Showing 3001 words to 6000 words out of 174305 words
Chapter 2 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
Mai Jama'a ya kafamin a ƙofar gida na mutanen shi ba,abu dai ya zama jaraba ko yana nan ko bashi sai ka samesu a ƙofar gidan nan ga shegun yan matan nan da kullum suke zaryar zuwamin gaisuwar munafunci,
mutum shi ba shugaban ƙasa ba,shi kuma ba gomna ba,amma mutane su dunga binshi duk inda yayi ɗiyyy.. To ni dai ina nan ina mishi addu'a Allah yasa a cikin mutanen nashi babu na ɓoye,atoh kaiko farin jinin ai ya yi yawa.. Ka san shi yasa nayi tsayin daka wajen rabashi da zaman cikin makaranta nace ya dawo nan ya zauna a gabana,to kaiko duniyar ce ta lalace,ba mata kaɗai akema fyaɗe ba harda maza,haka kurum inzo ina nan kwance ina baccin asara cikin AC,aje can wasu kattin mata suma jikana fyaɗe in shiga uku.. Huuuuu! Aiko da ƙulli ya ci amanar kokoh" ta ƙarashe faɗa tana tsuke fuska,tace
"Amma kaga nan duk rashin kunyar yarinya in tazo,ni zan takama ƴar banza burki,yo ina abun kisisina faso a ido? Bayan duk sun gama zubar da ajin,inba lalacewa ba wai mace kebin saurayi tana neman soyayyarshi kaji taɓewa fa salon su ruguza min tarbiyyar da nayi shekaru ina daura shi akai, ah ah nikam badani ba wallah .."
******""""
Masha Allah to gashi nan dai ina rokon ubangiji Allah yanda na fara rubutun nan lafiya ya bani ikon kaishi har karshe cikin amincin sa,
#My first novel ina fatan zaku soshi🤍
#Ummiee~Zaria
# 22/4/2023
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*
*👨👩👧👦DANGINA!👨👩👧👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_
ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_KarKu manta wannan ɗin shine littafina na farko kumin uzuri a inda nayi kuskure.
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._
*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}
*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._
_Bazan taɓa mantawa da ku ba aminan ƙwarai,ina kuma alfahari da kasancewa ta cikinku,ko ban kira suna ba kun san kanku,mutanen Family House. Na gode³ ƙwarai da ƙarfin gwuiwar da kuka bani,wajen rubutun littafin *DANGINA* ubangiji ya biya da aljannah._
*MOM TEEMAH*
*AISHA HUMAIRA*
*JIKAR HAJIYA*
*CHIDA*
```Page 2
***Shi dai Sadeeq dariyar ta kawai yake kwasa yanaci gaba da murkushe mata gyadar data gama goranta mishi kafin ta bashi,
"Kai ya haka daga ɗan sammane kuma saika Kama ka wani tasamin gyada a gaba kayita tumur musa!?
Nifa dan kar kaga rowata ne yasa na taya maka,Gaskiya dai ku canza hali dan Wannan ba halin musulmin kwarai bane atoh ina ma amfanin kwaɗayi!, Allah ma shedane Wannan kwaɗayin naku ba'a wajena kukayo gado ba can dangin iyayen ku mata kukayo gadon shi ku anayin gadon abun arziki ku kuna na tsiya"
Bai tsaya jin karshen zancen taba ya cika hannun shi da gyaɗar sannan ya mike dan yasan kaɗan daga cikin aikin hajiya ne yanzun ta nemi tara mishi jama'a kamar ba itace ta bashi gyaɗar kan radin kanta dan ganin damanta ba.
"Au to dan na fadi gaskiya shine kaima ka mike wato ga jarabab biyar tsohuwa ko wani mara mutunci a cikin ku dana fara mishi magana saiya tashi ya bani waje, To wallahi nikam da bakina ko uban ninku basu isa su hanani magana ba,
Dan ma Allah ya taimakeni nayi tsaye akan ku da addu'a da da nefa yanda na soya gyadar nan haka zatayi batar dabo ko sama ko kasa ban kara ganin ta kun biyo dare kun min fashin ta sai dai tashin zance, To shikenan kuma sai ace bazanyi magana akan gaskiya taba! Da zarar nayi laku²fa cutata zakuyi su kuma iyayan ku da shegen son y'a'ya ko kunyi ba dai² ba basa iya saku a daki su ladafta sai suyi ta sanyi² kamar ma tsoron ku suke,
Kuma idan ka fitan ka kiramin shima daya gagaren duk kuzo ku koma gaban iyayen ku, ban iya wahala biyu nayi na iyayen ku yanzun kuma gaku to bazaku karasa tsofar dani ba
Haka kawai kuna bigewa da zuwa hutu kuna zuwa kuna taramin taron mutane a gida kun maida min gida kamar gidan baitil mali to gidan nan dai na mijina ne bana iyayen kuba,"
Haka taci gaba da sababi itafa idan jidalin ta ya motsa ko dogon numfashi bata shaka saita gama tayi ta numfarfashi,
Kuma fa duk wannan fadan da take Sadeeq din da take dashi tuni ya dade da barin mata falon.
Shiko *MAI JAMA'A* koda ya fito majalisar baiyi mamakin rashin ganin *HAFSA* da *NUSAIBA* ba dan yasan daman bazasu bari ya same su a wajen ba sai dai yaji bakin cikin yanda kullum suke zubar mishi da kima to wallahi basu kaɗai ba harda ma sauran yan wahalan duk saiya shata musu layi tunda basa tashi yin jakancin faɗar su sai a kofar gidan nan tunda duk doɗaɗɗiyar kwalwa garesu, sun ma maidashi wani ɗan iska tunda duk wanda yaga suna faɗar idan ya tambaya cewa za'ayi akan shi suke faɗar.
Sallama yayi Sannan ya koma kan kujerar da take dimun da iman a matsayin tashi ya zauna,
Karfa kuyi zaton majalisar irin ta yan zaman sa idon unguwane!
Inah tashi majalisar ta ban²ta da tasu domin da yawan mutane ma *FADA* suke ce mata kamar yanda yake rubuce a jikin shagunan da suke laye a kofar gidan na Hajiya Innah wato *FADAR~MAI~JAMA'A* Hatta da shagunan idan kwatance zakayi sai ka Kira *FADAR* Kafin a gane, Manyan Shaguna ne da suka kunsa Shagon ɗinki na Mata da mazan ƴan gayu, Shagon aski na maza masu ji da kansu, Shagon saloon na ƴan matan da sukejin cewa sun isa , Shagon kayan masarufi,Babban Restaurant, Shagon karshe shine na kallon kwallo domin shi yafi sauran girma dan haka wajen kamar karamar kasuwa haka yake cika da mutane a koda yaushe, Sai kuma gefen da aka ware na buga table tennis dasu snooker , Gaskiya dai yanda aka tsara wajen dole ya burge mai kallo dan haka wajen bashi rabo da matasan yan gayu mata da maza.
Kuma duka shagonan mallakin *ABDUL-KHAREEMU* ne jikan Hajiya Innah. Wato *Mai Jama'a*
Ita kuma fadar tana daura da shagunan ne. Babbar falo ne sai dai ba ginin bulo aka mata ba anyi amfani da Aluminum da glass mai karfi ne wajen ginata sannan aka zagaye ta da burglary dan bata kariya ga yara masu kiriniya ta yanda ko sun jefa dutse bazai cimma glass din ba balle ya fasata,
Hajiya dai tace fadace ta magulmata domin dai indai ba sun zuge glass din bane to kai na waje komin kwa²rka baka sanin wake ciki amma su duk Abunda ake a wajen a kan idon su yake faruwa.
Sannan an kawata cikin ta da duk wani abun bukata da za'a iya samun shi a falo na alfarma tun daga kan Kujerun zama, Kayan kallo fridge don sanya² abubuwan sha kai hatta da labulayen da aka zagaye falon dashi abun kallo ne gaskiya dai an gyara wajen dai² da zamani, Duk da falon ya kasance majalisa ta maza domin duk wani abu na matasa idan ya tashi anan sukeyi tun daga kallon kwallo zaman meeting dama duk wani Abu mai mahim manci daka iya tasowa, Sai dai ita wannan Majalisar ba maza kadai take dauka ba harda zafafan yan matan dake ji da kansu, Wasu yan makaranta ne anyi karatu tare, wasu kuma yan wahalan fataucin soyayya ne da suke fakewa da kawo dinki ko saloon ko zuwa cin abinci dan suzo su gwada sa'ar su ko tarkon su zai kama kurciya, wasu kuma yan matan sauran yan majalisar ne wasu ko zuwa kawai sukeyi asha hira su wuce, To haka dai wajen yake kullum baya rabo da mutane ko uban gayyar na gari ko bashi akwai masu kula da Fadar shi sukuma masu shaguna suna harkar kasuwancin su.
Haka dai suka kare zaman wannan rana ba tareda wani daga cikin su ya tada maganar abunda ya faru tsakanin *hafsa* da *Nusaiba* ba.
*Wannan kenan*
*******
Cikin garin zaria
*Unguwar Malamai* note(nasa sunan unguwan ne kawai bawai dan akwaita ba).
Unguwace ta manya kuma fitattun malaman da akeji dasu a cikin garin na Zaria, Gidan *malam Almustapha* wanda mafi yawan mutane sukafi Sanin shi da *Malam Almu* yana daya daga cikin manyan malaman da suke rayuwa a cikin unguwar tsayin shekaru,
Babban gidane wanda suka gada tun fil'azal dan haka gidan ya kasance babban gidan daya kasu kashi² kowa da sashen shi. *MALAM ALMUSTAPHA*(Baba Malam) shine babba dan haka ya kasance shine matsayin uba a wannan gida tunma kafin gushewar iyayen su, Yana da mata biyu da yara mata 8 da maza 12 duk da kasancewar shi babban malami
allah bai jarab ceshi da yawan aure² ba domin duka matan shi biyu auren zumunci ne uwar gidan shi mai suna *Ameena* yaran gidan ke kiranta da (innan mu) ita din yar uwar shice ta jini da mahaifinta dana malam iyayen su daya,
Sai matar shi ta biyu mai Suna *Hadiza* (dije) itama dai yar uwace ta fannin uwar su mahaifiya.
Malam yana da kanni 4 maza 2 mata 2 maibi mashi namiji shine *ADAMU*(Baba Adamu) Shima babban Malami ne a cikin gidan yake zaune da matar shi daya da yaran shi 3 maza 2 mace 1 sunan matar shi *MURJANATU* (Aunty Murja) Bashi da yara da yawa saboda baiyi aure da wuri ba , Mai bin shi ita kuma mace ne *AISHA*(Momin Abuja) ita kuma a Abuja take aure dan haka ita da iyalanta can suke zaune, Sai *Mukhtar* (BabaAuta) Shi kuma professor ne yana karantarwa KASU shima anan cikin gidan yake zaune da matar shi 1 *Hauwa'u* Jidda (Momi Hauwa) da yaran shi 8 maza 5 mata 3. Sai *Fatima*(Momi Zahra) itace autar su ita kuma tana Auren wani babban dan kasuwa ne a Kano,
Ahalin malam duk da kasancewar su manyan malamai basu zauna haka ba suna Noma kuma suna hadawa da kasuwanci dan haka suke da rufi asiri sosai.
Sai dai kuma Allah yayi malam Almu cikin mutane masu wata irin baud
ɗaɗɗiyar hali sannan Allah ya mishi wata irin kwarjinin da mutane ke shakkar shi yana da kwarjinin da ba kowa yake iya hada ido dashi ba, Kai hatta da matan shi na aure suna bala'in tsoron saɓa mashi daga su har yaran su,
Ya kasance shi mutum ne mai magana guda 1 inyace eh to eh din zai tsaya akai ko tama saura daɗi ko kartayi su suka jiyo,
Malam mafaɗaci ne kwarai domin da zarar ya shigo gida duk wani mai guntun kiriniya dole ya natsu dan tun kafin ya iso gyarar muryar shi ke isarma na cikin gidan isharar gani nan tafe, Sannan bai yarda ya shigo gida ya iske matan shi zaune da yaran su a tsakar gida da sunan suna hira ba,
yanzun zai Kama sababi cewa "sun tasa yara a gaba suna koya musu gulma da tsugudidi" Dan haka ko zaune suke da zarar sunji motsin shi kowacce zata shige daki kota Kama wani aikin, Hakan kuma bashi zaisa su tsiraba dan saiya duba ko ina duk inda ba'a share da kyauba ko kuma ya dawo ya cimma ba'a kammala abinci ba to aiko ya dunga surfa faɗa kenan, shi dai haka nan Allah ya yishi ya iya fada harda marar dalili dan wallahi ko kajin gidan suka dameshi da kyar kyara ko cara sanyawa yake a tattare su a yanke,
Sai dai kuma duk wannan halin faɗar nashi Allah yama malam son jama'a yana kuma da farin jini wajen al'umah kodan yanda yake kyautata musu, yana kuma da kyauta sosai dan haka gidan shi ko yaushe basa rabo da baki gashi dason zumunci yana son yan uwan shi sosai alkhairin shi bai tsallake kowa ba harda jama'ar unguwa,
Malam yana da wata akida wacce kusan kowa yasan shi da ita , ta kin ilimin boko sosai yake nuna kyamar shi ga duk wanda ya karkata ma ilimin boko da akida irinta nasara duk da cewa ilimin bokon ta yawaita sosai, Dan haka ya zamana tun daga kanshi har zuwa kannen shi basuyi karatun ba,sai dai ya yarda ya kashe ko nawa ne ya tura su zuwa kasashen musulunci domin nemo ilimin islama, ba'a samu sassauci ba har sai da Malam Adamu yayi tsayin daka wajen nunama malam cewa shima fa ilimin bokon yana da ranar shi domin shi *Malam Adamu* ba mazauni bane mutum ne mai yawace² gari² kasa² yake zuwa yawon neman ilimi fitan da yakeyi ne yasa ya fahimci a wannan rayuwa ba ilimin islama kadai mutum yake bukata ba ya dace a nema harda na zamani dan haka ya fantsama neman ilimin, Sanda yayi wani dawowa ne ya samu malam da maganar dakyar dai ya shawo kanshi ya yarda cewa ya yarjema yaran shi maza da kanin shi *Muktar* su fara zuwa shima iya secondary kadai da kyar ya yarda matan suma aka sanya su da sharaɗin primary kawai zasuyi kuma hakan ce ta kasance, badan malam yasoba yanaji yana gani *Adamu* ya kai yaran makaranta.
A haka har wasu daga cikin su suka kammala aka aurar da matan mazan kuma shida kanshi ya rarrabasu zuwa kasheshen musulunci domin karo ilimin addini,
Duk da Ana ganin cewa malam yayi sauƙi a lokacin amma koda ya tashi aurar da Autar su da kuma yaranshi mata da suka kai aure a lokacin bata canza zani ba, kamar yanda kowa yasan cewa baya bada auren yaran shi mata ga kowa sai yayan manyan malamai ko Kuma wani babban mutum ko yan kasuwa shi dai har yanzun bai yarda ya hada zuria da ahalin boko zallah ba, dan har yanzun baya shan inuwa guda da ƴan boko.
Sannan kuma duka yaran shi dana yan'uwan shi dake zagaye dashi shine yake zaɓa musu mazajen aure kedai sai dai ace miki (ki shirya kina da baƙo) ko ya miki ko bai miki ba wannan ke kika jiyo domin dai wannan zuwan da baƙon yayi bazai kara dawowa ba sa ranar aurene zai biyo baya, maganar fahimtan juna bayan auren kwayishi a gidan ku.
Sai dai adalci daya da yake musu shi baya tallan yaran shi ma kowa haka kuma baya fidda ma yarinya mijin aure sai ya jira ta samu manema akallah 3 sannan shi da kanshi zai bincika wayafi nagarta a cikin su wanda ya ciri tuta shi zaiba sauran suyi hakuri, Haka kuma shi baya bada auren mace kamar sadaqa a'ah duk wani Abu na neman aure sai yasa kayi shi kuma in an kawo wanda bai mashi ba zaisa a canza, sai dai bai yarda da zaryar zuwa zance ba, haka kuma baya amsan karamin sadaki domin yana kafa hujja da cewa y'a'yan yan boko ma da sukayi karatun zaman duniya basa aurar da yaransu da arha ballantana shi da zai aura maka mahad daciyar Alqur'ani mai tsarki.
Sannan kuma shi a tsarin shi baya aurar da yaranshi ma talaka domin dai yace "bazai saida akuya ta dawo tanaci mishi danga ba" dan haka saiya duba mai rufin asirin da yasan zai iya rike mishi ɗiya da kyau kafin ya bada auren ta. Sai dai yana rangwame wa yaran shi maza shi namiji yana da damar auro yarinya komai talaucin babanta idan ma ya Kama shi malam din da kanshi yakan dauki nauyin komai da iyayenta zasu mata na kayan daki amma fa banda *y'ar boko*! Hakan kuma ba iya kan ƴa'ƴan shi ya tsaya ba harta da ƴa'ƴan yan uwa ko makota in uba bashi da hali shi yake tsayawa a matsayin waliyyi haka kuma shi zaiyi ma yarinyar kayan ɗaki,
Shi dai Allah ya sani har gobe baya shiri da duk wani dan boko.
Sai dai duk wannan taka tsan² din da yake wajen ganin ya katange iyalanshi daga shiga sabgar boko Abunda bai sani ba tuni kannan shi biyu sunyi zurfi
ƙwarai a cikin shi, domin sun gane cewa tafiyar tafi armashi idan ka haɗa ilimin duka biyu domin sun faɗaɗa karatun su sama da iya sacandiren dashi Malam ya sharɗanta musu ,
Dan haka shima Mukhtar ya dage sosai ya maida hankali wajen karatun shi duka biyun, kuma acan wajen yawon neman ilimin nashi ne ya haɗu da *Hauwa'u*Jidda ita din ta kasance yar babban gidace wadanda suka jiku da ilimin boko da islama soyayya mai tsafta suke gudanarwa a tsakanin su ba tareda Sanin