Showing 60001 words to 63000 words out of 174305 words

Chapter 21 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1902

irin kallo yace,
"Oh kema kin zama karamar yarinya kenan da zaki zo ki sani gaba kina min kuka a gaban sirikan ki"

Maida duban shi yayi zuwa kan sauran jama'ar gidan da duk sukayi cirko² yasan tabbas da baya gidan da tuni sunbi bayan Sarki.

"Tsayuwar me kukeyi toh ku koma ciki zanbi bayan su yanzun"

"Ah² Malam karkace zakayi tuki da kanka bari dai a Kira wani cikin yaran nan suzo su tukaka inyaso mu ma biyo bayan ku zuwa anjima, kaji"

Aunty Murja data kara waya tana magana basu san kowa ta Kira bane, bayan ta sauke wayar take cewa.

"Na Kira Yayan su Sa'eed zai zo yanzun bari in dauko mayafi sai mu biyoku a baya dan Allah Baba Malam karka hanamu zuwa komun zauna hankulan mu bazasu kwanta ba"

Tana karasa fadin hakan ta juya sasanta tana goge hawaye, suma sauran matan haka suka juya kowaccen su jikin su a mace.
Ficewa Baba Malam yayi zuwa waje dan ya jira zuwan Sa'eed.

A gefen Sarki ko koda ya fito waje dauke da Aminatu ya iske Kwaro ya kunna motar dan haka bai bata lokaci ba ya shige gidan baya, Meelat da Maryam dake biye dashi a bayane suma suka bude gaban motar dukan su biyun suka shige a yayin da suka kasa dauke idanuwan su akan Meenal kuma har zuwa lokacin basu bar kukan da suke ba,
Wata uwar tsawa ya daka musu mai kad'a hantar ciki wanda yasa suka shige cikin jikin juna suka cikwuikuye kansu,
Tsawar da harta Kwaro dake tuki sai da ya kusan sakin kambun motar.

"In bazaku min shiru ba ku fice in daina jin muryoyin ku kai kuma Malam kar ka maida hankali akan tukin ka ka dage ka watsar damu kaga sai muyi mutuwar kasko tunda haka kake muradi in kuma tukin ne baka iyawa kaima ka fice ni zanja motar bana son shiririta".

Aiko gum su Meelat sukayi ba wacce ta karayin koda nishi mai karfi ne a cikin su.

Sorry for am late😒
#Ameenatu. 🧕🏻
#Team Sarki. 🤴🏼
#Team Mai Jama'a. 🤵🏻‍
#Sheikh Naseer.👨🏻‍💻
#Ummiee~Zaria
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*

*👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_

ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._

*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}

*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._
*Ga masu tambayar littafin daga farko zaku iya tuntuɓata kai tsaye da wannan number ɗin 08061358462,*
Karku manta littafina kyauta ne banyi shi dan in siyar ba dan haka karkuji ɗar kuba duk wanda kuke so.

Free book ne yan bati a dage da karatu Wannan page din zato da sammatsi idan mai karatu yazo karatu ya tsallake duka na saman ya koma can kan na karshen shine cikakken page 20 ayi hakuri.
a daure a dunga comment atoh.

```Page 20

can na kasan karshe zaku karanta ba sauran ba.
................. **** Ina zamu nufa Sarki?"
Kwaro ya tambaya a yayin da suka fice daga cikin layin suka nausa kan babban titi,

"Asibitin Dr Mubarak"
Ya bashi amsa a takaice,
Kuri Sarki ya kafe fuskar Meenal da kallo a son shi na gano ko tana numfashi ko kuma numfashin nata ya dauke! dan shifa tsakanin shi da Allah bazai so daga taimako yar mutane ta mace mishi a cikin mota ba, in ma macewar zatayi gara ta bari ya mikata hannun likitoci tukun, atoh dan bazai yarda tasa shi a bakin duniya ba.

"Wai Ibrahim ba nace ka kara gudun motar nan bane? Numfashin yarinyar nan fa banga yana fita da kyau ba karta mace min a cikin mota,"

Maida duban shi yayi inda su Meelat suke rungume da juna

"Ku fadamin wai ma meke damunta ne haka,
wani irin ciwo ne wannan?
Banji jikinta yayi zafi ba amma gashi sai zufa take hadawa,ko dama haka take nata ciwon? "

To shi yanzun fisabilillahi so yake su fada mishi gaskiya ko ka'ka, kai jama'a ina ai gaskiyar nan kam bata faduwa a wannan lokacin dan ko *tuntuben harshe* by Surayyah.... Sukayi sukace ma Sarki period ke sata haka, lallai za'ayi balbalin bala'i tsakanin su da Meenal inta farka, yo sukam da kunya ta haifa Ina ma zasu iya fada mishi gaskiya.
Dan haka sai suka fara kallon kallo a tsakanin su wannan na dungurin wannan an rasa mai bashi amsa a cikin su,

"Baku nan ku suna ciwone kuma din ko wani kalan iskanci ne nike magana kuka kyaleni? "
Ya tambaya a kausashe,

Umm'ummm umm damaa damaaa muma muna cafeteria ne aka ce, akace mana wai waii Amina bata da lafiya,
Suka hada baki wajen bashi amsa, sai Maryam ce ta kara da cewa,
"Kuma wallahi muma bamu san mike damunta ba lafiya lau tazo makaranta da safe, har zuwa lokacin da akayi break bamuga alamar bata da lafiya ba koh Jamila? "

"Eh Wallahi koni banga alamar ciwo a tareda ita ba, sai dai sai dai dama ummm dama tanayin irin wannan ciwon kuma Baba Malam ne ke mata Addu'a Mommy Hauwa kuma ta bata magani".

Sai kuma suka fashe da kuka cikin kukan nasu sukaci gaba da fadin waiyo su Allah shi kenan Meenal zata mutu ta barsu.

****

Sarki da kanshi ne ya cirota daga cikin motar bayan sun isa cikin asibitin, bai tsaya jiran wani abuba yayi cikin asibitin da ita dauke a hannun shi su Maryam suka rufa mishi baya,

Ma'aikatan asibitin ne sukayi saurin taran shi a kokarin su nason su karbeta a hannun shi sai dai bai basu dama ba yaci gaba da kutsawa suna mishi jagora har zuwa emergency inda ya shimfideta a daya daga cikin gadajen dake dakin sannan ya juya ya fito domin ya basu damar gudanar da aikin su.
Suko su Meelat gaba daya kasa zama sukayi gashi kaf cikin su babu mai waya a tareda ita dan dokar makarantar ne ba'a yarda dalibai suje da waya ba, inko kaje da ita har aka kwace tofa kai kajiyo,

Kwaro daya biyo bayan su ne ganin su a tsats tsaye cikin rashin rashin sukuni yasa shi umartar su akan su samu waje su zauna yana mai Kara kwantar musu da hankali akan zata samu lafiya,

Shiko Sarki fitowar shi daga emergency din yayi dai dai da karar da wayar shi ta dauka alamun Kira,
"Malam"
Ya ambata a bayyane kafin ya amsa kiran,
"Assalamu Alaikum"
a can bangaran Malam yake tambayar shi cewar suna wani asibiti ne dan gasu a hanyar zuwa,

"Malam ai da bakayi wahalar fitowa ba, tunda Ina tare da ita zan kula da komai da za'a bukata dan yanzun haka ma tana ciki ana dubata nasan insha Allah zata samu lafiya bada dadewa ba"

"Angode da kokari Malam Sufyan amma ai baza'ayi haka ba, kaida Kake kan hanyar komawa bakin aikin ka, ya kuma zakaje ka tare a asibity da sunan kula da mara lafiya kamar ba dangi a gari? Iyi ai bazai yuwu kai kuma ka tauye kanka ba koh, yanzun dai kuna wani asibitin ne dan gani nan tafe da Sa'eed "

"Muna Asibitin Dr Mubarak"
Sarki ya amsa ma Malam dashi gamida yanke kiran, yaso Malam ya zauna basai yaba kanshi wahalar zuwa ba domin dai ko zuwan yayi ba wani Abu zaiyi ba, sai dai yasan Malam bazai taba iya zama a gida cikin kwanciyar hankali ba alhalin Aminatu na asibiti kwance, yarinya kamar ita kadaice d'iya a cikin dangi,

Ba'a dauki mintoci ba su Malam suka iso.
"Malam Sufyan ai gara kuzo ku kama hanya kar kuyi dare duk da kace gobe jirgin hantsi zakabi zuwa Lagos nasan bazaka rasa yan kimtse²n da zakayi ayau inka isa Kaduna ba".

To Baba Malam bari likitan ya fito muji ko ta farka in naga jikin da sauki sai mu kama hanya in kuma abun yayi tsanani sai a canza asibiti,"

"To ba laifi hakan ma, sannu da dawainiya kaji Allah dai ya maka albarkha ita kuma Allah ya bata lafiya, wallahi haka take fama da wannan ciwon na mara duk karshen wata magani dai babu kalar wanda bamuyi mata ba, kullum nida sauran mutan gidan tafe muke wajen nema mata maganin ciwon nan amma kaga dai har yanzun shiru, hatta uwarta dake kuri ita likitar mata ta gaza a al'amarin ciwon nan, kuma Innan su ta shaidamin tun fara al'adarta take fuskantar wannan kalubalen na ciwon mara mai tsanani, dama ni shirina nace nida kaina zan daukota zuwa asibiti dan so nike likitocin sumin Karin bayani akan ciwon nata dan gaskiya abun bana wasa bane, ita kuma uwar gaba daya banga alamar ta damu da wahalar da y'ar kesha ba dan har yanzun banji gamsas shiyar bayani daga gareta akan ciwon ba"
Sai da ya dan goge zufan daya tsatstsafo wanda take nuna alamun cewa shima din a dame yake kwarai kafin yaci gaba da cewa,

"Tun tashin yarinyar nan ita bamai yawan laulayi bane shi yasa in ciwon ya tashi duk sai tabi ta firgice, Allah Kasai yasan azabar da take sha yar karamar yarinya da ita"

Fitowar daya daga cikin Nurse din dake kula da Aminatun ne yasa su Maryam mikewa sukayo wajen ta suna mai tambayar ta da cewa...
"Ya jikin ta?
Ta tashi kuwa?
Meya sameta? "

Haka sukaci gaba da jero ma nurse din tambayoyi ba kakkautawa,

"Ah ah sister's ku kwantar da hankalin ku ya'r uwar ku zata samu lafiya nan bada jimawa ba Insha Allah dan yanzun hakama ta farka"

Karasawa wajen Sarki tayi.

"Ga wannan abubuwan da ake bukata ne ku amso zamuyi mata amfani dashi kafin Dr ya fito daga labour room"
Alamu ya mata da hannu cewar ta mikama Kwaro takardar,

Mikewa Sa'eed yayi "bani takardar in anso!
Tana mika mishi takardar ita kuma ta koma ciki,

Jin cewa Meenal ta farka yasa suka danji sa'ida a cikin zukatan su, nan da nan Sa'eed ya dawo, Nurse din dazun ne ta Kara fitowa ta amshi kayan ta koma ciki,

Ba'a dauki lokaci ba su Aunty Murja suka iso asibitin gayya guda kamar wadan su masu kai Amarya,
Da mamaki Malam yake kallon su, inba haukaba ya zasu kwaso iyalan gida gaba daya su taho suzo su tare a asibiti subar gida ba kowa alhalin yaran su na gab da dawowa daga makaranta, yanzun kuma Idan yace zaiyi magana sai sugar laifin shi suce ya fiye fada ko yanzun dai sunci albarkhacin Sarki ne amma Ana basu damar ganin Aminatun zai korasu su koma gida asibiti aiba gidan biki bane, dan haka bai iya ce musu komai ba Allah kauda kanshi ma da yayi ya mike da niyyar barin musu wajen, sai dai kuma had yayi taku daya biyu ya juyo garesu,
"Ina fatan cewa babu wacce tayi gigin kiran Hauwa'u ko auta a cikin ku? "
Dukan su dukar da kansu sukayi aka rasa mai bashi amsa dan ba wacce Zata so ya sauke haushin ganin su diyyy din da yayi a kanta, shifa Malam mai iya mishi sai Allah dai wallahi ko shakka babu da basu biyo bayan su ba ko ace wasu suzo wasu su zauna tabbas saiya samun abun magana cewa dan ba cikin yaransu ne d'aya ke ciwo ba shi yasa suka zauna a gida wato inta mutu ma oho,
Amma gashi yanzun sun kwaso jiki sunzo sai wani daure fuska yakeyi Malam ho.
Uwar gidan shi ne ta wakilci sauran da cewa,
"Bamu kira Auta ba itama kuma Jiddan mun kirane dama muji ko Aminatun nada sauran maganin da take sha a gida dan mu taho dashi sai dai kuma bamu samu wayar nata ba har muka taho, ya jikin nagta? ta farka kuwa? "

Bai tsaya bata amsa ba yasa kai ya fice su kuma sauran matan suka samu wajen zama suna tambayan su Maryam yaya jikin na Aminatu,

Bayan zaman shiru da jiran tsammani da sukayi na wani lokaci Shannan ne wannan Nurse din ta Kara zuwa take fada musu cewar an canza ma Aminatun daki sai dai kuma sun mata allurar bacci bazsu so kuma hayani ya yasa ta farka da wuri ba,

"Zamu iya ganin likitan daya kula da ita? "
Sarki ya tambayi Nurse din,
"Eh to bari in mishi magana, ku biyoni in nuna muku inda aka maida ita"
Tace a yayin da ta juya zuwa wani hanyar daban ba wandavta fito daga ciki ba.

"Kira Baba sai muje yaga likitan koh? "
Sarki yace da Sa'eed,
"To Ya'ya"
Ya amsa a yayin da ya juya zuwa waje su kuma su Meelat tuni sun rufama Nurse baya zuwa dakin da aka kwantar da Meenal.

#Ameenatu. 🧕🏻
#Team Sarki. 🤴🏼
#Team Mai Jama'a. 🤵🏻‍
#Sheikh Naseer.👨🏻‍💻
#Ummiee~Zaria⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*

*👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_

ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._

*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}

*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._
*Ga masu tambayar littafin daga farko zaku iya tuntuɓata kai tsaye da wannan number ɗin 08061358462,*
Karku manta littafina kyauta ne banyi shi dan in siyar ba dan haka karkuji ɗar kuba duk wanda kuke so.

Free book ne yan bati a dage da karatu a daure a dunga comment atoh.

```Page 20

................. **** Ina zamu nufa Sarki?"
Kwaro ya tambaya a yayin da suka fice daga cikin layin suka nausa kan babban titi,

"Asibitin Dr Mubarak"
Ya bashi amsa a takaice,
Kuri Sarki ya kafe fuskar Meenal da kallo a son shi na gano ko tana numfashi ko kuma numfashin nata ya dauke! dan shifa tsakanin shi da Allah bazai so daga taimako yar mutane ta mace mishi a cikin mota ba, in ma macewar zatayi gara ta bari ya mikata hannun likitoci tukun, atoh dan bazai yarda tasa shi a bakin duniya ba.

"Wai Ibrahim ba nace ka kara gudun motar nan bane? Numfashin yarinyar nan fa banga yana fita da kyau ba karta mace min a cikin mota,"

Maida duban shi yayi inda su Meelat suke rungume da juna

"Ku fadamin wai ma meke damunta ne haka,
wani irin ciwo ne wannan?
Banji jikinta yayi zafi ba amma gashi sai zufa take hadawa,ko dama haka take nata ciwon? "

To shi yanzun fisabilillahi so yake su fada mishi gaskiya ko ka'ka, kai jama'a ina ai gaskiyar nan kam bata faduwa a wannan lokacin dan ko *tuntuben harshe* by Surayyah.... Sukayi sukace ma Sarki period ke sata haka, lallai za'ayi balbalin bala'i tsakanin su da Meenal inta farka, yo sukam da kunya ta haifa Ina ma zasu iya fada mishi gaskiya.
Dan haka sai suka fara kallon kallo a tsakanin su wannan na dungurin wannan an rasa mai bashi amsa a cikin su,

"Baku nan ku suna ciwone kuma din ko wani kalan iskanci ne nike magana kuka kyaleni? "
Ya tambaya a kausashe,

Umm'ummm umm damaa damaaa muma muna cafeteria ne aka ce, akace mana wai waii Amina bata da lafiya,
Suka hada baki wajen bashi amsa, sai Maryam ce ta kara da cewa,
"Kuma wallahi muma bamu san mike damunta ba lafiya lau tazo makaranta da safe, har zuwa lokacin da akayi break bamuga alamar bata da lafiya ba koh Jamila? "

"Eh Wallahi koni banga alamar ciwo a tareda ita ba, sai dai sai dai dama ummm dama tanayin irin wannan ciwon kuma Baba Malam ne ke mata Addu'a Mommy Hauwa kuma ta bata magani".

Sai kuma suka fashe da kuka cikin kukan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login