Showing 144001 words to 147000 words out of 174305 words

Chapter 49 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1872

ya raka hajiya data rike hannun Meenal dam kamar wani ne zai kwaceta a hannun ta har suka bar office din yana bin su da kallo ne kawai kanshi a d'aure,
Kenan idan ya fahimta dai dai duk wannan shekarun Sarki bai tab'a kusantar yarinyar nan ba kenan?
To me yasa?
Ganin bashi da mai bashi amsa dole ya mik'e ya fito dan yana buk'atar tabbatar da cewa tafiyan zasuyi kamar yanda Hajiya tace ko kuwa,

Hajiya ko suna fitowa daga office din ta samu AK da Sa'eed a bakin kofar d'akin Sarki, hakan kuma yayi daiยฒ da isowar wasu daga cikin kannin Sarki mata da maza, in baku manta ba dama akwai hidimar bikin da akayi a gidan nasu Sarki kuma bawai an gama watsewa bane,

Hajiya bata saurari kowa a cikin su ba taci gaba da jan hannun Meenal zuwa waje, sai da suka kusa kulewa sannan ta juyo,
"Kai Abdul Khareem kazo ka tukamu mubar asibitin nan in kuma baka tashi ba mu k'arasa titi mu samu abun hawa"

Tana kuma gama fad'in hakan taja hannun Meenal suka fice bata jira jin ta bakin shiba, duk juyawa sukayi suna bin ta da kallon mamaki sai dai babu wanda ya iya tankawa a cikin su,
Sallama yayima Sa'eed shima ya take musu baya, dan yasan indai Hajiya ce tsaf zataje ta nemi wani abun hawan suyi tafiyar su su barshi a asibitin.

Hakan kuma bazai hana ta d'ibi laifin duniyar nan ta jibge mishi ba....



Sorry yau dai page din ba tsayi aci da hak'uri ayi bacci๐Ÿฅฐ



*UMMIEE ZARIA*โœ๐Ÿผ
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA!*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆโšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ
~{{MY FAMILY }}~

*FREE BOOK*

*RUBUTAWA*
*UMMIEE ZARIA*โœ๐Ÿผ


``````Page42....


A bakin motar ya same su tsai-tsaye,
Hajiya dai sai uban gyacci takeyi bala'i na cinta, dan sosai ranta ya b'aci da bayanin da Dr ya mata cewar Sarki ciwon sha'awa ke damun shi.

Sanin cewa infa ya kulata suna iya raba hali a titi yasa baice mata ci kanki ba sai ma bud'e musu kofofin motar da yayi shi kuma ya koma mazaunin direba ya kunna motar suka fice daga harabar asibitin,

" kai Jama'a ke takwara amma ban tab'a sanin mijin ki digirgirarren mara mutunci bane sai yau, wallahi da ace ba'a gabana likita ya rattafo jawaban nan ba dad'e duniya babu abinda zai hana in karyata duk uban da zai kawo min labari koda ko kece,
ace ni ina nan a gefe ina ta mishi kallon tausayi ina mishin kallon mijin da mata tayi ram dashi sai yanda taso take juya mishi akalar rayuwa, dan mak'iyin uban shi ashe qalau yake tsayin shekarun nan ya kafe min jika a gida Bata da aiki saina gyaran gida da girki, matan aure nata haihuwa ita ko ashe ko tsallake sirad'in farko batayi ba! "

Sai da ta tafa hannuwa cike da jimami dan fa sosai abun ya dake ta, bata tab'a tsammanin hakan ba, dan haka ta ci gaba da cewa..

"To ni yanzun laifin wama zan gani?
Iyii laifin iyayen ki da suka dauke ki suka mik'aki gidan shi a zaton su na samar miki sauk'i akan lalurar da Allah ne ya aza miki ko kuma shi sokon da aka wanke mishi yarinya d'anya shakaf aka mik'a mishi amma ya wofantar,
Oh ni Ameenatu yanzun ashe da banyi tsayuwar daka wajen nema miki maganin ciwon maran nan naki ba da tuni ashe kin dad'e da zama gawa, to gawa mana jama'a tunda dai likita ya tabbatar musu cewa da an miki aure kin fara kwanciya da miji ciwon zai gudu,
Ni wallahi ba abun inyi Allah ya isa ba to ban san ma katamam men wanda ya dace da Allah ya isar nawa ba,
Iyayen ki da suka miki auren cushe suka mik'a min ke inda ba'a tab'a kallon ki da daraja ba koshi mijin daya ajiyeki a gida ya maida min ke baiwa, to duka dai ko ban fad'iba dama sai Allah ya saka miki cutar da aka miki,na tabbatar da ace Vida kike tsayin shekarun nan Allah yasan kalar mazajen da zasu dunga gware wajen fafutukar neman auren ki, yanda kike tsoka d'aya a miyar nan ai ba k'aramin mai sa'a bane zai tsamoki wallahi, ni kuma sai na tankad'e su na rairaye kafin in tayaki zab'ar dankwalele a cikin su"

"Hajiya dan Allah kiyi hak'uri kiyi shiru, nidai tunda kin san komai kawai kisa ya sakeni, in baya sona nima ai ba son shi nikeyi ba, lokacin da akayi auren da ace na bujure ai kowa gani zaiyi kamar bani da tarbiya, to da bani da hakki ba ga abinda ya biyo baya ba"

Katseta Hajiya tayi da cewa..
"Yo ke yar nan har sai ma kin fadamin yanda zanyi? Ai an daiyi d'aya ba k'ari wani lalacewar ce ta sameni dazan zuba ido ina kallo ki koma gidan nan kici gaba da zama kamar wata hoto, ah ah wallah anyi na farko kuma na k'arshe ba k'ari na baya ma allah yasa ya zame miki kankaren zunubi ya kuma baki ladan zama"

Sai kuma tamai da Hankalin ta kan AK,

"Kai dan mai karfi kaji min wani bala'in da yake neman yimin karan tsaye a rayuwar jika?kana fa jina tuntuni ina sababi inba zaka sanya baki ka tayani jimami ba ina laifin ka bani hakuri tunda dai kasan an b'atamin! "

Bata jira ya amsa ba ta d'aura da cewa,

"Wai shi wancan sojan mijin nata da muka kai asibiti ne likita yace min wai ciwon sha'awa ke damun shi, kaji min wani zunubin ganganci wajen marar rabon can fa, mai mata kamar jikata a gida, amma ya iya zuba mata ido tsayin shekarun nan"

Gefen titi ya gangare da motar sai da ya kasheta sannan ya juyo,
Kan Meenal ya fara jefa kallon shi sai yaga ta juya fuska tana kallon waje ta window din motar a yayin da ta kudundine a cikin hijjabin jikinta, sannan ya maida kallon shi kan Hajiya bayan ya d'aure fuskan shi sosai,

"Hajiya wai ke mai yasa kika fiye son shiga cikin abinda babu ruwan kine?"

"Kai dakatamin dan Allah"
Hajiya ta fad'a tana katse shi,
"Karfa kace zaka fad'amin maganar banza akan abinda kowa yasan akan gaskiya ta nike,
Ana fa magana ne akan rayuwar auren jikata au kenan wato tunda ni nazama tsohuwar kawai so kake in koma gefe in rungume hannun inci gaba da kallon yanda rayuwar jikata zaiyi ta walagigi, ita ba budurwa ba ita ba zawara ba ita kuma ba cikakkiyar macen aure ba,
To wallahi kayi ta kanka domin kasan ni dai ko kaine ka auro mace ka ajiye yar mutane a gida babu sauke hak'k'i ni mai iya mata jagora ta maka ka a kotune a nema mata hakkin ta balle kuma rayuwar jikata mace ake magana, dan haka bawai ra'ayin ka nike nema anan ba yita kanka kawai, to nima in banda abuna ma miye nawa nasaka a cikin zancen cikakkun mutane kaida ko tsayayyar budurwa baka da ita mtws"
Ta karashe da jan tsaki..

"Koma dai menene karki shiga batun nan balle kice zaki raba shi da matan shi"

"Kai kaci uban ka, har nice zaka fad'ama abinda zanyi?"
"Amma Hajiya ai baki san hujjan shi nayin hakan ba koh,"

"A zaton ka har wani hujja gareshi wanda zan tsaya nema?, to nikam koda hujjar ko babu magana taje karshe wannan aure a yanzun kam yazo karshe indai ina raye zanyi tsaye wajen kwatoma jikata hakkin ta"
Sanin da yayi cewar duk fa abinda zai fad'ama Hajiyar ba lallai ta fahimta bane yasa shi kunna motar sukaci gaba da tafiya,

"Gidan ta zaka mai damu ta kwashi kayan ta mu wuce tare dan ta gama kwana a shegen gidan can"

Dara dam dam haka zuciyar ta wani irin bugawa,
Taya ma shida yaketa kokarin K'ara nesan ta kanshi da yarinyar nan Hajiya zata ce wai gidan ta zata koma,

A fili ko sai ya ce

"Amma Hajiya tun kafin mu taho na fad'a miki cewa inada nawa uzurin nima, in kin matsa sai tabar mishi gidan aiga gidan su nan a cikin unguwan ta koma can ta zauna mana miye kuma kice wai gidan ki zata koma da zama, bayan ga iyayen ta a raye, ki tuna cewa kafa Kakarta ce kawai! "

"Sannu ubana!
Eh nace sannu ubana!!
to bata komawa gidan nasu kafata kafarta, in kuma ni ban isa insa ka abu kayi ba kana iya juyemu ko anan tsakiyar titi ne kayi tafiyar ka,
Kaga ka fita a idona in rufe fa, tunfa da nace ka kaini gidan ta kakemin kananun kunkuni, naga dai ita shegiyar motar tun kan a haifo uwar ka nike shiga ina tuk'awa balle kamin tijara,"

"Eh koma mai zakice sai dai kice amma ni bazan je inyi jira da sunan d'auke matar wani bayan mijinta yana asibiti kwance ba, nama zama babban banza kenan zan dai sauke ku ai itama tana da mota sai kuyi amfani da natan kuje duk inda zaku"

Sosai Hajiya ta dunga sababi yanda kuka san ko shi AK ne Sarkin daya b'ata mata rai, kamar yanda ya fad'adin kuwa yana sauke su bai b'ata lokaci ba ya juya yabar unguwan,

Sai da yayi nisa da unguwar sannan ya nemi gefen hanya a kofar wani shago ya faka, bude kofar motar yayi ya fita ya k'arasa cikin shagon, bai bata lokaci a ciki ba ya fito da ruwan gora mai sanyi a hannun shi, yana kawowa wajen motar ya bud'e murfin gorar ya jefar,
d'aga kanshi sama yayi ya fara duldula ruwan a cikin bakin shi yana shan ruwan, sai da yasha kusan rabi sannan ya dan duk'a kad'an ya maida gorar ta saman kanshi yaci gaba da duldula ruwan akan shi yayin da ruwan ke gangarawa har cikin jikin shi, jifa yayi da goran a gefe bayan ruwan ciki ya k'are sannan ya bud'e kofar motar ya shiga ciki yana faman sauke ajiyar zuciya a jejjere kamar wanda yayi wasan tseren gudu.

"Innalillahi wa'innah ilairir raju'unยณ, waiyo Allah zuciya ta"
Ya fad'a yana danne zuciyar nashi da yake jin tana mishi zafi sosai ta ciki da hannun shi,

"Waiyo Allah na wai me yake shirin faruwa dani ne?
Me yake damu na ne? Astagfirullahi ya Allah na tuba ka yafeni, ya Allah kayi min maganin damuwa ta, Allah ka san wahalar da nike sha alhalin tana nesa dani, mutuwa kawai zanyi inta dawo kusa dani, bazan iya rike abinda nike ji yana min yawo a cikin jini na akan taba, Allah ka kawo min mafita na alkhairi, Allah karka bani ikon sab'a maka wajen aikata aikin ashsha, waiyo Allah zuciyata "

Ya k'arasa fad'a hawaye na gangarowa daga cikin idanun shi zuwa kan fuskar shi,gwanin tausayi, in wani yace soyayya zai narka zuciyar *ABDUL KHAREEM AHMAD MAI JAMA'A* Har ma ya zubda hawaye tofa ko duniya ba lallai su yarda da hakan ba, amma ku kalle shi yanzun yanda ya koma cikin dan kankanin lokaci wai a hakan ma dannewa yakeyi.

******

Ku sani cewa ita soyayya ba k'irk'iranta akeyi ba,
Asalima itace takeyin kanta,
Haka zalika idan ta fad'awa *Mace* ko *Namiji* mai rauni ba'a jimawa in ba'ayi dace ba tofa sai dai ku tsince *shi* / *ta* a wani kalar mawuyacin hali, domin ita soyayya babu ta inda bata iya kutsawa dan ganin ta girgiza rayuwar maiyin ta,
*Soyayya* ba kamar bacci bane da zaizo maka ba tareda *ka*/ *ki* n san yazo ba.
Ita *soyayya* aduk inda zata shiga tofa saita sanar domin saita tab'a duk wani abu mai mahimmanci dake tare da *ke*/ *kai* tun daga kan *zuciya*, *lokaci*, *tunani*, kai in ba'ayi dace ba tana iya taba harda ma lafiyan maiyin ta,
in ba'ayi sa'a ba sai ku tsinci mutum a dawanau yana shan magani.

*kai* ko *ke* babu wanda yafi yafi karfin soyayya domin ita ba shawara take nema ba a yayin kasantuwar ta, afkuwa kawai takeyi a sanda maiyi baiyi zato ba,
*ita soyayya batayin duba da matsayi*, *arziki*, *nasaba* ko kuma wani abu makamancin hakan yayin afkuwarta,
Abu d'aya tafi dogara akai shine *silar faruwan ta*,
A zaton AK mutum shike zab'ar ma zuciyar shi abinda zata so dama wacce bai kamata taso ba,
a nashi hasashen gani yake cewar shine zai zab'ama kanshi kalar macen daya kamata yaso,
ana shi ganin zuciyar shi tana da karfin da zata iya kare kanta daga ko wani irin harin soyayya da wata zuciyar ka iya kai mata,
Ya dad'e yana taka tsantsan,
ya dad'e yana kokarin kare zuciyar shi daga cutar daka inya janyo mishi rauni ko fad'uwa, ya dad'e yana ikirarin cewar shi yafi k'arfin so, *me akayi akayi soyayyar ma da har shi zata nemi hana shi sukuni*
Sai dai kuma takan tsan tsan,
wayau da dubarun shi basu canza komai ba na daga cikin kaddarar da Allah ya tsara mishi akan *Soyayya*.
Wanda hakan ya zama abun bakin ciki a gare shi wanda yake da tabbacin cewa duk fa ranar da asirin shi ya tonu tofa hak'ika shike da jin kunya, domin a bin takaici ne ace soyayyar ta fallasa aka k'aramar yarinya,
Yayi iya bakin kokari wajen danne abun a zuciyar shi ya kuma hana kan shi kusan ci da abar son nashi a yunkurin shi na yakice son,
A sanda abar son nashi ta kucce kuma sai yayi zaton cewar ai hakan ma nasarar shice koba komai zai iya kiran hakan da *TA FARU TA K'ARE* tunda bai fallasa halin da yake ciki ba balle kunyar duniya ta dame shi,
Sai dai kuma mai makon samun sauk'i sai yawan tunani ya kunno mishi kai domin a kullum inya zauna bashi da abin tattaunawa da zuciyar shi sai hasashen wani hali ita abar son nashi take ciki a inda aka mik'a ta,
Sau dayawa tausayin ta kan kama shi harma yakan ga laifin kanshi na cewa mai yasa a lokacin baiyi kwani yunkuri ba! Mai yasa a lokacin ya gazayin yak'i akan abar son nashi, yasan da yayi yak'i inda rabo a lokacin data zama nashi, inko ta zama nashin
Koba komai zata kasance cikin farin ciki inya zamana cewa a *Gidan shi* take ba a gidan wanda bai san darajar taba,
Haka dai yayi ta fama wajen ganin ya yajice yawan tunanin ta domin abinda yake da tabbaci akai shine *Soyayyar ta* ba kamun wasa tayi ma zuciyar shi dazai iya cirewa kai tsaye ba,
Sai dai yakan gode Allah akoda yaushe domin a dalilin ta shima ya d'andana d'aya daga cikin gefen soyayya mafi kuna, wato kaso wanda baima san kanayi ba, kai kuma bakama san ta yanda zaka nuna mishi son ba,

Hakika ya yarda yana cikin jarabawar rayuwa mafi zafi a zuciya,
Dan babu abu mafi ciwo irin kaci gaba da son abinda kasan ba zaka tab'a samu ba, mafi hatsarin ma shine *Soyayyar Matar Wani* yayi azumi !
yayi sallah !!
yayi salati!!!
yiyi rok'o zuwa wajen ubangijin al'arshi akan ya cire mishi ita a zuciyar shi amma ko abun yayi sauk'i da zarar ya ganta tofa sai ciwon nashi ya dawo sabo fil,
Hakan nema yasa gaba d'aya yake k'aurace ma duk wani abun da yasan zai ha'dasu,

A da can baya yakan ji fasuwar kai da alfahari aduk sanda yaga mata na bibiyar shi da k'okon barar Soyayyar su.
Hakan yakan sashi alfahari har yake jin girman kai a ganin shi ai mata sune ya dace subi shi domin dai babu abinda ya rasa a cikin abubuwan da mata keso,
Amma a yanzun sosai yake tausaya ma matan yakan kuma zaunar dasu ya fad'a musu cewar suyi hak'uri, yanda sukeji akan shi shima d'in yana jin sama da hakan akan wata,
tunda kuma ya rasata ya yardar ma kanshi cewa a fannin soyayyar ne bai da sa'a dan haka ya K'ara kulle zuciyar shi gudun karma wata zuciyar ta k'ara samun damar shiga dan zuciyar shi tana iya tarwatsewa in hakan ya faru.

Shi da yake ta bakin kokarin ganin yaba komai baya fisabilillahi shine kuma kwatsam wai Hajiya ke shirin kwaso yar mutane ta kawo gidan da yake rayuwa ta ajiye bayan tasan abu mai mahimmanci ne ya zaunar da shi a garin nan bai wuce kan nashi harkokin ba,
Shifa bawai bak'in ciki yakeyi ko kuma murna ba, ah ah halin dai dazai iya kasancewa a ciki yake tsoro, domin yasan a cikin su uku shine zaifi cutuwa a yanzun.

Bai bar wajen ba har sai da ya samu kira daga Yusuf wase cewar yana gida yana jiran shi.


*****

Koda AK ya sauke su ciki suka shige,
"Maza shiga ciki ki harhad'omin duk wani abun da kika san zaki buk'ata anan kusa,"

"To" Meenal ta amsa dashi sai dai kuma a yanayin ta kai tsaye bazaka iya fassara halin da take ciki ba, sai dai kuma gaba d'aya bata da kuzari,

Tsaf Hajiya ta taya ta suka shirya kayan tun daga kan takaddun karatun ta, kayan ta na sawa dama sauran su, saida suka cika bayan mota taf da kaya sannan Hajiya ta kaso wutar gidan ta kuma kulle duk d'akunan da kayana Meenal suke ta ciro makullayen suna shirin fita a gidan ne shigowar uwar gida ya tsaida su.

****

Abinda ya faru a can asibiti kuwa bayan fitan su Hajiya kananun maganganu ne suka fara tashi, a cewar su taya ita Meenal a matsayin ta na matar shi daya kamata ta tsaya akan shi zata tsallake tayi tafiyar ta,
To abun gulma dai baya kad'an dan haka tuni suka fara kiraye kirayen waya suna kai rahoto,
Haka sukaci gaba da zaman asibitin har zuwa sanda itama uwar gida ta iso asibitin tare dasu Innar yara,

"Ina Meenal?"

Innar yara ta tambaya dan su basu san cewa bata asibitin ba,
Tsagal d'aya daga cikin kannen Sarkin wanda suke uba guda ta bata amsa da cewa,

"Meenal tunda muka shigo nan ko zama bamuyi ba suka fice anan ita da kakarta har yanzun kuma bata dawo ba"

Amsa mata Innar yara tayi da cewa,
"to kila dai taje d'auko wani abun a gida ne, kuma ai ko tana nan din ma dama ba wani abun zatayi ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login