Showing 138001 words to 141000 words out of 174305 words
Chapter 47 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
abun, meya faru?"
"Akwai Hajiya kuma abubuwa sun faru yau, sai dai kuma kafin in fito shi Ya Sarki yazo har d'aki ya sameni aka cewa abunda ya faru in barshi a cikin gidan ma'ana kar in fad'ama kowa"
"Yace miki karki fad'ama kowa kuma shine ni kika d'auko kafa kikazo dan ki fad'amin?
To amma tunda kinzo ai bazan kore kiba miya faru ne haka?"
Gyara zama Meenal tayi ta koro ma Hajiya tsaf abinda ya faru harda ma maganganun da Teemah take fad'a mata aduk sanda suka had'u, dama ikirarin da tayi yau cewa zasuga abunda zai biyo baya.
Salati da sallallami Hajiya ta d'auka tana kankance ido cike da masifa take cewa.
"Amma dai ke koh Aminatu kinji haushi, wallahi kin dai ji haushi albasa batayi halin ruwa ba, Ina ce komai nawa kikayi gado kamar yanda kikaci gadon sunan,
Innah ashe da saura, yanzun nan ki zauna har wata kishiya tayi asubancin shigo miki gida ta fetsa kalar nata rashin mutuncin kina cikin gidan a raye kina kallon ta baki shek'a da gudu zuwa cikin kitchen din ki kika d'auko tabarya kikayi ma kanta fashin kwakwa inya so duk abunda zai faru ya faru ba,
Ah gaskiya baki kyauta min ba, ni da wannan zancen da kika kawo min ai zanfi farin ciki in kirana zaman sulhu akayi police station Bayan kin rotse mata kai wallahi,
Ke wai ma tsaya, Ina magungunan da kwanakin baya nace ki dunga zubawa a binci in zakiyi girki?
Kar dai kice min duk uban wahalar da nasha wajen ganin an kammala had'a muku maganin nan a banza ya tashi bakiyi amfani dashi ko sau daya ba?"
Ta tambaya tana tsare Meenal din da kallo,
Ita ko soshe² ta kamayi alamun rashin gaskiya, hakan ne kuma yaba Hajiya amsar tambayar ta cewa Meenal din batayi amfani da maganin ba.
"Wai a Ina kikayo gadon sakarcine Meenal?
Kin san maganin miye na baki kuwa?
Maganin karin ko wani irin asirine fa, da zarar Allah yasa aka dace sai kiga da mutum yayi amfani dashi duk wani mugun abun dake jikin shi sai ya warware cikin kankanin lokaci kuma insha Allah wani bazai k'ara cin galaba akan ka ba,
Tun wancan lokacin da kika bani tabbacin babu abinda ya shiga tsakanin ku nike tsaye kanki dan ubanki wajen amsar miki taimako ashe ni kikema kallon sha² Ina ta gantalin ganin Allah ya tsareki daga sharrin kishiya,
Ka tseta Meenal tayi da cewa,
"Allah Hajiya duk wanda kika bani dan ni inyi amfani dashi nayi, na wajen nashi ne kawai tsoro yasa ban zuba mishi ba gudun kar wata rana ya gani yayi zaton ko Ina da nufin cutar dashi ne"
"Eh ke baki da nufin cutar shi amma ai shi gashi ya cusa ki a cikin gida ya kafe kamar hoton enlargement, baki mishi amfanin komai saina gyaran gida da girki,
Ita kuma dan ubanta ki barni da ita badai takamar ta matsafa ba, to mu bama tsafi amma mun yarda da kudurar ubangiji, dan haka lokaci yayi da nata wasan zanje karshe, su magungunan da nike bakin ya kikeyi dasu? "
Suna nan a cikin magunguna na,
To abunda za'ayi yanzun tashi kije maza ki had'amin kansu, zan aiko a amsa min anjima ko kuma kilama in shigo unguwar naku da kaina dan na dad'e banje ba, kuma bance ki fad'ama kowa abinda yake faruwa ba"
"Hajiya"
Ta kira sunan sai kuma tayi shiru,
"Ya akayi akwai wani abun ne kuma?"
Hajiya ta tambayeta.
"Hajiya ni so nike ya sakeni, kinga baya sona nima kuma ba son shi nikeyi ba, nidai gara ya sakeni kawai zaman da nayi da Allah ya bada lada,"
A dar dar tayi maganan dan bata san yanda Hajiya zata fassara maganar nata ba.
"Baki fara son shi ba kike nufi duk wannan shekarun da kukayi da aure? "
"Hajiya ni ban tab'a jin son shi a zuciyata ko sau d'aya ba"
"To Ina amfanin ka zauna da wanda baka so har karshen rayuwa, ai tunda har kin tabbata bakya son shi kwantar da hankali yar nan indai Ina raye an gama miki dole, wannan aure kam sunan shi matacce insha Allah dama kaddara ce tasa aka d'aura zaren to yanzun kam nice zanyi tsayin daka wajen tsinke shi, amma dai karki tada hankalin ki a yanzun dan dole mubi komai a sannu, dan in muka matsa ita waccan matar tashi gani zatayi kamar ta samu nasara akanki kenan,
Yanzun abunda zaifi shine mu maida hankali wajen karya kadarin ta, kinji ko yar albarkha, ni dan dai ma kince baki sone da sai ince kiyi hak'uri kiyi zaman ki a gidan ki, dan yanzun dai ko kin fito ya riga ya b'ata miki suna kowa kallon bazawara zai dunga miki"
"Nidai Hajiya koma me za'a kirani na yarda amma na gaji da auren nan haka"
"Yo yar nan tunda kikace kin ganji yanzun kam ai babu dole, Allah dai yayi maki zab'i mafi alkhairi.
Bayan baro warta gidan Hajiya koda ta dawo gidan su Sarkin ta shiga suka gaisa da jama'ar gidan kafin ta fito ta shiga gidan Malam,
Tun tana gidan su take ganin kiran Sarki a wayar ta amma tayi kememe tak'i d'auka dan tasan bazai wuce yace abinci yake nema ko wani abun yake buk'ata ba,
Sun dan taba hira da Malam a cikin hirar ne kuma ta sako mishi zancen addu'ar da take so ayi ma Sarki,
Shiru yayi yana nazarin ta, amma ganin bata mishi wani k'arin bayani ba yasa shi amsa mata da cewa za'ayi insha Allah,
Bayan ta shigo gidan ta dakin ta ta wuce kai tsaye taje ta ajiye tarkacen data shigo dasu sannan ta kama hanyar zuwa wajen Sarki,
Da sallama ta shiga sai dai kuma bashi a falo, tayi kamar zata juya sai kuma zuciyar ta ta mata ishara da cewar ta duba dakin baccin shi,
Tun daga cikin corridor d'in da zai sadaka da d'akin nashi ta fara jin wani irin nishi nishi wanda ta rasa gane kanshi,
A haka dai tayi karfin halin k'arasawa ta bud'e kofar d'akin ta shiga bakin ta dauke da sallama,
Abunda idanuwan ta yayi tozali dashi ne yasa zuciyar yayi kwance kwance ya yanke ya fad'i har wayar hannun ta da Hajiya ke kira ita kuma take kokarin Amsawa ya kucce daga hannun ta zuwa kass...........
Babu editing duk inda kukayi karo da mistake please ignore it 🤨.
Huhuhuhh, bafa ayi komai ba tukun yanzun ne wasan zai soma.
Toya kukaji page din yau,
Jiya banga comment da yawa bafa🙄
*Ummiee Zaria*✍🏼
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: 🔱⚜️👨👩👧👦 *DANGINA!* 👨👩👧👦⚜️🔱
~{{MY FAMILY }}~
*RUBUTAWA*
*UMMIEE ZARIA*✍🏼
`````` *Page 40*....
Da gudu ta k'arasa shiga cikin d'akin bakin ta na faurta kalmar Innalillahi wa'innah ilairir raju'un....
Haka taci gaba da maimaita wa,
a rud'e ta doshi inda yake kwance yana ta faman mulmule akan tile's d'in d'akin domin alamu sun nuna cewar tsabar azabar ciwone yasa shi fad'owa daga kan gadon badan ya shirya ma hakan ba.
"Ya'ya!
Ya'ya!!
Ya'ya mai ya same ka? waiyo Allah na dan Allah ka tashi meke maka ciwo?, innalillahi dan Allah ya'ya ka tashi dan Allah muje asibiti, yama zaka zauna a gida Bayan kasan baka da lafiya!
Ni ai ban san cewa ciwo kakeyi shi yasa kake ta kirana ba da nazo tun d'azun, kasha magani kuwa? Ina kake ajiye maganin ka in d'auko maka? meke maka ciwo ka fad'amin sai in d'auko maka maganin a d'akina in baka dashi anan"
Take tambayan shi cikin kuka domin duk ta rud'e wannan shine karo na farko da take ganin zafin ciwo yasa Babban Namiji mulmula a kasa,
Shiko tsabar azabar ciwo ne yasa gaba d'aya ma baya gane mai take cewa, dan sosai yake jin ciwon bada wasa ba,
Shi bai san me yasa a cikin kwanakin nan yake yawan fama da sha'awa ba,domin dai a iya sanin shi har yazo garin nan ya gama kwanakin da zaiyi lafiya lau yake komawa ba tareda ko sau daya yaji cewar yana buk'atar keb'ewa da ita ba, dan sau tari sai ma inya koma Kadunan ne abun ke damun shi har sai yaje Lagos ya sauke damuwar shi sannan yake jin dai²,
To amma yanzun kam abubuwa sun canza mishi domin wata rana sai yaji kamar yaje ya nemi yarinyar nan sai kuma ya rasa kwarin gwuiwar shi, yayi zaton in Teemah tazo zai sauke a kanta sai dai hakan bai samu ba,
wannan dalilin nema yasa ranar ya nemi Teemah sai kuma akayi rashin sa'a bata cikin tsarki, yasan za'a iya samun matsala inya kwana a wajen ta shi yasama ya gwammace ya dawo gida ya kwana a ranar,
Ita kuma tayi zaton daya kwana a gida ya nemi Meenal ne shi yasa tazo tayi nata kalar haukan daga karshe kuma gashi ta tattara ta tafi ta barshi da bala'in da bai san inda zai samo mafita ba.
Shi dai ba dan iska bane domin dai a can baya da yayi rashin ji ma ba'a hayyacin shi yayi ba kuma a iya shaye² ya tsaya baiyi neman mata ba har zuwa sanda yayi aure, balle kuma yanzun da har yake da yara sun zama yan mata, to shida keda yan mata Ina zai yarda ya tab'a yar wata a rama akan nashi.
To yau dai abun ya gagara domin daren jiya ma bai samu yayi bacci wadatacce ba saboda tsabar ciwon daya kwana dashi, yau kuma yayi zaton ko in ya shiga cikin mutane ko abun zai lafa sai dai kuma abunfa ba sauk'i.
Ganin yana neman mutuwa ne fa yasa ya dawo gida a zaton shi ko Meenal bataje makaranta ba tunda ai da safe tace mishi bata da lafiya,
So yayi yazo ya lallab'ata yau dai yaji ya gani ya kuma amshi auren sai dai kuma tun shigowar shi falon ya tabbatar da cewar bafa ta cikin gidan domin dai baiji kamshin girki ba dan dai yasan tana dawowa daga makaranta indai yana garin take fad'awa kitchen domin had'a mishi abincin rana, tanan wajen kam yana respecting dinta dan kai tsaye zaice abinda ya rasane a wajen Teemah ita yake samu a wajen ta,
Yaso kwarai ya daure sai dai yaufa abinda yakeji a jikin shi bamai dannuwa bane ganin cewa zai iya cutar da kanshi domin dai har magani ya sha amma ba sauk'i hakan yasa ya yanke shawarar gara kawai ya kirata ta dawo gida in yaso komai ta fanjama fanjam domin dai aiba abun kunya zai aikata ba ta dawo kawai ta bashi hakkin shi, dalilin da yasa yayi ta danna mata kira kenan har zuwa sanda ciwon yaci k'arfin shi ya mulmulo ya dawo kasa yana jiran ta Allah ta kasance,
Sama² ya dunga jin tana kiran sunan shi cikin kuka, sai kokari take ta d'ago shi daga inda yake kwance sai dai kuma inah! Wane ita ta iya d'aukar shi!
Soja nefa tsayayye wanda ko a tsaye yake bazata iya ture shiba balle kuma yana kwance sharbam,
Ba karamin salaamah ya samu a yayin da ya tabbatar cewa ita dince ta shigo dakin ba, domin ko babu komai bazaiyi wasa da wannan damar ba, zaiyi amfani da ita yanda ya dace dan yasan dai inba haka ba tofa koda ace macewa yayi sai dai yazam cewa ya mace a banza indai ta itane yayan shine kadai zasu zama marayu,
tunda ita dai ba fad'in shi ta sani ba duba da cewar koda safen yau saida ta maimaita mishi cewar ya saketa kowa yaje yayi harkar shi.
Sauran karfin daya rage mishi yasa wajen jawota ta fado cikin jikin shi, shi kuma yayi amfani da hannayen shi wajen nad'eta a jikin nashi ta yanda ya tabbatar bazata iya mikewa ba.
kam² ya damketa damka bata wasa ba, yayinda zafin damkar yasa ta fasa ihu ita a zaton ta ko zafin ciwon ne yasa ya damketa, tunda itama in tana ciwon mara duk wanda ta samu damkewa takeyi,
Iya kokarin ta tayi dan ta kucce daga jikin shi sai dai d'an bawan Allah keme me yakiya, sai ma k'ara mamaye ta da yakeyi yana cusa kanshi a cikin k'irjinta.
"Ya'ya ka cikani inje dakina in kawo maka magani kasha, insha Allah kana sha zaka warke garas kamar ba kai ba"
Shiru ba amsa sai ma hannun shi guda daya fara amfani dashi wajen shafo gadon bayan ta zuwa wajen kwankwason ta,
Kamar wacce aka kwashe fuskarta da mari haka ta zabura jin yakai hannun shi kasa yana tattaro rigar jikinta data kasance doguwa yanayo sama dashi,
"Innalillahi yaya dan Allah ka dena nice fa Meenal ba Maman boy ba!, nidai dan Allah ka cikani in kira wani ya kamamin mu kaika asibity dan kana bukatar ganin likita"
Ta fadi hakan a yayin da take ta kiciniyar kwacewa daga jikin shi,
Shiko kamar dutse haka ya koma mata dan yasan dai duk tsiyar ta bata iya kwacewa a hannun shi, dan haka sai ma ci gaba da yayi wajen ganin ya samar ma kanshi nutsuwa,
Hannun shi data rike ya danne wanda hakan ne ya bashi nasarar jawo rigar har zuwa saman cikin ta,
Dambe sosai take kokarin yi dashi dan ganin ta kwaci kanta a hannun shi fad'i take....
"Yaya kayima girman Allah dan darajar iyayen ka kayi hak'uri, Inma dan d'azun ban had'a maka abun kari bane yasa kake fushi dan Allah ka yafemin wallahi bazan kara ba, nidai dan Allah kayi hak'uri kaji wayata ke k'ara kuma wallahi Hajiya Innah ce ke kirana zata aiko a karb'a mata sak'o, nidai dan ka dena wallahi bana so"
Sosai jikinta yaci gaba da rawa zuwa lokacin ko ai inda za'a auna jinin ta ba k'aramin hawa za'aga yayi ba,
To jama'a fisabilillahi Ina dalili aure shekara sama da Biyar miji bai tab'a neman kaba sai yau kawai daga taimako yana neman haik'e mata, so yake yace mata tsayin shekarun nan mantawa yayi da hakkin ta wanda har hakan yasa mutane ke mata kallon tana shaye shayen maganin hana d'aukar ciki sai yau ya tuno da hakkin nata ko ya'ya abun yake,
Da kyar ya iya fusgo kalmar bakin shi ya iya furtawa a fili da muryar shin nan da zafin ciwo yasa ta k'ara komawa masha Allah...
"Ki tsaya fa karkisa inji miki ciwo!"
"Iyyehh kuwa jama'a ku kawo min d'auki waiyo Allah Ya Sarki dan soyayyar ka da manzon Allah ka rufamin asiri wallahi tallahi ban shirya ba"
Ihu sosai take mishi da kururuwar cewa itafa bata shirya ba, shiko mugun ko takan ta baibi ba illah ma maida hankali shi da yayi wajen ci gaba da cakuda mata jiki, sai dai kuma duk yanda yaso samun damar had'e bakin su saboda ihun da take tak'i yarda bori kawai take uwa wata wacce ke shirin tada aljannu tana neman dauki,
Jin saukar bakin shi akan ajiyar da Allah yayi a kirjin ta yasata fasa wani uban ihu tana fad'in kalmar shahada kamar wacce ke gargaren mutuwa,
"La'alaha illallahu muhammadur Rasoulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam,
Shi kenan kwanan ki ya k'are Aminatu tun baki ga auren Besty din kiba, shi kenan Aminatun Malam zata mace tun bata zama cikakkiyar likita ba, Allah Sarki Malam za'a kashe makani tun ban gina maka gidan sama mai hawa biyu ba, waiyo Allah Yayan mu to aima ba haka akeyi ba, babu sallah ba kaza a farma amarya Sam wannan baya cikin shika shikan kwanciyar aure, ni wallahi bazan yarda ba ai nasan ita matar ka ba haka kaje mata babu kayan siyan baki ba, saini da ba'a so ne za'ama fashin budurci da rana tsaka, wallahi nidai tunda uwata ta haifeni banji inda aka tab'a nemar amarya da rana tsaka ba"
(Nidai nace Meenal kila bakin nan bazai mutu ba sai an shiga daga ciki)
Ture kanshi take ta kokarin yi dan sosai fa take jin ciwon yanda shiba jaririba amma ya wani kafa mata bakin shi dake cike reras da jerin hakoran shi a inda tunda tayi wayau take boyesu ga kowa, dan Allah jama'a maiya had'a babba da kayan da jarirai kesha, ga wani uban zafi da take jin suna mata wanda yasa babu shiru ta fara mishi k'ananun kuka a zaton ta wai ko zai tausaya yaji k'anta ya kyaleta,
Sai dai mai makon hakan sai ma mirginata da yayi ya mai data kasan shi yaci gaba daya mutsa mata jiki,
"Dan Allah dan Annabi karkayi a kasan tile's, ko wacce amarya a saman gado ake mata shi da lallashi shine ni za'a bajeni a tiles saboda dama ba sona kakeyi ba wato bari ka kasheni ka huta,"
"Zaki tsaya to in na mai dake saman gadon?"
Ya tambaya ba tareda ya tsagaita da aikin da yakeyi ba,
Kuka ta fashe dashi sosai.
"Wai dan Allah da gaske kakeyi? Nifa Ina ce baka da lafiya ne shi yasa na shigo"
"Maganin nike so ki bani ai!"
Cak ya daga ta zuwa gadon, yana ko ajiyeta babu b'ata lokaci ta daka wani shegen tsalle ta dira ta d'ayan gefen tana sauke rigarta daya tattare,
"Ina kike tunanin zaki gudu kije? Ke aiko wani ne yace miki zan barki ayau keda kanki zaki ce mishi k'arya ne kalli nan ki gani fa"
Ya fad'i hakan yana mata nuni da gaban jallabiyar dake jikin shi daya taso,
Ai da gudu ta maida idon ta ta rufe jikin ta na rawa taci gaba da rokon shi akan ya rufa mata asiri ya kyaleta,
Komawa yayi ya duk'e dan tab'atan nan da yayi mai makon yaji sauki Ina sai ma k'ara kunnuwa yaji yayi,
"Kizo nace"
"Ai wallahi bazan zo ka kasheni da ranar Allah ba"
Ta bashi amsa tun ma bai rufe baki ba, sannan ta d'aura da cewa...
"Kuma wallahi kana k'ara tab'ani zanje in fad'ama Malam"
Duk da yanda yake jin ciwo amma saida ta bashi dariya kuji fa wani shirme wai zata fad'ama Malam.
"Me zaki ce mishi?"
Ya tambaya.
"Umm umm nidai kawai ka barni in tafi Ina ma ruwan