Showing 93001 words to 96000 words out of 174305 words

Chapter 32 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1875

yaga ta tashi tsaye car cikin kwanciyar hankali bane yau ta nemi farayi mashi hankoro, shida baya taba iya shiga irin yanayin da yake ciki a yanzun inba sanyi yayi sanyi ba koshi din ma sai in kamar yana kallo haka yaci karo da masu fararen kunnuwan nan da allah bai yi halittan kunya ajikin su ba suna aikata aikin nan da Allah ya hana har sai ka biya sadaki ba shine kawai yake jin irin hakan amma yau a banza a hofi shedan yana neman ya kaishi ya baro shi.
Runtse idon shi yayi da karfi bayan ya kai hannu ya danne alkalamin dake shirin tona mishi asiri a tsakar gidan fa jama'a, auzubillahi minal shaidanir rajeem haka yaci gaba da mai maita wa, a kokarin shi nason fitowa daga halin da shedan ya jefe shi, wallahi wani irin kunya yaji ya sauko ya lullube shi, Allah dai ya isa kuma bazai daina Addu'ar Allah ya mashi katangar karfe tsakanin shi da shaidan ba, yanzun nan dan Allah da wani yazo ya ganshi a haka mai zaice mishi? Shike nan sai a fara mishi kallon wani dan iska fa,
Lallabawa yayi ya shige sashen shi kuma har lokacin bai daina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan ba. Dan wallahi yau da shedan din nan mutum ne babu ubanda zai hanashi ya faffashe mishi fuska wallahi, amma yayi alwashin har yarinyar nan tabar gidan nan bazai kara bari su hadu ba.

***

Bari mu leka gidan uwar gida.

Daga ita har yaranta sunyi kokar dan ganin cewa kota waya ne sun samu Sarki sai dai ina kwata² hakan yaki samuwa domin ko duk ya watsa number din su a inda ko sun kira shi bazasu samu ba,
Haka dai suka had'a karfi da karfe suke ta hidimar shirin auren da dukiyoyin su domin harta gyaran gidan shi su suka dauki nauyi sun kuma yi bajin ta kwarai dan sunyi komai fiyema da wanda shidin zai iyayi dan ganin cewa sun faranta ran uwar gida,

Ganin cewa biki yana ta matsowa babu labarin ango yasa suka shirya cewa daya daga cikin kannin shi ya shirya ya tafi har Lagos din ya shaida mashi cewa Uwar gida fa bata da lafiya kuma tace tana bukatar ganin shi, ita kuka Dr Mubarak suka kira yazo gida ya daura mata ruwa domin a zahiri dama tana bukatar shi dan gaba daya taki kwantar da hankalin ta ganin takeyi kamar in Sarki bai k'ara auren nan ba tofa shike nan zata rasa shine gaba daya.

Kunsan duk abunda kakeyi sai ka samu mai maka bacci da ido daya domin ko ashe tun bayan zuwan da Hajiya tayi gidan Malam tayi tijarar da yasa maganar auren na Meenal fitowa cikin kishiyoyin Uwar gida aka samu wacce ta kira Teemah saboda tsabar kwarewa a iya munafunci wai ta kirane ta mata Allah ya sanya alkhairi na Karin arzikin da mijinta ya samu, sosai teemah tayi mamakin kiran domin ita dai iya sanin ta bata san wani abun alkhairin daya samu sarki wanda har mutanen zaria zasu kira su taya ta murna akan shi ba dalilin hakan ne yasa ta tambayar me yake faruwa domin dai su Lagos lafiya lau suke,
To dai uwar gula dama abunda take so kenan dan haka ta fad'ama teemah cewar ai aure akaba Sarki anan cikin family harma an tsaida rana yanzun haka ma an gama komai na shirin biki,
Sosai abun ya kadama Teemah zuciya amma da yake yar barikice bata bari ta nuna cewar ta jijjiga dajin zancen ba sai ma Addu'ar Allah sanya alkhairi da tayi ta yanke wayar ta.

Wani irin katoton ashariya ta lailayo ta maka akan ahalin Sarki tundaga kan manyan harda wadanda basuzo duniyar ba duk saida ta tabbatar ta kwashe ma kowa albarkha, tafayi hauka son ranta sai dai tayi alwashin cewa aure koh! Ita bazata hana shi aure ba tunda har aure suke so ayi auren saboda tanan nema zata kara tabbatar musu da cewa ita din taci dubu sai ceto Allah ya kaimu lokacin biki lafiya, tafa cije kwarai ta yanda hatta kawayen ta babu wacce ta fadama cewar mijin ta zai mata kishiya kai in ma ta bari akaji ai taji kunya wallahi wai Ita Teemah ita ce har uwar miji zata ma kishiya dan wannan ai bazata ce mijin ta zai mata kishiya ba dan a yanzun kam tasan wallahi ko cocaine Sarki ke shak'a bai iya yace zai mata kishiya, to su shirya zata aje kowa a matsayin shi kamar yanda ta saba, a zaton su tana raye har zata zuba ido wata karamar yarinya ta shigo mata gida harma ta kwanta mata da miji tayi ciki itama ta haihu God forbid over her death body ai gara ace bara raye da dai taga zuwan wannan ranar.

Koda dan sako ya iso daga zaria akan cewar uwar gida bata da lafiya tana bukatar ganin Sarki ko kadan bata tada hankalin taba sai ma dama data ba Sarkin akan in ya isa yasa a gyara mata gidan ta itama in an kwana biyu zata zo ta duba jikin Uwar gidan, yaji dadin furucinta sosai a ganin shi ta fara saukowa tunda har gashi ita da kanta yau ta furta zataje duba jikin mahaifiyar shi, bai san cewa ita tayi hakan bane saboda ta samu lokacin da zata shirya ma zuwan kishiyar nata da kyau.

A ranar da suka isa zaria hankalin Sarki ya tashi matuka a yanda ya samu mahaifiyar shi domin kwanciya tayi nakwa nakwa tamkar wacce tayi doguwar jinya, ganin ta a cikin wannan hali sosai ya daga mishi hankali ya faraji a jikin shi cewar bai kyauta ba, ga kuma yanda hatta da yaran shi suke ta mamman ne mishi saboda ko suma sunyi kewar shi, hakan nan a kasar zuciyar shi yakejin bai kyauta ba sai dai koshi bai san dalilin daya hanashi zuwa garesu ba, shifa zaima iya cewa gaba daya ma mantawa yayi dasu wallahi.

Ganin da uwar gida tayi cewar jikin shi yayi sanyi kwarai yasa ta bijiro mishi da bukatar ta cewa son take a daura auren shi da Aminatu kamar yanda ta fada mishi tun tuni dan tana son taga auren kafin ta mutu dan a cewarta tasan ciwon ta bana tashi bane, sosai dai tayi mishi hannun ka mai sanda had'e da nasiha a matsayin wasiyyarta a gareshi,
Da yake abinda ke dawainiya dashi yafi yin tasiri ne a sanda yake tare da Teemah hakan yasa cikin kwanakin ya maida hankalin shi kachokan wajen ganin ya kula da mahaifiyar shi da kuma son ya cika mata burin ta na auren da take son yayi duk da allah ya sani wallahi ba ya bukatar Karin kowani aure a yanzun dai, to shi mai yake nema a yanzun da baya samun shi a wajen matar shi? Su dai kawai dan basa son teemah ne shi yasa suka kasa yi mata uzuri, amma tunda sun dage da maganar auren zaiyi kowa ma hankalin shi sai ya kwanta, to amma Teemah fa? Zuciyar shi ta tambaye shi, ya gode Allah ma da tace zata zo inya so in tazo zaiyi kokarin fahimtar da ita yanda abun yake, shifa yanzun damuwar shima yanda suka tashi suka zubama yarinyar can da suke kira matar da zai aura kaya a gidan sama da kasa duk kayan tane ga kuma Teemah tace a gidan zata sauka shi dai kawai nema suke su sakashi cikin damuwa, ga kuma wata magana da uwar gida keyi na cewan wai yaje ya samu yarinyar yaji ko tana bukatar wani abun na sha'anin biki, yanzun fisabilillahi shi da girman shi da komai sai yaje yasa a mishi sallama da yarinyar can dako hankali bai isheta ba wai da sunan yazo wajen ta, kai ina ai sai dai ya nemi wani ya aika, shi babban damuwar shi ma yanda duk suka wani kira abokan aikin shi dana kasuwancin shi suka fad'a musu maganar bikin yanzun haka zasu zo suga amarya wata yar ficika a wajen bayan kowa yasan tsarin shi.
(Jama'ah Sarkin nan mafa dan rainin wayau ne ku fad'a mishi da babbar murya cewar muma auren dole za'a mana ba son shi mukeyi ba🙄).

isowar su Moon sosai ya kara sa Meenal ta sake jikin ta suke abubuwan su ita da kawayen ta kullum kuma tana lissafin kwanakin da suka rage mata ta koma gida aci gaba da hidima da ita da yike ma ba wani shagalin biki za'ayi ba walima ce kawai aka shirya za'ayi su kuma sun shirya yin zaman yinin su a gidan su Meelat yanda zasu fi sakewa,
Tun ranar da shedan ya nemi sa AK yayi abun kunya ya kama kanshi ya kiyaye duk abunda zai had'a shi da Meenal a cewar shi amarya tsautsayi gareta dan a yanda ya tara ta da yawa din nan yasan inya riketa tofa bazata sha ta dad'i a hannun shi,
Sai dai a yan kwanakin sosai su Moon suka matsa mishi akan alkawarin wayar daya musu da dad'ewa akan in sun gama secondary zai siya musu manyan wayoyi dan so suke suci biki da wayoyin su a hannu yanda zasu samu daukar hotunan biki.



Share Please
#Ummiee~Zaria⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*


*👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_



ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._

*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}

*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen.


```Page 29


kuyi hakuri wannan page din yayi double in kunzo karatu , ku karanta na can k'asan shine cikakken page ba sauran na zaman ba.

Washe garin ranar kamar yanda Hajiya ta buk'ata haka Mommy Hauwa ta had'a Meenal da kayan ta zuwa gidan Hajiyan,Bayan ta fad'a mata cewar magani zataje sha a gidan, hakika hakan baima Meenal din dad'i ba domin a cewar ta zirga zirgan zai mata yawa a matsayin ta na Babbar ya'yar amare ga kuma ya sa'eed daya kamata ace itace zata tsaya akan batun komai na bikin shi domin dai itace taje ta zaiyana ma Malam halin da Billy take ciki saboda ganin da tayi shi Sa'eed d'in baiyi yunkurin komai ba har yanzun ,
dan ma Allah ya taimake ta sun riga sun kamala exam's din su gaba daya ai da hidimar ta mata yawa wallahi,
Koda bukatar Hajiya na komawarta can Tudun wada yaje kunnen Malam baiyi musu akan hakan ba domin koba komai yasan zamanta acan din shima zaifi mishi kwanciyar hankali domin tabbas intana nan sai an samu mai dogon bakin dazai furta batun auren nata a gaban ta wanda shi kuma bai shirya fuskantar ta da maganar a yanzun ba.

Ita ko Hajiya kaf yayan ta saida ta kira takai musu karar cewa Malam ya nuna mata mulki da isa akan jikarta ya nuna mata bata da wani matsayi ta yanda har ya iya sanya auren jikarta ba tareda sanin taba, dan haka tana bukatar ganin su in ma bazasu samu damar zuwa ba tofa kowa ya turo da nashi gudun mawar dan tama fi bukatar kud'ad'en da zasu turo akan zuwan nasu domin kayan yar gata takeso ta had'ama jikarta kodan Malam yasan cewa kullum cikin shiri take ita batayi gadon tsiya ba,
to dai suma tunda Allah ya sa sun san ko sunzo a lokacin ba wani tsiyar zasuyi ba domin infa Hajiya ta kafe ta kafe kenan yasa sai kud'ad'en data buk'ata suka tura mata, ita kuma taci gaba da shirye shiryen ta na auren jika,
Tsaf ta shiga ta fita tabi kwakwafin wanda za'a aurama jikar tata, acan ne kuma tajiyo abinda batayi tsammani ba, wato ashe kiyayyar da Malam kema Jiddan ta har ya kai ya d'auki yar Jidda yaba yaron dan uwan shi da matar shi ta gagari uban kowa!
Yanzun da ace bata raye kenan haka za'ayi auren ba tareda an shirya Meenal din ba gayarta za'a dauka akaima kishiya wato taji dadin nakasa ta da kyau tunda an mata auren gani kasheni, to ai in sun san wata basu san wata ba ita kam da ranta da lafiyarta bazata sadaukar da rayuwar Takwarar ta a banza ba wallahi , dan haka tuni itama ta zage damtse wajen neman ma Meenal din duk wani maganin da tasan na tsarin jiki ne sai da ta tanade shi atoh maye yaci kanshi ba dai jikarta ba,
Satin farko na komawar Meenal gidan bata fuskanci ko wani damuwa ba, domin dai Hajiya bata takura mata sai ma nan nan da takeyi da ita wajen ganin ta jata a jiki dan Wallahi in tana mata wani abun sai taga kamar ba Hajiyar data sani bace wannan wata daban ce, dan a yan kwanakin sosai Hajiya ta tsiri yawon zaga dangi da ita ga janta da takeyi suna shiga kitchen tare tana koya mata kalolin girke girke, harma da sauran ayyukan gida kuma duk inda suke bukatar zuwa yawon rabon anko da katin biki Dan gidan Master ne ke zuwa yana kaisu kuma Hajiyar bata hanawa dan sosai yakeji da Meenal d'in a kokarin shi nason ta bashi dama ya gabatar da kanshi a gidan su tunda gashi allah yasa har za'a aurar da k'annin ta yasan koya nema baza'a hanashi ba domin shi baik'i ba wallahi a had'a bikin ma dana kannin nata,
amma yasan Hajiyar tashi ba yarda zatayi da hakan ba
sosai fa ta samu yanda take so a wajen Dan gidan Master dan sosai ya bud'e mata bakin aljihu take ta dandake kan nerori domin dai duk abunda take so jiki na rawa yake mata shi, shi dai yana son Aminatu sai dai duk nacin shi har yanzun Meenal bata yarda ko Hajiya ya shiga ya gaisheta ba,

Gashi kuma kwanan nan ta lura ba Hajiya da Malam kadai ba yanzun harta da Mommy Hauwa sosai take sake mata fiyeda lokutan baya domin abun mamaki kulum cikin tambayan ta abunda take so take ga yawan daukarta da sukeyi zuwa kasuwa ita dasu Meelat zuwa siyayyar kayan da take zaton nasu Raheenat ce domin dai dama ko yayyin su maza in zasuyi auren Mommy ne ke had'a musu kayan auren, dan haka sai bata damu ba a zaton ta tasan kila dan Mommy tasan in tace su Raheenat d'in suzo suje kasuwar tasan ba lallai su sake jiki su zab'i abubuwan da suke bukataba shi yasa, dan haka ta zage damtse da zuciya d'aya ta maida hankali ta dunga d'aukar duk abunda taga ya mata kyau dan tasan dai auren dole ne za'ama kannen ta to amma inta bada nata gudun mawar wajen ganin an shirya musu dakunan su da kyau tasan hakan zai rage musu damuwa,

Bawai k'ana nan siyayya kad'aiba hatta da kayan gado dasu kujeru komai ita ta zab'a musu sai dai abunda bata sani ba harda nata kayan ta zaba'a domin komai itama sai an tambayeta choice din ta, cikin sauk'i dai abubuwa sukaci gaba da tafiya,


Biki ya rage saura sati biyu Mai Jama'a ya duro Zaria domin duk wainar da ake toyawa baya gari yaje Lagos akan wasu harkokin su dan haka bashi da masaniya akan abinda ake ciki , ita kuma Hajiya hidindumun data sa a gaban ta sun sha mata kai dan ga kuma bikin Billy jikar Turai dan haka ko a waya bata tuna ta bashi labarin abunda ke faruwa ba, a kuma sati biyu da bikin ne Hajiya ta sama Aminatu takun kumin fita domin zuwa lokacin ta gama hada duk wani tanadi da tayi domin gyarar jikar nata, ta kuma fad'ama harta da masu gadin gidan cewa koda wasa suka k'ara barin Meenal din ta fita saita b'ata musu rai wallahi.

Ganin cewar Meenal ba had'in kai zata bata ba yasa ta fada mata cewar maganin ciwon marar tane ta amso mata kuma ka'idar maganin sati biyu ake shanshi kuma in an fara amfani dashi ba'a zuwa ko ina gida ake zama dalilin ma da yasa tace Jidda ta maido mata da ita nan kenan, in kuma bata buk'atar ta warke ga kofa nan tana iya komawa gidan su,
Saida Meenal ta kirga kwanakin daya rage mata kafin zuwan al'adarta sai taga kwanakin duka basufi goma ba, to kenan in har tabi umarnin Hajiya ta zauna tayi amfani da maganin tana sa ran kenan wannan watan lafiya lau zatayi al'adarta kamar na sauran mata, gashi kuma dama tsoron da take ji kenan domin lokacin zuwan nashi a lissafin ta zaizo a cikin bikin ne dan Haka ba komai zata jure zama dai na kwana kin a gidan Hajiya ai mai sauk'i ne in aka hada da wahalar da take sha duk wata, sai dai gaskiya za'a takura mata dan bata gama rabon katin biki ba amma ba damuwa tunda gasu Moon zasu iso ga kuma su Meelat a gefe, sai dai kuma ya zatayi da yan anacen samarin ta da bata amshi kudaden data yanka musu na anko ba?dan fa kaf dinsu kowanne da harajin data d'aura mishi,
Wannan ma ba damuwa tunda dai ga waya shi dai D'an Master tasan shegen kwakwa gareshi dole sai yazo inda take dan ma ta gode Allah iliya dan mai karfi bayanan balle yasa mata ido,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login