sadda ta juyo ta zubamishi dara-daran idanunta ba wanda ke ƙara tsumashi, kamar yanda duban nasa lumsassun idanun ke tarwatsa tunaninta har ta rasa kalar wanda za ta yi. Sai dai a wannan karon, a yanzun, a kuma wannan rana, ji ta ke ta samu kwarin gwuiwar kallon abin kaunarta tsakar ido, ba kuma don jin raini ba, aa, babu wannan tsakaninsu har abada sai wani irin kauna da ta ke jinsa daga ƙasan zuciyarta. Ba ta san lokacin da hannuwanta ya sauka saman fuskarsa ba kamar yanda ba za ta tuna sadda ta ɗora leɓɓanta bisa nashi ba. Hussein ya ji kalar soyayyar da bai tsammaceta nan kusa ba, bai ɗauka za ta miƙa masa wuya har haka ba, sai da tsayuwa ta nemi gagararsu duk kuwa da irin riƙon da ya yi mata ba na wasa ba kafin ta samu ta daidaita kanta ta rungumeshi. Daidai saitin kunnensa ta shiga magana tamkar mai raɗa.

"Kai ne burina, bani da sauran burin da ya wuce kai. Ka zame min wani jigo babba a rayuwata. Soyayyarka da kulawarka su kaɗai ne abin buƙatata. Koda nayi soyayya a baya, ban ji abinda nake ji a kanka ba, ban kuma samu farin ciki kwatankwacin wanda nake ciki a kwanaki ƙalilan da nayi tare da kai ba. Idan har za ka riƙe ni da amana, ni Ramlat zan zame maka tamkar raƙumi da akala. Dama ni ce a ƙasanka, muddin rai, zan maka biyayya. Ba zan ketare ɗaya cikin umarninka ba, wannan shi ne burina. Ka tayani addu'a akan Allah Ya bani ikon cikawa."

Bai ce mata uffan ba sai janta da ya yi suka ƙara faɗuwa duniyar masoya.

***
   BAYAN KWANAKI UKU..

  KANO.

A hankali ta shiga fiddo bandir-bandir na dubu ɗaya daga cikin ƙatuwar ledar da ta zo da shi, Gora banda satar kallon ledar da haɗiyar yawu ba abinda ya ke yi, jikinsa har rawa ya ke dakyar ya yi kokarin tankwasa kansa. Har ta kammala ya tabbatar sun cika yanda ya ce, sannan ta mayar ledar ta miƙamasa bai ce uffan ba. Haka itama Hajiya Batool da ta tattara gwala-gwalanta ta siyar ta haɗa da siyar da motarta har ta samu suka kai milayan biyu, ragowar kudin ta adana su a banki.

Gora ya gama haɗa miliyan bakwai cif a hannunsa kafin ya kyakyace da muguwar dariya duk suka dubeshi fuskarsu a sake don sun san sun cika sharuɗɗa kuma za su ga aiki nan ba da jimawa ba. Ko ba komai su na tuna aikin da ya yi musu tun farko da suka ji dadi.

"Lallai dagaske kun shiryawa buƙatunku, toh ku sa a ranku kamar dama duk wani bala'i da ku ke gani a yanzu mafarki ne don kuwa ina mai ba ku tabbacin cewa burinku na dab da cika. Hussein zai dawo wurinki kamar yanda ita kuma matarsa za ta faɗa duniya ta lalace. Ke kuma! Ɗanki zai dawo gareki koda ace bangon duniya matarsa ta kai shi. Idan ya dawo ko a ranar ki ka ba shi umarnin ya saki matarsa, ba za ki rufe baki ba zai aikata."

Don farin ciki sai ga Hajiya Zeenatu da Batool na sakin shewa har da cafkewa. Gora ya dinga washe hakora ya kalli wannan ya kalli waccan. Can kuma ya turɓune fuska kamar gaske  ya hau magana.

"A daren yau, ni da kaina zan shiga cikin dajin Falgore, anan baƙaƙen aljanun suka yi umarnin na zartar da dukkan yankan da za'ayi na mutum da na dabba. Gobe kamar war haka, ku dawo na ba ku maganin da za ku yi amfani da shi idan suka shigo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login