Showing 129001 words to 132000 words out of 174305 words

Chapter 44 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1889

nema yasa yaci gaba da zuba mata ido dan yaga iya inda ruwan nata zai tsaya da gudu,
Kallon ta yake harzuwa sanda ta warware lullubin data rufe asirin jikin ta dashi wanda a wannan lokacin shima ji yayi kamar asirin dake cikin zuciyar shi take warware wa, yayi kokarin ganin ya raba kanshi da kallon abunda yasa ya haramta gareshi amma Ina bai samu wannan kwarin gwuiwar ba dan haka yaci gaba da k'are mata kallo har zuwa sanda ta duk'a da niyyar d'auko hulanta dake kasa, kasancewar a wannan lokacin ta fuskanci ainihin inda yike ga kuma dukawar da tayi hakan yaba wuyan rigar jikin ta damar zazzagowa hakan yasa daga inda yake zaune tsaf yake Ina hango lafiyayyun na shanun ta da suke nan kamar an d'auko an dasa mata su, I zuwa wannan lokacin kam ko kifta idanuwan shi daga kanta baya iyawa, hakan nema ya zama sanadin da tana d'agowa suka h'ada ido da ita,

Duk wannan iface iface da sambatun da takeyi tsaf yake jinta, ga abun dariya amma halin da yake ciki yasa bazai iyayi ba dan wani irin kullewa cikin shi yayi irin kullewar da bazai iya yaushe yayi irin shi ba yana daga zaunen nan tsabar azaba bai san sanda ya nemi kifewa yana dafe cikin nashi ba, ga azabar da yakeji da kuma ihun yarinyar nan data bud'e murya tana mishi hauka, ganin Infa baya taka mata burki bane tana iya fashe mishi dodon kunne hakan yasa shi cike da dauriyar daya aro ma kanshi ya d'ago kanshi yana korar shaidan a cikin zuciyar shi.
Wata irin tsawa ya daka mata wacce tasa ta komawa ta kankame jikin ta waje guda,

"Ki rufemin baki a wajen nan, ki kuma zo ki fita min a d'aki kafin in k'araso wajen nan wallahi zane ki zanyi ciki da wajen ki,
Kai wai ubanwa ma ya baki izinin shigowa d'akin nan ne iye?"

Ya tambaya cike da hargagi,

"Ba dake nike magana ba, uban waye yace ki shigomin d'akin iye, wato ashe rashin hankalin ki da nike gani ya wuce tunani na, zaki kama hanya ki shigo d'akin namiji kamar wani d'akin mijin ki dan iskanci har kin samu zarrar cike lullubi ba tareda tunanin cewa wani na iya shigowa ya sameki babu lullubin ba"

Ita dai Allah ya sani ta samu sa'idah ne kawai a sanda ta tabbatar da cewar ashe dai mai d'akin ne ba aljanin da tayi tsammani ba,

Jin yana ta b'abatu bata da niyyar tashi yasa shi Kara daka mata tsawa.

"Wallahi Β³ idan na mike sai kinji ba dadi tashi ki fitar min a d'aki mara wayau kawai, kuma Allah yasa in kara ganin kin fito gidan ki bada dogon hijabi da kyakyawan shiga ba, tunda shi mijin naki ya zama sakaran namiji shi yasa ya sanya miki ido kina shigar da kikaga dama kina fita, shima sakarai dabai kishin iyalin shi, to ni nan zan gyara mishi zama wallahi"

Sif Sif Sif ta mike jiki ba kwari, dan tasan yanda ya rufe ido yana bala'in nan ba sauraren hakurin da zata bashi zaiyi ba,
Harta kai bakin kofa tana shirin ficewa ya kara daka mata tsawa da cewa.
"Shi wancan kullin kayan naki wani shegen ne kika barma zaki zo ki d'auka ki fitar min dashi daga d'aki ko sai nazo na had'a kanki da bango? "

Baya baya ta dawo jiki duk ba lakka, tasan cewa AK jarababbene amma batayi zaton ya iya masifa haka ba,
Haka dai ta dauki kayan harta kai tsakiyar falon taji ya kira sunan ta,
Wanda hakan yasa dole ta tsaya cak ba tareda ta iya amsawa ba,

"Wallahi in na k'ara ganin kafar ki a gidan nan nan kusa sai na zane ki, kuma zansa a samin ido akan ki ki tabbatar bakya zuwa ko Ina daga Makaranta sai gida, inba haka ba ni zan biyoki har gidan naki in gyara miki zama tunda shi mijin naki naga alamar dan kwali ya kamata ya koma d'aurawa ba hula ba"

Sif Sif ta fice daga falon,

Duk magan ganun daya gaya mata bataji zafin suba sai da ta fito, aiko a bakin kofar ta tsaya ta bare baki tana kuka, yana daga ciki kuma yana jinta dan shima fa kanshi da ace yana da hali ihun zaiyi ta kwararawa wallahi,

Muguwar yarinya kawai, inda yasan tana d'akin ai koda wasa bazai shigo ba, ita bata san yana kauce mata bane saboda gudun take iyakoki...........


*Babu editing atoh* inda kukaga kuskure ku wuce shi kawai kuje gaba


*Ummiee Zaria*✍🏼✍🏼✍🏼
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: βšœοΈπŸ”±πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *DANGINA!*πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ”±βšœοΈ
*Free book ga masu buk'ata daga farko zaku iya magana dani kai tsaye* 08061358462

*Rubutawa*
*Ummiee Zaria*✍🏼

'''''Page 37.


Alhamdulillah rayuwa fa yana ta tafiya, karatun su Meenal yayi nisa sosai domin yanzun haka dai shekara 1 kachal yayi saura su kammala wanda hakan ne zai basu daman amsa sunan likitoci kai tsaye ba tareda shamaki ba,
a kuma wannan lokacin ne aka tsaida ranar auren Meelat da Musty duk da dai ita Meelat taso yayi hak'uri har sanda zata kammala karatun ta amma ya nuna mata gara ayi a wuce wajen kawai,
Maryam dai kam duk yanda Sadeeq ya so akan ta yarda shima ayi nasu bikin kafin ta kammala, k'iyawa tayi a cewarta bazata iya had'a hidimar karatun ta dana aure ba, dan haka badan yaso ba haka nan dai ya hak'ura dan yasha fama sosai kafin ta amshi tayin soyayyar shi,
A gefen uban gayyar shiko dai D'an mai karfi har yanzun dai babu wata tsayayya, domin ta gefen shi tsakanin shi da mata babu wani abunda ya canza, dan harta da su Meelat da suke matsayin yan matan manyan abokan shi ba wani sake musu fuska yake yiba,
Kwata kwatama yanzun halayyar shi k'ara juyewa yayi ya zamana ko yana gari ma ba kasafai zaka ganshi a majalisar shi ba, matan da ke zuwa wajen kuma domin shi tuni ya warware musu zaren rashin mutuncin shi tass ya musu hauka akan duk ma yarinyar data k'ara kallon su da suffa ta burgewa harta rayama zuciyarta cewa tana son shi to wallahi ta kuka da kanta,
Hafsa ko bata shafama kanta lafiya ba har sai sai wata rana data cika mishi ciki, a lokacin yayi tafiya kusan na wata uku baya gari sabon shine muddin yayi tafiya zuwa wata k'asar ko ka kirashi a waya ba lallai ya d'auka ba zaifi sauki ma in ace sako ka ajiye mishi ba kirar waya ba, to a wannan tafiyar nashi haka yarinyar nan ta taso mishi rayuwa a gaba domin a kallah kullum sai ta mishi kira sama da hamsin amma tsabar wulakanci mutumin nan ko sau d'aya bai amsa kiran ba, kuma bai kirata yaji dalilin kiran ba.
Ganin bazai dauki kiran bane yasa taje gidan Hajiya ta tasa ta a gaba da kuka aka cewa ta rufa mata asiri tasa baki AK ya fito suyi aure domin a lokacin itama a gefen ta sosai abubuwa suka kwab'e mata,
Domin dai d'aya daga cikin tsoffin samarin da suka dad'e suna mata hidimane, wanda shi dai yaji ya gani yana sonta kuma auren ta yake son yi, dan dai itama d'in bata rasa komai ba tana da kyanta ga kuma diri irin na manyan mata data mallaka, toshi dai ganin shekara da shekaru yana mata hidima amma kullum yayi mata maganar aure sai ta zame bayan tun tana karatu yake naci a kanta harta gama tuni tana aikin ta kuma yayi bincike ya gano cewar shegen yaron da tanace ma so akan shi kwata kwata babu mata a gaban shi balle kuma ita da kusan tare suka taso,
A yanda yake son ta inda ace shi wanda take so d'in yana sonta tofa babu shakka zai hak'urane ya barta ta aure shi, amma binciken da yayi akan yaron ya tabbatar yaron bazai aure taba, tunda ko shi ba auren ta zaiyi ba ai gara shi yayi duk yanda zaiyi ya aureta yakai d'aki ya adana dan sonta yake da gasken gaske.
Bai tsaya jiran jin ta bakinta ba koh ya tura iyayen shi wajen nata iyayen kafin ta an kara har sun kalmashe bakin zaren,
Tayi hauka sosai cewar tana da wanda take so, jin wannan kalmar a bakin ta ba bak'on abu bane domin dai kaf ahalin ta sun san yanda take hauka akan AK dan inhar kana son kayi shiri da Hafsat tofa sai ka nuna kana son AK anan ne zakaci moriyarta,
Dama suka bata akan cewar tunda bata son Anas d'in da ya fito neman auren ta tofa sun bata wata uku ta fad'a ma AK d'in ya fito, in kuma hakan bai faruba tofa ta sani su kuma nan da wata Biyar suka yanke ranar bikin ta,
Su kuma sunyi hakan ne dan su bata dama kartaga kamar sunyi son kai sun aurar da ita ga wanda bashi take so ba, domin dai sun san tunda wad'ancan shekarun suka shud'e AK bai so tan dahar zai nemi auren ta ba, tofa wata uku bazai canza komai ba,
Dalilin hakan duk tabi ta tashi hankalin ta ta tayar ma wadanda ke tareda ita da nasu hankalin,
Domin dai tayi iya bakin kokarinta akan yanda zatayi magana dashi ta fad'a mishi halin da take ciki amma hakan ya gagara kira kan kira har bata san sau adadin kiran data mishi ba amma yaki amsa wayar ta,
Tabi dukkanin abokan shi dan su h'adasu amma shi kuma mugun dukan su ya musu warning akan koda wasa karsu yarda su kira shi a sanda suke tare da ita,
Tofa ganin bata dace a ta fannin su bane hakan yasa ta yanke hukuncin tunkarar Hajiya tasan AK yana ganin girman ta sosai kila in hajiya tasa baki zai yarda ya aureta,
Ita ta yarda zata zauna dashi duk da baya son ta tasan soyayyar da take mishi zai wadace su.
Taje gaban Hajiya tayi kuka tayi roko wanda har saida Hajiya ta tausaya mata, ta kuma bata shawara akan taje tayi ta addu'a in auren ta da AK alkhairi ne allah ya tabbatar,
Taji sanyi sosai a yanda hajiya ta zaunar da ita ta mata nasiha ta kuma ce mata zatayi magana da AK din,
Bata bar gidan ba sai da taba masu gadin gidan sallahun cewa in ya dawo su kirata, ta basu number d'inta sannan ta musu alkhairi kamar yanda ta saba duk zuwan da zatayi gida.
Sai dai kuma dawowan na AK bai zamo mata alkhairi ba domin a sanda labarin dawowar nashi ya riske ta batayi k'asa a gwuiwa ba ta d'auko mota ta taho,
Koda ta iso ta iske shi a cikin jama'ar shi na majalisa suna ta hirar su ta yau da kullum,
Zumud'i da murnar dawowar shi yasa kashi hamsin cikin d'ari na tashin hankalin da take ciki ya kwaranye, domin AK fa namijin gaskene burin ko wacce mace,

Tunda ta shigo unguwar ya na hango motar ta ya b'ata fuska, kafin ta k'araso wajen kuwa bayan tayi parking a gefe ya tashi tsam a majalisar ya wuce cikin fadar shi, taji dad'in hakan sosai domin koba komai zata so dama su tattauna abunda ya kawota wajen shin a sirrance, bata bi ta kan yan wajen ba ta take mishi baya.
"Kiran me kikayi ta min ne da kullum sai kin kirani sama da sau ashirin bayan kin san na tsani yawan kira? "

Ya tambaya ba tareda ya nemi guri ya zauna ba,

"Ka zauna please Abdul!"
Ta fad'a cike da marairaice wa a tsammanin ta ko hakan zaisa ya taimaka ya saurare ta.

Kujerar shi yaje ya zauna kamar yanda ta buk'ata,
"Ina jinki! Meke faruwa? "

Bata iya zama akan kujera kamar yanda ya zauna ba sai ma k'arasawa kusa dashi da tayi ta zauna a kasa tana fuskantar shi wato dai zama irin na d'alibi a gaban Malami,
Kaf halin da take ciki na auren ta da ake shiryawa da damar da iyayen ta suka bata akan shi ta zayyano mishi,
Daga karshe ta k'are da rokon cewa ya rufa mata asiri ya aureta ita wallahi ko baya sonta yaji ta gani zata iya zama dashi a hakan yardar shi kawai take nema,
"AK ka dubi girman Allah da kaunar da nike maka ka taimaka ka aure ni, wallahi Ina son ka son da na tabbatar ma kaina cewar idan na rasaka tabbas zan iya rasa lafiya ta"
Duk kalaman bakin ta saida tayi kokarin amfani dasu dan ganin ta shawo kan AK amma a banza, daga karshe dai tun sunayin zancen a sirri sai da abu ya fito fili domin kuka sosai tasa mishi tana rokon shi Allah annabi ya ji tausayin ta ya aureta amma gayen nan saboda bak'ar zuciya ko a jikin shi, yadai fad'a mata cewar aishi dama tuntuni yace mata taba samarin ta dama tayi auren ta itace tak'i domin shi dai dama bai tab'a kallon ta ta fuskar soba balle akai batun aure,
A takaice dai abubuwa gaba d'aya basuyi dad'i ba dan fitowa tayi ta dunga rokon jama'ar dake majalisan akan susa baki ya yarda ya aureta, shi kuma hakan ne ya tunzura shi harda cire belt yana neman zane mata jiki, dakyar da ban baki aka cusata a mota wani daga cikin su yaja motar suka bar unguwar da ita, tun daga ranar kuma yasa kafar cin uban duk yan matan dake zuwa majalisar indai yana nan, hakan ne kuma yasa ya kara maida kanshi busy sosai domin duk ragamar kasuwancin su a hannun shi yake hakan kuma bai hana shi karatun da yakeyi wanda kullum Hajiya take mita akai ba, a cewarta kwalayen da yake tarawa indai ba tikitin ketare sirad'i bane tofa ya rufama kanshi asiri ya bar karatun nan haka dan in karatu fa yayi yawa yana tab'a kwalwar mutu, shidai ko tana surutun ta baya kulata dan yanzun ya maida azumi kamar sallar farillah, hajiya tasha tsare shi da tambayar cewa ko kisan kai yayi ne bata da labari akan yawan azumin da yakeyi, wanda shi kuma yana azumin ne saboda ya rage ma kanshi bala'in da yake jin yana kara kusanto shi a kullum, daga karshe dai har sai da aka kai matakin da ko Zaria bai son zuwa dan daya rufe idanuwa wasu hotuna ke haska kansu a cikin idon nashi, memory d'in da kullum yake fatan Allah ya goge mishi su a cikin zuciyar shi dan zaman su a rayuwar shi gani yake bala'ine kawai dan ko kusa bazai kusan ta hakan da alkhairi ba.

****
Kasancewar aski in yazo gaban goshi dama akace yafi zafi hakan yasa kwataΒ² yanzun Meenal bata da lokacin kanta balle na zaman gida dan hatta da baccin ta a yanzun ya zama ragagge ko islamiya ma tuni ta sallama shi duk da yanda take son karatun nata kuwa, sai dai takanyi kokari once in a while taje wajen Malam suna hira suna d'an duba wasu littafan dan wani zubin hatta da weakened bata samun lokacin kanta sai na karatun data sa gaba kawai domin kowa dai yasan yanayin karatun likita ba karatu ne da zakace zakayi mishi sakwaΒ² ba,


Tuni kuma batun rashin haihuwarta yayi tambari a dangi tun wasu nayi a bayan fage har aka kai matakin da akeyin shi kai tsaye sai dai a kullum cewa suke maganin hana haihuwa takesha tunda gashi yanzun Billy nada yara uku duka maza Raheenat ma ukun gareta Sa'adatu ce dai mai biyu itama dan tayi b'ari ne,dan harta da wad'anda sukayi aure a bayan su tuni sun haife.

Malam yasan cewa Meenal bazata wani sha wani abu dan karta haihu ba domin kowa yasan yanda take da son yara balle kuma yanzun da su Raheenat suka hayayyafa dan haka shi yafi tunanin ko dai lalurar da tayi ta fama dashi a lokacin da take gidane na ciwon mara ya janyo matsalar rashin haihuwar dan haka shi da kanshi yake had'a mata magunguna yana kai mata, sai dai ko kusa bata tab'a amfani dasu ba, hatta Mommy Hauwa tasha rubuta mata magunguna da sunan ta amsa ta gwada sai dai ita ta kasa fayyace ma Mommy gaskiyar abunda ke faruwa tun sanda Hajiya ta kwabeta akan cewar karta fad'ama kowa.

Ita dai Allah ya sani duk surutan da mutane keyi bai tab'a damunta ba, domin ta riga ta tabbatar ma kanta da cewa son ta ne kawai Sarki bayayi, kamar yanda itama har yanzun bata tab'ajin wani abu ya tab'a zuciyarta akan shiba, ita da take ta karatun ta ina ita ina d'aurama kanta damuwa, can da yawar shi,
Ai koda bai fad'a mata baki da baki ba ta sani baya sonta zama dai yake da ita na dole kawai dan bashi da yanda zaiyi shi yasa tsayin shekarun nan bai tab'a d'aga kai ya kalleta a matsayin mace ba, duk da sau tari takan so ta kafa ayan tambaya akan wani kalma da Maman Boy ta tab'a fad'a mata wani zuwa Zaria da tayi bikin d'aya daga cikin kannin Sarki inda ta shigo har gidan ta jefeta da kalmar "yar gadin gida a haka zakiyi ta zama har ki gaji ki fad'ama iyayen ki su rabaki da mijina, domin dai nasan yanzun in yarinta ne yasa kike zaune da mijin da har yau bai iya had'a shimfid'a dake ba, nasan akwai lokacin dake da kanki zaki buk'aci kasancewa da d'a namiji in kuma baki samu a gida ba kina iya fita waje ki nema, ni kuma bazan zuba ido a kawo min shege cikin zuria taba"

Wannan kalaman na Teemah sun dad'e suna buga karar rawa a cikin kan Meenal,
To kenan hakan yana nufin matar shi tasan cewa Sarki bai tab'a neman taba?
Tsabar yarinta yasa Meenal ta watsar da zancen a gefe taci gaba da harkokin ta kosu Meelat bata ba labari ba dan tasan idan ta fad'a musu suna iya cewa ita taje gareshi abunda ita kuma bazata tab'ayi ba kenan.
Teemah fa da gaske ta shirya tsaf ma wasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login