Showing 96001 words to 99000 words out of 174305 words

Chapter 33 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1879

dan kwanaki ya buga mata kashedi akan inya k'ara ganin ta da wani saurayi da sunan yazo wajenta to yasin a gaban saurayin zai kakkafta mata mari, kuji wata magana fa irinta masu afa kwaya dan Allah shida yake tara yan mata a kofar gidan su waya mishi magana sai ita dan yana mata bak'in ciki yaga tauraron ta ya fara haskawa to ai bashi kad'ai bane mai farin jini wallahi.
Ita fa gaba d'aya bata damu ba domin dad'inta kawai takeji cewa zatayi bikin kannen ta cikin koshin lafiya batareda mutane sun taru akanta suna faman yi mata sannu kamar mai ciwon mutuwa ba.

***
Bayan dawowar AK yayi mamakin ganin Meenal kwana 1&2 a gidan batareda ta koma gidan suba dan iya sanin shi yasan inba dai su Moon sunzo ba tofa bata yarda ta kwana a gidan ranar dai ya gaji da ganin nata dan Allah ya sani yarinyar nan fa ba karamin takura mishi takeyi in yana waje ba, dan yanzun ma wani sabon iskanci ta tsira da zarar ta hango shi saita fara mishi wakar da in tanayi yake jin kamar ya shako wuyarta har saita daina numfashi kafin ya saketa, wai shi yarinyar nan take ma wakar.. .. ..

Turun turun tuzuru wai yaushe zaka auree...
Tuzuru wai yaushe zaka aure.... Tanayi tana gyada kai.

Wai shiii, shidai shi din nan da girman shi da mutuncin shi da gemun shi da komai amma tsabar rainin da yarinyar nan ta mishine yasa har take mishi wakar tuzuru wai yaushe zaiyi aure, insha Allah duk ranar daya riketa sai ya fada mata taje gida ta tambaya shekarar Baban ta Adamu nawa yayi a duniya ba tareda mata ba in yaso sai tazo ta had'a shekarun da nashi aga wayafi wani zama tuzuru a lokacin!
(Kai jama'a dan Allah ku dunga ma jikan Hajiya fad'a dan ya iya dukan kwano, insha Allah ni kuma saina tuna maka wannan maganar zuwa gaba)

Suna zaune a falon Hajiya tuwo yake ci kamar yanda kowa yasan yafi son cin abinci mai nauyi, "kinyi wanka da ruwan maganin dana hada miki? " Hajiya ta tambaya Meenal wacce fitowarta kenan daga d'akin da Hajiya ta sauke ta a ciki, "eh nayi"ta bata amsa tana wucewa cikin kitchen da plate d'in dataci abinci a hannun ta, Saida yaga kulewar ta sannan ya waigo gefen Hajiya,
"Me yarinyar nan takeyi a gidan nan wai?"
"Ban gane me takeyi a gidan ba! naga nan ma ai gidan sune"

"Eh na tambaya ne saboda na san ba zuwa takeyi haka nan ba balle kuma harta kwana gashi kuma tunda na dawo nike ganin ta a gidan kuma na tambayi bala yace min tayi kusan sati a gidan ko laifi tayi a gidan su ta gudo nan? "

"Kai dai ka sani da neman ba'asin ka, yarinya ita da gidan kakan nin ta ka kama tambayar me takeyi gaskiya dai ka canza hali wallahi"

Ta fada tana karkata dan kwalin kanta zuwa gefe a dai dai lokacin ne kuma Meenal din ta fito daga kitchen waya kare a kunnen ta amma cikin su babu mai iya jin abinda take cewa a wayar harta wuce su ta koma d'aki,
Sai da Hajiya ta tabbatar ta shige sannan ta baro kujerar da take zaune ta koma wacce mai jama'an yake kai, duk wannan kusancin da suka samu bai wadace taba sai da tayi kasa da muryar ta sosai tana kara kallon kofar dakin da Meenal ta shiga kai da ganin yanda takeyi ko ba'a fad'a maka ba kasan cewar irin gulmar nan dako kud'a ba'a son yaji abinda za'ace shi take Shirin yi.

"Aure fa uban ta zai mata karshen watan nan.... "

Wani irin mummunar shaka romon daya surb'a a lokacin ya mishi domin har cikin kwakwalwar shi romon ya wuce, aiko sai tari ya biyo baya domin a lokaci guda yaji kirjin shi ya d'auka da wani irin rad'ad'i kamar na wanda aka watsama barkono akan ciwo, dan haka tari yace bani wajen, tari yake mai cike azaba idanuwan shi har sai da suka zubda hawaye dan azabar da yakeji,

"Subhanallah innalillahi sannu ! sannu!! sannu!!! Abdul sannu, haka Hajiya ta dunga jera mishi sannu ba k'ak'k'autawa sannan ta mik'a mishi ruwa ya samu yasha kafin ya samu tarin ya lafa mishi da kyar,
"Sannu yajine ya tsarke ka koh ai Saida na fad'ama takwara ta rage attarugun data zuba dan kar yayi yaji amma tace min farfesu in baiji yajiba baya dad'i wannan ai daukar Alhakine,
Kara shan ruwan zakaji ya sake ka"
Karbar ruwan yayi ya kara sha yana mai jingina kanshi a jikin kurerar, ba tareda ya iya cema hajiya komai ba duk sannun da take mishi kuwa dan so yake ya tuna abinda yaji ta furta wanda yayi silar da yasa roman nan haura mishi saman kai,
Saida yaji yadan sarara sannan ya kamo hannun Hajiya guda dake kusa dashi, jajayen idanuwan shi da basu koma dai dai ba har yanzun da jansu ya zuba mata.
"Hajiya mai kikace d'azun? "

"Umm bari kai dai Mai gida ai wallahi nasan dole ka tayani jimami, kai ma kajishi wani bambara gwai koh? Wai Yar wajen Jidda fa za'ama aure karshen watan nan yau dai saura yan kwanaki"

Bai bari takai karshen zancen taba ya tari numfashin ta da cewa

"wai wancan yarinyar ce za'ama auren?" Ya fad'i hakan yana nuni da hannu zuwa d'akin da Meenal ta shiga,
Saida ya k'ara gyara zama ya fuskance ta da kyau sannan ya k'ara cewa
"wai auren gaske ko na wasa kike magana akai Hajiya"

Wani kallon karfa ka raina min wayau Hajiya ta mishi sannan ta bashi amsa da cewa "dama akwai auren wasa ne Abdul Khareemu? Kuma kayi kasa da muryar ka karka tadamin b'alli dan ita kanta yarinyar bata san da zancen auren ba dalilin da yasa ta dawo gidan nan da zama kenan har zuwa lokacin bikin dan ba'a son ta sani,"
Sai da ta b'ata fuska cike da jimami ta d'aura da cewa "kuma kaji wani cin amana Soja fa zasu aura mata Sojan ma mai mata harda yaran shi 4 ba kuma iya nan tashin hankalin ya tsaya ba domin dai ita matar sojan in fad'a maka babu ubanda bai san yanda ta shanye mijin ba sai yanda taga dama take juyashi ko iyayen shi baya tunawa dasu saboda ta gama shanye shi ta sud'e tass wallahi , amma dan cin amana aka d'auki jikata aka bashi, fadamin dan Allah inba sun shirya ganin bayan jikata ba mai zai sa suyi haka yarinyar dako ruwan zafi bata iya dafawa ba sai da tazo gidan, shi yasa kaga na kasa zaune na kasa tsaye ina ta faman shiga da fita wajen neman mata magungunan tsarin jiki, atoh ban nemi kowa da sharri ba duk wanda ya nufamin jika da sharri shi zaiga abunshi,
To bagashi ba d'aukotan da nayi yayi amfani tunda a yan kwanakin nan fa tare muke shiga kitchen ina nuna mata abubuwa dan Sam Jidda bata koya mata komai ba kamar dai bani naba jidda tarbiya ba wallahi kuma a haka suke son aurar da ita, nayi magana iyayen ka sunce wai babu ruwana ai iyayen ta sun fini iko da ita, to fisabilillahi so suke insa ido a nakasa min rayuwar jika? "

Shidai tunda ta fara magana fuskan ta kawai ya kafe da kallo wai aure Aurefa wai za'ama waccen jinjirar wannan aure za'a mata ko raino dai za'a kaima mijin? Ga manya manyan yan mata nan ba'a aurar dasu ba sai wannan yar tatsitsitar hanci duk majina kai cike da rashin kunya, Allah ya sani ya tausaya mata ya kuma tausaya ma wanda za'a daurama auren ta dan yasan zai sha fama.
Babban abun da yake k'ara d'aure mishi kai kuma shine cewar da Hajiya tayi wai yarinyar bata san da batun auren ba, to kenan dai auren dole iyayen ta zasu mata? Shifa tsakanin shi da Allah sosai abun ya daure mishi kai domin shidai kullum yakanji ana maganar auren dole bai taba gani ba sai gashi yau a kusa dashi, haka nan kawai kuma sai ya farajin tausayin yarinyar yana shigar shi, karamar yarinya a rasa ma mijin da za'a aura mata sai soja kuma ma mai mata harda yara koya zataji duk ranar da taji batun auren?
"Lallai akwai rikici " ya fad'a a bayyane,
"Akwai shi kam sai dai muyi fatan Allah yasa auren shine mafi alkhairi a gareta" Hajiya ta amsa mishi dashi
"Ameen" ya amsa dashi yana yunk'urawa da niyyar barin wajen domin a yanzun kam bayajin zai iya cin wani abu kuma dan gaba daya abincin ya fita akan shi.
"Tafiya zakayi kuma baka gama cin abincin ba? "

"Nakoshi Hajiya sai da safe" ya fad'a yana ficewa daga side d'in gaba daya, sai da ta kwashe kayan sannan itama ta shige.

*Satin biki.*

Tako ina fa kowa ya shirya ranar auren kawai ake jira,
Su Aisha Moon da iyayen su duk sun iso garin Zaria,
sai dai suma komai da sukeyi cikin taka tsantsan sukeyin shi domin dai kar a fasa maganar harta koma kunnen Meenal saboda su sun samu labarin bikin auren harda Meenal amma iyayen su sun kwab'esu akan su kama bakin su,
Hajiyar ku ko ta dage da shan magani domin duk abinda hajiya ta bata amfani take dashi a sonta na ganin anyi hidimar biki da ita lafiya, samarin ta kuma tuni ta amshi kud'ad'en ankon data yanka musu, wasu sukan zo har nan gidan ne in sunzo takan saci jiki ta fita ko kuma ta tura Rukayya ko su Meelat su amso mata in tana buk'atar wani abu a gida kuma cikin yayyen ta wani ke kawo mata domin shima dai ya sa'eed yayi busy da nashi shirin bikin,
Zuwa yanzun kam ba karamin tausayi Meenal keba AK ba domin dai shi Allah ya sani har yanzun bai fara mata kallon mace ba balle kuma wai ace matar aure, hakan nema yasa yau da ta fito daga sashen Hajiya zata sashen Hajiya jummai ya k'ura mata ido cike da tausayinta,

Kai jama'a Allah dai ya tsine ma shed'an la'anan ne inba shed'an da kitsama mutum mugun abu a zuciya ba dan Allah yana zaman zaman shifa a kofar gida cikin abokan shi kirar wayar shi da wani abokin kasuwancin shi yayi ne hakan yasa dole ya shigo gidan dan ya samu damar amsa wayar a tsanake, bayan ya gama wayar ne fa sai ya d'an zauna dan akwai wani number d'in da abokin zai turo mishi shine fa kafin shigowar number d'in yarinyar nan ta fito tana waya, kuma yasan dai wayar nan bazai wuce da shegen yaron nan Bash D'an gidan Master ba dan yanzun yaga ya bar k'ofar gidan nan bayan ya sauke d'aya daga cikin kannen shi ta shigo gidan, yana mamakin ta yanda har yanzun saurayin nata bai san da batun auren da za'a mata ba, koda yake abune anatayin shi a munafunce, da farko dai yanda take ta fara'a har fararen hakoranta dake jere gwanin sha'awane ya d'auki hankalin shi har yabi fuskar nata da kallo, tofa a kokarin shi na ganin ya dauke fuskar shi akanta ne yayi k'asa da idon shi, shine dan wulakanci irin na sharrin shedan idanuwan shi suka wani ja burki suka tsaya kyam akan kirjin ta doguwar rigar atamfa ce da akayi ma dinkin fitetgown a jikin ta ga shi kuma d'inkin yayi dai² da jikin ta kuma dan iskanci haka nan ta wani fito a binta ko lullib'i babu, shi dai bai san yanda akayi daga kallon fuska ya koma karewa sauran sassan jikin ta kallo ba, Allah ma yaga zuciyar shi bai kalleta da wani manufa ba sai dai sharrin shed'an yasa ya kasa d'auke idon shi a kanta dan koda ta wuce shi ya zamana ta juya mishi baya haka yaci gaba da kallon ta zuwa lokacin kuma sai yaga kamar ma da gangan takeyin wani abun saboda yanda duk inta motsa shima jikinta yake motsawa gaba d'aya kasa katabus yayi har sai da ya dena ganin ta bayan ta kule ma ganin shi, a rayuwar zai iya rantsewa da Allah cewa yaune rana ta farko daya tsaya ya karema halittan wata d'iya mace kallo domin duk wad'anda ke binshi baima da lokacin su balle har ya bata lokaci wajen kallon surar wata a cikin su,
Inba shed'ana irin na shed'an ba duk wannan kallon bai wadatar da shiba har Saida zuciyar shi ke raya mishi wai duk wannan abubuwan da ya gani fa a jikin yarinyar nan a hakan ma fa wai dan bata gama girma bane to in tafi haka kuma ya zata zama kenen? Haka kawai shed'an ya fara hasko mishi ita a matsayin cikakkiyar budurwa, bakon al'amarin da ba kasafai yafiye samun shiba,
sai ga shi yau da rana tsaka sharri irin na shed'an yana so yasa shi a shiga uku domin dai sai ga shi gaba d'aya tsigogin jikin shi da duk wata jijiyar da jini ke yawo a jikin shi ta motsa domin dai alkalamin rubutun shi da koshi bayace ga ranar da yaga ta tashi tsaye car cikin kwanciyar hankali bane yau ta nemi farayi mashi hankoro, shida baya tab'a iya shiga irin yanayin da yake ciki a yanzun inba sanyi yayi sanyi ba koshi din ma sai in kamar yana kallo haka yaci karo da masu fararen kunnuwan nan da allah bai yi halittan kunya ajikin su ba suna aikata aikin nan da Allah ya hana har sai ka biya sadaki ba,
shine kawai yake jin irin hakan amma yau a banza a hofi shedan yana neman ya kaishi ya baro shi.
Runtse idon shi yayi da karfi bayan ya kai hannu ya danne alkalamin dake shirin tona mishi asiri a tsakar gidan fa jama'a, auzubillahi minal shaidanir rajeem haka yaci gaba da mai maita wa, a kokarin shi nason fitowa daga halin da shedan ya jefe shi, wallahi wani irin kunya yaji ya sauko ya lullube shi, Allah dai ya isa kuma bazai daina Addu'ar Allah ya mashi katangar karfe tsakanin shi da shaidan ba, yanzun nan dan Allah da wani yazo ya ganshi a haka mai zaice mishi? Shike nan sai a fara mishi kallon wani dan iska fa,
Lallabawa yayi ya shige sashen shi kuma har lokacin bai daina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan ba. Dan wallahi yau da shedan din nan mutum ne babu ubanda zai hanashi ya shak'o wuyar shi ya faffashe mishi fuska wallahi, amma yayi alwashin har yarinyar nan tabar gidan nan bazai kara bari su hadu ba.

***

Bari mu leka gidan uwar gida.

Daga ita har yaranta sunyi kokari dan ganin cewa kota waya ne sun samu Sarki sai dai ina kwata² hakan yak'i samuwa domin ko abinda basu sani ba shine tuni Teemah duk ta watsa number d'in su a inda ko sun kira shi bazasu samu ba,
Haka dai suka had'a karfi da karfe suke ta hidimar shirin auren da dukiyoyin su domin harta gyaran gidan shi su suka d'auki nauyi sun kuma yi bajin ta kwarai dan sunyi komai fiyema da yanda shid'in zai iyayi dan ganin cewa sun faranta ran uwar gida,

Ganin cewa biki yana ta matsowa babu labarin ango yasa suka shirya cewa daya daga cikin k'annin shi ya shirya ya tafi har Lagos d'in ya shaida mashi cewa Uwar gida fa bata da lafiya kuma tace tana bukatar ganin shi,
Dr Mubarak suka kira yazo gida ya daura mata ruwa domin a zahiri dama tana bukatar shi dan gaba d'aya tak'i kwantar da hankalin ta ganin takeyi kamar in Sarki bai k'ara auren nan ba tofa shike nan zata rasa shine gaba daya.

Kunsan duk abunda kakeyi sai ka samu mai maka bacci da ido d'aya domin ko ashe tun bayan zuwan da Hajiya tayi gidan Malam tayi tijarar da yasa maganar auren na Meenal fitowa cikin kishiyoyin Uwar gida aka samu wacce ta kira Teemah saboda tsabar kwarewa a iya munafunci wai ta kirane ta mata Allah ya sanya alkhairi na Karin arzikin da mijinta ya samu, sosai teemah tayi mamakin kiran domin ita dai iya sanin ta bata san wani abun alkhairin daya samu Sarki wanda har mutanen Zaria zasu kira su taya ta murna akan shi ba,
dalilin hakan ne yasa ta tambayar me yake faruwa ? domin dai su Lagos lafiya lau suke,
To dai uwar gulma dama abunda take so kenan dan haka ta fad'ama teemah cewar ai aure akaba Sarki anan cikin family harma an tsaida rana yanzun haka ma an gama komai na shirin biki,
Sosai abun ya kad'ama Teemah zuciya amma da yake yar barikice bata bari ta nuna cewar ta jijjiga dajin zancen ba sai ma Addu'ar Allah sanya alkhairi da tayi ta yanke wayar ta.

Wani irin katoton ashariya ta lailayo ta maka akan ahalin Sarki tundaga kan manyan harda wadanda ma basuzo duniyar ba duk saida ta tabbatar ta kwashe ma kowa albarkha,
tafayi hauka son ranta a gidan ta ita kad'ai sai dai tayi alwashin cewa aure koh! Ita bazata hana shi aure ba tunda har aure suke so ayi auren saboda tanan nema zata kara tabbatar musu da cewa ita d'in taci dubu sai ceto Allah ya kaimu lokacin biki lafiya, tafa cije kwarai ta yanda hatta kawayen ta babu wacce ta fad'ama cewar mijin ta zai mata kishiya kai in ma ta bari akaji ai taji kunya wallahi wai Ita Teemah ita ce har uwar miji zata ma kishiya dan wannan ai bazata ce mijin ta zai mata kishiya ba dan a yanzun kam tasan wallahi ko cocaine Sarki ke shak'a bai isa yace zai mata kishiya rana tsaka kamar saukar aradu ba, to su shirya zata aje kowa a matsayin shi kamar yanda ta saba, a zaton su tana raye har zata zuba ido wata karamar yarinya ta shigo mata gida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login