Showing 99001 words to 102000 words out of 174305 words
Chapter 34 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
harma ta kwanta mata da miji tayi ciki itama ta haihu God forbid bad thing over her death body ai gara ace bata raye da dai taga zuwan wannan ranar.
Koda d'an sak'o ya iso daga zaria akan cewar uwar gida bata da lafiya tana bukatar ganin Sarki ko kadan bata tada hankalin taba sai ma dama data ba Sarkin akan in ya isa yasa a gyara mata gidan ta itama in an kwana biyu zata zo ta duba jikin Uwar gidan, yaji dad'in furucinta sosai a ganin shi ta fara saukowa tunda har gashi ita da kanta yau ta furta zataje duba jikin mahaifiyar shi, bai san cewa ita tayi hakan bane saboda ta samu lokacin da zata shirya ma zuwan kishiyar nata da kyau.
A ranar da suka isa zaria hankalin Sarki ya tashi matuka a yanda ya samu mahaifiyar shi domin kwanciya tayi nakwa nakwa tamkar wacce tayi doguwar jinya, ganin ta a cikin wannan hali sosai ya d'aga mishi hankali ya faraji a jikin shi cewar bai kyauta ba, ga kuma yanda hatta da yaran shi suke ta mamman ne mishi saboda ko suma sunyi kewar shi sosai dan ko a waya basajin duriyar shi balle kuma na uwar su, hakan nan a kasar zuciyar shi yakejin bai kyauta ba sai dai koshi bai san dalilin daya hanashi zuwa garesu ba, shifa zaima iya cewa gaba daya ma mantawa yayi dasu wallahi.
Ganin da uwar gida tayi cewar jikin shi yayi sanyi kwarai yasa ta bijiro mishi da bukatar ta cewa son take a daura auren shi da Aminatu kamar yanda ta fada mishi tun tuni dan tana son taga auren kafin ta mutu dan a cewarta tasan ciwon ta bana tashi bane, sosai dai tayi mishi hannun ka mai sanda had'e da nasiha a matsayin wasiyyarta a gareshi,
Da yake abinda ke dawainiya dashi yafi yin tasiri ne a sanda yake tare da Teemah hakan yasa cikin kwanakin ya maida hankalin shi kachokan wajen ganin ya kula da mahaifiyar shi da kuma son ya cika mata burin ta na auren da take son yayi duk da allah ya sani wallahi ba ya bukatar K'arin kowani aure a yanzun dai, to shi mai yake nema a yanzun da baya samun shi a wajen matar shi? Su dai kawai dan basa son teemah ne shi yasa suka kasa yi mata uzuri, amma tunda sun dage da maganar auren zaiyi kowa ma hankalin shi sai ya kwanta, to amma Teemah fa? Zuciyar shi ta tambaye shi, ya gode Allah ma da tace zata zo inya so in tazo zaiyi kokarin fahimtar da ita yanda abun yake, shifa yanzun damuwar shima yanda suka tashi suka zubama yarinyar can da suke kira matar da zai aura kaya a gidan sama da kasa duk kayan tane ga kuma Teemah tace a gidan zata sauka shi dai kawai nema suke su sakashi cikin damuwa, ga kuma wata magana da uwar gida keyi na cewan wai yaje ya samu yarinyar yaji ko tana bukatar wani abun na sha'anin biki, yanzun fisabilillahi shi da girman shi da komai sai yaje yasa a mishi sallama da yarinyar can dako hankali bai isheta ba wai da sunan yazo wajen ta, kai ina ai sai dai ya nemi wani ya aika, shi babban damuwar shi ma yanda duk suka wani kira abokan aikin shi dana kasuwancin shi suka fad'a musu maganar bikin yanzun haka zasu zo suga amarya wata yar ficika a wajen bayan kowa yasan tsarin shi.
(Jama'ah Sarkin nan mafa dan rainin wayau ne ku fad'a mishi da babbar murya cewar muma auren dole za'a mana ba son shi mukeyi baπ).
isowar su Moon sosai ya kara sa Meenal ta sake jikin ta suke abubuwan su ita da kawayen ta kullum kuma tana lissafin kwanakin da suka rage mata ta koma gida aci gaba da hidima da ita da yike ma ba wani shagalin biki za'ayi ba walima ce kawai aka shirya za'ayi su kuma sun shirya yin zaman yinin su a gidan su Meelat yanda zasu fi sakewa,
Tun ranar da shedan ya nemi sa AK yayi abun kunya ya kama kanshi ya kiyaye duk abunda zai had'a shi da Meenal a cewar shi amarya tsautsayi gareta dan a yanda ya tara ta da yawa din nan yasan inya riketa tofa bazata sha ta dad'i ba a hannun shi,
Sai dai a yan kwanakin sosai su Moon suka matsa mishi akan alkawarin wayar daya musu da dad'ewa akan in sun gama secondary zai siya musu manyan wayoyi dan so suke suci biki da wayoyin su a hannu yanda zasu samu daukar hotunan biki.
Share Please
#Ummiee~Zaria
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: βοΈπ±π¨βπ©βπ§βπ¦*DANGINA!*π¨βπ©βπ§βπ¦π±βοΈ
"""""Page 30
Meenal kuzo muje Ya Ak yana kiran mu,
d'ago kanta data d'aura akan pillow tana waya da D'an gidan Master tayi tana maida duban ta zuwa ga Moon dake maganar,
"In kunje kuce mishi nayi bacci" ta fad'i hakan k'ara maida hankalin ta kan wayar da takeyi dan sosai takejin dad'in waya da Bash dan tsaf yake maida kanshi karamin yaro yayi ta biyema shirmen ta.
" kutmelesi lallai nema Babin nan Kin ma isa kisa inyi k'arya! Wallahi inya tambaya cewa zanyi kince baki zuwa, Moon taso muje waya sani ma ko alkhairi ke kiran mu"
Banza Meenal tayi da ita su kuma ganin hakan suka sa kai suka fice basu k'ara bi ta kanta ba.
Tana nan a kwance tana ci gaba da wayar har suka dawo, da gudun besfa suka shigo d'akin suna ihun murna suka wani kankame ta suna cigaba da ihu,
"Ke dallah ki yanke wayar nan haka, alkhairin Allah ya same mu da rana tsakar nan"
Aisha ta fad'i hakan tana karb'e wayar Meenal d'in ta kashe ta gaba d'aya,
"Ke miye haka bamu gama maganar da mukeyi ba fa kike kashe min waya dan Allah,
Ni bani wayata kina ganin ina zaman zamana Bash yana neman ya kwanto min kurar da zata cinye ni har kasusuwa na"
Babu wacce tabi takan abinda take cewa a cikin su sai ma kwalayen dake hannuwan su da suka mik'a mata a tare. Surprise suka had'a baki wajen fad'a cikin ihu.
"Ke Beb please bar wannan zancen a gefe duba kiga abunda muka samo" cewar Aisha, bin kwalin wayar Meenal tayi da kallo a yayin da ta wuntsulo babu shiri zuwa inda suke " ke Sister kamar fa kwalin waya nike gani,ko idanuwa na ne basa gani da kyau?" Hannuwan ta bibbiyun ta mik'a ta karb'i kwalayen a hannun su,
Aisha ce mai taya ta bud'ewa dan Moon gaba d'aya tsabar zumud'i yasa ko zama ta kasa murna kawai takeyi ji take tamkar ta lashi tafin kafarta tsabar dad'i,
Bayan sun fidda wayar daga cikin kwalayen su kuwa haka suka dunga kallon wayoyin kamar wasu sabbin shiga,
"Ke Moon wallahi wannan irin wayar dake hannun Aunty Sas ce, wooo mu yan mata muma mun faso gari, Allah dai ya k'ara arziki Mai Jama'a wallahi Ya'ya ya dad'e bai burgeni irin yau ba, ashe da rabon muma zamu rike babbar waya yar shafa"
kashewa sukayi ita da Moon cike da farin ciki gefen Aisha Moon ta zauna,
"ke Sister ai wallahi Ya AK dan aljannah ne kin san Allah dayace muzo cikina harya d'ura ruwa all my thought nayi zaton ko waccen mai zubin yan ruwan ta fad'a mishi tsokanarta da Meenal tayi d'azun ne shi yasa nike ta rara gefe, Allah dai yabar mana Yayan mu ya nuna mana ranar auren shi ku kwakw kwaso Alanta da shoki wallahi"
"Kaiii.. wai ban fa gane ba ,ku tsaya mu nawa ne a wajen nan? " Meenal ta tambaya.
"Uku" suka had'a baki wajen bata amsa.
"To mu uku amma kuma naga wayoyin kwaya biyu kacal tawa wayar fa? " ta tambaya tana daure fuska,
"nifa ban son halin wariya da nuna yan ubanci ya zai baku waya bai bada nawa ku kawomin ba?"
"Dallah rufema mutane baki Malama ba saida mukace miki yana kiran muba? Fad'amin wani amsa kika bani ? cewa fa kikayi muce kinyi bacci, to badan halin kiba dai yace in kin tashi kije yana neman ki"
"To aini da nace kuce ina baccin nayi zaton an kai mishi gulma nane, kunga karku kunna wayoyin bari inje in amso nawa in dawo, kuma Malamai bari inje in dawo in baku labari D'an gidan master zai ballo min ruwa wai zai tura iyayen shi wajen Malam a mishi tambayar aurena "
"Tambaya? " suka had'a baki wajen furtawa suna masu zaro idanuwa waje,
Moon ne ta kalli Aisha sannan ta d'aura da cewa "neman aure cikin neman aure kenan fa? Tab"
Meenal batabi takan abunda Moon tace ba ta fice daga d'akin tana mai cewa bari taje ta dawo, har ta fita kuma ta dawo ta d'auko wani zumbulelen Hijjabin Aisha ta zumbula ta fice daga d'akin,
Bayan fitar ta Aisha ne ta kalli Moon,
"Waike mai yasa bakin ki bashi da kintsi ne? Yanzun da kikace neman aure cikin neman aure data fahimci wani abun kuma mai zakice mata? "
Shiru Moon tayi ba tareda taba Aisha amsa ba sai can ta nisa kafin tace, "Aisha wallahi ina matuk'ar jin tausayin Meenal ban san ya zataji a yayinda batun auren ta kai tsaye zai isa zuwa gareta ba? karfin hali kawai nikeyi wajen danne harshe na amma ni banji dad'in da aka boye mata ba, auren mutum yau sauran kwanaki amma ace mutum bai sani ba! Kalli yanda take ta shirye shiryen ta hankali kwance, kina jin fa saurayin ma da take ikirarin tana so d'in ma ta kasa bashi daman zuwa gaban iyayen ta saboda ya nuna auren yake so da wuri" ta karasa fad'a hawaye na taruwa a idon ta,
Matsowa kusa da ita Aisha tayi, "Moon duk yanda kikeji nima inajin kwatan kwacin hakan to amma ya zamuyi tunda iyayen mune suka zab'i su boye mata nasan suna da nasu dalilin nayin hakan, nidai Addu'a na Allah yasa mijin yana son ta nasan in shi yana son ta komai zaizo da sauk'i domin shi zaiyi k'ok'arin cusa mata soyayyar shi a hankaliΒ², kuma ai su dama gidan su kinsan da wuri ake musu aure sai dai gaskiya nima inajin tausayin Bash dan na lura kaf cikin samarin ta yafi sauran sonta itama kuma naga alamar kamar tana d'an son shi duk da dai kullum tana cewa bata wani son shi nasan karya takeyi. Amma dai kiyi hakuri ki rufa ma kanki asiri karkiyi katobaran da maganar auren nan Meenal zataji shi a bakin ki tunda har su Meelat suka kasa fad'a mata to kema kisa ido"
Bayan fitowarta kai tsaye d'akin shi ta wuce dan tasan ba lallai ace harya koma majalisar shi ba dan tana lura bai fiye zama a wajen da rana fatse fatse ba,
Jiyo karar TV yana aiki a falon hakan yasa dole sai da ta bud'e murya ta kwad'a sallama yanda zai jiyota,
Daga ciki shi kuma bayan ya amsa Sallamar kana ya bata umarni akan ta shigo,
Su uku ne a falon, Musty, Yusuf Wase, sai kuma shi Dan mai k'arfin, kamar wata ta Allah haka ta durkusa har kasa tana gaishe su kamar malamar islamiya, su dai sauran amsawa kawai sukayi ba tareda sun raya komai a cikin ran suba, shiko gogan k'are mata kallo kawai yakeyi da mamaki yau kuma bayan dogon hijjabin data aro harda wani gaisuwar munafunci kuma har k'asa.
kai shifa yaga alamar shi kad'ai yarinyar nan ta raina ma wayau wato saboda tasan abun da ta aikata d'azun shine yanzun ta wani zo kamar wata ta Allah, to shidai bazai biye mata su zama d'aya ba.
"Zauna mana kin ma mutane tsaye a Saman kai"
ya fad'a yana mata nuni da kujerar dake gefen shi,waje ta nema ta zauna d'in kamar yanda ya buk'ata,
"Ya Musty an gama mana d'inkin mu kuwa? Kasan gobe zan koma gida! "
"Haba Bestyn mu kayan Amarya guda ai dole a had'a shi da wuri, Mai kyau bata fad'a miki nakai mata su wajen ta jiya bane? "
"No bamuyi waya ba yau dan dama tace min yau bazata shigo nan ba sai da yamma"
Katse su AK yayi da cewa.
"Malam idan kana son magana da itane ka bari in sallameta tukun na, amma yanzun nina kirata! "
Ba tareda Musty ya tanka abunda AK d'in yace ba, ya mik'e ya shige ciki yana cema Wase "Yusuf in zaka fita ka tasheni please".
"Gani Ya'yan mu" tace jin shiru bai kara cewa komai ba.
"Miye ma sunan ki? "
Dagowa tayi ta kalle shi,
Dan Allah jama'a inba neman magana ba kuji min wani tambaya fa, "Wai yauma ka k'ara manta sunan nawa? "
Shiru yayi bai bata amsa ba, ita kuma dan a zauna lafiya burinta dai ya bata wayarta ta samu damar fecewa a d'akin in yaso sai ya ciji kanshi ma in yaso, hakan yasa ta bashi Amsa da cewa "Meenat, Meenal, Ameenatu yar Baba Malam"
"Shekarun ki nawa? "
"Saura kad'an in cika 17"
Sai da ya d'ago idanuwan shi yayi mata kallon mintoci sannan yana ci gaba da kallon nata yace "mai ya had'aki da wacce tazo nema na d'azun har kika mata rashin kunya? "
Saida ta wani d'auke kai tana hararar gefe sannan tace "to ba ita bace kawai zata wani shigoma mutane gida kai tsaye kamar gidan, su kuma kawai daga gani na kamar wata nid'in yar aiken ta ce zata wani cemin (Kee shiga ki kiramin Abdul) ta fad'i hakan tana kwaikwayon muryar Hafsan, To shine ni kuma nace mata ba ke ba sai dai Keke, to kawai daga nace haka shine zata wani tasomin tana min masifa harfa kamar zata rufeni da duka ta ringayi wai na mata rashin kunya ni kuma nace mata ai da bata baro gidan su tazo gidan su saurayi ba da nima ban ganta ba balle in mata rashin kunyan"
Shiru tayi bayan takai nan a labarin da take bashi, jin ta tona ma kanta asiri, itafa matsalarta d'aya shine bata iya shirga karya ba, atoh gaskiyarta take fadi sai dai uban kowa ya mutu.
"Uhummn ina jinki cigaba ai ba iya nan aka tsaya ba sai kuma kikace mata me inajin ki? "
Shiru tayi tana rarraba idanu,
"Kimin magana"
ya fad'i hakan a yayin da ya d'auko kwalin wayar dake gefen shi wanda tunda ta shigo falon idon ta ke kan kwalin kuma tsaf yake ankare da ita,
"Kinyi shiru ko iya abunda ya faru kenan? "
"To ba ita bane tazo gidan mutane kuma ta kama musu masifa, in ma aikena zatayi ai sai tace min kanwata shiga ki kiramin Yayan ki Abdul in yana ciki,cikin lalama koba komai ai tunda ta haifeni ai bazan k'i zuwa ba, to ni kuma da naji haushi ne nace mata ai itama gashi nan ta zama tuzuruwa kullum tana yawon zuwa wajen saurayi bayan tasan ba auren ta zaiyi ba"
Zumbur ta mik'e ta koma can bakin kofa,
"Wallahi kika sake kika bar d'akin nan kin ma kanki"
ya fad'i hakan a yayin da yake nunata da kwalin wayar hannun shi,
bubbuga kafafuwan ta ta farayi a k'asa cike da shagwaba irin na sakakkun yara sannan tace "ai wannan d'aukar alhaki da jan raine in dai dan Allah zakama mutum abu ai basai ka tsaya ka fara tono tsofaffin laifukan da yayi maka ba, kuma dai ai koba komai Allah yana son mutum mai yafiya mai maida komai ba komai ba, kuma ni ai taimakon ta nayi dan Manson Allah S, A, W cewa yayi in kaga mutum yana aikata ba daiΒ² ba ka fad'a mishi gaskiya in yaso ko baiyi amfani da abunda ka fad'a ba kai dai ka fita hakkin shi, kuma ai kowa yasan cewa ciwon y'a mace na y'a mace ne, itama inaga ta rasa mafad'a ne shi yasa basu fad'a mata cewar ta hakura dakai haka nan ba tunda dai kai ba auren ta zakayi ba.
"Keee ni nace miki budurwa tace ita dama harda zakice min ba auren ta zanyi ba?"
"Allah kuwa budurwar kane tunda itace kullum take zuwa wajen ka harma fad'a takeyi da sauran yan matan ka, nidai in saboda itane dan na fad'a mata gaskiya kake fushi to kayi hakuri "
Yusuf wase dake zaune a falon tuntuni duk da hankalin shi yana kan film din da yake kallo a Tv amma tsaf kunnuwan shi yake Jiyo mishi tattaunawar da akeyi tsakanin AK da yarinyar data lissafo sunayen ta har guda hud'u kuma wai duka ita ke amsa sunayen ne yayi dariyar da har saida sautin dariyar tashi ta fito fili, lallai Allah da iko yake ashe yana raye zaiga ranar da wata d'iya zata iya fuskantar abokin shi irin haka gaba da gaba yana fadar magana tana maida mishi da amsa ba tareda tsoro ko fargaba a cikin muryar taba? Wacece wannan yarinyar da har AK ya zauna yake mata magana a hankali haka bada taratsi ko hargagin daya saba ba,
Dan haka ya dago kanshi dan ya kare mata kallo, ga mamakin shi sai ya hango wata yar karamar yarinya wacce in ba karya idanuwan shi suke mishi ba kai tsaye zai iya cewa shi kamannin ta ma tsaf yake mishi kama dana abokin shi sai dai kawai dan ita mace ce, cire duban shi yayi daga kanta ya mayar kan fuskar AK dan ya kara tantancewa sai akayi sa'a suka had'a ido shima AK din kallon shi yakeyi,
Gira d'aya Wase ya d'age ma AK alamun lafiya?
"Dariyar me kakayi? "
AK ya tambaya.
"An hana dariya ne? "
Shima ya maida mishi da tambaya maimakon ya bashi amsa,
"Malam tashi kabar min falo ka wuce ciki! "
"Kai harka ma isa kace in tashi, dan uban ka bakaga ina kallo bane? "
"Kaje ciki kayi kallon"
"Kai banfa zuwa ko ina wallahi anan nayi niyyar zama garama kayi ta kanka"
Muryarta ne ya katse su yayin da,
Ta kira sunan AK da wata irin shagwababbiyar murya "Ya Abdul"
"Ai nace miki