Showing 147001 words to 150000 words out of 174305 words
Chapter 50 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
tunda ga yayan su,"
Duk wannan surutun uwar gida bata tofa musu kalma ko daya ba, tun bayan gaisuwar da sukayi ta tambaye su mai jiki suka amsa mata ciki suka lek'a suka iske shi yana bacci shine dalilin da yasa suka dawo nan d'in suka zauna,
"Sa'eed ka samu ganin Dr Mubarak din ne?"
Uwar gida ta tambaya,
"Ah ah ban samu ganin shi ba domin lokacin dana iso yana tare da Hajiya innah da Meenal,"
"Muje ka rakani ina son ganin shi"
Ta fad'a tana mikewa,
Tashi suma kannin sarki sukayi da niyyar rufa mata baya.
"Ku zauna bana buk'atar rakiyar ku, muje Sa'eed"
Komawa sukayi suka zauna din badan sun soba dan tabbas sunso suje su jiyo abinda yake damun shi,
Jagora Sa'eed ya mata zuwa office din na Dr sun iske shi yana ta faman cike ciken wasu takaddu,
Da sallama suka shiga bayan nocking din farko da Sa'eed yayi Dr ya basu damar shiga,
Mikewa yayi daga kan kujerar da yake zaune yana ma uwar gida barka da zuwa,
"Kai Sa'eed haka akeyi? Ya zaka wahal dasu su taho bayan nace maka suma wadancan ka sallame su su koma gida dan shima insha Allah ina saran daya tashi zamu bashi damar komawa gida,"
"Kai DR kamar baka san halin suba, kaima kasan bazasu zauna ba" Sa'eed ya bashi amsa.
"Ba laifin shi bane likita, ai gara muzo dai muga halin da yake ciki dan Babana ba gwanin ciwo bane nasan ba abu kad'an bane zai kawo shi kwanciya asibiti"
"Bismillah to ku zauna"
Zaman sukayi kamar yanda ya buk'ata,
"Meke damun shine Dr?"
Numfasawa yayi sannan ya maida duban shi kan Sa'eed,,
"Dan bamu waje ina son magana da ita! "
"Babu buk'atar fitar nashi domin da Sarki da Sa'eed duka yara nane, kuma Sa'eed ba yaro bane balle inyi fargaban cewa in yaji wani abun zai yad'a a waje, dan haka fadamin meke faruwa kanka tsaye karka boyemin komai"
Kamar yanda ya korama Hajiya bayani haka ita ma ya fada mata silar ciwon na Sarki harda abinda Hajiya ta fad'a mishi kafin taja Meenal su bar asibitin duk sai da ya kora mata komai daya faru,
"Innalillahi wa'innah ilairir raju'unΒ³ abinda yaron nan ya aikata kenan,? "
Shi kawai uwar gida ta samu damar cigaba da maimaitawa, yayin da shi kuma Sa'eed mamakin maganar yayi mashi mugun dukan daya koma kamar hoto sai kallon Dr Mubarak kawai yake cike da mamaki,,,
"Nagode Dr"
Uwar gida ta furta a yayinda ta mik'e, tana gama furta hakan kuma ta fice Sa'eed na take mata baya,
"Ku tashi mu tafi jikin nashi da sauk'i Dr yace da zarar ya farka zasu sallame shi,"
Haka ta tasa k'eyar su duka sai Salman kawai aka bari k'anin Sarki ne shi din,
Tace mishi ya zauna in Sarkin ya farka sai su dawo gida tare,
Bayan dawowar su kowa gida ya shiga amma ita kai tsaye gidan Sarkin ta wuce,
Tayi sa'a tana shiga motar Meenal na shirin ficewa daga gidan, wanda ganin uwar gidan ne yasa Meenal din daka tawa tana fad'ama hajiya cewa "ga maman Ya Sarki nan"
"To me zamuyi mata, ko sunje asibitin ne basu ganki ba ta biyo dan taji dalili, to ni ai dai dai nike da kowa kashe motan dan in samu bata sak'o da kyau atoh"
Zagawa gefen da Hajiya ke hakimce uwar gida tayi,
"Barka da yammaci Hajiya"
"Barka kadai yame jikin?"
"Alhamdulillah Dr ma yace zuwa anjima zasu bashi sallama saurin da nike tayi kenan dama in iske ku"
"Allah sarki ai kuwa da kin b'ata lokaci bazaki same muba, ina fatan kuma shi likitan ya shaida miki komai kamar yanda nima ya fad'amin?"
"Kwarai Hajiya na samu labarin komai, kuma banzo nan dan in hanaki tafiya da ita ba, nazo ne dai dan in banki hakuri wallahi ban san duk abubuwan da suke faruwa ba kenan tsayin shekarun nan,
Kuma insha Allah tunda har ya nuna baya muradin ta ni nan da kaina zan amso mata takardar ta kamar yanda na zama silar had'a auren"
"Ah ah to madallah! Madallah!! Abu yayi kyau dan dama nima shawarar dana yanke kenan, yanzun dai in Allah yasa ya rubuta sakin sai kibayar a kawomin can gidana, in kuma babu hali nima da kaina ina iya dawowa gobe in amsa tun da kince anjima zai dawo, kuma kiyi iya bakin kokarin ki ki hana iyayen su maza jin batun nan dan nasan tsaf zasu hana suce bazaiyi sakin ba, kuma in hakan ta faru nidai ba hakuri zanyi ba daga karshe ma ina iya ganin laifin ki wallahi tunda dai kece uwar shi, jikata dai hakuri iya hakuri tayi shi to allah ya bada lada ya kuma had'a kowa da rabon sa, ke Meenal tuk'a mota muje yamma na dad'a yi"
Ficewa sukayi daga gidan ita kuma uwar gida ta karasa wajen masu gadi,
Gargadi ta musu sosai akan koma waye yazo gidan karsu barshi ya shiga indai ba mai gidan bane, sannan karsu sake su fadama kowa cewar Meenal bata gidan.......
*Ummiee Zaria*βπΌ
π₯°π₯°π₯° Son so my people
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: π±βοΈπ¨βπ©βπ§βπ¦ *DANGINA!*π¨βπ©βπ§βπ¦βοΈπ±
~{{MY FAMILY}}~
*FREE BOOK*
*RUBUTAWA*
*UMMIEE ZARIA*βπΌ
````` *Page 43*.....
Bayan Uwar gida ta koma gida wayar Salman ta kira ta fad'a mishi cewar da zarar an sallame su su taho nan gidan ne kai tsaye bawai gidan Sarki ba,
Sauran yaranta dake nan gida wadanda basu gama komawa nasu gidajen ba sun so su kawo suka akan dalilin da yasa Meenal tayi tafiyar ta tabar Sarki a asibitin a matsayin ta na matar shi, ganin suna son suga laifin Meenal din data biyema kakarta ta tafi,
hakan yasa ta taka musu burki akan cewa ita ma Meenal din bata da lafiya ne shi yasa bata zauna ba, wasu daga cikin su sunyi Na'am da hakan wasu ko sun daijita ne kawai, domin dama dai ba komai ne in kayi zaka burge wani ba.
Bayan isar su Hajiya gida, masu gadin gidan tayima magana suka kwaso mata kayan Meenal zuwa cikin sashen ta, dakin dake kusa da nata suka sa kayan,
Ita ko Hajiya tun bata zauna ba ta d'auki waya ta fara kiran Turai (kakar billyn ya Sa'eed in baku manta taba).
Babu b'ata lokaci bayan Turai ta d'auki wayar hajiya tace
"Turai komai kikeyi dan Allah ki sake shi ki taho gidana ina buk'atar ganin ki da gaggawa"
Bata tsaya jin ta bakin Turai ba ta yanke wayar,
Hajiya Jummai ne ta shigo sashen da sallama.
"Hajiya barkan ku da dawowa, ina daga falona naga ana sauke kaya daga motar Meenal shine ma yasa nace bari in taho in gani ko bak'i mukayi?"
"Bari! Bari!! Bari kawai Jummai aini yau ni naga abinda yafi zare tsayi, ai dama ko baki shigoba nida kaina zanyi kiranki ki taho muyi jimamin tare,
To gata nan dai na taho da abata gida tunda zaman gidan mijin ni dai banga ranar shiba"
Tunda Meenal taji Hajiya zata fara rattaba zance ta mike tsam, ta haye sama, dan haka nan sai take jin zuciyarta Sam ba dad'i,
"Banfa gane ba Hajiya! Auren nata ne ya mutu bayan barin ta nan gidan d'azun ? Ina ce d'azun nan tabar gidan nan, to koma warta gidan ne har akayi saki ko yaya?"
"Ji Jummai da wani batu, toni in sakin akayi har zan damu kaina ne! Kawai mugunta da bak'in hali irin na soja mutumin nan yaje ya kafe min jika a gida yana kallon ta kamar hoto"
"Banfa gane ba wallahi Hajiya"
"Aifa Jummai ba ganewa zakiyi ba tunda ban miki bayani ba, ke dai nemi wajen zama dan in kin ji abinda ya faru kina iya yanke jiki ki fad'i,"
In kunga yanda Hajiya keyi zakuyi zaton wani k'aton zunubi Sarki ya aikataπ€£.
Wurjanjan haka Turai ta iso falon na Hajjaju ko damar yin sallama bata samu ba,
"Innah lafiya kuwa meya faru kingan nifa haka na fito daga gida zuwa nan takalmi na wari da wari?
wane ne ya mutu hala?
dan daga yanda naji kina magana na tabbatar ba lafiya ba"
Wajen zama Hajiya ta nuna mata da hannu batareda ta ce k'ala ba,
Zaman ko tayi a gefen data nuna mata.
"To masha Allah anan kusa dai gidan duniya kune kad'ai zan kira da shakikai na wadanda zan fad'amu duk wani abun da ke damuna in na kuka ne muyi tare haka ma in dariyar ce muyi tare,
Nasan dai dukan ku baku manta yanda auren Takwara ta yar wajen Jidda ya kasance ba?"
"Kwarai bamu mance ba"
Suka had'a baki wajen bata amsa,
"Masha Allah, kuna dai sane da yanda aka munafunce ni aka bayar da jikata har a kasa ranar aure ban samu labari ba sai da biki ya rage saura sati 3,
ku biyun nan ku kukayi tsayin daka a sanda naso in botsare cewar ban yarda ayiwa jikata auren dole ba, kuka bani hakuri inaji ina gani aka d'auki karamar yarinyar nan aka aurama Soja mai mata harda yara 4 a lokacin dan kawai ya kasance dan uwanta"
"Kwarai kuwa haka akayi"
Turai ta fad'a tana kara gyara zaman ta dan sosai ta k'agu taji me ya faru.
"To dai yarinyar nan a hakan kowa ya shaidane domin dai taba marad'a kunya wajen yima iyayen ta biyayya ta kuma amshi auren duk da bason mijin take ba, hasali ma ashe tana da wanda take so daban amma burinta nayin karatu yasa ta kasa bashi dama ya gabatar da kanshi,
To ku bud'e kunne kujini da kyau, wai kun san cewa tsayin shekarun nan 6 da watanni da auren su amma shi mijin bai tab'a kusantar taba!"
"La'ilah ha'ilallahu muhammadur Rasoulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam, innalillahi wa innah ilaihir raju'un, lahaulah wala kuwwata illah billah to shi dama bashi da lafiya ne kuma ya yarda aka aura mishi ita, ko ya abun yake?"
Jummai ta tambaya cike da jimami, ita ko Turai salati kawai takeyi tana sanar ma ubangiji,
"Ke Innah wai wannan maganar naki gaskiya ko wasa?"
Turai ta tambaya itama dan wannan batu kam ai yafi kama da tatsuniya, jama'a inba tatsuniya ba a ina za'a kaima namiji mace kamar Meenal ace wai shekara da shekaru bai tab'a taba,
"To dai kuma zaku gama jimami ne ku fuskanci gaskiya, domin ni tun shekarun baya na san da batun, to a lokacin tsakani da Allah na ta'allaqa hakan ne da sharrin matar shi dan kowa dai yayi mata shedar tsafe tsafe, bayan na qara binciken ita Meenal din ta tabbatar min da cewa ko d'aki guda basu tab'a had'awa ba sai na fara neman musu maganin karin asiri dana tsarin jiki,
Bayan ni na saki jiki cewar ita tayi musu amfani da maganin kamar yanda na fad'a mata ashe ita shashashan iya wanda na ware a matsayin nata kawai tayi amfani dasu sauran kuma ta ajiye a gefe, to nidai tun sannan ban K'ara tambayan ta ya ake ciki ba, tunda dai kullum na tambayeta ya suke zaune cemin take lafiya lau, to indai yanke muku zance,
Ke Jummai ai wajen ki ta fara sauka data shigo d'azun daga makaranta koh?"
"Eh kwarai kuwa wajena taci abinci tayi sallah ma kafin ta iso nan"
"Madallah to ashe wai bikin da akayi na k'annen mijinta ita kishiyar nata tazo kamar yanda ta saba......
Kaf abinda ya faru a yau din na zuwan Teemah gidan da kuma komawar da tayi gida ta cimma Sarki ba lafiya dama abinda likitan ya shaida musu harda had'uwar su da uwar gida kafin su baro gidan meenal tsaf ta kwashe ta rattafa musu "
Koda ta gama koro musu bayanin shiru tayi suma ta basu damar tofa nasu albarkacin bakin,
"ku dakata ban san ko kun hango abinda ni nike hasashe ba,"jummai ta fada,
"Me kike hasashe ne?"
Suka tambaya suna kallon ta dason jin me hasashen nata ya k'unsa,
"A nawa hangen sai nike ganin wannan abun fa ba haka banza bane ya auku, tabbas akwai wata a kasa, tunda tun farko dama kowa yasan cewar matar shi matsafiya ce, bakwa ganin kamar itace ta aikata wani abun ta yanda shi bazai tab'a jin sha'awar ita Meenal din ba?"
Turai ne ta amsa da cewa,
"Ah ah Jummai babu wani batun asiri rashin soyayya ne kawai tunda gashi har likita ya tabbatar da cewa ciwon sha'awa ne ke damun shi, ita dai Meenal din itace ya jingine tunda ai gashi nan baro baro cewa da lafiyar shi"
"Banki ta naki ba Aunty Turai amma nima nawa maganar tana kan hanya, saboda dai komai kiyayyar da miji yakewa mace akwai ranar da in sha'awa ta kamashi dole zai ture zancen wannan kiyayyar a gefe ne ya nemeta domin itafa sha'awa bata san yaren rashin soba inba haka ba dan me ake cewa ruwan kashe gobara basai mai kyau ba, Ko kun manta ne cewa in ana son a shiga tsakanin ma'aurata babu ta inda ba'a bi, *misali*
*Wasu zakuga an sakar ma ita matar warin jiki*,
*Wata matar kuma jini ake sake mata*
*Wata ko tsoron mijin za'asa mata ta dunga kallon shi kamar dodo*,
*Shi kuma wani mijin a duk sanda yaje kwanciya da matar sai ya rasa kuzarin shi na d'a namiji ta yanda bazai iya kusantar taba*,
*Ko kuma ita mace a mata asirin da in mijin yaje neman ta sai gaban ta ya koma irin na namijin ko kuma wajen ma ya shafe gaba d'aya*, akwai hanyoyi da yawa da ake amfani dashi wajen dakushe alaqar aure tsakanin mata da miji,
To ita dai Meenal din ina ganin in ba'a samu daya daga cikin abinda na lissafa a kanta ba to sai dai insha mijin ne akayi nasarar cire mishi sha'awar ta a duk sanda yake tare da ita.bari in kira Meenal din muji ta bakin ta"
"Meenal" Hajiya ta kwalama kira,
Jin shiru bata amsa bane yasa ta kiran Larai,
"Larai haura sama ki kiramin Meenal ku sauko tare"
Taren ko suka sauko.
"Meenal zoki zauna anan tambayar ki zanyi"
Hajiya Jummai tace,
Zaman Meenal tayi kamar yanda ta buk'ata,
"Ke takwara ina fatan dai baki kira kowa kika shaida mishi cewa kina gidan nan na d'auko kiba koh? "
Hajiya innah ta tambaya tana kallon Meenal din.
"Ban fadama kowa ba"
"To kin kyauta ma kanki, kuma ki jini da kyau koda uwar kice ta kiraki bance ki d'auka ba dan nasan suna samun labarin bakya gidan zasu fara kira suji ba'asi kin san kuma ba uzuri zasu miki ba iyakacin suce ki koma, in kin koma koh kin san abinda kika baro nedai zaki tarar dan yanda shi mijin bai damu dake ba suma iyayen naki bana tunanin sun damu dake tunda har suka iya banzatar dake tsayin shekarun nan babu wanda a cikin su ya damu da sanin yanda kike rayuwa a gidan mijin da suka zab'a miki, gaba d'aya ma sun manta cewar auren dole suka mashi, to wallahi kinji dai na fad'a miki dan haka ko malam nema ya kiraki karki sake ki koma, in kuma kinsan kasa zaki watsanin a ido kina son mijin ki to tun kafin dare yayi ko kuma kizo daga baya ki kullaceni gara ki shaida min gasu Jummai nan su mai dake gidan ki atoh, dan ku yaran yanzun wani abun za'ayi dan a muku gata ku kuma sai kuga kamar cutar ku akeyi"
"To ni Hajiya nace miki zan koma ne dama?"
"Baki ceba amma ai gara in kara tabbatar wa a gaban su Jummai dan sumin sheda in magana ya tashi dan yanzun na tabbatar laifin duniya akaina kowa zai daura gani zasuyi kamar nice keson kashe miki aure, nasan babu wanda zaiyi la'akari da zaman da kikayi a gidan ba tareda wani abu ya gifta tsakanin ki da mijin ba,
Kaini ai nagode allah da Allah yasa kaf cikin yarana da jikokin babu dan iska,
Ku duba ku gani fa yanzun dan Allah in wata yarce aka ma irin auren nan hakan ya biyo baya mai kuke zaton zai faru? Ai wallahi tikitin iskanci ta samu kyauta, sai gashi jikata ko karar shi bata tab'a kaiwa wajen wani dan ya danne mata hakki ba, matan yanzun da ko mijin suka samu baya kai musu yanda suke so sai dai ku tsinci maganar a kotu anje gaban alkali batun kashe aure, in Kuma hakan bai samu ba shi kenan sai mace ta fara rab'e rab'e tana bin wasu mazan, allah dai ya shirya mana zuria"
Ameen duk suka amsa mata dashi baki daya.
"Meenal nace wani irin zama kikayi da mijin ki tsayin shekarun nan? So nike ki fad'amana komai bakin gaskiyar ki munan dukan mu babu wacce bazatayi tsaye wajen kwato miki hakkin kiba in munga za'a tauye ki,
Fad'amin shi din kina jin tsoron shine shi yasa koya neme ki bakya yarda ko ya abun yake"
Jummai ne ke tambayar ta.
"To aini bai tab'a nema na ba wallahi, abinda shekarun baya ma ko sashena baya shigowa daga baya nefa inya shigo ya fadamin abinda yake buk'ata sai ya koma d'akin shi,"
"To ke da baya zuwa mai yasa bakya binshi can nashi d'akin?"
"Kai" Meenal ta fad'a tana zaro ido waje,
"Eh baki san in miji baizo inda mace take ba ita macen ba laifi bane dan ta bishi, ai babu laifi akan hakan ko kin tab'a zuwa ne ya koroki?"
"Ah ah ni gaskiya ban taba zuwa ba, Kuma fa ko abu yace in kawo mishi da nakai yake cemin Ina iya tafiya"
"Kenan dai kina so kice baku tab'a samun kusanci dashi ba kwataΒ²? "
"Eh gaskiya bamu tab'a ba"
"To me ya faru ayau da har yayi sanadin da ciwon shi ya tashi tunda dai likita yace ciwon sha'awa ne ya kama shi"
Shiru Meenal tayi ba amsa.
"Karkiji kunya ki fadamin gaskiyar abinda ya faru"
A daburce ta fara ba da labarin yanda ta iske shi a kwance a kasan tile's yana murgine murgine dama yanda yaso kusantarta tak'i duk da bawai ta bud'e musu komai bane amma haka take magana kunya duk ya gama rufe ta.
"Tashi ki koma d'akin ki"
Jummai ta bata umarni bayan ta gama sauraren ta, aiko kamar jira take dama domin tuni tayi bacewar b'at a wajen.
"Kun fahimci wani abu a labarin ta"
"Yo mu me zamu fahimta ko , bayan kinsata a gaba kina mata tambayoyi irin naku na tsofaffin lauyoyi,"
Cewar