Showing 48001 words to 51000 words out of 174305 words
Chapter 17 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
mala'ikun duniya, police duka da mucciya sojoji tsallen gwaɗo.
"Ke dallah ki nutsu kina haka sai kin tona mana asiri tukun hankalin ki zai kwanta kinga saiki shirya kwana a cikin cell da hujja amma nikam wallah ba uban da ya isa ya kaini cell, dallah ni muje da shegen mugun fatan ki har kinsa na fara rasa kwarin gwuiwa ta,
"Kin tabbata babu abinda zai biyo baya kawata?
Meelat ta tambaya,
"Me ko zai biyo baya! Iya kacin in ma antada maganar tambaya cefa kawai za'a mana,toke bakin ki na ciwo ne da bazaki iya basu amsa ba? To tsaya kiji nidai nasan bai wuce in ma shi wancan ya buɗe mana aiki ace aje neman muba bari kiji mai zai faru,
Daga police station kai tsaye nasan gidan mu zasu,in sun isa nasan kowa zaiyi mamakin mai kuma ya kawo police gidan Malam dan sojoji aka saba gani a unguwar ba su ba,in sunyi katari sun cinma Malam nasan baza'aja maganar da tsayi ba , akasin hakan ko duk wanda suka cimma tsakanin Baba Adamu ko Baba Auta nasan abinda zasu fara tambaya shine "
ina muke?
dan haka cikin gida za'a shiga a tambaya su kuma sun san bama gida dan haka kowa zai bada shedar cewa bama gidan tun safe, police zasuyi tambaya cewa "ina muka je?
Su kuma zasu ce,
" munje gidan ya Mashkur"
nasan ba zasu hakura ba zasuyi zaton ko daga police station can zamu koma dan haka zasu kwasa su tafi,in kuma shi wancan Kwaron ya kaima Sarki labari to nasan da Sarki zasu isa gidan ko wasu daga cikin yaran shi in kuma yayi mutunci nasan zai ce dasu su koma bakin aiki shi zai neme mu, amma kafin nan dole wani daga cikin gidan zai kira wayar ɗaya daga cikin mu in bamu ɗauka ba zasu gidan acan kuma za'a basu tabbacin bama nan,
Daga can kuma gidan su Besty zasu nufa,dan haka zuwa gidan su Besty cancel ba wannan maganar a yanzun,
daga nan muna gama siyan awarar Tudun Wada zamu koma dan Gara muje muyi hakuri da halin Hajiya damu koma Sarki ya haɗamu kwana ɗaki guda da karnukan shi dan wallahi ban kwanan cell nikam.
Huhuhhu chakwakiya kenan an gujema police da soja za'a fada hannun iliya ɗan mai karfi😂🥳,
Hausawa sunce da babu Gara ba daɗi shi yasa na daure na baku babu dai yawa gobe in Allah ya kaimu da rai da lafiya ma ɗaura.
Share Please
#Ummiee~Zaria
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*
*👨👩👧👦DANGINA!👨👩👧👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_
ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._
*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}
*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._
_*Ina mai bada hakuri sakamakon jina shiru da kukayi, to gani na dawo insha Allah zamu cigaba daga inda muka tsaya, Nagode.
*********/////////.
Page 15
*Mai Jama'a*
Cikakken sunan shi,
shine *Abdul Khareem Ahmad*{A,K,A Mai Jama'a} ɗa na uku a cikin jerin gwanon yara 5 ɗin da iyayen shi suka mallaka, sannan ya zamto ɗa mafi kololuwar soyuwa a wajen uwar shi Aminatu wacce ta kasance yar Babban ahali masu tsatson Naira domin sosai ahalin ta suke da *Kunbar Susa* Littafin Surayyahm.
wacce a kullum take takaicin yanda Hajiya Innah ta janye mata shi daga gareta domin dai tun bayan daya kammala matakin karatun shi na sakandire Hajiya tayi mata awon gaba dashi zuwa Zaria sakama kon yanayin kasuwan cin Abba Ahmad mahaifin shi daya mai dashi kasar Saudiya, a babu yanda mahaifiyar shi Amina zatayine yasa ta iya tsallakewa ta tafi ta barshi bawai dan taso hakan ba sai dan tasan Hajiya zata kula mata da Abdul fiye da kanta.
Bayan dawowar shi zaria ne ya jona karatun shi a ABU Zaria dashi da abokan shi 2 Sadeeq da Musty waɗanda suka kasance abokan shi ne suɗin tun na yarinta sai Yusif wanda shi kuma a nan ABU suka haɗu har suka zama Abokai kasancewa shima ɗin ɗan sharholiya ne irin su AK dan haka tuni ya saje dasu suka cigaba da bada wuta.
Ak, Musty, Sadeeq, Yusif sun kasance the hottest young billionaires dake tashe a cikin makarantar ABU a wancan lokacin sun kasance masu class kyau gata gamida wayewa tareda ilimi atako wanni fannin dan haka a kullum mata suke kan kawo musu hari saboda kasancewar irin mazajen dako wacce mace ke fatan samu.
Sun ɗauki karatun su da matuƙar mahimmanci matuka dan haka koda yaushe cikin burgewa da class ɗin su suke, sai dai duk cikin su huɗun babu wanda ya kama kafar AK domin Shi dai haka Allah yayi shi da wani irin izzah da kwarjini duk da bai haɗa jini da sarauta ba sai dai izzar kuɗi tuni ta daɗe da huda jinin jikin shi domin shiɗin dan gata ne gaba da bayan shi.
Rata ne mai matukar tsayi tsakanin shi da talauci, sai dai duk wannan arzikin daya buɗe ido a cikin shi baisa ya zama cikin wasu matasan masu kuɗin da suke wulakanta marasa shi ba sannan kuɗin gidan su baisa ya zaman to cima zaune cikin matasan da babu ruwan su da tunanin dogara da kansu ba,
daga shi har abokan shi duk da kasancewar su ɗalibai a wancan lokacin hakan bai hanasu neman halaliyar su ba duk wata harka da za'ayi kuɗi na halak su shigo sun san shi dan sosai suka kware wajen iya juya biyar ta zama goma domin dukan su kasuwanci suke karanta kasan tuwar su yaran manya shima ya taka rawar gani matuka wajen habakar kasuwancin su, abokan takar su sukeyi gwanin burgewa babu munafunci balle kuma hassada suna farin ciki da farin cikin dayan su haka kuma suke baƙin ciki da baƙin cikin dayan su duk da halayan su daya banbanta kuwa domin Sadeeq da Musty mutane ne masu fara'a sosai suke da sakewa basa da ɗaure fuska, Shiko Yusif miskiline kafi mahaukaci ban haushi amma shi miskilancin nashi ya hada da sarautar dake yawo a jinin shine kasancewar shi ɗan sarkin Wase.
Shiko AK a fuskar shi in ka kalle shi kai tsaye ba zaka sashi cikin mutane marasa fara'a ba saboda yanda baida sake fuska matukar ba tareda su Sadeeq yake ba indai a cikin School ne bazaka taɓa ganin dariyar shiba balle harya kalli wata macen koya nemeta, ina sam dan tsabar ya raina ma mata da aji ko course mate ɗin shi mata baya sakar musu fuska balle ya sake dasu saboda tsabar gudun raini domin a kullum yana daraja girma da class ɗin shi, uwa uba kuma ego da yake ji dashi akan ganin matsayin sa kyawunsa da kuma dukiyar sa hakan yasa yake ganin shiɗin dole komai girma, kyau, class, gata, ilimi, da kuma dukiyar mace dole ta kallesa ta ƙara kallon sa duk da a rayuwar sa babu halittar daya raina wayan su kaman mata a ganin shi mata basu da darajar da har shi zai kallesu balle yaji yana son su,gani yake lalacewa ta same shi duk ranar da ya fara son wata Ƴa to hakika dole yakai kanshi asibity dan yasan baya cikin hankalin shi, dan haka babu waɗanda yake ma kallon zararru waɗanda suke buƙatar a mikasu dawanau irin masoya banda kallon taɓaɓɓu harda kallon makaryata ma yake musu inba karya ba mai zaka dunga faɗama yarinya.
yanda yake ganin sauran abokan shi na kiran yan mata su share a wanni suna waya mtws wannan ma ai tsabar zubar da ajine shi wallahi kullum cikin takaicin su yake, shi dai gaba ɗaya baiga abun burgewa a cikin soyayya ba dan haka kullum cikin neman tsari yake da soyayya tayi gabas shi kuma yayi yamma.
Shi ina shi ina mata fisabilillahi domin a ganin shi su ɗin basu ɗauki kansu da darajaba dan tun bai san kanshi ba yake ganin yanda mata ke ribibin shi har gobe kuma dai bata canza zani ba.
Sauda dama idan su Sadeeq suna fadin cewa har yanzun akwai matan da suke tare da budurcin su ma'ana basu taɓa kusantar wani namijin ba yakan kallesu ne kawai saboda iya hange dai baya tunanin akwai su, kai ko akwai ma yana ganin badai cikin gari ba sai dai daji wanda suke can ɗin ma yasan duhun kaine da rashin yancin kai yasa haka,
Kamar dai yanda aka sani kudu garuruwan su da mutanen cikin su da tsananin wayewa yayin da wani wayewar harta zarta tunanin mai hankali ta zama iya shege tsagwaron ta domin da yawa daga cikin ɗabi'un su anan arewar mu da zarar ka gwada aikata daya daga cikin nasu dabi'ar to fa kai tsaye ne za'a kiraka da sunan DAN ISKA KO YAR ISKA da babban baki kuwa.
(Dan uwatai ko ubanwa yace mai tarbiyar yaran Arewa ɗaya yake dana yan kudu oho😒)
Saboda shidai tunda ya tashi yayi wayau a garinda aka raine shi yake ganin yanda ake wata irin badakala ta yanda yarinya zata baro gidan ubanta tazo ta tare a wajen saurayi koda ko saurayin yana zaune tare da iyayen shi ne hakan bazai sa yaki dura mata ciki ba,
wani ma haka zai ajiye macen harta hayayyafa daga karshe kuma kaga basuyi aure ba har tsufan su yayin da wasu kuma matan nasu iskancin ma a gaban iyayen su sukeyin kayan su ,
shi kanshi tun tasowar shi yake gwagwar maya da migayun halittun nan Mata kullum cikin binshi suke suna mararin shi da dama a cikin su basu iya boye mishi tarin maitar sonyin mu'amala ta banza dashi sai dai kuma shi Allah yasa mishi kyamar su, sai dai har kwanan gobe bai daina fuskan tar hare²n matan da suke son yayi harkallah ta banza dasu ba, dan haka a ganin shi wani sauran daraja ya rage na mata da zai gani kuma tunda gashi a kullum cikin binshi suke duk inda yasa kafa sai mata sun maida nasu,
Shidai Allah yayi shi cikin mutane masu sa'ar rayuwa domin kaf rayuwar shi baisan wani abu waishi damuwa ko bakin ciki ba ballan tana kuma wani abu waishi takura inba na matan da suke maitar shiba, kwata² bai san zafin rashi na komai ba dan bai taɓa nema ya rasa ba,
ga kuma gata da yake samu wajen dangi na uwa da uba karma asa mutan gari a lissafi iya ahalin shi kadai ma sun isa,
domin tun yana ciki Allah yasanya ma iyayen shi matukar kaunar shi haihuwar shi kuma ta kama a dai² ranar sallan layya bayan dangi na nesa dana kusa sun hadu wannan dalili yasa tun ranar daya fito duniya ya samu sunan Mai Jama'a, sunan daya zama linzamin farin jinin shi a wajen al'ummah domin kam ya amsa sunan dan yana da kyawawan hali da kuma saukin kan da inhar ka zauna dashi koda na mintocine sai kaji ya burgeka, sai dai daga in kana nesa dashi bazaka mishi kallon mutum mai saukin kai ba gashi dason taimako sannan shi ko alkhairi zai maka bazai taba barin wani ya sani ba ko kai da yamawa bazai bari ka sani ba domij yana da wakilan da suke mishi irin wadan nan aiyukan in ana neman taimako,
Da fari ba karamin dizgi da yankwana wa ya dinga ma yan matan dake binshi a cikin makaranta ba sai dai kuma su matan da alama hakan ma burgesu yakeyi bai sha fama kanshi lafiya ba har saida yaga suna neman mai dashi mahaukaci sannan dan dole ya koyi iya zama a cikin su a bashi da yanda zaiyi dole ya koyama kanshi yanda zai dunga tolerating din su sai dai fa duk da hakan bai yarda ya sakar musu fuskan da zasu mai dashi kamar wani abokin wasa ba duk yanda yake ganin girman ki da zarar yaga zaki zame mishi cingum zai kakkabe ki ne tsaf dan shi baya son naci wallahi, sai dai fa duk yanda yaso Hafsa da Nusaiba yaran nan biyu shi bai taba ganin marasa zuciya irin suba, ita dai Hafsat makaranta ɗaya sukayi tun daga matakin sakandire amma tsabar jaraba da kuma kasancewarta yar gata kyankyasar inji yar dady da momy sai da tayi yanda ta shawo kan iyayen ta a maimakon kasar waje da suka so turata tayi karatu ta dawo arewa tayi joining ABU saboda tsabar son da takema AK gani take da zarar yayi mata nisa tofa wata daban zai so ba ita ba, koda tazo ABU maimakon karatun Law ɗin da kowa yasan cewa shine burin rayuwarta ajiye shi tayi itama ta ɗauki course ɗin masoyinta a burinta na kasancewa dashi akoda yaushe,sai dai a banza wai an tsikari kakkausa duk da yasan dalilin ta nayin hakan kwata² hakan da tayi bai burge shiba sai ma kara zubewa da class dinta yayi a wajen shi dan a cewar shi indai soyayya gaskiya ne ai namiji ne ya dace yaje yayi ta fataucin ta a wajen mace,
batun yau tasan halin kayanta ba dan haka tuni ta koyama kanta kiyaye duk abubuwan da tasan baya so, sai dai a gefe guda kuma kullum cikin tashin hankali take da sauran mata akan shi dan ba karamin kishin shi take ba dan haka koba zancen so in taga mace na zakewa akan AK take yin fito na fito da ita, duk da yana sane da haukan da take akan shi hakan bai taba sawa ya kalleta da sunan soyayya ba shifa kallon aboki ma yake mata class ɗaya fa sukayi rayuwa a sakandire tun daga Js har zuwa Ss class to shi made &in shi zaima kallon budurwa kamar mai fama da bakin iyaye fisabilillahi sai dai yana daga mata kafa koba komai yanda take kiyayewa bata fiye zake mishi ba hakan yasa shima yake ɗaga mata kafan yasan dai duk tsiya dole inta gama makaranta ta tattara ta koma gaban iyayen ta, shi hauka yake da zai auri tsarar shi,
Ita kuma Nusaiba da farko kallon mai hankali yake mata saboda ba karya tana da nutsuwa yarinyar gata da yawan gaisuwa hakan yasa duk dashi bame yawan wasa da mata bane haka dai yake daurewa yana mata raha dan yana matukar son a dunga girma mashi shine saboda taga yana sake mata fuska yarinyar nan ta kwance mishi zani a kasuwa ta wani samu Musty da batun wai son Mai Jama'a takeyi, to dai tundaga ranar itama dai ta kabar da daman daya bata amma munafukar kullum sai ta fake da wani abun take nema ta biyo ta inda tasan zata ganshi a cikin school in kuma lokacin weakend ne bata da sukuni haka zatayi ta zarya a cikin unguwa ,
abun fa bana wasa bane domin dai yan matan nan da tun anayin abun a cikin makaranta sai gashi sun fara biyo shi gidan da suke zaune a offcampus da sunan wani abu ya shige musu duhu ta fannin karatu kasancewar su guraye a fannin karatun su dama su Musty basu da matsala da yan matan todai a hankali a hankali gidan su ya zama wani karamin hall din karatu sai ya zamana ko wani abune daya shafi student ya tashi a can za'ayi. Tun AK na nuna bacin rai har sai da ya kawo na mujiya ya zuba musu na dole.
Yawan ziyarar da hajiya ke kai musu a duk sanda taso ne yasa ta fara ganin canje² domin dai duk zuwan da zatayi sai ta cin ma gidan da students ba kuma iya maza ba duk da a gaban idon ta tasan abinda ya shafi karatun sune yake kawo su gidan amma hakan bai sa ta samu kwanciyar hankali ba duba da yanda zamani ya lalace tana tsoron Allah tana tsoron yaran zamani atoh duk da dai duk weakend a tudun wada Ak yakeyi wani lokacin ma su duka huɗun ke zuwa amma dai ita sam hankalin ta bai kwanta da yanda yan mata ke zarya a gidan ba,
Tasan halin jikanta sarai mutum ne mai kyankyami da son cin abinci yana da bala'in tsafta ta jiki dama ta muhali domin koda yaushe tsaf zaka ganshi yasha wanka yana bulbula kamshi sai dai fa shidin ƙaton zero 0 ne indai a wajen kula da tsaftar muhalli ne bai iya komai na gyaran waje ba duk abinda ya shafe shi tun yana gida dama uwar shi ke kula mishi dashi dan haka koda ya zo Zaria Yar Aikin Hajiya ta amana Larai ke kula mishi da ɗakin shi, abinci dama ba'a ko ina yake iya ciba duk da bashi da zaben abinci amma shidin ma'abocin son tuwo ne sosai yake son cin abinci mai nauyi dan haka baya rabuwa da motsa jiki a koda yaushe,
sam Hajiya bata so yanda yaki zaman gidan ta ya zabi zama a cikin samaru ba amma bata da yanda ta iya haka ta kyale shi to ko