Showing 33001 words to 36000 words out of 230725 words
Ya busa numfashina Abba, babu wani abu da ke tsakanina da Aliyu face soyayya mai tsafta. Wallahi Abba ina sonsa. Don Allah ka yi hakuri."
Abba kusan kasa motsi ya yi a wurin, ya kuma rasa bakin magana don ganin komai yake kamar a mafarki. Hajiya kuwa ta yi shiru don ita lamarin ma ya fara bata tsoro, ta kuma kasa yarda da cewa asiri ne Aliyun ya yi mata kamar yanda su Zulaihat suka ce, ta riga ta san kafiyar diyarta.
"Me kenan? Ke za ki fadamin waye Aliyu ko sai na tattaki yanzu?"
Yaya Munir ke zancen cike da mamakin jin sabon lamarin da bai da masaniya a kai. A jiyan ne yake ji daga bakin Bilkisu batun hirar da ta yi da Hilal wanda yake tsoron sauyin da ya soma gani a wurin Ramlat din har yana goyon bayanta da ganin kawai yanayin karatu ne. Sai ga wata sabuwa inji ƴan caca.
Sanin halin Yaya Munir dagaske zai iya tattakatan yasa ba shiri ta basu labarin Aliyun a taƙaice da kuma tarihinsa. Don tsabar bakin ciki bai san sadda ya mike ya shiga kai mata duka ba ta duk inda ya samu, sai da Abba ya dakatar da shi sannan ya koma mazauninsa yana huci.
"Rabu da ita Muniru, kyale ta. Abinda kika manta Ramlatu, Khalid ba ya magana biyu. Ina miki rantsuwa da Allah ko za ki mutu sai dai ki mutu a dakin Hilal, ba kuma zan fasa daura aurenki a lokacin da muka sanya da magabatansa ba. Idan ke din ɗiya ce ta halal, ba za ki watsamin ƙasa a ido ba. Na miki uzuri a wannan karon, na kuma dauki hakan da kika yi a wauta. Daga yau, yanzu a daidai wannan lokacin, kar ki kusa na kara jin wani tashin tashina game da Ali.."
"Ka yi hakuri Abbana, don Allah ka yafemin. Wallahi ina sonsa, bana son Hilal, na tsaneshi! Abba kar ka yimin auren dole."
Wannan karon Hajiya ce ta mike tana kuka tana mai rufeta da duka.
"Kaicon ɗiya irinki! Haihuwarki ba ta ƙareni da komai ba! Wallahi gwara naga mutuwarki da ganin wannan rana."
Babu wanda ya yi yunkurin kwatarta a hannun Hajiyar, ita kanta Ramlat ta gwammace ta mutu a hannunta. Ta gwammace koma mene ta tarar muddin za'a yarda da zaɓinta. Kuka da dukan Hajiyar bai kashe bakinta daga magana ba.
"Ku yimin rai ku bar ni na auri Aliyu, wallahi shi kadai nake so. Ku yafemin don Allah. Yaya Munir ba'a yi maka dole ba! Kar ka bari a tauyemin rayuwa."
Anan ne Abban ya dakatar da Hajiya, ya dubi Munir wanda idanunsa suka kaɗa, ji yake kamar ya shaƙe Ramlat ta mutu ko iyayensa zasu huta da bakin cikinnan. Mamakinsa bai wuce na yanda akai ta shaƙu da soyayyar gayen ba, yaushe aka fara da har ya zurfafa?
"Idan wannan shi ake kira da so, na yi tirr da irin naki. Ina miki kallon yarinya mai biyayya ashe ba haka kike ba! Ke kuma Rabi'atu har yaushe ki ka bari yarinyarnan ta yi nisa da soyayya haka ba tare da kin sanarmin ba? Wane irin zama kike yi da ita? Ina tsoron ace mu ne ba mu kula da kiwon da Allah Ya bamu ba! Muniru yau ba gobe ba, duk inda Aliyu yake a gidan Justice Abdulrahman Buba, ka nemomin shi."
Daga haka Abban ya bar falon a fusace har walkiyar da ake zubawa tana hasko falon ga kuma ruwa da ke zuba kamar da bakin kwarya. Yaya Munir ya shiga rarrashin Hajiya kafin ya nemi ta ba shi dukkan wayoyin na Ramla ya gani, hakan tasa suka mike zuwa dakin Hajiyar ba wanda ya kalleta fuskokin a haɗe. Ganin haka Ramlat ta mike da saurinta ta faɗa ɗaki ta kulle gudun kada ma Yaya Munirun ya fito ya hau ta da duka a karo na uku. Jikinta ko'ina tsami yake yi, fuskarta kuwa shatin hannun Hajiyar ce kwance a kai. Tausayin kanta da na Aliyu ya kamata, ta sani ko giyar wake Abban ya sha ba zai yarda da aurensu ba. Ba kuma zai kira Aliyun bane don magana ta nuna rarrashi ko tausayawa, tana da tabbacin gargadi ne zai yi mishi da kuma datse alaƙarsu.
***
Komai sai ya sauya, tun daga ranar da Abba ya yiwa Aliyu cin mutuncin da ba ta taɓa zaton ya iya ba akan ya bar masa ɗiyarsa, komai sai ya sauya. Daga Aliyu, zuciya ya yi ba kuma da kowa ba sai Abban, ya kuma ci alwashin ko guduwa ne zai iya yi da Ramlat, son da yake mata ba zai tafi a banza ba. Hatta ita kanta Ramlat ji ta yi idanunta sun rufe ta bar ganin kowa da gashi akan abinda take so, kullum ganin da take auren dole zasu yi mata. Amrah yanzu ta bar bata goyon baya, hatta Umma mahaifiyar Amrah ta ji koken Hajiya ta kuma rantse kan bata da masaniyar fitar da Ramlat ke yi zance a gidanta.
"Amma kuma ta ƙare! Ba za ta kara faruwa ba Hajiya Rabi, wallahi yarda da tarbiyyar yaran ce ta sanya duk muka saki jikinmu da su, ashe ba haka ba. Allah Ya kyauta." Cewar Hajiya Balki kenan uwa ga Amrah.
Abba ya tara yaransa kaf meeting, ya Kuma rantse akan duk wanda ya bar Ramlat yin zance a gidansa bai yafe ba. Ba kuma ga Aliyun ba, hatta da Hilal.
"Mutuncin hira a zo gidanku a sameki, don haka ban yarda ba. Ba kuma zan lamunta. Kar ki kuskura na ganki da yaronnan Ramlat, ko labari ya riskeni sai kin gayawa aya zaƙinta. Tunda ba ki da mutunci a yanzun ba kya ganinmu a mutanen da suka isa su fadamaki ki ji."
Ta ɗago kai ta dubi Abban wanda tsakanin lokacin da aka soma maganar har ya rame. Ta dubi ƴan uwanta, sakon hararar da kowanne ke aikamata ya sanya ta sadda kai ƙasa.
"Nikam Abba da za ka yimin iznin tafiya da ita gidana ina ganin kamar zai fi. Da kaina na kaita makaranta kuma na je na dawo da ita gidan. A ganina wannan hanya ce kawai zamu bi mu toshe duk wata kofar da zai sadata da wannan gayen."
Rafee'ah ce ta cafe zancen Yaya Munir.
"Wallahi nima hakan naga zai fi."
Murmushi mai ciwo Abban ya yi.
"Kayya, ku bar wannan maganar. Ko kun manta alaƙar ita Bilkin da Hilal? Bana son su fahimci komai. Hakan zai janyomata tsana daga dangin shi Hilal din. Ku barmin ita anan, amanarta a karkashinmu take, za kuma mu yi iyakar kokarinmu."
Kukan da ta fasa ne ya sanya suka maida hankali gareta. Miƙewa ta yi ta zube saman gwuiwoyinta, duk a zatonsu kukan na nadama ne da kuma sauya ra'ayi, sai dai tun kan aje ko'ina ta basu haushi.
"Ku yi hakuri don Allah Abba, ku yafemin. Da ace akwai yanda zan yi na cire Aliyu daga zuciyata da na yi. Abba idan aka yimin auren dole zan iya mutuwa!"
Wannan karon Abban ne ya kai mata duka, bai fasa dukan ba yana fidda hawayen ganin wannan rana na bakin ciki, babu kuma wanda ya hanashi.
"Ka yi hakuri Abba! Ka tausayamin ka auramin wanda nake so! Zan iya mutuwa wallahi!"
Kalamanta suka kara harzuka zuciyarsa, yana cikin dukan sai gani akai ya zube. Da wani irin gigicewa iyalinsa suka yi kanshi.
"Abba! Abba!!" Fadin Zulaihat, Rafee'ah har ma da A'isha wacce ke jin tsanar Yayarta har cikin ranta.
Hajiya kuwa salati take tana karawa daidai sadda Yaya Munir ya daukeshi ya yi hanyar waje babu ko takalmi a kafafunsu. Babu wanda ya kara bin ta Ramlat suka dunguma zuwa motar Munir dake shirin fita. A'isha ce ta dawo a guje ta dauki Hijabin Hajiya ta koma, ta dai ga Ramlat ko motsi haka ta fice. Bayan tafiyarsu ta dawo ciki, Indo sabuwar mai taya Hajiya aiki ta fito daga ɗakinta.
"Auta meke faruwa?" Kuka kawai A'isha ke yi ta kasa amsawa. Ganin Ramlat shimfiɗe a ƙasa ya sanya Indo da matukar razana ta yo kanta.
"Innalillahi! Ramlatu! Ramlatu!!" Sai dai ko kusa babu alamar za ta motsa. Ta miƙe da jiki na rawa ta shiga kicin ta dauko ruwa ta hau yayyafamata. Cikin sa'a kuwa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ta bude idanu gami da fadin.
"Na shiga uku Abba kar ka mutu, kar ka auramin shi."
Indo ta san inda zancen ya dosa, ko ba komai ta tsinkayi abinda ke faruwa a gidan kwanakinnan, ta taimaka mata ta kai ta daki. Sai sannan ta dawo hayyacinta sosai. A gigice ta mike tsaye har tana jiri.
"Abba, Abba, ina Abba?"
Ganin ba amsa kwakkwara wurin Indo ya sanya ta maida akalar tambayar ga A'isha dake faman kuka.
"Ai ke kika kashe mana shi idan ma ya mutu. Sun tafi asibiti."
Kasa nutsuwa ta yi ta fito bayan ta zura hijabi, asibitinsu daya ne a duniya, ma'ana inda ya kasance na family dinsu.
Zuwansa gidan kenan adalilin son ganinsa da Abban ke yi, da kansa ya kirashi a jiyan cewa ya zo yau din zasu yi wata magana. Hakan yasa shi zuwa cike da faduwar gaba don ko motarsa bai shigo da ita ciki ba. Kiciɓus ya yi da sanyin idaniyartasa, sai dai ruɗun da ya gani saman fuskarta ya sanya shi tareta a hargitse.
"Meke faruwa Ramlat? Ina za ki je?"
Ta tureshi kusan a gigice ta dakamasa tsawa.
"Dalla Malam ka kyaleni! Nace bana sonka! Bana sonka! Ka rabani da farin cikina, ka rabani da iyaye da yan uwana! Yanzu kuma sanadinka Abba na can asibiti kwance! Ka fita a hanyata!"
Ta yi maganar tana kuka kafin ta ja tsaki ta giftashi ta fice a gidan ta mika hanya. Hilal wanda ya kasa kwakkwarar motsi, idanunsa suka kaɗa. Sai kuma ya lura da hatsarin da ke cikin tafiyarta ita daya a wannan halin, komai zai iya faruwa. Da zafin nama ya shiga motar ya tayar, wani wawan ribas ya yi ya kuma sha gabanta gami da bude murfin motar.
Ta dubeshi, ta san muddin ba ta hau ba babu yanda za ta yi, kusan ma titin ba ababen hawa sosai, cikin sauri ta shiga. Magana daya da ta shiga tsakaninsu bai wuce sunan asibiti ba, daga haka kowanne ya yi shiru zuciyar na tafasa.
Hilal kam ya kasa gaskata abinda ya ji daga bakinta, mutuniyar da ya ke ji kamar ana kara mishi sonta a kowace daƙiƙa. Har suka isa asibitin, ba ta ko bari ya saita parking ba ta ɓalle murfin ta fice da gaggawa. Shima fitowar ya yi ya bi bayanta cikin sanyin gwuiwa.
I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/JS1CQzbtN9
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem
Ina mika gaisuwa ga duk wadanda aka yi wa rashi. Allah Ya musu rahama. Ya kyautata namu zuwan. Ameeen
12)
Su Hajiya ta soma hangowa a tsaye a ƙofar wani daki wanda nan take jikinta ya bata Abba ne ciki. Kai tsaye ta doshi dakin, kafin ta kai ga murɗa kofar ta ji an fisgota har tana faduwa, dama jikinta ba wani kwari ba, ko'ina kuma ya mata tsami sai dai hakan bai sa ta yunkura ta mike ba tana kallon Yaya Munir dake tsaye yana mata banzan kallon da ba ta taɓa gani daga gareshi ba.
"Kin zo ki karasamana shi? Kin ji labarin bai mutu ba shi ne kika biyoshi asibitin?"
Ganin bai lura da Hilal dake tahowa ba ya sanya Rafee'ah saurin yin magana murya a dan bude kadan.
"Hilal sannu da zuwa, tare kuke?"
Hakan da ta yi sai ya ankarar da Yaya Munir, ya dubeshi, shima karasowa ya yi yana dubansa kafin kuma jiki a sanyaye ya dauke kai ya durkusa ya gaida Hajiya da tambayar mai jiki. Ramlat ta ja gefe ta zauna saman kujera a ɗarare, kanta a cikin cinya tana kuka.
Bayan ya gaisa da Munir ne yake jin abinda likita suka ce.
"Ba wani abu bane, kawai ƴar damuwa ce ta sanya hawan jininsa tashi, amma da sauki. Likitan na ciki shiyasa muka fito."
"Ya Salam, dama yana da hawan jini? Allah Ya ba shi lafiya kuma Yasa kaffara ne."
Suka amsa da Amin. Yaya Munir ya kasa bada amsa ta farko ga Hilal, su kansu basu san Abban da hawan jini ba sai dai sun yi amannar koma mene adalilin damuwar da ya saka a rai game da Ramlat ne. Basu jima sosai anan ba likita ya fito, ya dubesu.
"Kun yiwa Abbanmu yawa fa, a yanzu bama son wata damuwa da za ta tashi hankalinsa. Ina rokonku idan ba damuwa a kyaleshi da mutum daya zuwa gobe idan ya samu ya ɗan huta sai ku dawo."
Zancen likita ya yi matukar tasiri a zuƙatansu. Aka ba Hajiya damar ganinsa, ta shiga, yana kwance idanunsa a rufe. Ba ta so ta mishi zancen da zai tayar da hankalinsa karo na biyu hakan yasa ta fita. Yaya Munir ya ce zai zauna abinda zasu bukata a ba direba ya kawo don haka duk suka dunguma zuwa motar Hilal don tafiya gida, yayyun banda harara ba abinda suke watsawa Ramlat a fakaice. Tana ji tana gani ta ƙara hawa motar mutumin da ta kira a maƙiyinta karo na biyu. Har suka isa gida ba wanda ke magana. Godiya sosai su Hajiya suka yi mishi kafin su fita, har sun soma tafiya ya kira Ramlat. Kaifafan idanun Hajiyar ce kawai ya dakatar da ita, ta juya ta isa wurinsa yayinda suka shige cikin gida.
"Kiyi hakuri, a karo na ba adadi ina kara ba ki hakuri. Ban san irin son da kike yiwa shi wanda kika samu har kike ganin ya fi ni ba Ramlat, sai dai kowane irin so kike mishi, bai yi zaton za ki mance da ni haka da sauri ba. Na dauka soyayyarmu soyayya ce mai tsafta da muka soma a karon farko da muka fara sanya juna a idanu. Bansan me na miki ba kika tsaneni har haka, sai dai inada yaƙinin muddin muka yi aure ni Hilal sai na mantar dake batun kowane namiji da yardar Allah. Ina kara jaddadamaki ina sonki, ina miki kaunar da ban san adadinsa ba. Ba irinki ake samu a kyale ba Ramlat. In Sha Allah komai zai wuce, zan jure."
Bai tsaya jin amsarta ba don yasan masu zafi ne, bai tsaye kallon fuskarta ba (dama tun soma maganar bai kalla ba), yasan ba zai ci karo da murmushinta mai tafiyar da damuwarsa ba. Motarsa ya shiga sai dai ya kasa tashinta, kallonta yake tana tsaye a inda ya bar ta, bayanta yake iya hange ba fuskar ba. A hankali kuma ya ga ta soma takawa ta shiga gidan.
"Me na yiwa Ramlat? Ina da wani aibun ne?"
Ya samu kansa da yin tambayar da ta tafi a iska don babu mai amsawa, kifa kansa ya yi saman sitiyari. Tun babu wanda ya san damuwarsa, tun yana kokarin dannewa har ta soma fitowa fili. Kullum kamar ana ƙaramasa sonta, har yau bai yarda ba ta sonsa ba. Asiri ko tsafi ba abu ne da ya yi amannar su na tasiri ba a koyaushe, sai dai haka kawai yake zargin sauyawarta da cewa asiri ne. Yana sonta, ba ya jin kuma zai iya rabuwa da ita. Zai jure dukkan kunci da tsananin da zai fuskanta daga gareta.
Yasan muddin ya tunkaro gidansu a haka, babu ɓata lokaci Mahaifiyarsa za ta gano damuwar dake kwance saman fuskarsa, don haka ya yanke shawarar zuwa ga Yayarsa wacce ko ba komai za ta sanyashi dariya, mace mai raha da kirki. Idan kuwa aka ɓatamata rai, mutum sai ya toshe kunnensa daga habaici da bakaken maganarta.
Gyaɗi-gyaɗi, anan gidan Anti Fareeda yake. Yayarsa ta farko a wurin iyayensu. Daga ita sai Murja kafin kuma shi.
Da yaranta ya soma cin karo, hangame baki ya yi ganin ƴaƴan Murja, Hanan da Ammar suma a gidan. Wannan ya ba shi tabbacin itama Murja na gidan.
Duk yanda ya so kaucewa kar su gane damuwarsa hakan ya faskara, akwai shakuwa tsakaninsu, kamar yanda kuma suka saba magancewa juna su yi su binne ba tare da kowa ya ji ko ya gani ba. Basu da dadi su duka idan an taɓosu. Don haka ya zaɓi ya ɓoye abinda ke tsakaninsa da Ramlat.
"Yanzu kai Hilal ka kyauta? Kasan ina kasuwanci shi ne ka tsallakeni ka damƙa ragamar lefe ga Bilki? Abinda ka yimin a wurinka shi ne daidai?"
Murja wacce ba ta fiye barin magana a cikinta ba ta kasa hakuri sai da ta fesar duk kuwa da idon da Fareeda ke mata akan ta yi shiru. Ya ɗago ya dubeta.
"Nayi zaton duk daya muke. Amma ki yi hakuri wallahi ban kawo komai ba, na yi amfani da cewa Billy tana tare da su, za ta fimu sanin ra'ayin Ramlat. Na tuba kaina bisa wuya don Allah."
Harararsa kawai Murja ke yi, Fareeda ta cafe zancen tana murmushi.
"Ai sai ki yi hakuri, ya fiki gaskiya. Bilkisu da mu duk abu daya ne. Wannan ba karya, kuskuren da kike ganin ya yi miki Allah Ya ba ki hakuri Yaya Babba."
Suka yi dariya, anan ne yake musu batun service dinsa tunda result ya fito.
"Ai kai auren gata za'a yi maka, ga gida ga mata ga kuma kudi shaƙe a account dinka. Banda kai, wa Baba zai yiwa haka?"
Fadin Murja cike da zolaya, suka yi dariya gaba daya.
"Shi fa kadai ne namiji, ke kuwa mene ba zai gani ba? Allah dai Yasa ka kammala service cike da sa'a kaima ka tsaya da kafafunka."
Murmushi ya yi, zamansa da yayyunnasa ya mishi amfani kwarai, ko ba komai kaso tamanin cikin damuwar da ya ƙunso sun ragu.
"Naga Amaryartaka ma ta sauya, ɗan kiran da take mu gaisa ta bari. Idan na kira wayarta kuma a kashe. Naji Umma ma ta ce ta jima rabon da su yi waya."
Maganar Murja kenan karo na biyu wanda ya katse tunaninsa. Nan da nan ya basar.
"Af na manta ma, yanzu haka daga asibiti nake an kwantar da Abba ba lafiya amma da sauki. Ita kuwa Ramlat jarrabawa ce ta sa Hajiya karɓar wayarta."
Duk suka sanya salati cike da jimami kafin su yi fatan Allah Ya ba shi lafiya. Ya jima sosai