Showing 186001 words to 189000 words out of 230725 words

Chapter 63 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1075

kin yi goshi wannan karon ba shakka. Allah Ya sanya alheri ya nunamana lokacin."

Ta rasa yanayin da ta shiga. Ta kasa amsawa hakanan ta kasa cewa komai don haka kawai sai ta mike ta fita tana murmushin yaƙe.

"Ayiririri!"

Guɗar da ta ji yasa ta waiga, Baba Hajara ce yayar Hajiyarsu. Su uku ne kadai mata a wurin Hajjar, Baba Hindu, Baba Hajara sai Hajiya. Mazan kuwa su uku, Kawu Jamilu, Kawu Bello da Kawu Sunusi, su ne manyan maza a ɗakin.

Jiki a sanyaye ta gaida ta kafin ta karasa ɗakin Hajja itama Baba Hajara na daga bayanta.

Hajja ce zaune tana shan fura, tana ganin Ramlatun itama ta saki fuska.

"Kishiyar ce a tafe kenan? Sannu da zuwa."

Ita dai ba ta ce uffan ba, Affan ya karasa a guje ga Hajja. Zama ta yi gwuiwa a sake kafin ta maida hankali ga Baba Hajara.

"Wai Baba lafiya?"

Baba Hajara ta zauna tana dariya, ba ta kai ga magana ba Hajja ta katse ta.

"Na rabaki, idan ba so kike tarihi ya maimaita kansa ba. Ki bari ta ji komai daga bakin Ubanninnata. Ai ba abinda zamu ce ga Dakta (Baba Dakta) sai godiya da fatan alheri. Allah Ya biyashi da aljanna. Yanda yake nunamaku kulawa kamar ƴaƴan da ya haifa a cikinsa, Allah Yasa aljanna makoma. Na ji ma ance ya kawomaku kayayyakin abincin azumi, to nan ma haka ya aikomin. Wannan bawan Allah sai fatan alheri da fatan Allah Ya jiƙan iyaye."

Baba Hajara ta amsa da amin, itama Ramlat ta amsa ta hanyar motsa lebbanta amma dukkan wata gaɓɓa ta jikinta ta yi sanyi. Can kuma sau ga shigowar saƙo. Hussein ne. Ta bude hannunta har rawa ya ke don yanzu ta kasa fahimtar komai.

_*"Ban yarda da dukkan wani so da za'a yi shi kafin aure ba. Ban kuma yarda akwai kulawar da namiji zai yiwa mace ba da za ta kere kulawar miji ga matarsa. So da kauna na gaskiya ya fi ma'ana idan aka zama mallakin juna. Ina taya junanmu murna."*_

"To wai me yake nufi?" Ta tambaya a fili bayan ta karanta ya fi sau biyar amma ba ta gane komai ba.

"Wa kenan?" Hajja da Baba Hajara har suna haɗa baki wajen tambaya. Ta ma kasa cewa uffan sai kai da ta girgiza tana sharar gumi ga kwalla cike a idanunta.

"Idan ma za ki saka ranki a inuwa tun wuri gwara ki sanya don wannan karon na tabbatar wanda za ki aura ba fetur ba, Allah Yasa tankin mai gaba daya za ki zazzaga maku, zai yarda ku mutu ƙurmus! Sawun giwa ya take na raƙumi!"

Hajja ke wannan sababin ta karashe da kurɓar furarta ta bar Baba Hajara da dariya. Ita dai Ramlat ba ta ce komai ba sai hawayen da ta shiga sharewa, gaba daya gaɓoɓin jikinta sun yi sanyi, yanzun kuma abin haushi ya ke bata.

"Yaya Ramlatu ki zo inji Kawun Zaure."

Wato Kawu Jamilu kenan wanda shi hanyar shiga sashinsa na daga wurin zauren gidan, ai ba ta ma jira Hauwa diyar Kawu Sunusi ta karasa faɗin saƙon ba ta yin zumbur ta miƙe tsaye har wayarta na faɗuwa amma ba ta ko damu da ɗauka ba. Tana ji Hajja na fadin.

"Kuma yarinya ta dawomin daki da baki kamar gonar auduga sai na yi ƙasa-ƙasa da ita. Maza Affan bani wayarnan idan mijinnamu ya zo sai ya siyamata wani."

Tana jin dariyarsu amma babu wanda ta tanka asalima baki ta turo ta ɗan ja guntun tsaki tsabar ɓacin rai. Haka ta dinga tafiya har sashin Kawu Jamilu, duk a zatonta shi kadai ne, sai ganin sauran Kawunnan da ta yi zaune ƙasan bishiya suna taɓa hira. Ta karasa gami da durkusawa ta kwashi gaisa. Suka amsa fuska a sake duk da cewar kanta a ƙasa yake amma sautinsu ya nuna hakan. Sai da aka gama gaisuwar da ɗan barkwanci kafin Kawu Jamilu ya yi gyaran murya ya soma magana.

"Toh Ramlatu, abu na farko shi ne mu miƙa godiyarmu ga Ubangiji domin Shi ya yi mana dukkan ni'ima. Ya kuma so ki da dukkan rahma da mu ɗin gaba ɗaya. Alhamdulillah."

Ya ɗan ja numfashi gami da gyaran murya sannan ya ci gaba.

"Kamar yanda ki ka ji daga bakin mutanen gida, abin alheri ne ya sameki. Babanki Dakta ya yi maki zaɓi bisa damar hakan da kika damƙa maki. Kar kuma hakan yasa ki yi zaton cewa shi da kansa ya haɗa auren, aa, shi yaron ma asali tun ana zancen aurenki da Dikko ya tunkari Baba Daktan da batun aurenki sai dai Baba Daktan ya ba shi hakuri ya kuma sanarmasa da batun Dikko, a karshe ya yi mishi kwatancen gidannan ya ba shi lambar wayar Kawunki Bello cewar yana iya zuwa nan wurinsa ya faɗamasa ko Allah Zai sa a dace. Da yake shima yaron nada hankali ya ce aa babu komai, ya yarda Allah bai kaddara ke din rabonsa ba ce. Ba ya son ya yi nema cikin nema. Wannan ne dalilinsa na janyewa bayan ya nemi alfarmar su bar maganar tsakaninsu. Yanzun ma da kika ji, magana ce ta kawo magana shiyasa ya faɗamana shi Babannaki. Sai kuma cikin ikon Allah lamarin aurenki da shi Dikko ya lalace, anan ne kuma bayan kin bar wuƙa da nama a hannun Daktan, ya ba wancan yaron iznin turo nashi magabatan bayan shawarar da ya yi da mu kuma muka amince. Alhamdulillah, Ramlatu ke ba yarinya ba ce, mun kuma sani, yanzun kin fi baya hankali. Kin kuma ƙara hankaltar rayuwa. Mun sani, wannan karon ba za ki ba mu kunya ba in sha Allahu."

Zufa sosai ta ke fitarwa, ta hadiyi miyau mai ɗaci, ba ta bar ambaton Innalillahi a ƙasan ranta ba har zuwa sadda Kawu Jamilu ya miƙomata damin kudi ƴan ɗari biya-biyar a baƙar leda bayan ya warware ledar ya turo kudin gabanta.

"Wannan ne kudin aurenki, dubu ɗari gashinan. Juma'a mai zuwa cikin yardar Allah za'a ɗaura aurenki da HUSSEINI MODIBBO. Ina ce haka sunan yake ko?"

Ya karashe yana duban yan uwansa da dariya, suka dara lokaci guda.

"Hakayake Yaya." Kawu Sunusi ya bada amsa.

Ta rasa me za ta ce, ta kuma rasa me za ta yi, a zaune ta ke amma jiri ta ke ji. Kanta ya yi wani irin sarawa, lokaci guda ya shiga ciwo. Hawayen da ta tsayar a ɗazun, suka ci gabada kwaranya su na ɗiga saman k
rafar ɗari biyar biyar din da Kawu ya ajiyemata. Wa ya faɗamusu sonta yake?




I just published "BABI NA HAMSIN DA SHIDA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1017117739?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=NPwmUPq5q%2BNDXCvudnu9VtPx9xZ93DXS%2BXNO4Gp8IGMT8cs%2FH9GyIFlv%2Fhb%2BKgVVkXrnM1fZVi41cUdjwyw1cEK3IG5H1c7vZKRmCwE0POba10BIvSct65MXWSFYf6%2Fz






🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️

_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

56)


'Me yake nufi da ni?' Ta jefawa zuciyarta tambayar da nan da nan ta samo amsar da ta ji wani mugun ɗacinsa. Hussein na nufin ra'ayinta ba komai ba ne, yana nufin koda ba ta sonsa ta rayu da shi. Ko kuma dai daga saƙon da ya turomata yana son ta fahimci ya gane tana sonsa amma ya dinga basarwa. Nan da nan ta ji wani haushinsa ya mamaye zuciyarta. Ta ci alwashin sai ta rama abinda ya aikata gareta, ba za ta taɓa yin musu a aurensa ba, amma ta rantse sai ya gane shayi ruwa ne.

"Allah Yasa hakan ya zamemin alheri." Ta ba Kawu amsa a hankali, gaba daya suka amsa da amin cike da jin dadi. Suka sanya mata albarka a karshe suka sallameta. Mikewa ta yi bayan ta share hawayen yanda ba za su gani ba, ba tare da ta ɗau kuɗin ba ta bar wajen. Kawu Sunusi zai magana Kawu Jamilu ya katseshi da zummar za su damƙawa Hajiya.

Ba ta wani jima cikin gidan ba ta yi musu sallama sai dai ba su fahimci komai ba don ta ɗan saki fuska kamar ba ita ba.

Koda ta koma gidan, ba abinda ta nunawa Hajiyarta. Wannan ya kwantar da hankalin Hajiyar don dama tun fitar Ramlatun ta ke cikin zullumin ta yanda za ta karɓi lamarin.

"Idan kin sauya kayan sai ki fito mu shiga kicin, na fadamaki yau Hassan zai shigo a gaisa."

Maganar Hajiya ta katse yunkurinta na shigewa ɗaki da ta yi niyya, ta juyo ta amsa da toh bayan ta haɗiyi miyau mai ɗaci.

***
Hajiya Zeenatu ta shigo falonta gaba daya jiki a sanyaye, likita ya duba ta amma ya ce bai gane komai ba, karshe aka haɗata da tests kala-kala akan ta yi ta kawo sakamako a gani. Ranta gaba daya a jagule ga wani jiri-jiri da ke ɗibanta. Turus ta yi ganin mutum zaune a falon. Ta daure ta shigo da fara'ar da bai kai zuci ba. Suka dubeta gami da amsa sallamarta.

Hussein ne fuskarsa cike da wani farin ciki sai AlHassan dake zaune yana amsa waya Madam dinsa Kausar, ganinta yasa shi yin sallama da ita.

"Ah, ɗan uwanmu zuwa babu sanarwa?"

Ya yi murmushi, sai yanzun dai ya zo gidan dan uwannasa don haka ba su hadu da Hajiya Zeenatun ba sai a yau, amma a Hotel ya sauka tare da Kawunsu Adamu wanda shi a yau da safe ya juya ya kama hanyar Adamawa.

"Hajjaju, Allah Ya huci zuciyarki. Nima zuwan ne ya tasomin babu shiri. Aiki na zo yi daga kamfaninmu na can. Ko shi Ogannaki haka ya gan ni babu zato ba tsammani."

Ta yi dariyar yaƙe gami da satar kallon Hussein da ya ɗora ƙafa ɗaya saman kujera hankalinsa ya koma kan waya yana zabga murmushi.

"Hakan ma ai daidai ne. Dama kuwa ina da saƙon da zan bayar a kaiwa Ɗiyata. Gwara da Allah Ya kawoka."

Ya yi dariya yana gyara zaman gilashinsa.

"Ba ki da matsala. Tana godiya."

Daga haka ta maida duba ga mijinta.

"Yallaɓai barka da hutawa."

Ta fadi da wani irin shagwaɓa wanda ya ba AlHassan dariya, sai dai ya haɗiye kawai ya miƙe.

"Bari na ɗan amsa waya." Yana kaiwa nan ya fice zuwa farfajiyar gidan, wannan ya ba Hajiya Zeenatu damar ƙarasowa ta zauna gefen Hussein. Ya ɗan dubeta da kulawa.

"Ya jikin naki?"

Cike da damuwa ta karya wuya.

"Likita ya duba ni, ya ce  ba zai gane taƙamaiman matsalar ba sai an yimin gwaje-gwaje.  Yanzu dai haka ya ban gwaji zuwa gobe zan koma mu gani. Amma na fi kaunar na hakura idan mun je London sai a yimin magani sosai."

Ya gyaɗa kai yana murmushin da ke ƙara tafiyar da imanin Hajiya Zeenatu a kansa.
  
"Saurin me ki ke? Ita lafiya ta fi komai ai. Ki kwantar da hankalinki. Tunda har kika ga na dakatar da aiki toh hakan na nufin na shirya koyaushe ne ma mu bar ƙasar. Abinda ya fi yanzu ki je goben ki yi gwaje-gwajen har a gano matsalar a shawo kanta. Gwara ki ɗan samu sauki sai mu wuce.  Amma fa sai mun fara biyawa Adamawa kinga su Dada kun gaisa."

Ko ɗarr ba ta ji ba, a wautarta gani ta ke har a sannan babu wanda ya gane da hannunta a ɓatan Hussein.

"Yanda ka tsara hakan za'a yi Ranka ya daɗe."

Kauda kai kawai ya yi bai ce uffan ba, ta mike ta haye sama. Ya bi bayanta da kallo, sai kuma ya yi murmushin mugunta. Shi kadai ya san me ya bar wa zuciyarsa. Tabbas sai Hajiya Zeenatu ta kusa haukacewa idan ta gano taƙamaiman shirin da ya ke yi.

Wayarsa dake ringing  ya duba. Hisham ne. Murmushi ya yi don ya san labari ya isa kunnensa.

"Kai dan iska ne fa! Wai me nake ji daga bakin My Princess? Dagaske kai ne ka kai kuɗin auren Ramlatu?"

Lumshe idanu ya yi, sunanta kaɗai idan ya ji sai tsigar jikinsa ya tashi. A hankali ya shafi sumar kansa.

"Mamaki ka ke yi? Ba haka ka ke so ba?"

Dariya Hisham ya yi.

"Haka nake so, sai dai ka rainamin hankali fa. Zan rama amma. Kar ka yi tunanin zan tayaka campaign."

Taɓe baki Hussein ya yi kamar yana kallonsa.

"Campaign after marriage? Ni zan yi abina dama."

Hisham ya ɗan dara don shi abin kam dadi ya yi mishi ba kadan ba. Addu'a ya yi da fatan alheri. Hussein ya amsa da amin kafin su yi sallama. Agogo ya kara dubawa, da sauran mintuna a kira sallar Magriba. Ya ƙagu ya ganshi a gidan su Ramlat. So ya ke ya sanyata a idanunsa. Bai zaci za ta ga saƙonsa ta shareshi ba, abin ya ba shi mamaki. Hakan yasa ya ke son zuwa ganinta da kansa.

***
Kawu Modibbo rai a ɓace ya ke amsa wayar ƙaninsa Adamu.

"Me ya kawoka Kano? Wato Adamu har wuyanka ya yi kaurin da za ka shigo inda nake ka kasa nemana? Idan kuma aka yi magana sai ka nuna ka fi uban kowa riƙon zumunci ko?"

Kawu Adamu da mamakin yanda Modibbo ya san da zuwansa garin Kano ya ba da amsa ta wayar.

"Wa ya fadamaka na je Kano?"

"Ɗanka Yahaya muka yi waya ya cemin ka shigo Kano tare da Hassan. Ko karya ya ke yi?"

Ganin yanaamsawa a zafafe ne yasa dole Kawu Adamu ya sauko ya shiga bada hakuri da fadin.

"Wani ɗan uzuri ne ya shigo da ni, kuma shigowar ta gaggawa ce shiyasa ban samu na karaso ba. Amma ayi hakuri don Allah."

Kawu Modibbo ya yi shiru, can kuma ya ce.

"Wane uzuri ne haka?"

Har Kawu Adamu zai ba shi bayani sai ya tuna roƙon alfarmar da Hussein ya yi mishi akan cewar ba ya son Kawun ya san da batun aurensa. Bai faɗamasa dalili ba ko ba komai dai ya sani Kawun bai kaunarsu, amma shi kuma ya ce ba komai zai mishi wannan alfarmar.

"Daurin auren wani ɗan abokina ne ya kawo ni."

Kawu Modibbo ya ji sai dai bai yarda ba, maimakon ma ya ci gaba da sauraronsa kawai sai ya yanke wayar. Shiru ya yi yana tunani, ɓacin ransa na ƙara ninkuwa. Yanzun ya lura yan uwansa da wadanda ma suka tsani Amina da Aminu a baya da kuma wadanda dama ke sonsu, duk sun hada kai, shi aka ware. Wani bakin ciki ya ji a ransa, karshen satinnan zai tattara ya je Adamawar tunda akwai bikin yar gidan ƴar uwarsu, Gwaggo Karime. Tunda gaba daya za'a hadu, zai kara zaman meeting da yan dakinsu ya ji dalilin wannan sabon sauyin.

***
Bakwai da mintuna, Ramlat ta hada lafiyayyen friedrice da gashin kifi wanda a gefensa ta soya dankali ta saka sai sauce. Ta yi zoɓon da ya ji kayan kamshi ta sanya a firij. Sosai ta saki jikinta musamman wayar da suka yi da Amrah ta kara ba ta shawarar yanda za ta tafiyar da Hussein har ya fahimci shayi ruwa ne.

"Sannunki, sai a je a kimtsa jiki. Allah Ya yi albarka."

Ta juya bayan ta dora komai saman tebur, ta dubi Hajiya da ke fitowa daga ɗaki. Murmushi ta yi kawai ta kauda kanta. Ita kadai ta san me ta ke kissimawa a zuciyarta. Kwafa ta yi don gani ta ke komai ma za ta iya kawai don Hussein ya fahimci ya ƙuntata mata.

Maimakon kimtsawar, sai ta zube saman gado, wayarta ta jawo. Missedcalls har uku duk daga Baban Hanif. Kafin ta gama shanye mamakinta sai wani kiran ya kara shigowa. Ta ɗaga da sallama, ya amsa.

"Allah Ya huci zuciyarki Maman Affan, ina ta kira an ƙi a saurare ni ballantana kuma a yimin uzuri."

Ta mike zaune.

"Ka yi hakuri, ba haka bane. Ba na kusa. Ina wuni ya gida?"

"Lafiya kalau. Babu damuwa, na yi."

Shiru ya ɗan biyo baya kafin ya ɗora maganar.

"Na so maganar da zan maki ya kasance gani ga ki, amma ba na tunanin yanzu ina da wannan ikon na zuwa kofar gidanku. Da farko ina mai ba ki hakuri bisa dukkan wani abu da ya faru a dalilin aurenmu. Na yarda haka Ubangiji Ya tsaramana. A gaskiya Ramlatu, tun fara zancen aurena da ke, iyayena suka dakatar da ni bayan bincikensu yasa sun binciko tarihinki. Sun kuma gane cewar aurenki biyu ba kamar yanda ki ka fadamin cewa aure daya ki ka taɓa yi ba. Duk da labarin aurenki na farko da aka ban, hakan bai sa na gwuiwata ta sare ba. Na ci gaba da zuwa wurinki, idan ba ki manta ba, kin sha tambayata meke damuna, na ce maki ba komai. Wallahi wannan shi ne dalili."

Ya ɗan tsahirta, itama ba ta ce komai ba don dama ta san hakan kan iya faruwa, sai dai ba ta zaci za ta ji zafin abin har haka ba.

"Kina ji na?"

Ya tambaya, ta amsa da Uhm. Sannan ya ɗora.

"A takaice dai, wancan dalilin shi ne yasa iyayena suka ce sam ba da yawunsu ba muddin na aureki. Ina kokarin shawo kansu ne sai ga kira daga Kawunki (Baba Dakta), ya yimin maganar turo magabata, na ba shi bayanin halin da ake ciki. A karshe ya nuna ya kamata na hakura tunda har iyaye ba su so. Koda an yi ba dadinsa za'a ji ba. Amma wallahi Ramlat ina sonki. Ba yanda..."

"Karka damu, komai ai nufin Allah ne. Allah Bai kaddara zan zama iyalinka ba. Mu bar shi a haka. Allah Yasa ya zamemana alheri."

Ajiyar zuciya ya saki har tana jin hucinsa kafin ya amsa da amin. Daga nan suka yi sallama tare da yiwa juna fatan alheri.

Ta kurawa wayar idanu cike da tunani, kenan wai wannan abu da ta kusan aikatawa har ake fasa aurenta dominsa, da ace ta aikata yaya kenan? Nan da nan ta ji kwalla ta cicciko a idanunta. Da yanzun tana cikin yanayi irin wanda Halima ta tsinci kanta, da yanzu ita an ma kashe ta. Tausayin Hilal da ya fadomata a rai ta ji, rabonsa da Kano yanzun wata kusan biyu kenan. Tun sadda ya zo ya yi musu sallama akan ya samu sauyin wurin aiki zuwa Benue ba su ƙara jinsa ba sai jefi-jefi idan ya samu hawa online a whatsapp sukan gaisa.

"Uncle oyoyo!" Muryar Ansar da Affan ta ji daga falon, wannan ya nunamata cewa Hussein sun shigo din kenan. Ta mike ta shinshina jikinta, gaba daya kamshin girki ta ke yi, dolenta dama ta yi wankan ko ba don shi ba don haka sai ta rage kaya ta ja zanin wankanta ta fada bandakin.

Bayan ta fito ta shirya tsaf cikin doguwar rigarta na material, ba ta shafa komai a fuskarta ba, shimfida darduma ta yi ta zura

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login