Showing 78001 words to 81000 words out of 174305 words
Chapter 27 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
su sanin ba!
Ki sani shifa abunda kake so burin ka akanshi bai wuce yanda zakayi saurin mallakar shi dan karya kubuce makaba, amma shifa? Ko a jikin shi bai damu ba ko sau daya bai taba neman dama dan ya gana da iyayena da sunan ya gabatar da kanshi a matsayin masoyin yarsu ba"
Haka dai sukayi ta tattauna al'amarin duk da cewar sosai Bilkisu ta girme ma Meenal nesa ba kusa ba amma taji dadin hirar daya gudana a tsakanin su, koba komai yau ta samu damar amayar da abubuwan da suka dade suna danne mata zuciya sakamakon kasancewar ta mace daya tilo a cikin dakin su, hakan yasa bata da wani abokin hira na sirri dan ita bata iya zama da kawa ta bude mata duka sirrin rayuwarta ba.
Badan hirar ta kareba dole ganin yamma na kunno kai yasa tayi sallama da Billyn wacce saida ta mata kyautar kayan zaki su sweet sannan ta hada mata da wasu kaya kala biyu wanda ta bada dinki aka samu matsala kayan basu shigeta ba, tun a lokacin dama ta kuduri aniyar Meenal din zataba kayan,
Sai da ta rakota har kofar d'akin Dadah sannan ta juya ta koma sashen su,
Meenal bata zauna ba koda ta shiga sakon da Dadan tace zata bata kawai ta amsa, sannan ta mata sallama bayan Dadan ta bata 1k da sunan tayi kudin mota.
Tun daga nesa kafin ka karaso majalisar hayaniyar matasan dake wajen zai baka tabbacin cewa masu wajen nanan, kamar yanda ita ma Meenal hayaniyar nasu ne ya shaida mata cewa yan anacen sun dawo,
Abun haushin kuma shine yau ba zallah bakin fuska bane kawai a wajen harda su Musty Sadeeq Wase dama wasu da bata sani ba,
Sai gashi duk rashin son gaisuwarta yau dole sai da ta musu gaisuwar duk da jam'i ta mika musu ita, dadin tama AK da baya wajen, Addu'a take Allah yasa baya cikin gidan domin tana shiga kayanta kawai zata dauka ta gudu gida wallahi.
Sai dai kash tana bude get din gidan ta hange shi zaune akan kujera waya kare a kunnen shi kuma nan inda yake zaunen nan wajen ta boye shower gel dinshi data dauko a dakin shi,
Kauda kai tayi tana karfafa ma kanta gwuiwa da cewa ta maze kawai ta wuceshi abinta,
Shiko tun shigowar ta gidan karar da kofar tayi shiya an karar dashi, sai dai bai nuna ko wani alama dazai nuna cewar yasan wani ya shigo gidan ba, kallon da yake mata ta kasan ido kuma bai zama lallai tajishi ba bare kuma ta gane yana kallon ta din.
Sai dai ga mamakin shi yauma din dai kamar kullum zuwa tayi ta gifta shi kamar dutse ne a wajen bashi AK Mai Jama'a ba,
Katse wayar yayi ganin abun fa na yarinyar nan yafara wuce tunani yana zaton inbai tantance mata aya da tsakuwa ba bazata shiga hayyacin ta ba, dan haka ya bude bakin shi cike da isa ya kirata.
"Keee zonan"
Taso tayi kamar bataji shiba ta wuce sai dai kuma kafin ma ta kara daga kafarta ya kara cewa,
"Koda wasa kika kara daga kafar nan da sunan barin wajen nan sai na karyaki"
Juyowa tayi tana zaro ido tace "ka karya ni, to nime na maka? Ai kee ka Kira ni kuma ba suna na kenan ba"
Galala ya tsaya yana kallon ta lallaima yarinyar nan,
Shikoh shi dai waishi yarinyar nan take so ta raina haka kowa? Shida manyan mata ma idan yana gaban su zakaga har rawar jiki sukeyi shine ita take da kwarin gwuiwar raina mishi da wayau, aiko in batayi hankali ba kafin tabar gidan nan saiya zane mata jiki tsaf in takamar ta rashin kunya ne shi shine Baban ta.......
Tofa🤣
Share Please
#Ummiee~Zaria
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*
*👨👩👧👦DANGINA!👨👩👧👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_
ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._
*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}
*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen.
Wannan page din naku ne mutanen Family house,
Rukayya
Saudath
Hajiyayye
Jikar hajiya (goyon kaka)
Har dama wadanda ban Kira sunan suba, ina fa son ku da yawa mutane na❤🔥
```Page 25
Aiko in batayi hankali ba kafin tabar gidan nan saiya zane mata jiki tsaf wallahi dan in tak'amarta rashin kunya toshi shine Baban ta,
Karasowa tayi tana wani ciccijewa kamar wacce ake jawowa da igiya.
"Gani"
"Aina ganki, ko kinga alamun inada ciwon makanta ne? zauna anan tambayan ki zanyi"
Gefen shi ya mata nuni da hannu a matsayin inda zata zauna d'in,
Kuri ta kafeshi da ido ita da zuciyarta suna tafka muhawara akan ta zauna din ne ko ta zabga da gudu ta fice a gidan, sai dai kuma tasan ko tace tayi gudun a banza dan tsaf in yayi tsalle daya zai cafkota , a babu yanda zatayi dai ta nemi waje d'an nesa kadan dashi ta zauna.
"Menene Sunan ki? "
Kai jama'a kujimin wani rainin hankali fisabilillahi wai sunan ta yake tambaya, to dan Allah inba neman rigima ba dan dai tambayar suna aida sai ya tambayetan kawai basai ya wani daure fuska wajen bata umarnin zama ba, dan ita harta fara hasaso laifin gyarar datama d'akin shine zai hukun tata akan shi.
A zaton ta na cewar ta kubuta yasa wannan Karon cikin d'an sakin fuska ta bashi amsa da "Ameena shine suna na amma Meenal ko Meenat ake kirana dashi a gida da makaranta"
Saida ya kauda kanshi gefe sannan yace,
"Ni kinsan suna na? "
Shiru tayi tana wuki² da ido a zuciyarta kuma cewa take, kuji wani maganar yan kwaya wai nice ban san sunan shi ba, to wani sunan ne a ciki ban sani ba, Abdul Khareem din ko Iliya dan mai karfi, ko Mai Jama'a ko kuma Ak.
A fili ko cewa tayi
"Na sani Mana sunan ka Ya'ya Abdul Khareem"
"Oh ashe kin san suna na? "Ya tambayeta yana mai dage giraren shi,
"Eh" ta bashi amsa.
"da kyau kinyi kokari,
Tambaya na biyu so nike ki fadamin ya alaqata dake take"
"Alaqa kuma? kawai dai ai kai d'an Kawuna ne Yaron Ya'yan Mommy"
"Ok idan na kasance Yaron kawun ki nidin menene matsayi na kenan a wajen ki? "
Babu bata lokaci ta bashi amsa da cewa,
"Ya'yana mana! kuma ai cewa akayi d'an mace da d'an namiji abokan wasan juna ne"
Ba tareda wani damuwa a cikin furucin nata ba ta kara da cewa,
"to kaga kenan nima abokiyar wasar ka ce"
Ta karasa fada da murmushi a fuskarta.
Kai innalillahi wa innah ilaihur raju'un, kai jama'a wai shi wani tsautsayi nema yasa shi kiran yarinyar nan, kuji wani rainin wayau fa da take fada mishi wai shine abokin wasan ta, bayan shi koda yayyen ta maza ma ba wasa yake ba sai ita da take nan kamar alakoro ne zata kalle shi ta kirashi da abokin wasan ta.
Katse shi tayi da cewa "in tafi? ana jira na a gida ko baka gama tambayoyin ba? "
"Kika tashi a wajen nan saina tokare ki ta yanda in kika kifa sai an nemo masu d'aukar ki, lallai ma yarinyar nan wato saboda kin daukeni a matsayin abokin wasan ki shi yasa kikamin rainin dakoh gaisheni bakya iyayi koh?
Ko a gidan kune ba'a koya miki gaisheda na gaba dake ba? "
Bata fuska sosai tayi ganin daga maganar arziki abun yana nemar komawa cin fuska, dan Allah jama'a bashi ya tambayeta ba ita kuma ta bashi amsa, kuma ita ai sam a cikin d'abi'un ta babu fadar karya, in har ka tambayeta gaskiyar zata fada maka wala ta maka dad'i ko kuma akasin hakan wannan kuma kai ka jiyo, shine dan wulakanci zaice wai ko a gida ba'a koya mata gaisuwa ba.
"Ba dake nike magana bane? "
Ciki-ciki ta amsa da cewar
"an koya min mana! "
"Oh ashe an koyamiki to meyasa ni baki tab'a gaisheni ba? Ko a cikin wadanda akace ki gaisar din babu suna nane?"
"Ah'ah kayi hakuri "
"No yarinya aiba maganar inyi hakuri bane so nike inji dalilin da yasa ko sau nawa zaki ganni saima kin daure fuska kin kauda kai kafin ki wuceni kamar kinga kashi, ko ina miki wari ne? "
"La'ilah"
ta fada tana zaro ido gamida cewa
"ni din? "
"Kwarai kedin fa ko cemiki akayi bana lura dake a duk sanda zamu hadu?"
Bata da amsar bashi dan haka tayi shiru, saima dukar da kanta da tayi tana wasa da ledar dake hannun ta,
"Uhummm ke nikejira"
"To... to.... toow nidai kayi hakuri, ba kai bane duk sanda mutum zai ganka kana cikin jama'ar ka, in ma an ganka kai kadai to waya kakeyi ni kuma shi yasa nike wucewa bana gaisheka"
"Wato in mutum yana cikin mutane bazaki gaishe shiba kenan? amma ai a hakan kike gaisheda su Musty su kuma miye alaqar ki dasu?
Bata bashi amsar tambayar farko daya mata ba sai ta biyun, inda tace
"to ai shi Musty sunan Baba Malam yakeda"
Saida ta gyara zaman takalmin kafarta ta kuma rike ledar hannun ta da kyau sannan ta daura da cewa,
"Kuma su ai dukan su suna da sakin fuska suna ma mutane dariya kai koh fuskarka kullum kamar ta shanu"
Tana gama fadar hakan kamin kiftawar ido ya hangota ta falfala da gudu zuwa sashen Hajiya.
Baki da hanci ya bude yana kallon ikon Allah,
Wato ma shi yarinyar nan ta Kira da mai fuskar shanu,
Da gaske dai kenan abokin wasan nata ta dauke shi.
Girgiza kanshi kawai yayi fuskar shi dauke da karamin murmushi,
"Allah ya shirye ki"
Baiyi yunkurin bin bayan ta ba sai ma sashen shi daya wuce dan koba komai hakika yana bukatar hutu dan haka zaije yadan watsa ruwa kafin yaci abinci.
Sai dai me? Yana bude d'akin nashi anan bakin kofar ya tsaya ya cire takalmi da safar dake sanye a kafar shi, sai dai kash domin ko baiyi taku mai nisa ba Allah ya hadashi da gamon shi,
wato k'afa yar hutu wacce bata dauke da faso ko kauje ga kuma danshin safa ne ya hade da santsin tayes sakama kon ruwan da har yanzun bai gama bushewa ba, aiko dai kafin ya ankara ji kake suuuuu tabb duwawun shi ya maku da kasa dan ainihin faduwar da ake kira faduwar yan bori shi yayi,
"Innalillahi Wa'innah Ilaihir Raju'un, waiyo Allah na wash bayana subhanallah"
Kalmomin daya dunga maimaita wa kenan cike da azaba dan wallahi yafa maku da kasa da kyau bawai faduwar wasa ba,
bai iya tashi a wajen ba saida yaji rad'ad'in da jikin shi ya dauka ya ragu tukun na, sannan ne ya lallaba da rarrafe ya karasa cikin dakin shi, wajen wardrobe din shi ya wuce da niyyar ya ciro kayan da zai canza domin na jikin shi dai sun gama nad'e sauran ruwan dake wajen, sai dai me? Yana bude kofar kayan da dama jira suke a bud'e kofar su zubo suka biyo kofar gaba daya haka suka danne shi da yake a duke yake,
Kaya! kaya haka dai ya samu yayi watsi da kayan a gefe, cike da jin haushi ya koma gefe ya zauna ranshi a bace can kuma ya fara bin d'akin da kallo dan ya tabbatar ba haka ya fita ya barshi ba to waye Hajiya taba key din dakin shi har aka shigo mishi,
dan yasan dai Wallahi wannan ba aikin Larai bane, to
" waye? "
ya tambaya a bayya ne, zuciyar shice ta bashi amsa da cewar
"yarinyar nan",
kai anya kuwa?
Yes itace dan tabbas dazun yaji kamshin turaren shi a jikinta,
"To kenan ita ta shigo min d'aki? Meya kawota dakina? Aiko zata sani wallahi"
Ganin sakar zucin bazai fishsheni bane hakan yasa shi daddafawa ya mike, dan gara yayi sauri yaje ya ritsata kafin tabar gidan, bai jira komai ba ya wuce gefen Hajiya hannun shi daya dafe da kwankwason shi.
*****
Da gudun ta tafado falon na Hajiya dan a zaton ta yana iya biyota,
Kiririf ta maida kofar falon ta rufe harda murza makulli.
Ke!
Ke!!
Ke uban waye ya biyo ki kika fadomin falo haka kamar wacce mutuwa ta biyo, ah gaskiya baki da kyakykyawar d'abia wallahi nidai kin dauki alhakina haka kawai ana zaman kalau zaki fadomin daki kamar an jeho ki mtws
Kuma ki koma ki budemin kofa dan ina kallon masu min shiga da fita ne tunda mutanen gidan basa nan,
Ita dai bata kula Hajiyar ba saima karasawa inda jakarta yake da tayi,
"Ita Turan da kika kai mata dambun sunan ubana ta kira ta zaga koh ya'ya ? dan banji kince min tace ta gode ba! "
"Kai Hajiya ba yanzun na shigo ba ko zama fa banyi ba, ai kin san dai dole zatayi godiyar kuma harda ma kaya Aunty Billy ta bani Dadah kuma ta bani wani sak'o wai in kaima diyarki"
"Wacece kuma Aunty Billy a gidan? Bakuwa sukayi? "
"Hajiya Bilkisu fa nike nufi ba wata ba"
"Allah Sarki itace ta baki kyautar kaya? "
"Eh Hajiya wai telan ne ya matasu sun matseta shine ta bani kin gansu! "
Ciro kayan tayi daga cikin ledar tana nuna ma Hajiya,
"Ah lallai kinsha godiya kuma kayan masu tsada ne, to Allah ya mata albarkha Allah kuma ya dubi zuciyarta ya fito mata da miji na kwarai tayi aurenta ta huta, dan nidai tausayi take bani yarinya bata rasa komai ba na diya mace amma ace miji ya gagara samuwa, aini dai dan kar inyi shish shigi ne dana nema mata miji wallahi, to yanzun abun alkhairin nema baya dorewa kar in hadata da wani in abu baiyi dad'iba ace nice sila,
amma inba haka ba aiko yaron kirkin nan Saddeequ nace ya nemi aureta nasan bazai kiba tunda masha Allah yarinya ce mai kyau wallahi sak kakarta turai to tsoro nike shi yasa ban mishi maganar taba"
Katseta Meenal tayi da cewa
"Hajiya Ya' Sa'eed ke neman tafa, kuma aurenta yake sonyi"
"Kai madallah, madallah too kice duk mune aiko na mata murna wallahi miji irin Sa'idu ai idan ka samu saika rike abinka kayi ta riritawa, to aiko zan samu Dadah da batun gara ace ya fito a musu aure tun kafin shima a neme shi a rasa"
Kwankwasa kofar da akeyi ne ya katse musu hirar da suke.
"Kinji koh? Shi yasa nace ki budemin kofata dazun amma da yike kunnen kashi gareki kikamin kunnen uwar shegu yanzun ai kya bude"
"Waye? "
Meenal ta tambaya a yayinda take bude kofar, bata samu amsar tambayar nata ba idon ta yayi tozali da AK da tambayar nata ya kara fusata shi,
Zaro ido tayi ganin shine,
"Waiyo Allah dan Allah kayi hakuri wallahi bazan kara ba"
Baice mata komai ba illah janyo hannun ta da yayi suka koma cikin falon.
"Hajiya me yarinyar nan taje yimin a d'akina? "
Ya fada a sanda suka karasa inda Hajiyar ke zaune tana kallon su,
"Mai kuwa zai kaita banda ta gyara maka d'akin tunda ba kowa a gidan, wani abune ya faru? "
Bai iya bata amsa ba illah juyawa da yayi ya jawo Meenal zuwa gaban shi baiyi wata wata ba ya sauke mata wani irin lafiyayyen rankwashin da sai da yasa takai kasa bayan ta fashe da k'ara nan kuma kukanta ya cika d'akin,
"Kai Abdul ka kiyayeni fa wani irin rashin mutunci ne zaka kawo yarinya har gaba na sannan kaci zalin dinta, na tambaye ka meta maka baka bani amsa ba shine kake kokarin bula mata kwakwalwa da gudumar hannun ka?
To kasan dai ko banyi Allah ya isaba sai Allah ya saka mata tunda dai ni na ce taje ta gyara dakin.......
Share Please
#Ummiee~Zaria
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*
*👨👩👧👦DANGINA!👨👩👧👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_
ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._
*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}
*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen.
Ina