Showing 150001 words to 153000 words out of 174305 words
Chapter 51 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
Hajiya Turai,
Yar karamar dariya Hajiya tayi sannan ta d'aura da cewa,
"Kamar dai yanda na fad'a muku ne d'azun ni nafi zargin akwai shiga tsakani a zaman auren yaran nan to hakan ne, domin dai a bayanan ta na gane cewar kwata kwata shi mijin nata baya son kusanci a tsakanin su, yanzun Kuma da aka samu canji ina da tabbacin cewa tabbas akwai inda aka samu tangarda kodai asirin ya karye ko kuma an canza sabon salo,"
"Ba shakka hakan yana iya zama gaskiya, to yanzun wani mataki za'a d'auka?"
Turai ke tambayan Jummai.
"Da farko dai zanso a fara kokarin karya komai dake tareda mijin, sannan sai a d'aura shi akan magunguna na kariya, koda yake magani baya aiki sai mutum ya had'a da addu'a gashi shi kuma bamu san ya yake ba wajen kula da ibada, babbar damuwar ma yanzun yanda Hajiya ta d'auko Aminatu daga gidan ta, kunga koba komai da tana can komai zaifi zuwa mana a sauk'ake,"
"Ko yanzun bazai gagara ba dan jikata dai na d'auko kayata kuma bata komawa gidan nan, magani kuma tunda dama nayi niyya da zuciya d'aya nida kaina zai kai in damk'a a hannun uwar shi ita sai tasan ta yanda zatabi dashi har yayi amfani dashi, saki ne dai sai ya saki takwara ta karma kowa ya bani hak'uri"
"Aunty Turai bakice komai ba"
"To me zance Jummai bayan aikin gama ya riga ya gama! Tunda tace sai yayi sakin ai sai muyi fatan ita yarinyar Allah ya mata canji na alkhairi shi kuma allah yasa iya wahalar kenan, ita kuma matar indai ya tabbata ita keda hannu allah ya shirya ta"
Sun tattauna sosai kafin taron ya watse,
***
Salman bai d'auko sarki sun dawo gida ba sai bayan ishsha'i zuwa lokacin kuma jikin na Sarki alhamdulillah sosai yaji sauki kamar ma bashine aka kwasa ranga ranga zuwa asibiti d'azun ba,
D'akin shi dake sashen Teemah ya shiga sai da yayi wanka sannan ya samu damar jero sallolin da ake binshi,
Ba kowa yasan yana gidan ba sai iya yan d'akin su, sai da uwar gida ta tabbatar yaci abincin da tasa aka kai mishi ya kuma huta sannan taje d'akin ta same shi.
Bayan sun gaisa ta mishi ya jiki ya kuma amsa mata da jiki yayi sauki ne ta miko mishi takarda da biron dake rike a hannun ta wanda dasu dama ta shigo d'akin,
D'aure fuska tayi sosai dad'e duniya bata tab'a sanin yanda akeyin dariya ba.
"Sufyaan Β³"
Sai da ta kira sunan shi sau uku yana amsawa da "na'am"
Sannan ta daura da cewa,
"A duniyar nan kana da wata uwa data fini matsayi a wajen ka?"
Duk da yanda zuciyar shi ke dakan lugude bai gaza amsa mata da cewa..
"Babu Hajiya"
"Da kyau, kenan ina da ikon da zansa ka abu kayimin kenan?"
"Kina da ikon kisani komai kike so inyi miki shi kai tsaye Hajiya indai hakan bai sab'awa shara'a ba"
Kara bata tayi sosai alamun ba wasa, sannan ta matsar mishi da takardar da biron zuwa gaban shi,
"Gashi nan sau nike in k'ara baka umarni kamar yanda na baka a lokacin da naso auren ka da yar uwar ka, yau ma ni din dai mahaifiyar ka ina mai baka umarni daka rubuta ma Aminatu takardar saki, domin yanke alaqar auren dani nayi silar had'ashi a tsakanin ku daga k'arshe kai kuma ka nuna min ban isa ba dalilin hakan ka ajiye yar mutane a gidan ka tsayin shekaru ba tareda ka tuna hakkin auren ta dake kanka ba, dan haka yauni zan sauke maka nauyin daka kasa d'auka, rubuta mata sakinta yanzun ka bani, bakuma nason saki d'aya ko biyu saki uku reras nike so ka zana a takardar gaban ka ka miko min nan, inyaso gobe sai ka had'a kayan ka kabi bayan matar so, na kuma gode maka allah ya saka maka da alkhairi ubana, ni dai bazan tab'ayi maka baki ba sai dai ina son in tuna maka cewa kana da yara mata gasunan saiti bida bi har su uku, ina fatan kar zunuban ku kaida uwar su ya shafi rayuwar su"
Shiru gaba d'aya Sarki ya d'auke wuta dan bai tab'a hasaso ko tsammanin zuwan wannan ranar ba.
"Ya ina magana dakai kamin shiru?"
"Dan Allah Hajiya kiyi hak'uri ki gafarceni, insha Allah na miki alkawarin gyara tsakanina da ita, karkice in saketa ban san da wani idon zan kalli Baba Malam ba........
Kuci shi da hak'uri in anci karo da mistake a tsallake dan banyi editing ba,
*UMMIEE ZARIA*βπΌ
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: π±βοΈπ¨βπ©βπ§βπ¦ *DANGINA!*π¨βπ©βπ§βπ¦βοΈπ±
~{{MY FAMILY}}~
*FREE BOOK*
*RUBUTAWA*
*UMMIEE ZARIA*βπΌ
```` *Page 44*.....
"Dan Allah Hajiya hakuri ki gafarceni,nasan ni mai laifine a gareku,na kuma cancanci amsar hukunci daga gareku na abinda na aikata,amma insha Allah na muku alkawarin gyara tsakanina da ita,zanci gaba da zaman aure da ita a matsayin cikakkun miji da mata, ina rok'on alfarman ku karkuce zaku shige gaba wajen raba auren nan, in hakan ya faru ban san da wani idon zan kalli Baba Malam ba."
Katse shi uwar gida tayi a fusace jin wani sabon salon rainin wayau da yake shirin bijiro mata dashi, inba rainin wayau ba da can daya ajiye d'iyar mutane a gidan nashi ya kuma wofantar da ita da wani idon yake kallon iyayen ta?
"Oh sai yanzun ne ka tuna da wani idon zaka kalli shi wanda ya baka ita a matsayin matar?,
Ka daiji kunya wallahi Sufyaan ka fad'i kasa ba nauyi, a zatona koda ace ni banci darajar haihuwar kaba shi Malam zai iya cin darajar da Allah ya bashi na zamowa tamkar uba a gareka duk da cewa bashi ne ya haifeka ba, yarinyar nan kowa ya shaida kaunarta da Malam keyi amma a cikin jerin maneman da suka fito neman auren ta duk ya shallake sauran ya baka ita,
Kasan tsayin shekaru nawa mukayi nida mahaifin ka mukayi muna bibiyar shi akan ya baka auren ta kafin ya amince?
Nayi zaton cewa ba Aminatu da take matsayin yar uwa kuma kanwarka ba koda ace acan gefe na koma na d'auko maka wata nakasasshiya kai mai tara hannuwan ka bibbiyu ne ka amsa ka kuma riketa da amana,
Kullum akayi haihuwa a cikin Dangi sai anyi batun Aminatu wasu na ganin cewar Allah ne bai kawo nata haihuwar ba yayinda wasu suka ta'allak'a rashin haihuwar nata da tsarin rashin haihuwa takeyi,
Surutai babu irin wanda ba'ayi ba yakai tun anajin kunyan ayi shi a gaban makusan ta sai gashi ya koma harta da uwarta mahaifiya bata tsira ba,
Kasan meye abun takaicin?
Ni din nan da kaina nasha zuwa inje in amso taimakon neman haihuwar in kai mata har gida, wanda ni a nawa zaton ko ciwon da kowa yasanta dashi na mara shine dalilin jinkirin haihuwar nata,
Idan na tuna hakan a yanzun har kunyar kaina nikejin yana kamani, idan ba ita d'inba wace yarinyar ce zata yarda a zauna a gaban idon ta a yad'a mata maganganu irin wanda yan uwanka ke mata akan cewar tak'i haihuwa,
Amma yarinyar nan da yike takance matar rufin asiri ko sau daya bata tab'a tunanin cewar zata tona abinda ke binne a tsakanin ku na tsayin shekaru ba ta gwammaci tayi ta had'iye komai ita d'aya, dan haka wallahi bazan k'ara yarda in jagoranci cin zalin d'in daka mata a baya ba domin ko inda ace d'aya daga cikin k'annen Kane hakan ya sama kaima nasan bazaka bari ba,
Ba kuma nazo jin ra'ayin bakin ka bane ko kuma ban hakurin ka nike buk'ata ba! Ah ah takarda dai zaka rubuta min yanzun basai an kwana gari ya waye ba, in yaso daga goben kana iya bude kofa ma masu zuwa maka jaje domin kaine ka tafka asara ita kam murna ya dace aje mata dan ina mata fatan samun wanda ya fika kodan albarkacin biyayyar da ta d'aure tayi ma iyayen ta na zama a gidan ka tsayin shekaru ba tareda ta nuna gazawa ko kuma ta ce zata bud'e sirrin ta ma wani, kai koh ni bazan maka baki ba sai dai ka sani yan magana kance ruwa cikin cokali ya isa mai Hankali wanka"
Duk yanda Sarki yaso ya k'are kanshi da son ta fahimce shi Sam uwar gida ta rufe ido tama hana shi magana, to me zaice mata bayan ya gama nunawa duniya cewar ita din bata isa ba, domin ai d'an daka isa dashi bazai maka haka ba,
Saki d'aya ya zana a takardar sab'anin ukun data buk'ata, copy biyu tasa ya rubuta ta rik'e daya a hannun ta d'ayan kuma tace ya rik'e a hannun shi gobe in gari ya waye yayi sammakon zuwa Tudun wada yakai ma Meenal d'in domin dai tuni tayi gaba Allah kuma yasa hakan shine mafi alkhairi a garesu, bata bar d'akin ba sai da ta k'ara jaddada mishi cewar karya sake wani yaji zancen sakin nan har sai bayan ya isar ma Meenal da takardar ta, kuma ko bayan hakan bata yarda in magana ya tashi iyaye sunce ya maida ta ya amsa cewar ya mayar da ita d'in ba gara ma ya h'ada ina shi inashi yabar garin a goben,
Wannan dare a wajen Sarki da uwar gida kai tsaye zamu iya kiran shi da bakin dare,
Domin dai kaf a tarihin rayuwar ahalin su ba'a tab'a samun kaddarar data gifta na sakin aure ba, tun daga kan mazan su har matan su, domin kowa ya musu shaidar cewa in sun auro ko sun aurar tofa sai dai mutuwa ta raba,
Sai gashi yau Allah ya kawo mutuwar auren daya kasance na *Dangi* daya ahali d'aya, auren farko da aka fara h'adawa a cikin dangi shine bai kai ko ina ba har ya mutu, innalillahi wa innah ilaihir raju'un, sosai uwar gida fa take cikin bakin ciki da bacin rai, domin laifin gaba d'aya ta d'auka ta d'aura a kanta a ganin ta itace ta jawo komai, da ace tun farko bata dage wajen nemawa danta auren Meenal ba da hakan bata faruba, tasan dad'e duniya yanzun bata da mafita domin yanzun kam mak'iyan ta sun samu sahihiyar damar da zasuci tuwo a kanta,
Ganin da tayi cewa tunani da rashin nutsuwar zuciya bazasu barta ta samu bacci cikin salama ba hakan yasa ta koma cikin makewayin ta tayo alwallah bayan ta fito ta haye kan sallaya ta fara gabatar da nafiloli, haka ta dunga ibada inta gaji ta zauna tayi karatun qur'ani shima inta tab'a kad'an sai ta ajiye taci gaba da Sallah tana kaima Allah kukan ta ba akan kowa kuma ba sai akan Sarki,roko take tana qarawa akan Allah ya tsare mata shi akan sharrin dukan wani abun k'i, Allah ya kawo daidaito a cikin al'amuran shi,
Lallai uwa uwace inba uwa ba wacece d'anta zai b'ata mata amma ta koma gaban ubangiji tana nema mishi dacewa,
Lallai yan magana sunyi gaskiya da sukace hannun ka baya tab'a rubewa ka yanke shi ka yar ( nidai nace k'arya ne wallah aka yanke k'afa ma balle kuma hannuπ).
To shima gafen Sarki hakan ne ta kasance domin gaba d'aya zuciyar shi a k'untace take har ma Allah Allah yakeyi gari ya waye ya tattara nashi ya nashi ya tsallake yabar garin, dan Wallahi sai yanzun yake jin nauyi da kunyar abinda ya aikata, ace da girman shi da komai har yarinyar da bata wuce yar cikin ba ta fishi hankali da hangen nesa,
Yanzun shi da wani kalmar zaiyi amfani ma wajen kare kanshi bayan abinda ya aikata, ace yarinya k'arama ta iya amsar auren ta kuma rik'e hannu bibbiyu duk tsayin zaman shi da ita idan yace ga wani abunda ta aikata mishi na rashin tarbiya yayi k'arya yasan sau da yawa yakan kirkiro wani abun dan ya b'ata mata amma ko ranta ya bacin haka zata danne bata tab'a kai karanshi wajen kowa cewa ya aikata mata ba dai dai ba, haka dai yayi ta sake sake bashi ya samu damar rintsawa ba har sai zuwa gaban nin asuba.
***
Washe gari daga masallaci Sarki ya wuce gidan shi,
Yana zuwa kuwa kayan amfanin shi na yau da kullum ya har had'a yanayi yana kai su cikin motar shi domin yasan in yabar garin tofa bai san lokacin dazai waiwayo ba,
Bayan ya gama sai da yayi wanka ya shirya tsaf sannan ya koma gidan su, shashen Malam Sulaiman mahaifin shi ya fara isa, ya iske shi yana batun karyawa a lokacin dan haka koda ya taya mishi bai musa ba suka zauna tare sukayi karin gaba daya, bayan kammala karin nasu ne kuma ya gabatar ma mahaifin nashi da zancen tafiyar gaggawar da ya taso mishi a daren jiya zuwa Calaba Cross River,
Malam Sulaiman man bai kawo komai ba domin bayau ne karon farko da tafiyar gaggawa take kama Sufyaan d'in ba, sai dai korafi da yayi akan cewa shida aka sallama daga asibiti yammacin jiya ina yaga kwarin jikin da zaiyi tafiya mai nisa haka?,
Daga karshe kuma ya mishi fatan alkhairi dafatan da cewa akan abinda aka sa gaba,
Yanda yayin da addu'ar da yaketa jeroma Sarki nasa albarkha sai jikin Sarki yayi sanyi, harya fara tunanin yanzun kuma ya mahaifin nashi zaiji in zancen sakin auren su ya bayyana bayan ya wuce, lallai shi yasa akace abinda babba ya hango yaro ko ya hau dala da gwauron dutse bazai iya hango waba, domin dai bacin ran dazai biyo baya na uwar gida ta gudar mishi shi yasa kenan tace ya shirya bayar garin, gaba d'aya kuma sai yaji tausayin iyayen nashi ya kama shi,
Daga sashen Malam Sulaiman na uwar gida ya wuce gaisuwar kad'ai ta iya amsawa kafin ta jefo mishi tambaya da cewa "ina fatan can ka nufa daga nan?"
"Eh"
Ya amsa mata a yayin da yaran shi suka baibaye shi kowacce na lissafa mishi abubuwan da take buk'ata bai bar gidan ba sai da ya sauke musu komai na kayan buk'atun su na yau da kullum ya kuma ba Salman sallahun cewar yaje gidan shi anjima su kwaso kayan abincin dake cikin store saboda kar a barsu su lalace,
Tsabar kunyar dake d'awainiya dashi ita ta hana shi shiga gidan Malam bayan fitan shi daga gidan su,
Domin a tsarge yake kwarai sai yakejin kamar duk wanda ya kalleshi abinda ya aikata yake kallo a tare dashi,
Gidan Hajiya ba bak'on waje bane, duk da cewar ba zuwa yake ba amma yasan bazai rasa gane gidan ba dan haka shi kad'ai yama kanshi jagora zuwa gidan yana tafe gaban shi yana fad'uwa,
Dan Allah ya sani shidai tun kafin auren su a had'uwar su na farko da Hajiyar yake jin shakkar matar tun ranar data gindaya mishi sharad'odin zama da jikarta, to gashi kuma yau zai kaima jikarta takardar saki a gidan ta, addu'a yakeyi, fata yakeyi cewa allah ya ceceshi ace harya shiga ya fita a gidan nan basu had'u da ita ba,
Bayan isar shi unguwar a kofar gidan ya faka motar shi sannan ya k'arasa bakin gate din gidan yama masu gadin gidan Sallama,
Sun gaisa a mutunce kafin ya sanar musu cewar wajen Meenal yazo inba damuwa yana buk'atar su mishi kiranta,
Daya daga cikin sune ya amsa mishi,
Shi kuma ya nemi kujera cikin kujerun da aka kirkira dan zama a cikin harabar gidan ya zauna yana tsumayen ganin wanda zai fito cikin ita ko k'akarta.
****a gafen Meenal ko tun bayan da Hajiya Jummai ta sallame ta da cewa ta koma d'aki a jiya tunda ta haura har safen yau bata yarda ta sauko ba, ba kuma komai takeyi a d'akin ba sai dai kuma gaba daya itama bazata iya cewa ga kata maiman abinda takeji a jikin ta ba, abinda ta sani kawai shine bata cikin walwala, harta abincin dare dama na safen yau can d'akin Larai takai ta sameta dashi,
Duk abinda takeyi tsaf hajiya take ankare sai dai itama shareta kawai tayi, domin dai aiko mak'iyin Kane ka rabu dashi na rana d'aya sai kaji kewar shi balle kuma mijin aure, tun jiyan taje ta amshi magungunan dake hannun Meenal din ta ware wadanda take buk'ata ta barma Meenal din sauran bayan ta jaddada mata cewar ta dage taci gaba da amfani dasu,
A daren kuma ta amshi number din uwar gida a hannun Meenal din ta kuma kirata ta shaida mata cewar tana son zata shigo wajen ta da safe, sai dai bata shaidama uwar gidan abinda zai kawota wajen taba,
Sai ma cikin kokonto data barta da tunanin cewar zata biyo bayan takardar sakin ne kamar yanda ta ambata mata a yammacin jiyan.
Koda Hajiya ta shirya ficewar ta kawai tayi da safen batareda tabi takan Meenal data maida kanta daddawar d'aka ba,
Fitan nata kuma sai ya zama hannun riga tsakanin ta da Sarki domin dai ita tana barin unguwar ne shi kuma yana shigowa.
Larai mai gadi yaba sak'on cewa Meenal nada bak'o, ita kuma bata tsaya bin diddigi ba ta haura sama ta shaida ma Meenal din.
"Waye?"
Meenal ta tambaya,
"Gaskiya ban sani ba dan ban tambaya ba,
"Kije ina zuwa"
Shine amsar da Meenal din ta bata,
"Ko za'a shigo dashi cikine Hajiya karama?"
Larai ta tambaya,
"Duk yanda kikayi"
Juyawa Larai tayi ta fito daga d'akin duk da bawai wani farin sani tama mijin Meenal din ba amma a ganin ta da Sarki jikinta ya bata cewa shine mijin na Meenal,
Dan haka tun kafin ta karasa inda yake ta fara gulmar shi a zuciyar ta.
"Gashi dai namiji cikakke son kowa kin wanda bai samu ba amma ace an wanke gangariyar mace kamar Hajiya karama an kai mishi tsayin shekaru ya kasa tab'uka komai, domin dai kowa yasan cewa indai badai akwai wani abun a k'asa ba tofa cikakken Namiji kamar shi bazai yuwu ace ya kasa sarrafa mace ba koda yake dai jiya taji Hajiya Jummai na fad'in cewa aikin asiri ne,.
"Hajiya karama tace ayi maka iso zuwa ciki"
Ta fad'a bayan ta isa inda yake,
Bayan ta yabi a yayin da take mishi jagora har zuwa falon na Hajjaju,
A nashi gefen ko duk