Showing 225001 words to 228000 words out of 230725 words

Chapter 76 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1053

so da kaunarsu ya ke ji na musamman a ƙasan ransa har yake ji inama daga jikinsa suka fito. Ya yi amannar son da ya ke musu, ko mahaifinsu sai hakan. Ramlat kuwa banda murmushi ba abinda ta ke yi, ganinsu tare na karamata annashuwa.  A ranar dai da kansa ya ce ta kwanta tare da yaran, ya tabbatar ta yi kewarsu.

Washegari aka shiga cikin biki, komai ya tafi cike da tsari. Ranar babu batun anko don kowa kayansa ya sanya, a rana ta biyu ne suka gudanar da yini da rana wanda kowaccensu ta sha ankon atamfa har su Aisha mutan Kano, don tun kafin su zo Ramlat ta aikamusu hoton ankon suka ɗinka.

Tun soma sabgar biki ba ta da wani lokacin kanta balle kuma na Hussein, hira ta ragu sosai a tsakaninsu. Sai dai ta kai mishi abinci, zaman da za ta yi wurinsa bai fi na mintoci ba. Wannan abu ya kai Hussein bango, gaba daya ma sai ya daina bari su haɗu. Da daddare idan ta leƙo, ya rufe kofar gam, da safe kuwa duk irin sammakonta ya fice daga gidan, waya kam  ko ta kira bai ɗagawa. Text na duniya ba ya kulata, sam ya kasa yi mata uzurin tana da baƙi kuma su na hidimar biki. Wannan damuwar ta sa a ranta, shiyasa ko ranar da ta kama na dinnerparty, kasa wani kataɓus ta yi. Tana zaune tana kallon kowa na shiryawa, maganar duniya su Zulaihat da su Kausar sun mata akan ta tashi ta shirya amma ta ce sam ta fasa.

"Adda Amal kina cewa ba za ki je ba, ga Hamma Hussein can ya ci uban kwalliya ya fita, kuma wallahi idanun ƴanmatan nan kamar su tsiyaye tsabar kallonsa."

Jin abinda Falmata yar uwar su Hussein ta Maiduguri ta fadi, ai sai Ramlat ta mike tsaye ranta na susa. Nan aka kwashe da dariya, har itama ta murmusa.

"Kishi kumullon mata, ki zauna dai kar ki je. Wallahi sai dai ki ji ana wani labarin."

Ita dai Ramlat ba ta biyewa zancen Rafee'ah ba ta shiga bandaki bayan ta rage kayan jikinta, tana ji su na mata dariya. Wanka ta ƙara yi duka rabin hankalin na ga tunanin Hussein, abinka da zuciya, sai nan da nan ta ji itama ai ya mata laifi, ta ji ya bata haushi sosai. Kwafa ta yi tana ƙara cuɗa sabulu a jikinta, aikuwa ta ci alwashin itama ko kallo bai isheta ba a wurin taron. Ta fito ta shirya, da yawansu sun fice har su Rafee'ah da maman Twins.  Aisha da Falmata da kuma Asma'u diyar Hajja Fatuma uwargidan Modibbo sai wata Hannatu itama daga Maiduguri, su ne kadai suka yi zaman jiran Ramlatun don su wuce a motarta.
   Leshinta da suka yi anko kalar milk kai adon golden brown ya yi masifar sama a jikinta, ya sha aikin stones shi ta fiddo ta zura. Falmata ta yi mata make-up na fitar hayyaci, kasancewar kwalliyar zamani mai kama da na aljanu bai damu Ramlat ba don ba irinsa ta fi yi ba, sai ta fito ta yi wani azababben kyau. Daman su Rafee'ah  yanda suka ga  ta sauya fatarta ta kara kyau da sulɓi yasa suka dinga yi mata zargin  mai ciki, ita kanta sauyawar na ba ta mamaki.

"Wallahi na fadamaki wani abu? Nidai ba ki taɓa kyau irin na yau ba, ko bikinki albarka."

Aisha ce ke maganar tana dariya,  harararta Ramlat ta yi ta ja guntun tsaki ba ta ce komai ba, wannan duk abinda ta yi ɗanawa Hussein tarko ta ke son yi yanda zai yi dana sanin wannan fushin da ya ɗauka da ita. Har tunani take ko wa ya sanya a gaban mota suka tafi? Nan fa ranta ya ƙara sosuwa. Ta mike ta yafa mayafinta golden ta dauki purse dinta mai kyalli shima golden, turare mai sanyin ƙamshi ta fesa kafin ta zura takalminta da ya kasance mahaɗin purse din, ta dauki mukullin motarta. Kuɗin liki kam dama tuni sun tsufa a cikin ƴar jakar don tun safe suka bada aka yi masu chanji kowacce ta adana abinta.

"Muje." Ta basu umarni, duk suka fito ta rufe ko'ina na gidan. Su Ummi na sashen Dada da yara ana ta wasa don yanzu ba su fiye wani kewar uwartasu sosai ba balle su liƙe mata.

Tana tuƙin amma fuskar ba wawalar a zo a gani musamman da ta ga dagasken dai babu motar Hussein a farfajiyar gidan. Aisha ta karanceta tsaf, ta san kishi kawai ke cin ƴar uwarta don haka ta bar janta da hira ta maida akalar hiran ga su Falmata dake zaune a baya haka har suka isa ƙayataccen ɗakin taron na FARHAS Event Centre (Dan Adam).

Farfajiyar wurin sai ɗaiɗaikun jama'a, sai da duk suka fita, sannan ta bi bayansu. Aisha ko jiranta bata tsaya yi ba don ba ta son a huce a kanta. Ta na takunnan mai girgiza zuciyar masoyinta kuma mijinta, wanda ya zama normal tafiyarta. Haka ta ƙarasa har ta shiga ciki. Wuri fa ya cika, gaba ɗaya kowa na zaune ana kallon MC wanda ya fiddo Amare da Angwayensu tsakiya yana basu umarnin zama saman wasu kujeru a tsakiyar wurin, wannan yasa hankalin da dama suna kansu ana dariya a nishaɗance. Sun haɗa ido, sai ta dauke kai kamar ba ta ganshi ba, wani irin tururi kanta ke yi ganin wata kyakkyawar budurwa a gefensa zaune, shi kuwa AlHassan Madam dinsa ce a gefensa sun ba MC hankulansu. Takaici ya sanya kawai ta ja kujera ta zauna ba tare da ta ƙarasa wurin su Rafee'ah ba, sai ma bayan ta zauna ta ɗago kai ta ga ashe ƴanmatan gidan kakannin su Hussein ɗin ne.

"Kai Adda Amal you look beautiful wallahi."
Ta dubi mai maganar Teema ta yi murmushin da bai kai zuci ba.

"Thank you. Kuma kun yi kyau."

Daga haka ta maida hankali da fiddo wayarta dake faman vibrating, ganin lambar Hussein kawai sai ta maida wayar jaka. Tana ɗaga kai kuwa ta hango su Kausar na ɗaga mata hannu alamar ta ƙaraso. Hannu kawai ta ɗagamata shaidar inda take ya ishe ta.   Sai da aka kira dangin Ango Tahir  don su yi liƙi sannan ta mike suka ɗunguma har su Teema, a hanya suka haɗe da su Rafee'ah aka shige fili, Maman twins na rantsuwar a farko ba ta ganeta ba. Sai dai su na liƙin tuni mazan suma suka taso don zazzage nasu aljihun, ta ɗaga hannu da nufin somawa ya kai hannunsa saman nata. Juyowa ta yi har fuskarsu na haɗuwa numfashinsu na gauraya wuri ɗaya.  A hankali ya zare kudin a hannunta ya shiga liƙawa kaf a kan Amarya da Angon, ta juya za ta wuce ya riƙe hannun gam suka fita tare. Maimakon su koma mazauni sai kawa ya yi waje da ita har wurin motarsa. Ta fincike hannunta, tuni idanunnata sun cicciko da kwalla.

"Ka kyale ni."

Hussein ya tsaya kawai hannunsa a kirji yana karemata kallo, ta yi mishi irn kyan da baki ba zai iya faɗi ba. Tsananin kewarta da son kasancewa da ita ne ke cin zuciyarsa.

"Da iznin wa ki ka zo nan?"

Ta tsuke baki, ya kuwa bishi da kallo yana cije lebba.

"Ka riga ka san da fitar ai."

Ta fadi cike da dakiya. Bai ce uffan ba ya juya ya yi amfani da mukullin motarsa ya bude, hannunta ya kama ya zagaya da ita ya bude gaban motar da nufin sanyata ciki. Ta dubeshi da zummar magana, sai dai yanayin ɗaurewarsa ya kaɗa hanjinta ba shiri ta hadiye abinda take shirin fadi ta shiga a fusace tana huci. Sai da ya zagaya ya zauna sannan ta dubeshi.

"Motata fa?"

Bai ce mata uffan ba ya yi ribas suka fice. Ranta ya ƙara zafi gashinan ko hoto ba su yi ba da Amaren balle kuma ƴan ankon.

"Amma kasan ba kai ka kawoni ba ko?"

Idan motar ta bata amsa, toh Hussein ya bata. Wayarta ce ta shiga ringing, ta ciro, kafin ta duba ko ta ɗaga ya karɓe. Ba ta san me aka ce ba  kamsr yanda ba ta san wace ce ba.

"Muna tare."

Daga haka ya katse kiran ya jefa wayar aljihun gaban riga. Ramlat dai har da hawayen takaici, ba ta bar haskoshi da waccan budurwar ba kamar yanda ta ke jin zafin raba ta da wurin bikin da ya yi.

Su na isa gidan ya sa hannu ya zare purse dinta yana kallonta tsakar ido Ta kauda kai tana tura baki. Dariya ma ta ba shi ya murmusa. Mukullin motarta ya zare ya miƙa mata. Yana unlocking kofofin ta bude ta fice zuwa sashinta ranta a jagule. Shi kuwa sai da ya ba direba mukullin da kudin mota akan ya koma idan an tashi ya taho da waɗanda suka je a cikinta.

***
Tana shiga ɗakinta ta faɗa saman gado ta shiga rera kuka kamar wata yarinya ƙarama. Ganinta kwnace saman gado tana kuka ya hau doka murmushi, kawai ji yake ya rama shariyar da ta dinga yi mishi a kwanaki biyunnan. A nutse kuma ya soma takawa har ya karasa gadon. Jin ƙamshin turarensa sai ta ɗago ta share fuska, kokarin mikewa  ta ke yi ya riƙo hannunta gami da jawo ta ta faɗa jikinsa. Kanta bisa kirjinsa gaba daya fuskarta ta nutse yayinda hancinta ke shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa. Lumshe idanu ta yi sadda ya sa hannuwansa gaba daya ya rungumeta tsam. Sai a sannan ta kara tabbatar da cewar ta yi kewar mijinta. A hankali ya zame ɗankwalin kanta ya shiga shafa gashinta.

"Duk kawaici da kauda kan da nayi maki don naga gudun ruwanki, ba ki gane ba ko? Kin maida ni kamar wani hoto, kin nunan sabgar gabanki ya fi ni ƙima da muhimmanci. Tun soma bikinnan ba ki da lokacina, ba ki damu da ni ba. Shikenan ni kuma sai na kasa nuna ɓacin raina?"

Yanda ya ke magana a tausashe sai jikinta ya yi sanyi, shakka babu kam, ba ta kyauta ba. Ta ɗago a hankali ta dubeshi tana narkar da fuska.

"Ka yi hakuri. Na sani ban kyauta ba, amma don Allah ka yimin uzuri tunda dai ka sani biki ne ake yi, ga baƙi ina da su."

Ya kama haɓanta suka tsurawa juna ido.

"Sai kuma ki ke jin nauyin kwana da mijinki don kina da baƙi? Ki ka kyalewa wasu ƴan matan shi su samu matsugunni a nan?"  Ya nuna kirjinsa yana ɗaga mata gira da murmushi.

Nan da nan kishin ya dawo sabo fil ta tureshi za ta mike, ya kara fisgota ya rike gam yana dariya.

"Na dauka kishiyar kike ra'ayi."

Ba ta san sadda ta harareshi ba, don mamaki sai ya yi dariya.

"Shiyasa na ganka da wata busashshiya kana yawo da ita a cikin bainar jama'a don ka zubarmin da ƙima a gane ni Ramlat ban da wata daraja da.."

Bai bari ta karasa ba ya tallafi haɓanta ya haɗe bakinsu wuri guda da zafi-zafi.

Tun tana yunkurin ƙwatar kanta har dai ta saddaƙar. Can kuma da kansa ya sake ta, ya mike yana dubanta da shanyayyun idanunsa. Da wata irin kasala ya miƙa mata hannu, ba musu ta miƙamasa, suka ɗunguma zuwa nashi ɓangaren. A nan kam alƙalami ba zai iya wassafa yanda masoyan suka kasance ba cike da matsanancin kewar junansu. Ranar dai dinner anan suka ci suka sha abinsu.

Koda jama'a aka dawo, ta sha tsokana sai toshe kunnuwanta ta yi kawai.

***
  Sati biyu da kammala biki, jama'a kowa ya watse, an miƙa Amarya Hafsat zuwa Kano, tafiyar da ba'a yi tare da Ramlat ba don sam Hussein ya ce ita da Kano ba yanzu ba. Haka ta hakura, Rasheeda kuwa Abuja aka miƙa ta wurin aikin mijinta.

Tun bayan bikin ya kasance Ramlat ba ta da kuzari, koyaushe tana kwance, wani lokacin bacci wani lokacin kuwa yanayin jikin ne kawai ba ya mata dadi. Dada kanta ta soma fahimtar sauye-sauyen Ramlatun, abinka da babba, sai ta ce mata lallai ta yi zamanta a ɓangarenta  ta dinga hutawa tunda a sannan Dada ba ita kadai ba ce, wata dattijuwa kuma yar uwarta dake Mubi, Mariya ta dawo nan domin taya Dada zama. Mace ce da ba ta taɓa haihuwa ba ga kuma girma da ya ɗan kama ta babu mijin aure. Ita kanta tana jin dadin zama da Dada.

Kamar koyaushe, yau dinma tana kwana a falo, daga ita sai vest fara mara hannu da wando pencil da bai karasa ƙaurinta ba. Tun fitar Hussein take jin tashin zuciya, ta rasa meke mata dadi. Kamshin komai a gidan ma ji ta ke yana hawa kanta, karshe ma miƙewa ta yi kawai ta zura dogon hijabinta ta zagaya ɗan barandarsu da ake hango garden ta shimfida ƙatuwar dardumarta ta zauna. Ba laifi ta ɗan ji sauyi, ahankali kuma bacci ya yi awon gaba da ita.

Sallama ya yi har sau uku shiru, da mamaki ya karasa shigowa falon a karshe ya shiga leƙa kicin da dakuna. Bandaki ma wayam, yana shirin leƙawa sashinsa ya hango ƙofar fita ta hanyar kicin a bude don haka ya karasa. Sosai abin ya ba shi mamaki, ba ta taɓa yin haka ba, ga dai iskar fanka da komai a falon amma ta dawo nan ta kwanta, yanzu kam ya yarda ba ta da lafiya. Karasawa ya yi ya sa hannu saman goshinta. Zafin da ya ɗan ji ne ya sa shi shafa gefen fuskar.

"Ya Salam."

Jin hannunsa ta yi firgigit ta farka da salati. Ya kama hannunta.

"Sannu Heart, dama ba ki da lafiya? Tashi muje asibiti."

Ta mike zaune tana shafe fuskarta, sosai kam ta yi bacci don har yamma ta kawo kai, ta tuno ko sallah ba ta yi ba.

"Ban yi sallah ba."

Ya taimaka mata ta mike, yana rike da ƙugunta suka ƙarasa ciki, sai dai su na sanya kai a falon ƙamshin airfreshner da ta fesa ya hautsina mata ƴan hanji. Tana kokarin zama jikinsa daga natata hanyar amfani da hannun damanta ta dora saman kirjinsa za ta tureshi, shi kuwa ƙara riƙo ta yake a rude yana tambayar lafiya. Sai dai ina! Tuni ta soma sheƙa amai har yana ɓata jikin Hussein. Nan da nan ta zaro ido a rikice, ba ta mance sadda ta yiwa Aliyu amai a jiki ba ya ɗauketa da lafiyayyan mari yana ɗura ashariya.

"Ka yi haku.."

"Shii! Muje ki wanke jikinki." Ya ja ta suka nufi bangarenta, sai da ya cire rigarsa da ta ɓaci har da singilet, kafin itama ya ciremata nata dogon hijabin. Bandaki ya shiga ya hada ruwa. Wankan suka yi tare, duk wani abin ƙamshi da ya ɗauko za ta girgiza kai ta ce ita ba ta so, Hussein dai murmushi ya ke da fatan Allah Yasa abinda yake tunani ya tabbata. Sai da ya daukomata kaya sannan ya wuce sashinsa ɗaure da tawul a ƙugu. Ƙananun kaya ya sa kawai ya fesa turare. Aikuwa tana jin ƙamshin turarensa ta fada bandaki a guje ta shiga sheƙa wani aman, koda zai shigo ya dakatar da shi kamar ta yi kuka.

"Ni bana son kamshin turarenka."

"Toh fa." Ya tsinci kanshi da faɗi, turaren da a baya take masifar so kenan, Sorry kawai ya furta sannan ya fita daga dakin. Kaya ya je ya sauya sai dai wannan karon bai yi gangancin fesa turaren ba. Suka ɗunguma suka wuce asibiti, ta waya ya shaidawa Dada ya kai Ramlat asbiti. Dada murmushi kawai ta yi da addu'ar Allah Ya bata lafiya.

Kyakkyawan albishir din da ya yi fata kuwa shi ya samu, wato dai ciki ne da ita. Yanda ya dinga tarairayarta tun daga asibitin har gida, ita abin ma kunya ya dinga ba ta.

Tun daga ranar kuwa kulawar da Hussein ke ba ta na musamman ne, tausayi sosai ta ke ba shi ganin yanda ta ke laulayi mai wahalarwa. Ita kanta abin tsoro ya dinga ba ta, gani take kamar wannan haihuwar farko ne za ta yi don komai sabo ta ke ganinsa.

Kafin watannin haihuwar su cika gaba daya ta sauya, ta rame, sai ƙaton ciki wanda scanning ya nuna ɗa ɗaya ne kawai. Kowa kallon mai haihuwar biyu yake mata, duk yanda ta so ya bari ta je Kano ta haihu ya ƙi, itama don kanta ta hakura da batun zuwa don ko nawa za'a ba ta a yanda take ji,  ba za ta iya bin hanyar Kano ba.

***
Bacci ya ke sosai, yayinda ita kuwa baiwar Allah ta zubawa silin din ɗakin idanu wanda hasken farin wata ya haska, mararta da bayanta babu inda ba ya ciwo, a hankali ta miƙe zaune tana cije baki, ta rasa ma ina za ta sa ranta, wani irin murɗawa da ya yi ba ta san sadda ta ɗakawa Hussein duka ba. Ya mike kuwa firgigit don a farko bai dauka mutum ne ya dakeshi ba, hannu yasa  ya kunna fitilsr bedside yana kallonta gami da ruƙo ta.

Ta matse hannunsa ƙam!

"Mutuwa zan yi wallahi!"

"No! Naƙudar ce? Bari muje asibiti."

Haka ya mike tsaye yana gyara zaman pyjamas dinsa. Dakyar ya samu nutsuwar ganin mukullin motar, ficewa ya soma yi da ita, Buzu Maigadi da  fitowarsa daga bandaki kenan, ya ajiye butar ya karaso da sauri ya taimaka ya karbi mukullin motar ya budemishi yana kwaranyo addu'ar Allah Ya bata lafiya. Lokacin wuraren ukun dare ne. Sai da Hussein ya zaunar da ita kafin ya koma a guje ya dauko akwatin da tun shigar cikin wata tara ta haɗa abinta.

Su Dada basu sani ba sai ƙarar buɗe kyaure da rufewa suka ji. Ba shiri ta fito ita da Baba Mariya a ruɗe, nan Buzu ke fadamusu Madam ce ba lafiya. Nan da nan a rude suka kira wayar Hussein, amma ina tana ta ringing bai ɗaga. A dole suka koma ciki don ba direban da zai kai su. Nafiloli suka shiga yi da addu'ar Allah Ya sauketa lafiya don sun sani loda sun je, ba abinda za su iya yi mata sai addu'ar.

***
Ramlat suna zuwa ko awa ɗaya cikakka ba ta yi ba ta haifo ɗanta namiji, sai dai kafin Nos ta yi wani yunƙurin, wata naƙudar ta kara zuwar ma Ramlatu, da mamaki Metron da Nos suka ƙara yin kan Ramlat, wannan karon sai da aka haɗamata da ruwan naƙuda, ba karamin galabaita ta yi ba, Hussein kamar kansa zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login