Showing 51001 words to 54000 words out of 230725 words

Chapter 18 - Karfen Kafa Book 1 Hausa Novel Complete

Unknown   

06 Jan 2025

1093

ɗan marayana? Yi dariyar mana."

Yanda ta yi din sai ya sanya shi murmusawa.

"Yauwa ko kefa Kakus, ke fa kika haifesu, ba wanda ya isa ya ketare umarninki. Idan ma sun gwada ki yi musu kuka da barazanar tsinuwa ki ga idan za su ƙi."

Ya ƙarashe murya ƙasa-ƙasa, bai damu da duk ma abinda za ta ce ko ta aikata ba, shi dai ya tsira a wajen Alhaji Yusha'u, ya biyashi kudadensa ya kuma farfaɗo da kayan shagonsa.

"A'a, bai kai ga nan ba. Ai idan an tafi ga hakan ban ma isa ba, shi a wa? Kai dai ka kwantar da hankalinka kawai. Da kaina zan kiraka na damƙa maka."

Sai sannan ya saki dariyar farin ciki, wannan ya kwantar da hankalin Abulle. Kauna da tausayin Aliyu na kara ratsa ta. Kusan dagaske babu mai sonsa a gidan, ta kuma sani halinsa aka tsana, toh hannunka kuma ai ba zai ruɓe ka yanke ka yarr ba.

"Yanzu ka sa ranka a inuwa dai. Wannan bushewar taka ne ban san ta menene ba Zakina. Kodai kishiyartawa ce ba ta kiwatamin Kai yanda ya dace?"

Ya sanya harshe ya lashi busassun leɓ ɓansa yana murmushi.

"Babyna tana kiwata fiye da zatonki. Har ta fi diyarku kula da ni."

Taɓe baki Abulle ta yi.

"Mu gani a ƙasa, wai an ce da kare ana biki a gidansu. To Allah na tuba ko sadda kake auren Muhibbat ka fi haka kyau da sheki."

Miƙewa ya yi gami da jan tsaki.

"Kinga Kakus na tafi, ba zai yiwu na tsaya sauraronki kina zagarmin mata ba. Sai anjima."

Bai bari ta kara tankawa ba  ya yi wuf ya fice a ɗakin ya bar ta ta dogon salati.

  Shi kansa ya sani yanzun sigari da kayan maye na kara hudashi yana shiga cikin jikinsa. Ƴan dabarun da yake yi ma a baya don kar gano komai zuwa lokacin ya gani ya daina. Shikenan kuma ba zai huta da rayuwarsa ba? Zai ɓata lokaci da tsoron mutan duniya. A'a. Ya gaji. Ba ruwan Ramlat a ciki, shaye-shayensa ne.
  Ya ayyana hakan a ransa.


***
"Saboda bishiyar kudi ce da ni?" Ya furta ransa na wani zafi, zafin ba na komai bane sai irin yadda Mahaifiyartasu ke biyewa son ran Aliyun kamar shi kadai ne jikanta.

"Kai AbdulRazaƙi, ni kake faɗawa haka? Na shiga uku ni Abulle, dama akwai ranar da zan yi magana ka nunamin iyakata? Oh duniya ina za ki da mu? Allah Ya jiƙan Malam, Allah Ya kawo nawa ajalin na mutu ku huta."

Justice ransa ƙara ɓaci, ya yi maimakon ya lallaɓata kamar yanda suke yi idan ta soma irin wadannan zantukan, sai ya hau faɗa, ta inda yake shiga ba ta nan ya ke fita ba.

"Nan kika ɗaurewa yaronnan gindi ya je ya haɗa lefen burga, ba yanda ba muyi don a tsawatar ba kika hau yi mana barazana da tsinuwa muka kama bakunanmu. Shi yaron bai an muna da details na dukkan abinda yake shukawa ba a gari? Ko an fadamasa don mun ba shi jari ba ma sanya idanu? Sai ki yi ta zama kina biyewa yaro yana ƙara lalacewa? Sisina ba zai ƙara shiga hannun Aliyu ba da sunan wai jari."

Yanda ya dage yana surfa ruwan faɗa sai Abulle ta yi lakwas ta kuma kasa kataɓus. Ko irin rikon da Aliyu ya yi ga ƴarsa bai sa ya ɗauki zafi irin na yau ba. Duk cikin yarannata ta fi su sanya da  kuma yanke hukunci cikin sanyin zuciya ba da hargagi ba, ta san Alƙali magana daya yake, idan kuwa ya yi to fa shikenan ta zauna. Yana da wahala ya yi ja in ka da ita, yau kam ko daga yanayin fuskarsa za ka fuskanci ransa dagaske a ɓacen yake don har wani ja-ja yake yi.

"To ai shikenan, zan aika kauye wurin Shehu,(mijin mai tayata aiki Ladidi da ta damƙa mishi amanar kiwo) ko bijimina ne sai a siyar na ba shi. Amma ka yi hakuri ka tambayeshi wanda ke binsa bashi ka biyamishi. Ka yimin wannan alfarmar domin Allah da Annabi s.a.w. Yaronnan maraya ne, babansa bai da karfi. Ni ce komai nashi, hannunka ai ba zai ruɓe ka yanke ka yar ba."

Ta yi maganar cikin karaya har da sharar kwalla, yasan har yanzu dai ana jika. Abulle ba za ta taɓa bari Aliyu ya san zafin nema ba da kansa, kowane gata burinta ta yi mishi. Ganin hawayenta ya sa shi saurin magana.

"Shikenan, bashi ko? Zan biyamishi, zan tura da kaina wurin Alhaji Yusha'un da ya ce yana binsa. Na san mutumin a yanzu shi ne shugaban ƴan kasuwar kwarin, da kaina zan biya. Wannan ya miki?"

Sai ta hau dariya da sanya albarka. Haka ya fita yana kara jinjina kaunar jika da kaka dake tsakanin bayin Allahn.

***
*Bayan Watanni Biyu*

Allah Madaukakin Sarki Mai sauya dukkan lamura, Shi ke da ikon mayar da talaka Sarki, ya kuma maida Sarki talaka. Kamar haka, Ya kawo sauyuka masu dama a rayuwar auren masoyan.



***
Handout ne a hannunta tana haskawa da fitilar waya. Ta bararraje a kan gado daga ita sai karamin vest da gajeran wando. Mace ce mai gashin jiki, ga zufa. Duk da kasancewar ta bude winduna ta daga labulayen dakin, hakan bai hanata jin zafi ba, karatun ma ba shiga yake ba. Aliyu kuwa tunda ya sa ƙafa ya fita da maraice, har yanzun karfe takwas na dare ba shi da niyyar dawowa.

Ta miƙe tana jan tsaki ta hau rage kaya ta faɗa wanka. Wankanta na biyu kenan daga Magriba zuwa lokacin. Ta goge jiki, wannan karon bata bi ta kan undies ba, ta zura karamar rigar bacci mai jikin cotton, duka-duka tsawonsa iyaka guiwarta ne. Ta tufke gashinta wanda rabonsa da relaxer tun na aure. Hakan yasa ya kakkarye, kitso kawai take buƙata yanzun.

"Haka za'a rayu babu wuta? Nepa ma ba samu ake ba? Tab."

Ta furta a fili, za ta iya cewa tun tasowarta ba ta san matsalar wuta sosai ba a gidansu. Koda zasu rasa wuta, na ƴan kwanaki ne. Yanzun kuwa a gidan Aliyu ta haura wata bata ga kyallin wuta ba. Ƴan Nepa sun musu zagaye ya fi kirga akan su biya kudi sai dai Aliyu ya ce bai da halin biya, suka gaji suka yanke jonin direct din da suka yi.

Banda wannan ma lamura da dama sun sauya, idan ta ga Aliyu ya yi cefanen kaza toh fa wata ribar mai tsoka ya ci a kasuwa. Naman miya na neman kakare musu. Duk wata cima ta jin dadi ya ja baya. Ta miƙe a hankali ta fito zuwa falo ta na kallon farfajiyar gidan. Motar Aliyu na nan kamar yanda ta zata don a yanzu sai ya shafe kwanaki biyu na bai fita da mota ba sai mashin da ya siya, duk a dalilin jarinsa ya karye.

Jingina ta yi jikin window ta kurawa hasken farin wata idanu tana tunani. Tunanin gidansu take, tunanin yanda aka yi watsi da lamuranta. Abba ya hanata taka gidansa, duk sadda ta ce za ta je sai ya ce mata duka-duka yaushe ma aka yi auren. Karshe ya rantse idan ya ga kafarta a gidan yanzu zai saɓamata.

*"Kewarku nake Abba, kewa sosai, babu wanda ke zuwa gidana, daga dangin Aliyu har ku, ya kuke so nayi da rayuwata? Har yanzu ba ku bar fushi da ni ba?"*

*Tana jin sadda ya yi murmushi mai sauti.*

*"Kiyi hakuri Ramlatu, muna sonki ne, da ba ma sonki ba zamu tayaki son abinda kike so ba kinji ko? Ki shekara tukunna, ki shekara. In sha Allah a sannan ko ba ki fadamin ba, ki taki da iznin mijinki ki zo mu gaisa. Hakan ya miki?"*

*Ba haka ta so ba, sai dai kuma babu yanda ta iya, ta amsa da toh yayinda kwalla suka cikamata idanu. Ba za ta iya fadawa Abba cewa Aliyu na shan taba ba har a gidan kuma a gabanta, tasan dariya zai yi mata. Don haka suka yi sallama bayan ta bada saƙon ya gaida Hajiya domin ba ta daukar wayarta.*

Ramlat ta sauke ajiyar zuciya, ɗumin da ta ji a saman fuskarta ya tabbatarmata da zubar hawayenta, ta sa hannu ta share. A yau ta tsinci zuciyarta da kewar ƙawa kuma aminiyarta Amrah. Gashinan dai makarantarsu ɗaya, abinda suke karanta ma ɗaya, sai dai koda wasa Amrah ba ta taɓa bata fuskar da za su gaisa ba balle magana ta haɗasu. Ranar da ta taɓa kuskuren yi mata magana, nan take Amrah ta yi mata Allah Ya isa idan ta kara nunawa ta santa. Wannan ne ya bata haushi har ta kasa ɓoyewa ta sanar da Aliyu, sai da ta yi danasanin fadamasa da ta yi don zagin Amrah ya yi, irin ashar din da idan wani zai ce mata Aliyun ya iya, za ta musanta.

*"Babu ke babu ita! Babu ke ba ita! Kika kara ma kulata nima ban yafe ba!"*

Kalamansa sun mata tsauri, ta yi danasanin furtawar da ta yi, kusan ma ba ya ganin mutuncin kowa nata yanzu, daga ta soma batun kewar gida zai ce ai basu damu da ita ba.

Tunaninta ya katse sadda ta ji ana ƙoƙarin bude ƙyauren gidan. Ta sa hannu ta share hawayenta gami da goge gumin da ya tsastsafo a goshinta. Maimakon ta ganshi da mashin, sai ta ganshi shi ɗaya, abinda ya daure mata kai bai tsaya rufe kofar ba ya soma kokarin nufo cikin gidan. Tabbas dai Aliyun ne kamar yanda farin wata ya haskamata fuskarsa da kuma t-shirt fa jeans din jikinsa.

A gaggauce ta koma daki ta sanya dogon hijabin sallarta kuma na zuwa makaranta har ƙasa ta fito rike da fitilar wayarta. A barandar kofar falon suka yi kiciɓus.

"Oops! Baby sorry. Ina mangareki ko?"

Ta hau murza idanunta, kirjinta ya shiga bugun tara-tara. Ga abu dai a gabanta amma ta kasa gaskatawa, hakan yasa hannu na rawa ta dago ta haske fuskarsa ido a waje.

"Aliyu?" Ta furta cikin tabbatarwa da kuma alamar tambaya lokaci guda, kafafunta ta ji sun hau wani irin mazari, kwakwalwarta ta kasa daukar abinda ta gani a fuska da yanayin gangar jikin Aliyun.

"Bani hanya Malama." Ya kara fadi cikin muryar ƴan maye. Ba ta da niyyar kaucewa ya kuwa bangajeta ta fadi ƙasa ya shige yana kundumar ashar. Ta kama leɓɓanta biyu da hannunta na hagu kamar mai karɓar punishment a makaranta, kukan take yi amma gani take kamar idan ta bude bakin ihu ne zai fito madadinsa. Tunawa da ta yi kofar gidan a bude yake ya sanya ta miƙewa ta je ta rufe. A hanzarce ta koma ciki, a falon ta sameshi ya zube anan kasan tiles yana maganganu barkatai marasa ma'ana da tsari.

"Aliyu? Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Aliyu me zan gani? Me..me...me?"

Ta kasa ƙarasawa tana sheshshekar kuka, ta zube a gabansa.

"Aliyu ka ce mafarki nake, don Allah ka daina yimin irin wannan wasan. Na yarda na sani taba kawai kake sha, ka bar yimin wasan maye, wallahi ba zan iya dauka ba. Na shiga uku ni Ramlat."

Ta ƙarashe tana mai riko hannunsa. Cikin wani irin dariya na shaƙiyanci ya kamo tufkar da ta yiwa gashinta da iyakar karfinsa har ta saki ƙarar azaba.

"Keee, au baby...don uwarki da kika aureni ba ki...san...ina..hawa...sama...ba? Baby...kin cinyemin kuɗina...na talauce...amma na tsira da hawa gajimare..."

Ta yi nasarar ƙwatar gashinta, da wani karfin zuciya don kuwa yanzun ba ta jin kowane karfi a jikinta ta mike za ta gudu daki, ba zato ta ji ya riƙe kafar sai ga ta yiff! Ta fadi saman tiles, baki da goshinta suka ƙumu a ƙasa. Kan ka ce me sun yi suntum! Kuka sosai ta soma.

"Ka kyaleni Aliyu! Don Allah ka rabu da ni karka kasheni!"

Ta firta jikinta na mugun rawa, za ta iya rantsewa ba ta taɓa yin ido hudu da mutum yana maye ba sai a ranar. Ta fi gani a akwatin talabijin.

Jikinta na rawa bai fasa rabata da hijabi ba kuma ya ketamata t-shirt din dake jikinnata ba, ya shiga sarrafata ya dora dukkan karfinsa a kanta. Fadi yake.

"Shege G-Baba...ya ce na yi son raina dake na huce....Baby farar ƙafa gareki...ubanki bai ban komai ba....Hahaha..uban Muhibbat har gida ya ba..."

Bai karasa ba sakamakon hankaɗashi da ta yi ya bugu jikin kujera, ta mike a guje ta shige ɗaki ta rufe da muƙulli. Anan cikin duhun ta zube ta shiga rera uban kuka, innalillahi wa inna ilaihir raajiun kuwa, ta ambata ya fi dubu. Aliyu mashayi?

Wani irin dunkulewa ta yi a wurin ta shiga risgar kuka. KEWA, yau kewar iyayenta da ƴan uwanta take ji. A yau ta yi dakacen biyewa zaɓin ranta. Tausayin kanta ne ya lulluɓeta. Ta yi kukan mai isarta, tana jin yanda yake surfamata ashariya ta uwa da uba mara kyawun sauraro, ya gaji da bugu ya kife anan, tana jin fita da saukar munsharinsa. Miƙewa ta yi kanta na wani irin bala'in sarawa ta zura doguwar riga, ta tattare takardun ta kwanta saman gado,yanda ta runtse idanu haka ta budesu. Baccin ya tafi, damuwa da bakin ciki sun tararmata sun tsaya a ƙahon zuciyarta. Nan da nan zazzaɓi ya sauka a jikinta, haka ta kwana tana rawar ɗari.

***
Sanyin asuba da kuma iskar dake kaɗawa ce, ta tasheshi daga baccin da ya shimfiɗe yana yi, ya bude ido gami da tallafe kansa da ya yi mishi wani gingirigim. A hankali hasken wayar Ramlat ta taimaka mishi wurin gane inda yake kwancen. Zumbur ya mike tsaye, komai ya dawo mishi tiryan-tiryan. Bai mance yanda ya sha magungunan mura na saka maye a tare da su Sa'ad ba a club. Ya je musu da ɓacin ran yanda a yanzun kasuwancinsa ya ja baya babu wani albarka, har ta kai ya rage facaka yanda ya dace, suka duramasa abin maye, ya yi ta sha babu kakkautawa duk domin ya ji sanyi. Bai kuma mance yanda suka kawoshi gidan ba, yana da tabbacin mashin dinsa ma can ya bari.

Wani wawan tsaki ya ja, ya gaji da wani ɓoye-ɓoyen banza. Shi da gidansa? Ai dole ma wataran ta san halinsa. Maimakon ya kwankwasamata, sai ya wuce dakinsa ya kara shimfidewa saman gado, babu tunanin tashi sallar Asuba.

A gefen Ramlat kuwa, dakyar ta iya lallaɓawa ta yi alwala ta yi sallah, jiri sosai ke kwasarta, ta mike ta koma saman gado, kwanciyarta ba jimawa ta ji amai na yunkurin tasomata. A guje ta faɗa banɗaki ta shiga yunkurin sai dai banda ruwa ba abinda ke fita. Ta gaji da yunkurawar ta wanke baki ta fito. Kifewa saman gadon ta yi ta shiga rera sabon kuka, tunaninta kawai mutuwa za ta yi. Babu wani mai sanyaya zuciyarta a yanzun, Aliyu tana fushi da shi, fushi mai tsanani. Gani take ta tsaneshi, ba kuma za ta iya ci gaba da zama da mutum mashayi ba.

***

Motsin bude ƙyauren gidan ne ya farkar da ita daga azababben baccin da ya kwasheta ba tare da ta shirya ba. Rana tarr a saman kanta, Allah Ya taimaketa ma babu makaranta, Asabar ce. Ba laifi jikin da sauki sai dai ciwon kan bai sauka ba, bakinta babu ɗanɗanon komai. Wanka ta faɗa. Doguwar riga jallabiya kawai ta zura ta daure kanta da ɗankwalinsa.

Cikin faduwar gaba ta bude kofar falon, don bata da tabbacin fita ya yi ko shigowa. Ganin ba kowa sai wayarta da kaya a yashe saman kujera ya bata tabbacin shi ne ya maido su wurin. A hankali ta taka ta dauka ta kai daki, gaban madubi ta kara tsayawa tana kallon yanda goshi da bakinta suka kumbura suntum. Hawaye ta shiga fitarwa, ba ta isa ta je wa Abbanta da wani zancen ba akan Aliyu. Sai dai kuma shi kadai ne ke sauraron ta, banda shi ko waya ta kira su Zulaihat sama-sama suke amsawa.

Kicin ta koma ta dafa ruwan shayi da kayan kamshi kamar yanda Hajiyarta ke yi, ta zauna tana sha. Ba ta jin cin komai don haka ko kulolin tuwon da ta yi ba ta kalla ba balle ta iya ɗumamawa.

Babu abinda ta iya gyarawa a gidan, nan falon ta naɗe tana rawar sanyi, ciwon kai ya fi na baya. Ruwan shayin da ta sha shima haka ta amayar da shi. Bacci wahalalle ya kara daukarta, ba ta ji ƙarar shigowar mashin dinsa ba, sai jin hannunsa ta yi saman goshinta. A firgice ta farka, ganinsa ya sanya ta zabura za ta ruga ɗaki. Ya riketa gam a jikinsa, kawai sai ta fashe da kuka jiki na rawa.

"Don Allah ka yi hakuri ka rabu da ni, na tsaneka Aliyu, meyasa ka ɓoyemin munanan halinka? Wallahi ba zan iya ci gaba da rayuwa da kai ba."

Ya ɗago fuskarta yana mai riko haɓar.

"Baby wannan shi ne so? Don kin ganni a halin da ƙaddara ta jefani shi ne za ki gujeni? Baby maimakon ki ji tausayina ki tayani addu'a? Meyasa kika zo kusa da ni? Kalli yanda na ji miki ciwo? Baby baki da lafiya, jikinki zafi, muje ki sanya hijabi na kaiki asibiti. Kinji?"

Cikin karfin hali ta fincike jikinta ta faɗa saman kujera tana sheshsheka.

"Kar ka kara kirana da Baby. Wannan kuma ba ƙaddara ba ce, son zuciyarka ne! Kana saɓawa Allah kana kiran hakan kuma da suna ƙaddara? Wallahi sam ban yarda ba!"

Kalamanta sun soma yi mishi zafi sai kuma ya danne, lallaɓata kawai yake don ba ta jin dadi, don kuma wani abu da ya ƙudurta a ransa game da itan. Wannan tasa ya gane faɗa da zafi ba nashi bane. Ɗakinta kawai ya shiga ya fito da dogon hijabi ya taho da wayarta.

"Haba, ashe wayarki ba chaji shiyasa na yi ta kira bana samunki. Muje idan mun fita na bada chaji. Ki tayani addu'a, akwai wani ciniki da zan yi yau, idan ya faɗa har kaza zan siyomana, na kunna mana inji. Rashin wutar ya isheni."

Maimakon ta ji sanyin kalamansa, sai ta kasa jin hakan. Asalima baƙaƙen maganganun da ya jefeta da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login