Showing 75001 words to 78000 words out of 174305 words
Chapter 26 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
dama gidan baki daya,
Da yike rana ta bude sosai hakan yasa babu yalwar jama'a a fadar yan sa idon kofar gidan,
Batama kanta sabon gaishe da kowa a wajen ba dan haka yanzun ma wucewar ta tayi abunta kamar bata san da wanzuwar kowa a wajen ba, a hakan kuma sai da aka samu wadanda suka rakata da kallo dan bala'i,
A farfajiyar gidan ta had'u da Aunty Billyn Ya Sa'eed tana kwashe kayan wankin dake jikin igiyar shanya,
"Oyoyo Aunty na"
ta fada tana mai rungume Billyn.
"Oyoyo Meenalin Baba Malam, yau kin tuna damu kenan? "
"Toda wa yace na manta daku bayan kullum sai nace ma Y'aya yace ina gaisheki, ko baya fada miki sakona ne? "
"Yana fada kai, nima Ina nufin kin dauke kafa ne a unguwar kwana biyu! "
"To ai gani yau nazo me aka ajiyemin? Bari dai in mikama Dada turai Dambun nan in fito nasan ba'a rasa kayan dadi a wajen ki Auntyn mu"
"Bari nima in ajiye kayan nan a ciki in biyoki dan dani za'aci dambun nan kam"
Karasawa sashin Dada Meenal tayi tana mai kwala kiran sunan Dadan kamar yanda takeyi duk in tazo gidan,
"Dadah!
Dadah!!
Dadan Hajiya innah, in baki fito kin tarbeni bafa komawa zanyi da abun dad'in dana kawo miki incema Hajiya bakya nan"
Daga cikin bedroom din Dadan ta amsa da cewa,
"Kujimin takadiran ci irin na yaran zamani, yarinya a baki sako ki kawomin shine saboda rashin son gaskiya kike batun komawa dashi kije kice bana nan, to aiko da kinyi ma kanki dan nima akwai abunda na tana da miki kinga nima sai in hanaki"
Ta karasa fada tana fitowa daga cikin dakin nata zuwa falo,
Itama dai kai tsaye ba zamu iya kiranta da sunan tsohuwa ba domin dai Masha Allah har yanzun tana nan a tsaye kyar kyakyawar farar bafulatanar ta wanda gayunta ya lullube tsufar , wanda tsabar hasken fatar tanema yasa tun tana yarinyar ta ake kiranta da sunan turai amma asalin sunan ta shine Fatima.
"Me Kakar taki ta baki ki kawomin ne? "
Ta tambaya a sa'ilin da takai zaune bisa kujerar falon,
Matsowa inda ta zauna Meenal tayi,
"Dambu ta girka shine tace in kawo miki"
"Madallah aiko Hajiya ta kyauta kamar tasan ina kwadayin shi, shiga kitchen ki dauko min plate da cokali ki gani yanzun zanbi ta kanshi"
Meenal na dariya ta mike taka cewa "Dadah kuma wallahi yayi dad'i dambun sai ma kinci zaki tabbatar"
"Ahaf yarinya ai nice zan baki labarin zakin Hannun Amina dan tun muna makaranta ita ke mana girki"
Fitowa daga kitchen din Meenal tayi dauke da plate har da ruwa da drink ta dauko dan tasan Dadah zata bukace su.
Fitowar ta yayi dai² da shigowar Billy falon,
"Ai kaji tsiyar yaran gidan nan yanzun nan fisabilillahi daga ganin wulkin kulan abinci shine sai da kika biyo sahu?
Wato kudai bazaku tab'a barin mutum yaci abu shi kadaiba balle yayi kiba irin na sauran Hajiyoyi to karkiji da wai wannan dambun yau dagani sai mijina keda rabo a cikin shi, dan haka juya baya ki koma inda kika fito "
Idan naga comment zan saki wani page din anjima in kuma kunyi shiru nima kujini shiru😎
Share Please
#Ummiee~Zaria
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*
*👨👩👧👦DANGINA!👨👩👧👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_
ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._
*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}
*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen.
💓💓 Wannan page din naki ne Aunty Binta Umar Abbale, Ina miki fatan alkhairi ubangiji Allah ya kara basira.
Wancan page din danayi posting d'azun nayi mistake mai makon 23 saina kara sa 22,
```Page 24
Gefen kujerar da Dadah ke zaune nan itama Billyn ta karasa ta zauna,
"Dadah kullum fa kece ke fada mana cewa ido gubane kuma rabon mutum kesa harya iskoka kana cin wani abun,
Zaifi dacewa inka taya mishi har sai dai in shine ya nuna baya ra'ayi to tanan wajen kai kuma ka fita hakkin shi,
To amma kuma Dadah yau nida kene za'aji kanmu akan dambun Hajiya? Kema kinsan daba abincin Hajiya bane ko kallon shi bazanyi ba balle har ya shigar min ido,
amma wannan dambun tun banyi ido biyu dashi ba ya shigar min rai, dan Allah ki sammun koba da yawa ba in maida yawu kar alhakina ya kamaki, kin san dai kobanza dama dambu na shake mutum"
Katseta Dadah tayi da cewa
" ke tsaya Malama naji kina dambu na shake mutum, to albishirin ki lafiya lau zanci nawa dambun harma in kora shi da ruwa kuwa, sai dai ke kuma kici kanki badan halin kiba dai zan sammiki amma ai jiya jiya nan na aika kizo ki kunsa min lalle a kafa kika k'i zuwa dan kina wajen hira da samarin da har yanzun kin kasa tsaida tsayayye kina nan kina ruwan ido gashi nan kannin bayan ki duk sunyi aure sun haihu, anya Balkisu lamarin ki basai nayi da gaske ba kuwa? dan dai gaskiya wannan nauyin jinin naki badai a dangin muba kila dai can kika kwaso shi"
Mikewa Billyn tayi fuuuu tayi waje cike da haushi,
ita Dadah bazaku tab'a zama kuyi hira ta arziki da ita ba saita jangwalo wani tsegumin kuma,
Su jama'a shike nan da zarar a kace a cikin gidan ku ko cikin Dangi kannin ki sun fara aure tofa duk idanuwa da bakin jama'a kanki zai dawo,
Sam basa la'akari da cewa kowacce mace kalar hasken tauraron farin jininta daban dana yar uwarta,
Kawai dan Allah yasa kannin ta mata yaran kishiyar maman ta sun samu mazajen aure tun kafin su kammala sacandire,
suna gamawa kuma aka musu aure sukaci gaba da karatu a dakunan su, shi kenan fa ta fara fuskantar wata kalar rayuwa ta daban a cikin gidan su dama wajen dangi, domin da wasa wasa sai gashi duk wasu tsararrakin ta tuni sunyi auren su wasu ma har sun hayayyafa,
A cikin dangi ko yanzun hatta kannin bayanta an aurar dasu tuni,
Kuma itafa bawai ta rasa maneman bane Ah'ah abun nedai baya lasting dan da zarar tayi saurayi karkarinta suyi wata biyu a tare ko sama da haka zaiyi batar dabo,
Sunyi kuka sunyi Addu'a ita da Ummanta dama duk wasu masoyanta amma dai shiru har yanzun sai dai tana da yakinin cewa addu'ar su bazai taba faduwa kasa a banza ba,
Yanzun nema da Sa'eed ke neman ta taga har yanzun bai daina zuwa ba dan a kallah sunyi kusan shekara a tare sai dai kuma kullum shima in ta mishi zancen ya fito ya nuna kanshi a gidan su domin iyayenta susan da zaman shi, amma kullum sai yace mata ta dakace shi tukun akwai abinda yake jirane,
To me mutane suke so tayi ne?
Wai su mutane a zaton su itama jin dadin tane zaman gidan da takeyi bayan ga kannin bayanta nan da yaransu,
Sai dai ya zatayi duk yanda taso aure ai dai ba itace mai alhakin aurar da kanta ba.
In hakan ne ai a cikin Danginsu har yanzun akwai maza tun daga kan samarin har masu matan, amma kaf cikin masu surutun dayi mata gorin taki aure ta tsaya jiran mai kudi babu wacce ta kwatanta hadata aure da d'anta,
To su mazan basuzo sunce suna sonta ba so ake ita ta fara bin mazan tana cewa tana son su ta yanda zata wulakanta kanta ko ya suke so tayi?
Ai tasha fada musu ita a shirye take ko auren dolen nema su mata, amma kuma babu wani yunkuri da sukayi har zuwa yanzun da takai kusan shekara 30 da haihuwa tuni ta kammala degree dinta har aiki ta fara, duk wani dawainiyar ta yanzun a kaso 100 ita Kema kanta kaso 70 duk dan ta ragema iyayenta wasu dawainiyar,
Amma hakan baisa ta tsira daga zagin da ake mata da sauran habaice habaice ba, dan hatta kannin ta mata da sukayi aure sosai suka raina ta
saboda daurin gindin da uwar su ta musu.
Kullum cikin fadama Allah damuwar ta take akan ya mata zabi mafi alkhairi kuma tana da yakinin cewa addu'ar ta bazata fadi kasa banza ba.
****
Bayan fitan Billy...
Rufe baki Dadah tayi da duka hannuwanta guda 2,
"Oh ya Allah maiya kaini wannan subutar bakin ni Turai yanzun sai yarinyar nan ta kullaceni tayi zaton ko nima ina cikin sahun makiyanta, Allah kadai gani kullum sallah ta biyar indan na daga hannuna saina roke ka akan kabaiwa wannan jika tawa miji na gari mijin nunawa sa'a, Allah badan halina ba Allah ka nuna min auren Balkisu in mikata d'akin auren ta da kaina Ya Allah"
Sai da ta shafa addu'ar a fuskarta bayan ta kammala sannan ta maida dubanta kan Meenal dake tsaye a gefe, dan itama yanda Billyn ta fita a fusace ya tab'ata dan tana da masaniyar yanda ake hantarar ta akan taki aure,
Shi yasa tayi matukar farin ciki sanda ta fahimci alakar soyayyar dake tsakanin Bilkisun da Sa'eed, kuma ko yanzun ta kuduri aniyar zata kaima Malam zancen dan tana da yakinin cewa son gaskiya Sa'eed din ke mata sai dai wani ra'ayin nashi can ne ya hanashi aure bawai dan babu halin yin auren ba,
wai shi zaman cikin family house ne bai so shi yasa yaketa wani kwale² bayan yasan cewa ko yafi kuturu naci Malam bazai barshi ya zauna a wani wajen daban ba.
"Amina zoki dibar mata dambun a wannan plate din da kika kawo min kinji, kuma karki wuce daga can ki dawo akwai sakon dazan baki"
"To" ta amsa dashi sannan ta karasa ta diba dambun ta fice daga falon bayan ta dauko wani plate din daban ta rufe dambun dashi.
Bayan ta gaisa da mutanen gidan dakin Billyn ta nufa dan tunda bata ganta a falon ba tasan tana can a dakin ta.
Duk sallamar da takeyi Billyn bata iya amsa mata yanda zatajiyo taba sakamakon kukan da takeyi,
Itama Meenal din bata damu da jiran amsar ba ta shige dakin dan tana jiyo sheshsheka na kuka a ciki,
Ilai kuwa kwance ta sameta a gadon ta rufe fuskar ta da pillow,
akan drawer din gadon dake gefe ta ajiye plate din dambun sannan ta koma da baya ta tura kofar d'akin data bari a bud'e,
Saman gadon ta haura har zuwa inda Billyn ke kwance, ga dai d'akin tubarkhallah yaji komai daya dace a sameshi a dakin yar gata, sai dai kuma ita ma mallakiyar d'akin bata cikin kwanciyar hankali kasan cewar d'akin ba d'akin auren ta bane, tafi fata da burin kasancewa koda a cikin kango ne indai har tasamu yancin da zata iya kiran kangon da d'akin auren ta.
Dago kanta Meenal tayi daga kan katifar ta maida kan a cinyarta, tafikan hannun ta tayi amfani dashi wajen share hawayen dake gudana a fuskar Billyn kafin ta daura da cewa.
"Aunty Billy dan Allah kiyi shiru kukan ya isa haka, dan nasan da kukane zai magance miki damuwar ki toda tuni kin manta komai kin dade a d'akin mijin ki, kuma nasan Dadah bata fadi hakan dan ranki ya baci ba domin duk masoyan ki zasuso su ganki a d'akin mijin ki"
Katse ta Billyn tayi da cewa,
"Meenal mantawa sukeyi cewa banice nike da ikon tsarawa kaina kalar rayuwar da nike so inyiba,
idon su ya riga ya rufe akan son ganin aurena gani suke kamar nice nike korar masu zuwa suce suna sona, alhalin tunda nike bantaba wulakanta wani saurayin dazai tun kareni da sunan soyayya ba, tunda na taso nasan ba'a yarjema yaran familin nan mata tsayuwa da samari ba har sai kin kammala sakandire,
Ni kuma Allah yasa tun Ina junior sakandire na fara samun masoya, tsoron kar a gane a gida a hukunta ni yasa bana sake musu fuska da kazo da zancen soyayya nike taka maka burki, har zuwa sanda nakai matakin aji 5 na sakandire ban dena samun masu cewa suna sona ba,
Amma kin san meya faru Meenal? "
Bata saurara dan jin amsar Meenal dinba ta daura da cewa,
"Tunda na shiga aji shida wato shekarar karshe dazan kammala secondary dina abubuwa suka canza min, duk masu bibiyata da suke jiran ingama makaranta su gabatar da kansu da daya² suka zare jiki na nemesu na rasa,
a haka har na kammala karatuna nayi zaman jiran result babu wani tsayayyen dazan nuna ince shi din saurayi nane,
Ganin shiru miji bai fitoba yasa Abban mu ya siyamin admission na koma makaranta naci gaba da karatu, to kingani dai gashi na gama makarantar tuni har aikina samu amma babu mijin aure har yanzun, bawai kuma dan babu masu cewa suna sona bane a'ah sai dai yawancin su da muguwar manufa suke zuwa min, daga Wanda in an kwana biyu zai fara tambayana Baby abokina wane yana birthday ki shirya muje mishi, sai mai cewa Baby zaki rakani waje kaza ko kuma ina waje kaza kizo ki sameni , mazan yanzun ba kunya ba tsoron Allah in bakiyi taka tsan² ba zasu afka miki,
dubeni ki gani Meenal koda ban fito na furta ba kowa yasan a shekaru na dole nima ina so ace Ina gidan mijina ne bawai gidan iyayena ba,
Amma Ina kowa ya kulle idon shi duk sun tattara laifin sun daura a kaina gani suke nike koron mazan, wasu kuma na cewa dan naga Ina da kyau shi yasa nike jiran mai kudi, sun manta cewa aure da mutuwa dukan su boyayyun sirri ne wanda ubangiji ne kadai yabarwa kanshi sani"
Kara maida kanta tayi ta kwantar a cinyar Meenal din tana ci gaba da sheshsheka.
"Aunty Billy Ya'yana fa, me yasa bazakice ya fito ba? Wallahi yana son ki, kuma nasan idan ya aureki zai kula dake"
Murmushin yak'e Bilkisun tayi,
"Humm Meenal kenan ke din har yanzun yarinya ce shi yasa, nasan bai zama lallai ki fahimceni ba"
"Na fahimta Aunty tunda gashi ai Ina gani duka kannen ki dake gidan nan mata sunyi auren sun barki dan haka nasan dole kina cikin kadaici koda ace ba'a takura miki da batun auren ba kuwa"
Zirgiza kanta kawai Billyn tayi.
"Meenal kenan kin san tun yaushe nasan Sa'eed kuwa? To bari kiji na sanshi da dadewa amma bai iya bude bakin shi ya fadamin kalmar so tun a sannan ba sai a watan nin baya ne ya furta min yana sona, yayanki ba karamin yaro bane da in yana son aurena ni zan tunkare shi kai tsaye, domin koba komai duk wanda yake tare dani a kallah yasan damuwa ta,
Bari in baki karamin missali da Mai Jama'a Ina son ki fad'amin daga tasowar ki zuwa yanzun fadamin yan mata nawa kikasan suna crushing akan shi?
wadanda duka a cikin su babu wacce bata shirya mutuwa akan shiba indai zai aureta, fadamin guda nawa ya aura a cikin su?
amsar shine ba ko daya, cikin su ni babu wacce nafi tausayama irin Nusaiba ki duba ki gani da gatanta da komai amma kalli yanda son wanda bai damu da wanzuwar taba yake wahalda ita, sai dai duk wahalar da take sha a banza domin har yanzun data dauki shekaru tana tura soyayyarta a gareshi bata samu sa'ar da soyayyar zata matsa ko inaba, domin ko a fuska bai taba banbanta ta da sauran matan dake kawo mishi cafka ba, to kenan in naci gaba da nuna naci na akan Sa'eed nima irin sakama kon dazan samu kenan"
Da sauri Meenal ta katseta da cewa,
"Oho musu su wadan nan ai basu da ajine kuma basu san ciwon kansu ba domin koni da nike karamar nan bazan iya cewa Ina son namiji ba"
Ta karasa fada tana wani hada rai da turo baki gaba,
"Yauwa to kin gani, Ashe kenan nima idan na tunkari yayan ki da batun cewa ya fito ya aureni na zama mara aji irin su"
"Ah ah Aunty aike son gaskiya kikema Yayana, kuma dan kince mishi ya turo ai hakan baya nufin zubar da aji ko wani abun daban, kinji dan Allah ki bashi dama ki mishi magana ko sau daya ne"
"Meenal ya zanyi toh domin shima har yanzun bai nemi damar ko sau daya daga gareniba, ko kin san cewa har yanzun gidan nan basu san da zaman soyayyar muba saboda bai bukaci