Showing 195001 words to 198000 words out of 230725 words

Chapter 66 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1069

za ta zo nan? Don naji ana cewa tare duka za su shiga dakunansu."

Kausar ke neman sani.

"Asabar za su zo. Ke dama ai yanzu ba zancen zuwanki Kano saboda matarnan. Su Hafsat dai da saura sai su je."

AlHassan ke maganar. Kausar ta jinjina kai.

"Allah Ya kaimu."

Shi dai Hussein loma kawai ya ke, yana kammalawa ya mike ya gyara bakinsa. Koda ya shiga munshari Hajiya Zeenatu kawai ke yi. Ya ja mata kofar bayan ya dauki abinda zai dauka yana tsakin takaicin aurenta. Tare da AlHassan suka shiga gidan Dada. Kullum ta gansu sai ta ji kamar an yayyafawa zuciyarta ruwan sanyi. Tana tare da su Baba Yakura yan Maiduguri da ma sauran yan uwan mahaiyarsu. Aka gaggaisa kafin ya yi musu sallama da zummar wucewa Kano.

"Allah Ya kaika lafiya Ango. Mu dinma ai yanzu zamu wuce. Kai dai tunda a jirgi ne za ka riga mu sauka."

Ya yi murmushi jin abinda Gwaggo Lubabatu ƴar abokiyar zaman kakarsu ta bangaren Uba da ke Mubi ke fadi, ya yi addu'a akan Allah Ya kawo su lafiya sannan aka kara yin sallama ya tafi.

***
  CIKAR BURI..

Gidan cike yake da yan uwa da aboka arziki, tun safe ake shige da fice na dora sanwa. Dangi an cika a madafi ana aiki ana kwasar hira. Fuskar kowa ka gani cike da farin ciki musamman Hajiya da har kwalla sai da ta yi don kuwa sun debemata kewar Abba. Cikar da suka yi ya motsa zuƙatan mutan gidan da tunanin Abba, bikin ganinsa suke yi tamkar na wata budurwa ba bazawara ba. Ƴan Daura da yawansu sun zo hakanan kafatanin mutan gidan Hajja su na nan. A bangaren Baba Dakta ma, hatta Kanwarsa Hajiya Nabila da yan uwan Umman Amrah duk sun hallara. Wannan shi ne kadai karar da zaa yiwa Hajiya mace mai son mutane da kuma zumunci. Don sun shaida, Hajiya ko ba ta je sabgarka ba, to hannunta zai je. Ba ta gajiya da kyautatawa hakanan marigayin Mijinnata. A ganinsu wannan ce karar da zaa yi.

Kowa ya bude baki ya ga cikar gidan cewa ake, har ma da auren Ramlatun, shima ya yi albarka kwarai. Duk wannan shagalin da ake, Ramlat na can tare da Amrah da kuma Rafeeah a gidan kwalliya. Dama tun ana gobe daurin aure suka je aka tsaramata lalle a ƙafa da hannu na gani na fada. Hakanan duk a ranar aka yi mata kitso sirara.

Maryam Cutie ce gwanar kwalliyar, tsayawa faɗin irin kyawun da ta yi ba'a cewa komai. Kasancewar Maryam kawar Rafee'ah kuma ba ta da matsala ne yasa ba su wani jima su na roƙo ba ta amince za ta bisu har Adamawa don yiwa Amarya kwalliya ta musamman. Ba ta samu matsalar hakan daga mijinta sosai ba don shi mutum ne mai fahimta hakanan sanin da ya yiwa Rafee'ah da mijinta ne yasa bai yi ja in ja ba.

"TubarakAllah Masha Allah."

Amrah ta fadi tana kallon Ramlat baki ya ƙi rufuwa tsabar kyawun da ta yi mata. Ko aurenta na farko ba ta tsaya ta nutsu an mata kwalliya kamar hakan ba. Murmushi Ramlat ta yi jin yanda su ke koɗa ta. Farin leshin wurin Muniru ta sanya an mata dinkin gown. Maryam Cutie ta yi mata dauri na gani na fada a karshe ta yafamata gyalen kamar yanda ya dace .

"Ke Ramlatu, kinga yanda kika sauya?"

Rafee'ah da ke tsaye gaban madubi tana dauri ke fadi, ita da Amrah suma duka Maryam ta fito da fuskokinsu ba laifi.

"Ya isa kar ku cinyeta."

Fadin Maryam tana dariya. Hotuna ta shiga yi mata tana mai yin alfahari da baiwar  iya kwalliya da Allah Ya ba ta. Ta tabbata fuskar Ramlat ko kasar waje za ta a haka, to fa za ta ciri tuta.

Sai wuraren sha biyu suka kama hanya zuwa gidan, ita dai Ramlat jikinta duk ya yi sanyi, fatanta Allah Yasa wannan ya zama aure na karshe a gareta wanda mutuwa ce kawai za ta raba. Allah kuma Ya ba su zaman lafiya.

Koda suka shiga gidan nan ma haka yan uwa suka yi caa ana ta koɗa kyawun da Amarya ta yi, kunya ta kamata ganin Hafsat diyar Dada, sai a sannan ta kula da zuwan yan Adamawan. Hafsat ta ja hannunta zuwa can falon Abba na baya da aka kai su, suka karasa ta durkusa ta kwashi gaisuwa.

"TubarakAllah, Amaryar Hussein kyakkyawa da ita." Matar ta fadi da hausarta da ba ta fita sosai. Ita dai Ramlat kanta a kasa tana murmushin jin kunya. Sai da Hafsat ta sanya ta zauna ta dinga daukarsu hotuna kafin a karshe ta yi musu sallama ta fito tare da Hafsat. Nan fa Hafsat ta shiga cikinsu aka dinga raha kamar dama can an shaku sosai. Su Nusaiba duk sun zo, daga mai goyo sai mai ciki.

Suna zaune a daki sai ga Salma da Bilkisu, dama Hunainah ita kam tun safe tana gidan, ko sadda suka shigi tana kwance ta yi rashe-rashe a saman gadon suna kwasar hira da kanwar miji kuma aminiyarta A'isha.

"Amarya Ramlat. "

Bilkisu ta fadi tana yamutse fuska musamman jin bakin cikin ganin Hunainah ta riga ta zuwa. A ranta ta ce 'Cusa kai.'

Ramlat ta gaidata da murmushi saman fuskarta. Ta mance rabon da ta sanya Bilkisun a idanu, gaba daya ta kara wani fari fat sabida shafe-shafe ga wani uban ƙiba da ta ke narkawa, ita kuwa Salma har tambarin baƙi-baƙi ya yi mata a fuska. Ramlat ta ja hannun Yasmeen  suna gaisawa, yarinyar yanzu ta bar sakewa sosai kamar a baya don dif haka uwar ta raba ta da gidan. Yanzun ma da biyu ne zuwannata, ba ta san mijin Ramlatun ba. Ko a hanya suna ta gulmar abin suna dariya don har Salma na fadin Allah Yasa wani Alhajin ne mai mata uku da katon tumbi. A jikinsu ba su taɓa kawo wai matashi mai jini a jika zai aureta ba musamman idan an san wacece ita.

"Murja da Fareeda ma suna tafe, Hilal ya fadamusu tunda ke ba ki iya gayyata ba."

Ramlat ta dubi Amrah, Amrah ta kanne mata ido don ta san gulma ce.

"Ayya, ban yi zaton za su zo bane. Allah Ya kawosu lafiya kuwa. Ina murna."

Bilkisu ta taɓe baki ita kuwa Salma murmushi ta yi ta dora kafa daya kan daya tana girgizawa. Sai dai kyakkyawar budurwar da suka gani da aka kirata da yar uwar mijin Ramlatun duk sai suka soma shan jinin jikinsu. A hankali Salma ta yi magana saitin kunnen Bilkisun.
  "Anya wadannan mutanen su na da labarin wace ce Ramlat a baya?"

Bilkisu ta ce "Oho musu, nikam daga suturar jikin yarinyar kamar dai ba karamin mutum shegiyar ta kwaso ba. Ai kuwa ƙafata ƙafarsu har Adamawan naje na ƙarewa danginnasu kallo sosai."

Salma da takaici da bakin ciki ya cika zuciyarta, ita kasa magana ma ta yi. Shekararta sama da ashirin da biyar yanzu amma ko auren fari ba ta yi ba, ga Ramlat har ta kara samun wani ɗanɗasheshan. Don jikinta ya fara ba ta hakan. Burinta yanzu a daura auren ya shigo ta karemasa kallo.

***
Yana kishingide saman kujera a gidan Hisham wanda ya shiga wanka, hotunan da Hafsat ta hankaɗomasa ta whatsapp ya ke aikin kallo, sosai ya yi zooming hoton Madam din tasa ya kasa kauda ido. Murmushi ya ke yana jin soyayya mai tsafta na kara mamaye ko'ina na zuciya da kwakwalwarsa.

Ba zato ya ji an fisge wayar, ya dan dago a ɗan razane don sam bai ji tahowar Hisham din ba. Hisham wanda ke daure da tawul ya ja tsaki.

"Aikin banza, sai afkin karewa mace kallo amma ba a iya tattali ba. To ka tashi, yanzu Yayanmu ya kira ya ce sun iso, ka tarbo su suna waje."

Hussein ya mike zaune gami da dan dafe kai kafin ya mike ya ja guntun tsaki yana gyara zaman rigarsa ta shadda fara ƙal sai dai babbar rigar na ajiye bai sanya ba.

"Ka ci gaba da shiga rayuwata. Kuma ma meyasa ya kiraka bai kira ni ba?"

"Ganin dama."

Daga haka Hisham ya yi ciki da wayar Hussein din a hannunsa don ya shirya, Hussein ya bishi da harara don sosai ya ragemasa nishadi, a bakin gate ya ci karo da su. Ganin wanda bai zata ba sai kawai ya tsaya kamar wani gunki baki a bude.

"RASHEED?!" Ya furta kai tsaye kafin da azama su yiwa juna wata wawuyar runguma da bubbuga gadon baya ana dariya. Can ya sakeshi suka kara cafkewa su na dariya. Nan da nan idanunsu suka kada kuma kamar wadanda ke shirin kuka. Tabbas sun yi masifar kewar juna. Bai ma ga sauran yan uwansa uku da ke tare da su ba sai da ya gama gaisuwar da Rasheed. Najib, Faruk da kuma Khalil duka Yola idan ka cire Faruk da ya zo daga Mubi.

"Allah Ya isa, ban yafewa  matarnan."

Rasheed ya fadi sadda suka nutsu suka zauna a falo. Murmushi Hussein ya yi.

"Ka bar damuwa da ita, ta kusa zama tarihi. Momi ta zo?"

Rasheed ya jinjina kai. Yana nufin mahaifiyarsa, Hajiya Binta.

"Yes tare muke, tana can Yola wurin Dada."

Haka suka yi ta hirarsu cike da nishadi, shi dai Hussein bini-bini zai duba agogo. Ganin lokacin sallah na ƙaratowa ya dubesu.

"Ya kamata mu hanzarta wuce masallaci ko?" Lokacin sallah ya gabato."

Me zasu yi ba dariya ba.

"Lokacin sallah ko lokacin daura aurenka? Kai Malam ba ka da kunya wallahi."

Faruk ya fadi yana dariya.

"Bar shi kawai, ai idan bai yi hakan ba bai cika sabon shiga ba."

Hussein dai har ga Allah sun soma ba shi haushi, dagaske so yakeya ga an hanzarta an tashi an tafi.

"Na rantse zan muku ƙofi yanzun nan ku ga maciji."

Ya fadi yana mai mikewa tsaye suka yi dariya sosai shi kuwa ya shiga zura babbar riga yana mai tafiya gaban madubin dake falon yana gyara zamanta. Karshe ma hular ya dauka ya shiga gyaramata zama yana ji AlHassan na cewa su tashi don da alama Angon  zai iya ficewa ya bar su.  Nan kuma wadanda ba su da alwala duk suka dora sannan aka kama hanya bayan Hussein ya feshe dukkan jiki da turaruka masu tsada da kamshi har kala uku. Bababn burinsa Ramlat ta zama mallakinsa kafin kowane irintsautsayi ya gifta da ba ma ya fatansa.

***

Misalin karfe biyu da mintuna, dubban jama'a suka shaida daurin auren HUSSEIN AMINU GIDADO da RAMLAT KHALID MU'AZZAM akan sadaki har dubu ɗari wanda nan take aka damƙawa Babanta Dakta matsayinsa na waliyyinta.

Bakin Hussein ya ƙi rufuwa, sosai daurin auren ya tara mutane. Hilal kansa sai da ya halarta, duk da Hussein ya san shi, haka suka gaisa faran-faran suka yi hotuna. A karshe aka dunguma gaida iyaye.


***
Babu damar sallah a wurinta sakamakon tana fashinsa, sai dai ta yi sujjadar godiya ga Allah kuma ta yi addu'a sosai.

Bayan ta mike ne Amrah ta ba ta tissue.

"Don Allah kar ki ɓata kwalliyar mana."

Ta karba tana goge hawayen.

"Kukan munafunci ne kawai, mace sai ka ce yau aka taɓa dauramata aure. Aure na uku?"

Bilkisu ta fadi da dariyar kissa, Hafsat jin ta ce aure na uku yasa ranta ya ɓaci, dadinta Hussein bai ɓoyemusu komai na labarin Ramlat ba. Dama tun zaman Bilkisun da irin kallon da suke jefamata ita da abokiyar rakiyarta ta ji sun ba ta haushi.

"Ko aure na nawa ne ai aure ne. Duk wacce ta san me ta ke yi dole zuciyarta ta karye a wannan rana, ko bakomai ta san nauyin da Allah Ya ɗoramata."

Maganar Hafsat ta zo wa su Bilkisu a bazata, wato dama sun san komai? Nan da nan ransu ya kara yin baƙiƙirin musamman Murja da Fareeda da basu jima da shigowa ba, suma dai ganin kwakwaf dinne.

"Muje falo ga Angon ya zo."

Fadin Muhibbat da ta shigo, ta ja hannun Ramlat suka fice, Aisha kam ji ta yi kamar ta goya Hafsat don dadi, balle kuma Rafee'ah da ke dariyar shaƙiyanci. Sosai Hafsat ta burgesu don kanta a waye yake ba karya. Ai su Bilkisu na jin haka suka bi bayansu rii duk domin su ganewa idonsu Angon Ramlatu. Ai kuwa sun yi kyakkyawan gani da ya birkita tunaninsu.

Yana durkushe gaban yan uwan Ramlatun ana kwasar gaisuwa, sai ga Amaryar. Nan da nan tsofaffi aka sjiga guɗa da kirari. Ya kasa kauda idanunsa a kanta, ita kuwa ganin irin kallon da yake mata babu kunyar ido yasa ta yi ƙasa da idanunta.

Tsakiya aka zaunar da ita shima ya zauna, yan uwa aka baibayesu mai hoto ya shiga aikin dauka. Kirjin Hussein banda bugu da sauri babu abinda ya ke yi, ji yake kamar ya ja ta ya sanya a babbar riga ya gudu da ita. Sai da aka kammala hotunan har da mutan Adamawa sannan Ango da tawagarsa suka fice.

Murja da Fareeda dai fasa yinin aka yi aka dunguma aka tafi yayinda Bilkisu ta daure suka zauna. Amma Salma rantsuwa take yi da ƙarawa cewa asiri ne kawai aka yiwa Hussein domin kuwa wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa, ko makaho ya shafa Hussein ya san ya wuce aurar Ramlat duk da dai itama ba baya ba.

***
Sai wuraren bakwai na dare sannan jama'a suka soma tafiya, wadanda suka rage da zasu je Adamawa ba su da yawa. Ramlat ta yi ɗai-ɗai saman gado tana hutawa duk ta gaji don yau ba karamin zirga-zirga ta sha ba a cikin gidan kawai. Kowa ya zo sai an kirata an ɗauki hoto, wannan zamani na hoto har haushi ya ke ba ta.

"Ke kinga mutuniyarki ko? Ta kasa ɓoye abinda ke cikinta? Kai Allah Ya rabamu da hassada mugun ciwo."

Amrah ke zancen ganin duka na dakin babu bare, daga su sai Nusaiba sai Aisha sai kuwa Hunainah dake sallah.
Murmushi Ramlat ta yi.

"Ni mamaki ma abin ya dinga ban, ta madubi fa ina kallon yanda suke hararata amma da mun hada ido sai su basar."

"Ke wa ya taɓa samun daukaka idan bai hadu da yan hassada ba? An fadamaki tsakani da Allah za ta je Adamawarnan? Ni wallahi ban san sadda Bilkisu za ta sauya ba. Gaba daya a farko kamar ba za ta yi ba." Fadin Rafee'ah wacce ke shan wani youghurt da ƴan Yola suka kawo.

"Dama DAN ADAM ance mai wuyar gane hali." Aisha ta furta.

Haka aka yi ta hira, har zuwa sadda Hafsat ta shigo da sauri ta hau kan gadon gami da sanyawa Ramlat waya a kunne. Ta kalleta kafin ta tambayi waye cikin rada-rada ta ce.

"Angonki."

"Assalamu alaikum."

Ta ji muryarsa sadda ta rike wayar sosai a kunnen, amsa sallamar ta yi.

"Shi ne kika kashe wayarki ko? Gaba daya kin sa na rasa nutsuwa."

Ta sauke ajiyar zuciya, ta tuna ashe fa tun a wurin kwalliya ta kashe wayar ba ta ƙara bi ta kai ba.

"Ina neman afuwa."

"Naji, amma yanzu ki fito ina mota. Gaisawa kawai zamu yi."

"Ka..."

Bai bari ta kai aya ba ya katse wayar, dole ta cire ta miƙawa Hafsat da hankalinsu gaba daya ba ya kanta. Ta matsa kusa da Amrah ta mata raɗa. Amrah ta murmusa.

"Kar ki manta dai, yanzu miji ne a wurinki ba manemin aure ba. Umarninsa za ki bi kawai. Ki je ba komai"

Ta mike ta gyara zaman dankwalinta ta yafa gyale sannan ta fice. Tana jin yanda matan dakin suka dauki sowa murmushi kawai ta yi ba ta ko juya ba.

A farfajiyar gidan ta ga mota sabuwa dal sai sheƙi ta ke, ba ta yi zaton shi ne a ciki ba sai da ta zo giftawa ta ji ya mata hon, hakan ya ba ta damar bude kofar don ba'a ganin na ciki. Shi din ne zaune kuwa, ta shiga ta rufe sakamakon AC da ke a kunne. Kamshin motar da kamshinsa sun hadu da sanyi sun saukarmata da ni'ima a zuciya. Ta dubeshi, ya cire babbar riga hakanan hular na ajiye saman gaban motar.

"Ina wuni."

"Lafiya."

Ya furta tamkar ba ya so. Can ya ce.

"Ya gajiyar biki? Anya kin ci abinci? Sai naga kamar kin faɗa."

Ita mamaki ma ya ba ta don haka ta kasa amsawa.

"Kin yi shiru."

"Uhm, na ci."

"Kin fa zama matata, amma na lura da ke tun dazu kamar murmushin dole ki ke yi."

Yanda ya yi maganar kamar zai yi kuka yasa ta dubansa, gaba daya ya juyo ya matsa dab da ita, ta ji nauyinsa, shi kuwa hakan yake so dama, tun shigowarta ya ke kokarin su hada ido amma hakan ya gagara. Za ta juya kai ya yi saurin riƙo haɓarta ya karkato da kan. Ta dora hannunta a saman nasa da zummar kautarwa. Sai dai ya rike hannun tamau.

"Please ka sakarmin hannu."

Ta ci gaba da kokarin kwacewa don ba ta shiryawa hakan ba. A hankali ya saki hannun.

"Na saki. Shikenan?"

Ba ta ce uffan ba.

"Ki je kawai, sai mun yi waya ko?"

Ta saci kallonsa, kamar dai fushi ya yi. To ita kuwa me za ta ce? Ina sabon da za ta sake don ya rikemata hannu?

"Kin tsareni da ido, ba na kyaleki ba?"

Yanda ya yi furucin sai ma ya ba ta dariya, ta kauda kai tana murmushi.

"Ni kike wa dariya?"

"Aa."

"Kin ma iya ki ci abinci, ni da ban ji ki ba kasa daurewa nayi da komai har sai yanzu da na zo na ganki. Idan na tsaya wassafa kalar farin cikin da nake ciki, zamu kwana mu wuni a nan."

A hankali ya jawo hannunta mafi kusa da shi ya damƙe cikinnasa. Wani yarr ta ji kamar yanda shi kansa sai da ya ji wani shock. Ya ƙurawa lallen idanu.

"Allah Ya bani ikon riƙe ki amana Ramlat. Ya ba ni ikon yi maki adalci a zamantakewarmu. Na san na ɓatamaki rai da yawa, amma ki yi hakuri. Haka nake, ban yarda da soyayya kafin aure ba, bayan aure ke kanki yanzu son zai fi maki armashi a kowace tafiya. Abubuwa da yawa ba ma sai na fada ba tunda ke ba yarinya ba ce ko?"

Ta saci kallonsa don gaba daya sautinsa ya sauya, gira ya ɗaga mata yana jifanta da tattausan murmushi. Ta kauda kai ta shiga kokarin zame hannunta.

"Na dauka zaman hakuri da biyayya kawai zamu yi ai tunda cikinmu ba wani mai kaunar ɗan uwansa."

Ba zato ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login