Showing 117001 words to 120000 words out of 174305 words
Chapter 40 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
taci gaba daci mishi uwa,
Dan yanzun kam ta k'ara tabbatar da cewar mijinta nata ne ita d'aya.
"Sarki ina son zan koma Lagos zuwa gobe fa domin akwai wani workshop din da zamu gabatar cikin satin nan kuma komai yana hannu na, sun kirani suna tambaya akan mai ake ciki kuma gashi ni ina nan, kaga kuma ya kamata dai kafin in tafi inje inga kanwata domin bai kamata ace har in koma baka gabatar damu a wajen juna ba, gashi kuma kai ka tare anan nasan tanacan cikin kewa"
"Haba Gimbiya nayi zaton kin d'auki hutu ne zamu d'an kwana biyu a tare ashe kwalele kikazo kiyi min"
Wata irin dariyar kissa take binshi dashi k'asa² cike da barikan ci tace "Haba Sarki na, ni harna isa inzo in maka kwalele kai da gonarka, sai dai ai kasan kodan saboda Boy dole in koma duk da dai nasan hannun dana barshi za'a kula dashi fiye da yanda zasu kulama da nasu dan kasan yanzun fa Boy ya doke matsayin kowa a gidan mu amma gara dai ace ina kusa da kayana, kai kuma dan ka bini mun koma tare aiba laifi bane! naga dai ko ka zauna ita amaryar taka ba wata tsiyar zata iya tsina na maka ba domin dai Sarki ai sai Gimbiyar shi"
"Tunda haka kikace zan duba in gani ko bamu tafi a tare goben ba in yaso zanyi kokari in biyo ki a baya cikin satin nan dama ko ba'ayi haka ba akwai abunda zai kaini Lagos d'in balle kuma kinzo kin min d'and'ani haukaci gashi duk kin wani kasa sakewa ki kula dani da kyau"
"Ah ah fa Sarki na bafa laifina bane domin dai kaine baka iya rik'e kanka da zarar an shiga filin wasa duk sai kabi ka rikice ka nemi fara kururuwa kaga kuma nan bafa gidan mu bane Hotel ne kasan kuma ina da kishi bazan so wani ko wata yajiyo muryarka a irin yanayin dani kad'aice ya dace naji shiba"
"Ohh haka ne wato ma ni kadaine bana iya rik'e kaina to bari mu gani yanzun waye zai gaza iya rike kanshi a wannan karan"
Ya fad'i hakan a yayinda ya yunkuro da nufin wawurar ta, gane nufin shi yasa babu shiri ta zabura suka fara zagaye d'akin daga karshe dai har yayi nasarar damk'ota yaci gaba da d'aura mata karatu.
Da yamma liss kuwa suka shirya shida ita kamar yanda ta buk'ata suka kama hanyar zuwa wajen Amarya,
Sai da suka fara shiga gidan su Sarki tayi ma mutanen gidan sallama wannan karan dai tsabar ta shirya ma abun harda gidan Malam sai da ta shiga ta kuma bi kaf sassan gidan suma ta gaishe su a karo na farko da dayawan sirikan gidan wadanda basu santa ba sukayi tozali da ita, ciki kuma harda sashen Mommy Hauwa saida ta shiga d'akin Malam shine na k'arshe inda ya had'asu ita fa Sarki ya musu nasiha akan suji tsoron Allah su kuma zauna da juna lafiya Allah kuma ya had'a kawunan su,
Itako a cikin zuciyarta babu kalar tsinuwar da batayi ma Malam ba domin tsaf labarin komai ya dawo kunnen ta na cewar ashe yarinyar ma auren dole yayi mata Dan hakan tasan bazata sha wahala ba wajen ajiyeta a matsayin ta, shine dan bak'in munafunci ya ajiyesu a gaban shi yana karanta musu suji tsoron Allah, to shi d'in yaji tsoron Allah ne wajen auren ma mijinta yarshi akayi mata kishiya babu shiri? Ko wani shegen ne yace mishi ita d'in irin matan su na Arewa ne da ake jerawa kishiyoyi kuma harma a zauna lafiya, hummm badai aure ba bismillah ayi zaman auren ta gani indai da mijinta ne,
Ummiee Zaria✍🏼
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱👨👩👧👦 *DANGINA!* 👨👩👧👦🔱⚜️
*It's a free book ga masu buk'ata daga zasu iya tuntub'ana kai tsaye*08061358462
""""""Page 34
Yauma dai kamar kullum gidan na Amarya Meenal ya samu ziyarar su Aisha, Maimoon, Maryam, Jameela harma da Rukayya,
Tun jiya Meenal d'in ke magana akan faten shinkafa take sha'awa dan yau d'in faten shinkafan suka girka wanda Maryam ce ta jagoranci girkin kasancewar kaf cikin su hannun ta yafi fad'awa a wajen sarrafa abincin gargajiya,
su dai sauran barsu wajen iya sarrafa kayan kwalam da makulashe,
Zazzaune suke a kasan carpets d'in dake shimfide a tsakiyar falon sun zagaye farantin faten dake tsakiyar su, suna sha suna hira.
Sai da Moon ta had'iye lomar dake cikin bakin ta sannan ta gyad'a kai gefe cikin kasalalliyar muryar da al'ajabi ya cika take cewa
" wani dan Allah ku bakwajin mamaki kamar ya kashe ku?"
Bata jira cewar su ba ta maida cokalin hannun ta cikin faranti tana mai k'ara gyara zamanta karamin murmushi ne kwance fuskarta sai da ta gama k'are musu kallo sannan ta bud'e baki tace,
"wai Allah mai iko wallahi kullum in nazo kofar gidan nan na wuto bakin gate har na k'araso ciki na iske Meenal zaune sai inyi ta mamaki wai Meenalin Malam ne a cikin gidan nan Matar Sarki kuma! , kai jama'a dan Allah inba Allah ba waye ya isa ya yanke hukuncin nan kai tsaye ai sai dai shi,! "
Kallon ta ta maida kan Meenal sannan ta had'e hannuwan ta guda biyun 🙏 alamun ban hakuri tana maida dubanta kan Meenal din taci gaba da cewa
"Nidai please³ 🙏 sister kiyi hakuri da duk shiriritar da nayi a baya ba laifina bane sharrin yarinta ne duk wanda ya kalleni ai dama yasan girman jikine kawai ba shekaru, Allah kuwa girma ne kawai ya riga hankali zuwa inba haka ba ina ni ina Sarki ai kowa ya san yafi k'arfina" hannu wanta ta maida kan kunnuwan ta ta rike su suma sannan ta tashi daga zaunen da take ta tsugun na still dai hannayenta rike suke da kunnen ta saita d'an duk'e kamar zata kai goshin ta k'asa sai kuma ta d'ago zuwa ga tsugun nin da take "kiyafe min sister! Ki yafe min³!! Kar kici gaba da kallona a matsayin wacce ke son mijin auren ki wallahi ni dama ban sa shi a zuciyata ba duk abunda nikeyi inayi ne kawai a lokacin dan in tsokane ki tunda naga bakyason ana miki maganar shi, Allah ya gani ko a mafarki ban tab'a zaton zaki zama matar Sarki ba wata rana".
Sake da baki Meenal ke binta da kallo yayin da su kuma sauran ke dariya k'asa² dan tun da aka gama biki babu wacce ta tada maganar yanda abun ya kasance dan babu wacce ke son ta kwanto ma kanta kura tunda ita uwar gayyar ta nuna musu bata son maganar dan haka sukaja bakunan su suka tsuke,
Kallon Aisha Meenal tayi
"Ke Aisha hala dai yarinyar nan ta fara zuk'e² da kurb'e²n kayan maye ba tareda sanin kowa bane? Ko kuma Ah² tsabar iskancin Lagos ne ya biyota har nan? Ashe ba k'arya Hajiya takeyi ba da tace kaji tsoron Allah ka kuma ji tsoron yan iskan Lagos, to na rantse in kika k'aramin maganar banza anan bazan k'ara kulaki ba har kibar garin nan tam! bama Sarki ba ah ah Saraki"
ta k'arasa fad'in hakan a zuciye tana jan kwafa taci gaba da shan faten ta,
Babu wacce ta k'ara tada maganar har suka kammala suka kuma gyara wajen sannan suka koma saman kujerun falon sukaci gaba da sha'anin su.
//////Babu sallama balle ayi zaton neman izinin shiga Teemah ta bud'e kofar falon kai tsaye ta shige, kasantuwar dukan su hankulan su ya d'auku akan kallon film din da sukeyi hakan yasa basuji motsin shigowarta ba har sai da ta iso tsakiyar falon,
kwas! kwas! Kwas d'in da takun takalmin ta yake badawa akan tile's d'in falon ne yajawo hankalin Meenal dake buga game da wayarta dan ita ba kallon film d'in take yiba,
sai dai kallon matar kawai taci gaba dayi ba tareda ta iya ce mata komai ba, to jama'a me zata ce mata? haka kawai mutum ya fad'o maka cikin gida babu koh sallama sannan kuma yanayin shigar matar babu ta inda ya nuna cewar tana da tabuwar hankali balle tace ko mahaukaciya ce ta kutto daga wani wajen ta fad'o nan ko kuma to kila dai makuwa tayi!
Dan haka da ido taci gaba da bin ta har zuwa sanda ta nemi d'aya daga cikin kujerun falon takai zaune tako d'aura kafarta d'aya kan d'aya abunta tana mai bin falon da kallon kurullah domin ai tunda aka gina gidan bata tab'a shigowa cikin shiba tadai ga gidan a hoto da video d'in da Sarki yayi ya kai mata a lokacin da ya so ta dawo gidan tak'i,
Ganin zaman nata a falon bai wadatar ba yasa ta mik'ewa ta fara zagaye falon, da kallo duka su Meelat suka bita dan sai yanzun suka lura da ita suna tambayar Meenal da "wacece" ita koh dage musu kafad'a tayi alamun oho bata sani ba,
Maryam ce tayi k'arfin halin gaisheta da cewa "ina wuni"
amma ko alama matar nan bata nuna taji abunda Maryam d'in tace ba sai ma basar da ita da tayi ta k'arasa wajen dinning table din dake gefe tana karema wajen kallo domin yanda ya k'awatu a idon mai kallo kwarai gwanin ban sha'awa ga mai kallo, gaba tayi ta k'arasa hanyar da zai sadata da kitchen ta bud'e kofar ta tura kanta ciki ba tareda ta zura gangar jikinta gaba d'aya ba, shima dai sai da ta k'are mishi kallo a zuciyar ta tana mamakin dukiyar da aka narka ma yarinyar nan, anya ma ba kud'in mijinta suka samu sukayi facaka dashi haka ba? Inba haka ba ai ita bataga alamar cewa sun mallaki dukiyar da zasu kashe ma yarinyar mak'udan kud'i har hakaba!
Bayan kuma ba ita kad'ai suka aurar ba waya sani ma ko baashi suka ciyo saboda gudun kar suji kunya dan ai daga ganin tsarin gidan duk wanda ya shigo dama yasan gidan yafi k'arfin a zuba mishi k'ananun kaya, to in ma dai baashin ne to su shirya maidawa mai kayan kayan shi in ya so a basu kud'in su su rage zafi,
dan Wallahi babu shegiyar da zata zauna mata a gidan da aka gina da sunan ta, baza tayi saurin korata a yanzun ba domin hakan yana iya b'ata mata tsarin ginin ta data d'aura amma yanzun d'in ma sai dai yarinyar ta zauna mata a matsayin yar gadin gida badai matar gida ba.
Fitowa tayi daga wajen taci gaba da zagayen d'akunan dake k'asa sai da ta gama ta juyo tana k'are musu kallo ganin su a tsatstsaye suna binta da kallo banda Meenal wacce ke zaune tanaci gaba da game d'inta kamar ma bata san meke faruwa a falon ba.
Sai da ta k'are musu kallon tsaf Addu'ar ta d'aya shine Allah dai yasa ba waccan yarinyar bace dai kishiyar nata! Domin tun kallon farko data mata taji gaban ta ya yanke ya fad'i,
Kallon su taci gaba dayi daya bayan d'aya
kamar yanda suma suke kallon ta cike da mamakin karfin halin ta, sannan ta bud'e bakinta da wani irin girman kai da isa tace
"Ita matar gidan bata iya fitowa ne a sanda bak'i suka shigo mata?"
Babu wacce tayi zaton cewa Meenal zata bata amsa a dai² wannan lokacin har sai da kunnuwan su ya jiyo musu muryar ta a yayin da take ba Teemah amsa da cewa,
"ita matar gidan takan tari b'akin da tasan da zuwan sune kad'ai bawai masu fad'owa daga sama babu gayyata ba,"
sai da ta d'ago kanta suka ma juna kallon ido cikin ido ita da Teemah sannan taci gaba da cewa...
"baiwar Allah ina ganin kamar makuwa kikayi dan haka ki d'an koma ta gefen hannun damar ki inaga kamar tanan kika biyo koh?
Bismillah kina iya komawa inda kika fito mun gode da gaisuwa"
Zaburo wa Teemah tayi kamar mai shirin rufeta da duka sannan cike da jin haushin abinda yarinyar tace mata itama ta maida mata martani da cewa,
"Ke din wacece da har zan shigo gidan mijina uban yarana kice wai in fita? gaki k'aramar yarinya dake amma alamu sun nuna baki da tarbiya"
Yunkurowa itama Meenal d'in tayi domin sosai itama kalmar karshe na matar ya b'ata mata rai wai itace bata da tarbiya dan haka ta maida mata martani da cewa "tarbiyar ne yasa naga an shigo gidan matar aure babu sallama"
Suna cikin wannan cacar bakin Sarki ya shigo falon Kwaro na take mishi baya,
"Mike faruwa anan? " ya tambaya ganin su a tsaye kamar wasu zakarun dambe.
Simi² su Meelat sukaja hannu wan juna suka shige d'aya daga cikin d'akunan dake kasan suka rufo kansu harda murza key,
domin dai wannan ai family issue ne sukam basu da ruwa a ciki, ganin hakan yasa ita ma Meenal din juyawa da niyyar barin falon sai dai kuma tana takawa Sarki ya tsaida ta da cewa
"dawo nan! ya ina magana daku kike shirin tafiya kuma"
Teemah ce ta tari numfashin shi da cewa...
"Baban Boy kar dai kacemin wannan mara kunyar yarinyar ce amaryar da ake ikirarin an aura maka?"
Bata jira amsar tambayar nata ba ta d'aura da cewa..
"Sarki wani kalar abin kunya kake shirin jawomin,
karasa matar da zaka auro ka had'amu kishi akan ka sai wannan yar kankanuwar yarinyar? ana ta cewa k'aramar yarinya nayi zaton zan ganta cikakkiyar budurwar da zamu goga zaman kishi da ita sai naga wannan abar... yanzun fisabilillahi a hakan ka iya nunata ma abokan ka yarinyar da a haife ka haifeta? Lallai yau na k'ara tabbatar da halin ku na ya'ya maza da kullum ake fad'a"
Zagayen falon ta farayi takai gauro takai mari hannuwan ta duka a saman kanta kamar wata wacce aka aikowa sak'on mutuwar uwa da uba a lokaci d'aya.
"Calm down please mana Teemah"
Ya fad'a yana shirin kamota dan sai wani abu take kamar wata mai shirin tada aljannuh, ita koh tashin hankalin ta shine ganin abinda batayi tsammani ba, tabbas an bata labarin cewa k'aramar yarinya ce, to amma ita idanuwan ta abunda suka gane mata shine cikakkiyar budurwa mai mulmulallan jiki da cikakken dirin da bako wani namiji bane zai iya mata kallo guda ya d'auke kanshi,
bayan wannan kuma ga wani irin masifaffen kyau data gano a fuskan yarinyar wanda ita kanta bata iya mata kallo guda ta d'auke kaiba ina kuma ga namiji irin mijinta da dama babu abunda yake bala'in burgeshi irin mace mai kyau kuma dirarra, wanda sanin kanta ne wad'an nan abubuwan su suka k'ara taimaka mata wajen shawo kanshi a lokacin data nuna tana son shi, domin shi dai mutum ne mai son matar fita kunya da hakan kuma take k'ara amfani da nata kyan da kuma salon kissa da kisisina ga kuma kulawa da kanta da takeyi duk dan kar dai ya hango wata a waje,
shine yanzun aka wani d'auki wannan yarinyar mai siffan aljannun ruwa aka aura mishi gata kuma da kana nan shekaru,
kai inahhh wallahi da sake dan bazata zuba ido aikin data fara ya lalace ba, ta sani sarai cewar babu kalar munafuncin da maza basu iyaba inhar ta barshi da yarinyar nan tofa yana iya mai data wata dankalin hausa a gefe yazo ya dunga hutawa da yarinyar nan domin dai akwai kayan hutun tabbas, ai ko da kulli yaci amanar koko wallahi.
"Teemah calm down please ki saurareni ina ce mun riga mun gama maganar nan already"
"No no no please don't tell me to calm down, ashe kaga irin kalar da kake so shi yasa dan bak'in munafunci tunda kasa k'afa ka baro Lagos ko a waya baka iya kyankyasa min abunda yake faruwa ba,
Wato ga Teemar banza da wofi tunda ni ka gama cinyeni ka zazzage ni tas na haifo maka yara daya biyu har hud'u wato na tashi aiki bari ka gudo gida cikin *DANGINKA* Ka nemi karamar yarinya ka aura, kuka wani had'a baki da kai da muna fukan *DANGINKA* suka baka auren yar shilar da da'ace ban biyoka na taho ba sai dai inji zancen auren a shanun tallah"
bai bari ta karasa ba ya katseta a tsawace...
" will you please short up your mouth before..... "
A zafafen ita ma ta katse shi da cewa...
"Before what Sarki? Nace before what? are going to raise your hands on me? Oh saboda kayi aure yau kuma duka na zakayi tun baka riga ka tare da amaryar ba? "
Sai kuma ta juya gefen da Meenal ke tsaye tana kallon ikon Allah dan kwaro dai shi kam tun fara hayaniyar su yayi sif³ sif ya fice daga falon,
Damk'a tayi shirin kaima Meenal ita kuma Allah ya bata ikon zillewa bata yarda Teemah ta kai hannunta gareta ba.
"Karki tab'a yarinyar nan Fateemah!"
ya fad'a a tsawace da muryar nan tashi mai amso amo in baku manta ba dama shi din muryar shi masha Allah balle kuma yana cikin bacin rai.
"Ka barni in rik'eta ta fad'amin da wani kalar asirin sukayi amfani wajen aure min miji, mai suka kulla da yasa tun ba'aje ko ina ba har ka faramin ihu, asiri suka maka wallahi ban yarda da yarinyar nan ba har dama iyayen ta dan anga Allah ya rufa maka asiri ne suka had'aku dan suma su dan gwali arziki"
Anzo gab'ar da mutuniyar fa bata iya daurewa, atoh dai bazai yuwu wata can so called kishiya ta shigo mata cikin gida kuma sannan ta nemi cin fuskanta dama na iyayen ta ba dan haka ta maida mata martani da cewa.
"Allah ya tsaremu da nufar wani da sharri balle har son zuciya ta kaimu ga aikata Babban sab'o wato yin asiri ga wani, inaga dai ita mai maganar bata yarda da Allah ba ko kuma dai abune wanda akai sabo dayi shi yasa akayi saurin tsarguwa! Alhamdulillah kuma ni iyayena ba makwad'aita bane balle son abun duniyar su yasa su bada aurena ga wani dan abun hannun shi, Inma kuma