Showing 72001 words to 75000 words out of 174305 words

Chapter 25 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1854

na kunama a cikin dakin nan,
In banda abunki ta Ina ma kunama zata samu hanyar shigowa ko ina a killace, Taho in gani dai"
Da kyar ta banbaro ta a jikin shi,

A gefen shi shikam zuwa lokacin wallahi abu dayane yasa bai yayyaka ma yarinyar nan marin da sai ta some ba, wato wanzuwar Mommy Jidda a dakin dan su Maryam tunda ta yanka ihun kiran kunama dama suka koma bakin kofa Hajiya na ficewa kuwa suka take mata baya.

Zaunar da ita a kan gadon Innar su tayi bayan ta kara gyara shimfidar gadon, ruwa ta mika mata ta umarce ta da tasha, babu musu koh ta amshi ruwan tasha tana sauke ajiyar zuciya,
Wallahi wannan dan karamin gumurzun da tayi a jikin shi ji take duk gabobin jikinta sun sage d'an karfin data fara samu duk tabi ta sadaukar dashi wajen daukar fansa,

humm wai shi yayi zaton zai shata musullah ne bayan haduwar su na karshe lafiyayyen rankwashi ya bata akai wanda saida ta kwana ta uni tana ciwon kai saboda tsabar cin zalin,
Wato yaga yasha wancan karan bata dauki fansa ta rama ba shine yau saboda tsabar rashin tsoron Allah tana kwance a gadon jinya zai biyota har cikin asibiti ya nemi kwaye mata fata.
To wallahi ita dashi ne dan bazata mishi sakwa² ya raina taba, kuma Allah dan dai Malam ya hanata yin Allah ya isa ma kowa ne amma wallahi da dabaka ken bak'u zata ja mishi nashi Allah ya isan mugu kawai wanda ko gyaran gadon baccin shi bai iyaba sai yasa an mishi,

*Abinda ya hadasu ya rankwashe ta last haduwar su kuwa shine*

Ranar wata asabar ne da safe, ta gama shirin ta dan sunyi niyyar zuwa gidan su wata kawar su a makaranta me suna Zulaihat dan su kureta domin kullum in tazo makaranta da kalar karyar da zata zabgaga musu cewar ita yar masu kudine, da baban ta a abuja yake aiki daga baya ne aka dawo dashi zaria,
Kuma su gidan su komai yi musu ake ita bata dadema data fara yin wanka da kanta ba,

dan dukan su a Cesar ta suna da nanny masu kula dasu,
wato dai yarinyar nan inta samu waje babu kalar karyar da bata bulala musu na yau daban na gobe daban,

dafarko tun suna dan yarda da ita daga karshe dai sun buga ma duk maganganunta alamar tambaya,
Kunsan student da iya kure da kuma bin kwakwakafi,
To suma dai hakan take a wajen su duk abunda kika fada so suke sai sun tabbatar barin ma in abun ya hada da 3full M wato su Meenal kenan,
dan yanda kullum take bada labarin gidan su hakan ya sanya su son zuwa gidan dan su ganema idon su abunda take labarta musu kullum,
Amma makarya ciyar yarinyar nan duk ranar da suka shirya zuwa saita nemo wani sankacecen karyar da zata gilla musu wanda zai hanasu zuwa, to daga karshe dai da suka gane bafa tason suje gidan nasu ne suma sai suka fita harkar ta dan sun kuduri aniyar kureta, harsu zata mayar wawaye kullum tazo ta dunga sharara musu karya, lallai sai sun koya mata hankali naga wasa ne.
dan haka a boye suketa binciken inda gidan nasu Zulaihat din yake domin su kai mata ziyarar bazata su mata dirar mikiya,

Todai bayan bincike sun gano gidan dai ashe a unguwar Alkali take, dan haka suka sanya ranar asabar a matsayin ranar da zasu kai sumame a cewar ai dama in mage data Kama b'era natsuwa takeyi.

sai dai shirin su ya rushe ne sanadiyyar zuwa gidan Hajiya daya kama Meenal na dole a wannan ranar hakan yasa batun zuwan su can din ya rushe.

Domin ta gama shirin ta tsaf da niyyyar tafiya Mommy ta shigo dakin ta bata sakon wani maganin ciwon kafar da Hajiyar ke amfani dashi akan Meenal din takai mata,
Haka a babu yanda ta iya badan taso ba haka ta amsa sakon wannan abu koh bai musu dadiba ita da yan koranta,

gashi ba hanya d'aya bane balle tace suzo su tafi in sun kai sakon Hajiya sai suje gidan su Zulaihat din,

Ta isa gidan lafiya taba Hajiya sakon fa tana Allah Allah tabar gidan ta dawo su tafi inda sukayi niyya kawai Hajiya ta wani bijiro mata da cewar taje ta gyarama Dan Mai karfi d'aki baya gari domin a kano suka kwana cikin abokan shi guda ke aure yau zasu taho da Amaryar,
to kuma tun jiyan yanda ya tafi yabar dakin haka nan yake, dan dama Larai ce mai kula mishi da tsaftar dakin sai ko Sadeeq in yana nan to kuma duk tare suka tafi, ita kuma larai tun jiyan taje Hanwa da sunan gaisuwar mutuwa sai kuma ta iske ana sha'anin biki dan haka ta zauna bata dawoba, Rukayya kuma ita da Hajiya Jummai suma sunje pambeguwa wajen wani biki, shi kuma gashi da tsirfar bala'i sai yace ba kowa yake son yana shiga mishi d'aki ba,
Dan haka zuwan Meenal yasa Hajiya turata dakin domin ta gyara mishi,
Ita hajiya bata san cewa tsakanin AK da Meenal banbancin jinsi bane kawai domin itama Meenal din babu abunda ta iya na kimtsa waje balle kuma ace wankin bayi da sauran su,


Koda Meenal ta fito fili ta fadama Hajiya cewar bata iyaba gwasaleta tayi da cewa tsabar kiwuya ne kuma duk abinta ko da jan gwuiwa ne saita gyara dakin nan.


A zaton ta aikin ne Meenal din bata so dan harda gori saida ta mata akan ita dai an cuceta a rasa wacce za'a bata takwara sai ita da take nan sululu kamar wacce ruwa yaci yarinya sam ba kama jiki,
Inah ita wallah koda tayi yarintar ta aiki babu kalar wanda yake gagarar ta dan haka tama b'ace mata da gani gyaran daki ne sai tayi.

Meenal kam ta kulu iya kuluwa dan haka tayi alwashin bazatayi shi da kyau ba,

Gaskiya dai kuma mutumin ku fada ya canza hali,

Domin dai koda ta isa dakin bashi da wani datti sai dan kurar da yayi amma fa duk gefen da kika jefa idon ki kayane a watse dan hatta da man daya shafa yana ajiye ne a kan gadon a bude ko rufeshi baiyi ba haka ya barshi towel din da yayi amfani dashi ma yana kan gadon ga kayan daya hargitso ya watso su kasa daga cikin wardrobe hatta da kofar wardrobe din bai kulle ba kai komai dai na d'akin yana bukatar kimtsi,
Yanzun fisabilillahi ita da nata kayan ma Raheenat ce keyin tsaye wajen kan kanta mata su shine yau Hajiya ta wani turota dakin wannan mutumin da sunan ta gyara, haba jama'a daki kamar na yaran da basada mafadi......


To wallahi zaiga aiki ganin idon shi kuwa.




Share Please
#Ummiee~Zaria
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*


*👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_



ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._

*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}

*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen.


```Page 23


To wallahi zaiga aiki ganin idon shi kuwa domin ko ita da ake ganin ta fiye nawa a hakan inta sa kanta tana kankanta waje yayi tsaf abunta,

Kan mirror din shi ta karasa bayan ta gama karema d'akin kallo, turarukan dake jere a wajen wad'anda batun yau ba take da fushin su,

dan ta dad'e tana ayyana yanda zata shiga d'akin ta saci turaren bata samu mafita ba sai yau Allah ya taimake ta tsuntsu daga sama gasas she dan haka sai ma ta zab'a ta darje wallahi,

Sai da tabi turarukan nan daya bayan daya ta dunga feffesa su dan ta tantance kamshin wanda tafi muradi sannan ta ware wasu kwalabe guda uku da sukafi kwanta mata a rai,
Sai dai bata san sud'in sune favorite din AK ba duk cikin turarukan yafi son su kuma sunfi sauran tsada domin ko,

Koda kudin d'aya daga ciki aka baka ya isa kayi jari ka kama kasuwanci,

ciresu tayi daga cikin kwalayen su ta adana su da kyau a cikin jakarta wacce dama da ita ta shigo d'akin sannan ta maida kwalayen turaren a inda suke ta yanda bazakayi zaton cewa babu komai a cikin suba,

kayan wardrobe din daya watso kasa ta fara kwashewa babu ruwanta da wani zancen ninke su haka nan ta dunga kwasa tana watsa mishi su a cikin wardrobe din,

da kyar ta iya rufe kofar saboda yanda kayan suka yamutse sai basu zauna da kyau ba, dan kana bude kofar zasu biyo kofar ne su zubo, oho ita Ina ruwan ta dan sauri take ta gama da dakin ta fece,



Gyaran gadon ma babu wani zancen kakkabewa haka tajajja gefe² n zanin gadon ta cuccusa , abun dai bako kyan kallo bargon ko daya kasance jibgegen gaske dama ko kusa ko alama bata ba kanta wahalar ninke shi ba illah ma yayiban shi da tayi ta maka shi haka nan a yamutsen shi akan gadon, tanayi tana nishi bayan ta gama gyaran gado kuwa babu zancen shara ta hau mopping din dakin, haka tayi cab'a cab'a da ruwa a ko ina tanayi tana mitar bayan ta ya rike gashi ko wankin bayi batayi ba.


Bayan gama mopping din kuwa gadon shi ta haye tayi shane² ita nan a dole saita huta sannan zata karasa sauran aikin,
Kamshin turarukan shi dana room freshener din daya kama d'akin kai hatta da gadon kanshi kamshin shi na musamman ne,

hakan yasa daga kishin gid'a da sunan hutu bayan ta gama kalle hotunan shi dake kafe a bang on d'akin ne ta kure 1 daga cikin hotunan shi da kallo wanda duk ciki shi yafi daukar hankalin ta, tana kallon hoton ne amma tana mitar cewa

"shegen kyau kamar mace, shi yasa ake cewa abu in ya cika kyau hadari ne dashi, ciki kuma harda auren namiji mai kyau, dan auren Namiji mai kyau tofa ki shirya shan maganin hawan jini,

gashi nan shi dan yaga yana da kyau da kuma kud'in da mata keso shi yasa yake wulakanci son ranshi"
Ganin ta kasa raba idon ta da kallon hoton nashi ne yasa ta runtse idanuwan ta bata son ya kayi ba dan kuwa wani daddadar baccine ya sad'ado ya saceta ba tareda ta shirya ma hakan ba .
Ba ita ta farka ba sai da Allah ya taimaketa kiran da Meelat ke mata ya tasheta dan Jamila fa badai nacin kiran waya ba inta fara jera kira sai tayi ma mutum Kira 50 a lokaci daya bata gaji ba.
Dan dole ta tashi badan baccin ya isheta ba ta karasa zuwa inda jakar nata ke ajiye kan mirror ta d'auki wayar.

"Kin dawo daga tudun wadan kuwa? "

"Ban dawoba bacci nema ya daukeni ban sani ba garama da kika kira, zuwa anjima kadan dai zan dawo kina gida ai? "

"Eh Ina gida, sai kin dawo din to"

bayin ta wuce kai tsaye bayan ta yanke wayar leka cikin bayin tayi, shi din ma dai babu wani alamun datti dan ko Ina kal yake har yana daukar ido sai dai shima kamar cikin d'akin ne kayan amfanin cikin bayin duk a yamutse ya barsu kayan wanki ma daya cire bai iya sasu a basket ba gefe ya watsa su,

jawo kofar tayi ta koma cikin dakin,
abayar data daura akan doguwar riga mai hannun shimin dake jikinta irin masu lafewa mutum a jikin nan ta cire harda dan kwalin, sannan ta kara komawa cikin bayin,
Hhhhhh mata fa zasuyi aiki.

Ta daiyi kokari wannan karan ta tsaya ta kwashe kayan wankin ta cusa su a basket din data gani, su showel gel da sauran kayan amfanin shiko sai da tabisu daya bayan daya ta duba dan ta tabbatar ma da kanta cewa bilicin yakeyi shi yasa kullum fatar shi ke kara walkiya.
Sai dai kuma duk ta duba jikin su bata ga inda aka rubuta cewar sabulan suna sanya hasken fata ba.
Bawai dan tayi na'am da hakan bane tadai mayar dasu ta ajiye ne kawai, shima kuma sai da ta zabi wasu shower gel guda biyu a cikin wadanda bai bud'e ba
a wajen .
dan bafa zatayi aikin banza ba ta tike tama shi gyaran daki ba lada bare la'adah,
Ganin cewa bayin babu wani dattin da zata b'atama kanta lokaci wajen wanke wa yasa ruwa kawai ta wau watsa ta dauraye bayin,
Bayan ta gama sai da ta nemi Leda ta zuba shower gel din nan dan tasan ganganci ne ta shiga dakin Hajiya dashi dan tana gani zata mata tereren ban kad'ane.

abayar ta ta maida sannan ta fito daga d'akin ta maida kofar ta rufe kuma har lokacin mopping din da tayi bai gama bushewa ba,sai ma wani wajen duk yayi jirwaye.

Can cikin wasu fulawan da aka kawata gidan dasu ta nemi waje mai duhu ta boye ledar kafin ta koma wajen Hajjaju,

Jin motsin shigowar ta ne yasa Hajiya lekowa daga cikin kitchen din da take ta aikin girki yau dambun shinkafa take son ci gashi kuma Larai bata nan dan haka ita da kanta take aikinta dan dama har gobe intaso ita da kanta ke shiga kitchen ta girka abunda take muradin ci,

"Ke y'ar nan badai har yanzun kina gidan nan baki koma gidan kuba? Nifa ban son kwadayi wallahi in ma dan kinga ina dambu ne yasa kika tsaya sai kinci kafin ki tafi to wallahi kadan zan sammiki dan masu jiran dambun nan yawa garesu"

Itafa Hajiya gaba daya ta manta cewar tasa Meenal ta gyara ma AK daki,,,,

"Aiko wallahi ban tafiya sai naci shi kodan ladan gyaran d'akin da kika sani,
Gashi nan duk jikina ma ciwo yake"

"Innalillahi wa'innah ilaihir raju'un oh ni Aminatu badai tuntuni kina dakin Dan mai karfi ba ?
wani irin sharan kirkine zai dauke ki awanni baki kammala ba? "

Sai da ta zuka numfashi da kyau dan ta tabbatar da kanshin da hancin ta ke jiyo mata sannan ta karasa kusa da Meenal din dan gazgata zargin ta.

"Amina tunda kika shigo falon nan naji kamshin turaren wutan da nasa ya dakushe,
Fadamin badai wanka kikaje kikayi da turarukan Abdul khareemu ba? "

Ta karasa fada tana tsatsare aminatun da idanu,

"Ni ba wanka dashi nayi ba kadan na fesa"

"Eh to lallai zoki tattara ki kama hanyar gidan ku dan wallahi ba kirki Abdul khareemu ya cika ba, kibar ganin Ina kusa kiyi zaton idan yaji kamshin turaren shi a jikin ki bazai nad'a miki na jaki ba,
kuma nikam ba hanashi zanyi ba dan shara kad'ai na turaki kiyi,
Allah yasa ma dai baki mishi wani barnar ba"

"Niba abunda na mishi, kuma Allah kuwa ban tafiya sai naci dambun nan"

"Da kyau ai wanda baiji bariba yan magana sukace zaiji hoho"

Cewar Hajiya tana gama fadin hakan ko ta koma cikin kitchen dinta tabar Meenal din a falon.

Waje ta nema ta zauna akan kujera abunta domin ita dai ko a jikin ta, jin shiru Hajiya bata fito bane yasata mikewa ta bita kitchen din,

Ba irin korar da Hajiya bata mata akan tafa wuce gidaba itako uwar taurin kan ta kiya, a haka har Hajiya ta sauke dambunta ta kasafta shi kamar yanda tace masu jiran dambun nada yawa hakan ne kuwa dan kaf dambun ya kare.
Ita dai tunda ta samu Hajiya ta zuba mata nata ta dauka ta koma falo taci gaba daba ciki hakkin shi,
Bayan ta gama ci alwallah taje ta daura ta gabatar da sallan azahar dan wasu masallatai sunyi kira, bayan ta idar tadan kara gyagy gyarawa sannan ta fito ta iske Hajiya itama akan daddumar da tayi nata sallah din anan falon,

"Ke Meenal shiga kitchen din nan ki dauko dambun cikin jar kullar nan dana ware a gefe ki mikata gidan su Balkisu ki kaima Turai, kuma sauran kije ki zauna kina mik'a mata ki dawo kizo ki wuce gida"

Batayi musu ba ta wuce kitchen din dan koba komai tana son zuwa wajen tsohuwar nan dan ita sam ba irin halin Hajiya Innah gareta ba, dan sosai take sakin musu fuska kuma duk in kaje saita nemi wani abun ta baka.

tana daukowa kuwa ta fice daga falon na Hajiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login