Showing 27001 words to 30000 words out of 174305 words

Chapter 10 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1860

_*Ina baran addu'a ga duk wanda ya karanta page ɗin nan yasa sister ɗina Fauziya a addu'a tana fama da rashin lafiya ubangiji Allah ya yaye mata.


```Page 9


Koda Sa'ad ya sauke su kai tsaye cikin gidan nasu Meelat suka shige, Babban gida ne mai kyau ginin zamani wanda aka kawata farfajiyar shi da fulawoyi masu kyan kallo saɓanin gidan Malam da yake sassa² wannan ɗin ya kasance a dunkule ne ta yanda hakan ya nuna cewar mazauna gidan basu da yawa, duk cewa dayau ne karon farko dasu Maimoon suka fara zuwa gidan hakan baisa sun maida hankali wajen ƙarema gidan kallo ba domin dukkan su babu wacce take da duhun kai a cikin su, dan in aka kwatanta wannan gidan da nasu gidajen iyayen wannan ɗin ba komai bane.

"Ah² Uwar Manya ce yau a gidan?" cewar mai gadin gidan bayan ya amsa gaisuwar dasu Meenal ɗin sukai mishi,
" Kai Baba Ayuba ko jiyafa nazo gidan nan ɗazun ma nazo shigowa ne dai kawai banyi ba",
" to barkan ku da zuwa a fito lafiya" ya faɗa a yayin da suke wucewa zuwa cikin gidan, koda suka karasa cikin falon Hajiya Kausar suka samu Mahaifiyar Meelat tareda ɗaya daga cikin yayyin Meelat din Namiji mai suna Mashkur suna duba wasu kaya,
da sallama ɗauke a bakunan su suka karasa shiga cikin falon sai da dukan su suka gaishe su sannan Meenat tama su Maimoon nuni da kujerun falon "ku zauna" tace dasu,
"Ƴar Malam yau kuma ziyarar dare aka kawo mana? Gara da kika shigo ma dan dama yanzun nike shirin inba ya'yan ku saƙo in yana wucewa ya miƙama Hajiya Jidda waɗan nan kayan" ta karasa faɗa tana mata nuni da wasu lesuka data ware su a gefe cikin kayan dake gaban ta,
"To ai Momin bata dawo ba can muka barota a Tudun Wada" Meenat ɗin ta faɗa tana karasawa inda kayan suke "Anty wannan kayan wai duk na Momy ne? to amma dai ba nata ita kaɗaiba harda nikoh? "
Take tambaya, "to ƴar jarida aida kin adana tambayoyin naki har ki kai mata kayan tukun dan nidai nan bani da amsar tambayan ki, kin ajiye baƙi a kujera ko ruwa baki dauko musu ba, Jameela" ta kwalama kira "Na'am Anty ina zuwa" Jameelar ta amsa daga ɗakinta,
"Ni ban san me kikeyi a cikin ɗaki tun dazun ba to fito kiba baƙi ruwa dan wannan mashiririciyar yanda ta tsareni da tambayoyi anan ba damuwa da basu ruwan zatayi ba,
"Anty ni zan wuce ga lokacin sallah ya karato zuwa goben kafin in wuce shago zan shigo mu karasa lissafin" Ya Mashkur ya faɗa a yayin da yake mikewa "ok to ba damuwa saida safen ka gaishe min da Aslam" ta faɗa itama tana mikewa "Ya mashkur kace ma Anty zan zo mata yawo gobe kaji amma a soyamin kaza",
cewar Meenat
"ke raba kanki ki rasa wajen zuwa sai gidan waccan marowaciyar da bata ƙaunar kowa yaje mata gida saboda tsabar rowa har kaje gidan nan ka fito ko ruwa bazata maka tayin shiba balle kasa rai da abinci mtsw ina ma amfanin rowa" Antyn tace sannan tasa kai ta wuce ciki ba tareda ta karabi ta kansu ba,
"Goben da ƙarfe nawa zakuzo? " ya tambaya, "Ya'ya in zamuzo zan kiraka"ta bashi amsa "ok to saida safen ku sai naji ki" ya fada sannan yasa kai ya wuce.
Falon ya rage saura su uku, kai ku tashi mu shiga ciki waccan ƴar rainin wayan bansan uwar me take a ɗakin daya hanata fitowa ba! Jagora ta musu zuwa ɗakin Meelat ɗin koda suka isa zaune suka sameta kan kujerar mirrow da waya a hannun ta, jin motsin bude kofar ne yasa tayi hanzarin ɗago kanta daga kallon wayar da take ta maida kallon nata zuwa bakin kofar, "ke wai wani salon wulakanci ne sabo kika samu kina jin motsin mu a falo kikaƙi fitowa kuma bawai bacci kike ba! ", cewar Meenat
"Ke dallah ai nasan dole zaki shigo bagashi yanzun kin karaso ba ta faɗa tana mikewa "Moon Aisha bismillan ku ku zauna mana please ku dena biyema wannan Autar Malam ɗin bari in kawo muku ruwa" ta karasa faɗa tana shirin barin ɗakin " ke in akwai meatpie ki ɗibomin zanje gida dashi" inji Meenat,
Bazan ɗibo ɗinba ai kila ni ƴar aikin kice kin ma rainan wayau! ta karasa faɗa tana hararar Meenat ɗin,
Haba abar kauna nice fa"Meenat ta faɗa tana marai raicewa Meelat bata ƙara bi ta kanta ba tasa kai ta wuce, kan mirrow inda Mealat tabar wayarta Meenat ta karasa ɗaukar wayar tayi sannan ta nemi waje a gefen gadon ta zauna tana cire naɗin gyalen dake kanta, call log ta fara dubawa idanuwan ta suka ci karo da wata special Number wacce itace number ta karshe da aka amsa kira daga gareta akallah kuma wanda ya kiraɗin yayi Magana da Meelat din na kusan mintuna 40,fita daga wajen tayi ta koma wajen ajiye saƙo anan ma taci karo da sakonni biyu dukan su kuma daga waccan number ɗin ne sai dai duka sakon ba wacce Meelat din ta bada reply akanta,
"Bebs ku matso ku gani yasin tarkon mu ya kama Zakara dan mu dai munfi karfin muyima kurciya tarko wallahi"
Cewar Meenat tana matsawa kusa dasu Moon sosai yanda zasuga abinda take son nuna musun,
"Dan Allah dai kice munyi sara akan gaba Sister? " cewar Moon, "ah kwarai kuwa to muɗin ai ba na wasa bane, "da fari dai bayan doguwar magana a waya ta kusan awa guda ga sakon nin da suka biyo baya "
dariya tayi sannan ta kara da cewa
" bari mu karanta sakon soyayya atoh da muna ganin wasu nayi yanzun muma yazo kanmu"
"Ke dallah kiyi ki karanta kina jamin rai na matsu inji me sakon ya ƙunsa" cewar Aisha cikin zakuwa, juyowa Meenat tayi tana hararar ta "ko kimin shiru ko inƙi karantawa wallahi tam" kara gyara zama dukan su su kayi ke in kika gansu zakice ko wani abu mai matukar mahimmanci zasu karanto a cikin sakon,
Ga abinda sakon farko ya kunsa:

Assalamu Alaikum Mai Kyau, Meelat akwai Matsala fa! dan ina zaton akwai abunda na rasa a jikina bayan rabuwar mu! Ki tayani nema idan kin ganshi ki adana min shi a wajen ki domin kece mafi dacewa da ajiyar shi dama,
Ki kasance cikin farin ciki daga yanzun har zuwa karshen numfashi.

*El~Mustapha*

Kallon² suka tsaya yi a tsakanin su bayan Meenat ta gama karanto musu saƙon, Bebs kun gane me sakon ke nufi kuwa? Meenat ɗin ta tambaya, tana mai kara maimaita karanta saƙon a karo na biyu,
Aisha ce ta mike ta fara rawa su kuma suna kallon ta suna murmushi saida ta gama rawar sannan ta dawo ta zauna, a dai² lokacin ne kuma Meelat ta shigo ɗakin hannun ta ɗauke da katon farantin data gero plates ɗin abinci ruwa dasu drink kan mirrow ta karasa ta ajiye shi sannan ta dawo tsakar ɗakin tana kallon su kamar yanda suma ɗin suke cigaba da kallon ta, "Nidai karku tambayeni komai yanzun ku bari har muyi sallah tukun sai in baku labari dan nasan wallahi harda jin gulma yasa kukazo"
ta faɗa tana hararar Meenat, Ke Baby inani Aminatu ina bacci banji ya aka kwana ba bayan nasan baiwar da Allah yama kawata nidai zoki taimaka ki shafamin labarin abinda ya faru karkisa inyi sallah ba cikin nutsuwa ba kinji dai yanzun nema ake kiran Sallah ɗin"
cewar Meenat, shareta Meelat ɗin tayi ta juya inda ta aje farantin data shigo dashi ta ɗauko ruwa da drink tazo ta ajiyema Moon da Aisha a gaban su " kusha ruwa ta faɗa sannan ta juya ta shige bayi batareda ta kara bi takan Meenat ba, "kutmelesi ke ni zakima iskanci kika shige kika barni, da kyau eh ba laifi yarinya to yasin ban barin gidan nan sai kin bani labari inba haka ba yanzun nan in maida mishi amsoshin sakon nin shi kin dai san halina tsaf bakya buƙatar karin bayani,"
"kin daɗe baki tura ɗinba" cewar Meelat tana shigewa makewayin, komawa tayi ta zauna "ke Aisha baki faɗa mana abunda kika fahimta ba" cewar Moon bayan ta cire goran drink ɗin da take sha a bakin ta,

"humm wallahi Ya Musty son Jamila yakeyi ku gane mana wai cewa fa yayi ya rasa wani abu a jikin shi, kuma wai inta gani ta adana, to na rantse zuciyar shi yake nufin ya rasa ta adana wato ta haɗa zuciyar shi da nata zuciyar wai shinan mai wayau bazai fito kai tsaye yace yana son ta ba"
"ke barshi dan Allah ai tunda aka fara haka duk taurin kanshi wata rana sai ya furta muje zuwa dai,
Kai ku tsaya nifa wallahi tsoro nikeji" cewar Moon, tsoron me? Suka haɗa baki wajen tambayan ta, gyara zama tayi sannan ta ɗaura da cewa "wai ku bakwajin tsoron a gida a gane kuna kula samari?
Ke wani saurayin muka kula? Meenal ta tambaya tana tsareta da ido, "shi Ya Musty ɗin mana!" Moon ta bata amsa, ke dallah ware wani munafikin ne zaije yakai labarin cewa Ya Musty nason Meelat a cikin mu? ta faɗa tana tsatsatsare su da ido, "ah² ni wallahi bazan faɗa ba",cewar Moon "to da dai yafi miki kuma ai wannan abun dukan mu zai amfana dan wallahi kuna ganin bikin nan in bakuyi wasa ba yan aiki zaku zama, kunaji dai ɗazun ake cewa wai wajen reception ba yara wai mune yaran suke nufi fa, amma kunga in muna da Ya Musty ai ba fashi sai munje dan kunsan wallahi indai Iliya ɗan Mai karfi ne ba bari zaiyi muje ba"
Ke wai waye Iliya ɗan mai karfin?" Meelat data ɗauro alwallah ta tambaya, Ya Abdul mana ta fada tana mikewa domin zuwa ɗauro alwallah itama, "kr wai wanda hajiya tasa aka kira mata dazun? Eh to ba laifi yaci sunan"ta karasa faɗa tana dariya,
Saida suka idar da sallah dukan su sannan sukayi zaman cin abincin da Meelat ta shigo musu dashi bayan sun zama ci Meenat ce ta janye farantin gefe, "ke kawata dan Allah ki bani labari meya faru a hanya ciniki ya faɗa kuwa?"
"Ai in ban baki labari ba na tabbata har mafarki sai kinyi yau to gyara zama kisha labari, amma dai kafin nan bani tuwon madara da ilokata sai inji daɗin baki labarin"
Mika hannu tayi ta ɗauko jakarta ilokar ta ciro ta mika mata gashi ni ban son jinini,
Abinda ya faru......
Bayan su Meenat sun wuce.
Ina yini" Meelat ta gaishe shi, "lafiya lau kanwata amma dai kin san saura kada) n kisa zuciyata ta tsaya cak koh? Waigowa tayi taɗan saci kallon shi, "yes kalleni da kyau ba wasa nike miki ba Allah da kin tafi batareda kin min sallama ba ba abunda zai hana ni suma",
Kai Ya Musty suma kuma ana zaune kalau?
Waiyo Allah Momina kinji wata murya mai daɗin amoh dan Allah kara kiran suna na a bakin ki inji, ban taɓa jin daɗin sunan ba sai yau" hannu takai kan fuskarta ta rufe tana murmushi, "kai dan Allah amma dai wasa kakeyi koh", ki taimake ni ki dena rufe fuskar nan Allah dan bakiga yanda murmushin ki ya kara kawata fuskar bane Allah cutar dani zakiyi muddin kikaci gaba da rufemin ita dan ni banki in gangare gefen hanya in faka kawai dan inci gaba da kallon fuskar mai kyau ba.
"Ah ah nidai kar kayi haka kaga jirana akeyi a gida"
To yane an mata bani labari na samu shiga kuwa? dan kawance nike so mu kullah, kin san kowa yana son mu'amalah da abu mai kyau toya zaki iya kawance dani? "
Kai Ya Musty to ai ba'a kawance tsakanin Namiji da Mace, "
Ke mai kyau waya faɗa miki?
Nidai na sani ai"itama ta bashi amsa,
"To yanzun kina nufin ban samu karbuwa ba kenan? " ya fada da karyayyar murya,
Ah ah ni ai bance ba" ta bashi amsa batareda ta kalleshi ba, "to in haka ne na samu shiga kenan, to dafari dai domin abota tayi karko ina bukatar phone number ɗinki ta yanda zan samu damar kiranki aduk sanda naso jin muryar ki, bani wayar ki "
Ciro wayar tayi daga cikin jaka ta mika mishi bayan ya loda number din shi akan wayar nata sai da ya kira wayar sannan ya waigo gefen ta "da wani suna zan miki saving number ɗin? Ya tambaya,
Zanyi saving da kaina" ta bashi amsa "oh right nidai Mai Kyau zansa a nawa Kinga duk wanda ya dauki wayar yasan mai kyau ce ke kirana,
Bai barta ta sarara ba haka yasa karamar yarinya a gaba yana ta bulaleta da kalamai a tsanake a haka har suka iso kofar gidan su Meelat ɗin sannan ya sauketa, ko a kofar gidan nasu ya ɓata lokaci sosai kafin ya juya ya koma ita kuma ta shige gida,
To kunji abunda ya faru.......

"Kawata faɗamin wani abu kin kware mai ko ah ah? Meenat ta tambaya tana kallon Meelat ɗin, ke dallah can ai kema kin san ko giyar wake nasha bazanyi saurin kware mai ba, koba a bakin ku naji kuna faɗar yanda mata ke musu layi ba? Yanzun ni fisabillahi ina ni ina sa kaina a shiga uku dududu fa shekarun mu basu kai 15 ba har yanzun shi yasa na kasa bashi amsar saƙon nin shi, kin san dai gidan nan har yanzun kallon jaririya sukemin shi yasa na kosa ingama sakandire ko sa faramin kallon matashiyar budurwa, "
Yauwa yanzun dai bazaki bashi amsar saƙon shi ko ɗaya ba in yayi magana kuma kice baki fahimci abinda saƙon nashi ya kunsa ba, karki sake koda wasa yazo gidan nan da sunan zance wallahi inba so kike acicci mana uwa ba toh, kidai rike mana shi a waya kaɗai ya wadatar inya matsa yana san ganin ki sai kizo gidan mu in yazo sai ku gaisa fakat,
Aisha karanto mana ɗaya sakon muji shi kuma meya ƙunsa "ta faɗa tana mikama Aisha wayar Meelat ɗin.


Sai kuma sako na biyu shima ga abunda ya kunsa.....

****Gaskiyar yan magana da sukama wannan rana laƙabi da Jummu'at babbar rana, domin nima ayau naci alfarmarta daga cikin nasabarta nayi katarin samun abunda ya girgizamin zuciyata, wato haɗuwa dake da nayi ayau.
Ki karanta da murmushi domin hakan yana karama kyan ki kyau,

El~Mustapha


Huhuhuhu kunji wani salo dan Allah gaskiya Ya Musty na kawo wuta, dan littafi zan nema in dunga rubuta kalaman nan ina adana ma future husband, oh my future husband were are you sai nan da shekara nawa zamu haɗu ne? Kayi ta kulamin da kanka kafin haɗuwar mu,"
cewar Meenal tana murmusawa.

Haka suka shantake suka dunga tsara yanda suma zasuyi shagalin bikin Anty binta ba tareda sun takura kansu ba, a haka har lokaci ya fara ja basu ankara ba, Hajiya Kausar ne jin shiru² basu fito ba yasata lekowa taga mai sukeyi.

Meenal halan dai yau kwana zakiyi a gidan nan Malam baya gari ne hala?
Cewar Anty,
La'ilaha Illallah Muhammadur Rasoulullah (s,a,w) Meenat ta faɗa tana wantsalowa daga kan gadon da take kwance, tsakani da Allah itafa ta manta da cewa ba'a gidan su take ba hira tayi daɗi ta manta cewar Malam tabbas zai neme ta, rarumar jakarta tayi ta lalubo wayarta 2 missed call ta gani daga Malam sai 3 missed call na Ya Sa'ad 1 missed call na Momin ta, kai ku tashi mu wuce gida wallahi Malam ya kira take faɗa a firgice, murumshi Anty tayi tana rufe kofar ɗakin take faɗin ai "dama nasan kuna nan kuna shuririta kin manta zakuje gida to kuzo ku wuce dai dare yayi kema bisu ku barni in sarara, ke Meenat karki Manta da kayan nan gasu nan a falo" daga haka ta koma ɗakin ta,
Moon ne tace "Meelat ga tsarabar ki kiyi hakuri ba yawa" cike da murna ta karɓa tana godiya, muma Anty ma tace in biku muje can gidan in kwana bari in dauki kayana" karamar jaka ta dauko ta zuba duk wani abunda tasan zata bukata a ciki Aisha ce ta ɗaukar mata jakar ita kuma ta ɗauki farantin data kawo musu abinci sannan suka fita daga dakin kitchen ta wuce su kuma Meenat ta musu jagora zuwa ɗakin Anty bayan Antyn ta musu izinin shiga, "Anty zamu wuce saida safe" to ƴaƴan Albarkha sannun ku angode da zumunci Allah yayi Albarkha ke Ƴar gidan Malam baƙi kukayi ne hala? "
Antyn ta tambaya "eh yaran yayyen Momi ne da sukazo yau" ah masha Allah to sannun ku kunji nagode kwarai Allah ya kara haɗa kanku"
Ameen suka amsa mata dashi, Meelat ne ta shigo ɗakin hannun ta dauke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login