Showing 153001 words to 156000 words out of 174305 words

Chapter 52 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1894

da yanda zuciyar shi ke kad'awa haka ya cije,
Ya nemi wajen zama ita kuma ta wuce kitchen ba tareda tunanin ya karya a gida ba ta had'o wani kayan karin ta kawo mishi, wanda hakan yayi dai dai da saukowar Meenal bata kula dashi ba har sai da ta kawo matakala na k'arshe, can ta tsaya kafin kuma tayi yunkurin komawa a zaton ta ko bai ganta ba,

"K'araso mana ya kike kokarin juyawa kuma? Wajen ki fa nazo"

Tura baki gaba tayi tana k'arasawa inda yake cikin kun kuni tace, "to kai ba kwance kake a gadon asibiti ba mai kuma kazoyi nan, Allah nidai in ma zuwa kayi ka tafi dani bazan bika ba,"

"Waye yace miki nazo in tafi dake ne?"

"To baga kanan ba, me kazoyi to?"
Mikewa yayi daga inda yake zaune ya tarbota,
Hannun ta ya kamo abinda bai tab'a aikatawa ba tsayin shekarun da suka kwashe a matsayin ma'aurata sai yau,

"Sallama nazo miki tafiya zanyi kuma ban san tsayin lokacin da zai d'aukeni ba kafin in dawo, ko laifi ne dan nazo miki sallama"
Ya k'arasa fad'a a yayin da ya zaunar da ita a kujerar daya tashi shima kuma ya zauna a gefenta.

"Meenal" ya kira sunan ta,
Bata iya amsawa ba illah maida hankalin ta da tayi kan kayan karin da Larai ta ajiye mishi,

"Bakaci komai ba?"
Ta tambaya tana kallon shi,
"Yanzun na karya kafin inzo nan bana tareda yunwa, Hajiya bata nan ne?"
"Hajiya ta fita bada jimawa ba"

"Meenal " ya k'ara kiran sunan ta a karo na biyu,

Shima din bata iya amsawa ba sai kallo data bishi dashi, k'ara riko hannuwan ta yayi cikin nashi,

"Meenal fadamin da gaskene kinfi so mu rabu kowa yaje yayi rayuwar shi? Karki boye min ra'ayin ki ki fadamin kinji"
Ya fad'a cikin yin k'asa da muryar shi,

"To ai ni dakai dukan mu ba son juna mukeyi ba, kuma na sani cewa kaima auren dole aka maka kamar yanda nima aka mun"

"Amma ni ai bance bana sonki ba, kokin manta ni dake *Dangi* daya ne?"

"Ah ah ni ban manta ba amma ai matar ka bata sona"

"To amma ai ba ita ke auren kiba nine mijin ki"

"To ai sai baka nan take zuwa gidan ta fad'amin maganar banza, dan dai bana fad'ama kowa ne shi yasa kaima baka sani ba"

"To naji ina kuma neman afuwar ki akan komai dani ko ita muka aikata miki tun daga ranar da aka daura auren mu zuwa yanzun da muke zaune anan ina fatan zaki yafe mana?"

Shiru tayi bata amsa mishi ba,
"Baki ce kin yafe ba"

"To aini kai bakamin laifi da yawa ba"

"To kadan din ma da nayi baki san cewa in baki yafe ba Allah yana iya kamani da hakkin ki, shi yasa nike neman yafiyar ki Kinga tafiya ce a gaba na yau in baki yafemin ba wani abu ya faru dani a hanya na mutu kinga ai zan mutune da hakkin ki"

Runtse hannun shi tayi sosai.
"Ah ah nidai babu abinda zai sameka ai ba yau ka fara yin tafiya kuma Kaje ka dawo lafiya ba,"

"Eh amma kuma kin san Allah babu ta inda baya iyayin ikon shi akan bawa koh!"

"To nidai ka dena cewa zaka mutu, na yafe ma kowa duk wanda ya b'atamin na yafe mishi duniya da lahira, amma nima ka yafe min kaji"
Ta k'arasa fada tana kallon shi,

"Mai kika aikata kike neman yafiya na kuma?"

Dariya tadan yi kasa kasa, tana kauda kanta gefe,
Da yatsar shi babba yayi amfani wajen karkato da fuskarta zuwa gareshi,
"Fadamin mana"
Ya fada shima da dan murmushin da bai bayyana a fuskar nashi ba.
"To ba ina ta tara kud'in da zan siyama Baba Malam Babban fili in gina mishi gida bane, shi yasa ni kuma Nike ta amsan yan kud'ade a wajen ku"
Ta karasa fada tana duk'ar da kanta cike da kunya, sai kuma ta kara shagwabe fuskarta kamar mai shirin yin kuka tace,
"To kuma shine kai kake maganar rabuwa tun kudin nawa basu gama cika ba, kaga ai saura kad'an in zama cikakkiyar likita, zuwa lokacin suma kudad'en asusuna zasu kai in siya ma Babana k'aton fili, kuma harda katuwar motar hawa Nike so in canza taka din nan dama nace sai na fara aiki kafin in fara ginin gidan,"

Ta karasa cike da muryar kuka,
Duk yanda Sarki yaso ya matse wannan karan sai da dariyar shi ya fito fili.

"To ai shi kenan tunda ma dariya na baka"

"Allah ya baki hakuri, yanzun billion nawa kika tarane, Kinga ai in cikon babu yawa koni basai inyi kundun bala in cika miki mu siya mishi gidan ba, bar batun fili dan hidimar gini yawa gareshi, mota kuma ai daman kayan miji na mata ne dan haka daga yanzun ta tashi a matsayin nawa ta koma naki, sai kuma me kike so fad'amin shima yanzun in cika miki shi?"

Dad'ifa ya kashe mutuniyar ku amma dai da yike yanzun ba kamar da bane an d'anyi hankali dan haka sai ta dake abunta bata wani nuna d'aukin ta a fili ba,

"Kinyi shiru"

"Nidai kabar kayan ka, kar mutane suce ka kwashe kudin ka da mota ka bani"
Ta karasa fada tana juyar da kanta gefe cike da tsiwa,
"Kema ai kince kayana, baki san cewa ko gidan nan kikace kina so zan baki ba?"

"Tab lallai ma ni wallahi babu ruwa na, kai baka san yanda har yanzun mutane basu dena surutu akan gidan nan bane,"

D'aure fuskar shi yayi yaci serious sosai,
Hannu ya mik'a ya d'auki ruwan dake ajiye yasha sannan ya maida hannun shi guda cikin aljihu ya zaro wasu envelope ๐Ÿ“จ guda biyu ya rik'o hannun ta ya damk'a mata,

"Meenal ina ganin lokaci yayi daya kamata in barki ko kema Allah zai had'aki da wani mijin wanda zai k'aunace ki yanda ya kamata miji ya k'aunaci matar shi, kiyi hak'uri nasan ban kyauta ba nasaki cikin jerin zawarawa alhalin kedin baki cancanci amsa sunan zawara ba, sai dai nasan ba kowa za'a shaida ma hakan ya yarda ba kamar yanda nima bazan iya cewa ga katamai man dalilin da yasa na kasa mai dake cikakkiyar matar aure ba tsayin shekarun nan,
Abinda na yarda dashi kawai shine cewa ke din iya zaman da Allah yayi zamuyi da juna a tare kenan, ina kuma fatan hakan bazai sa ki kullaceni ba dan hakan nema yasa na nemi gafarar ki tun fari, ina miki fatan alkhairi a rayuwar da zakiyi nan gaba sannan ina rokon ki kar rabuwar auren mu yasa kice zaki yanke alaqar dake tsakanin mu, ki kirani kai tsaye ko sak'on waya aduk sanda kike bukatar' wani abu ni kuma zan miki shi kamar yanda na saba akoda yaushe"

Zuwa wannan lokacin sosai Meenal ta fashe mishi da kuka,
Cikin kuka ta furta mishi "yanzun shike nan kana nufin sakina zakayi? Nima zawara za'a dunga kirana bayan kasan babu wacce auren ta ya tab'a mutuwa a *Dangina*"

"Kiyi hak'uri ki yafemin"

Sai da yayi aikin lallashin ta sosai kafin ta tsagaita da kukan da take mishi,

"Kace in tambaye ka duk abinda Nike so koh?"

"Eh haka nace kuma koba yanzun ba duk abinda kike so zan miki shi"

"Komai nake so?"

"Eh komai Ameenatu"

Hannu tasa ta zaro wayar shi dake makwale cikin aljihun gaban rigar shi sai kuma ta mik'a mishi,
"Budemin key din"

Amsa yayi ya cire wayar a key kamar yanda ta buk'ata,
Nata wayar ta bude itama shi dai yana kallon ta tana aikin danne danne a wayar har ta gama sannan ta maida mishi nashi wayan a inda ta zarota wato cikin aljihun shi,

K'aramin ๐Ÿ—’ memo din data gani akan stool din gefen kujerar da suke zaune ta d'auko, number waya, sunan mamallakiyar number din da kuma address ta rubuta sai da ta nan nad'e takardar kafin ta tura mishi a cikin aljihu, shi dai da kallo kawai yake binta,

"Na tura maka pic a wayar ka ina son duk sanda Allah yasa ka samu lokaci ka bud'osu ka duba kaji dan Allah please ๐Ÿ™ "
Ta fad'a hakan tana mai hade hannuwan ta alamun roko,

"Sunan ta da inda zaka sameta duka suna cikin takardar da nasa a cikin aljihun ka,

Ita din jinina ce sai dai a shekarun baya can ta tab'a furta cewar kana matukar burgeta harma tana jin zata iya auren ka,
Kafin alakar aure ta ratsa tsakanina da kai kullum in nayi magana da ita saita tambaye ni ya kake? Kana gari ko baka zoba? Duk da a lokacin tasan ba son hirar ka nikeyi ba saboda ni a lokacin haushin kusan cin dake tsakanin ka da Baba Malam nikeji gani nike kamar kana son ka kwace min matsayin da Nike dashi a wajen shi domin duk sanda kamin ba dai daiba idan na gaya mishi sai ya nemi hanyar da zai kareka duk dan dai kar inga bak'in ka,

Nasan saboda ni ne ta cire duk abinda takeji akan ka, hakan bai wadatar da ita ba har saida ta nemi afuwata bayan auren mu, tunda na aureka kuma take tsallake zuwa inda Nike indai ance mata kana gari,

Ba ina nufin dole sai ka sota ba, koda kuma kasota din ina neman alfarman karka shaida mata cewar ina da masaniya akan komai, dan haka na baka dama daga ranar da kaji a zuciyar ka cewa kana sonta zaka iya rayuwar aure da ita ka nemeta kar kuma ka gajiya har sai ka shawo kanta, ina fatan kuma bazaka watsamin kasa a cikin idona ba, nima kuma ina maka fatan alkhairi da fatan samun nasarar rayuwa nagode da kulawa.

Tana k'arasa fad'in hakan ta mik'e,
"Muje in taka maka zuwa kofar gida"

Bai iya cewa komai ba illah mikewa da yayi haka suka jera yana gaba tana bin bayan shi har suka fice a sashen,

A tsakar gidan sukayi kicibus da AK wanda tun barin gidan da yayi jiya bai dawo ba sai yanzun,

Koda ya hango su so yayi ya juya ya koma sai dai kuma sun rigada sunyi ido biyu da Sarki,
"Assalamu Alaikum" sarki ya mashi sallama gamida bashi hannu sukayi musabaha,

"Thank You for yesterday, Allah ya saka da alkhairi"

Da kyar AK ya iya bud'e baki ya amsa da cewa,

"Ba komai yiwa kaine ya jikin naka, Allah ya kara lafiya"

"Ameen jiki alhamdulillah"

Gaba sukayi shi kuma shige sashen na Hajiya, har bakin motar shi Meenal ta raka shi saida taga ya shiga sannan ta fara matsar kwalla,

"Wanene shi?"
Sarki ya tambaya,

"Shi wa?"

"Wanda muka gaisa dashi yanzun"

"Yaron yayan mamana"

"Anan gidan yake zaune?"

"Eh"

"Ki kula dashi yana da kirki kar kice zaki dunga mishi tsiwar da kika saba kinji"
Kauda kai tayi gefe tana murgud'a baki.

"Ai kai dan baka san halin shi bane shi yasa kace haka, amma shi din harma akwai wanda yakai shi rashin kirki ne"

"To allah ya baki hakuri zan wuce in hajiya ta dawo ki gaisheta na kuma gode da yanda kika tsaya kika saurareni muka fahimci juna, zansa Salman ya kawo miki motar anjima, maganar gidan Malam kuma zan bincika idan an samu zan tuntube ki a ina kike son gidan?"

"Ni duka bana so, bana son komai sai anjima"

Ta fad'a tana juyawa ta shige cikin gidan ta barshi anan,
Yad'an jima kad'an kafin ya kunna motar ya bata wuta yabar layin,

Ita ko tunma kafin ta k'arasa cikin falon Hajiya ta fara kuka,
Kuka kuma bawai irin kukan tabarar data sabayi ba a'ah takeyi sosai domin tsakani da allah sakin aure fa ba abune na wasa ba,
Shigar ta cikin falon yayi daiโ€™ dai da fitowar da AK yake shirin yi,
Bata tsaya wata wata ba takai mishi wata iriyar wawiyar runguma tana cigaba da ihun kukan ta kamar wacce akama ruwan bula lai,

"Shi kenan na zama bazawara ya sakeni, ya sakeni nima na zama sakakkiya, waiyo Allah na zama bazawara aure na ya mutu....."

Hihihihi haka ta dunga rusa kuka, kankame a jikin AK ko bata san wata rungume bane oho .
Kam kam ya k'ara rungume ta domin wallahi tunda yaji ta furta kalmar "ya sakeni" ya fara jin hajijiya na nema maka shi da kasa,

Innalillahi wa'innah ilairir raju'un, yayi ta maimaitawa yayin da jin fitar kalmar a bakin shine yasa itama ta kama sukaci gaba da maimaita a tare ba kuma dan tabar kukan da takeyi ba,
Haka yaci gaba da riketa a jikin shi har zuwa sanda kukan nata ya lafa sai hawaye da suka kasa tsaya mata,

Janta yayi sukayi zaune a kujerar dake kusa dasu, koda suka zauna d'in bata yarda ta raba jikin suba, domin idon ta ya rufe inda zata jingina taji dama dama kawai take nema.

"Larai" ya kira, dake gefen kitchen din rakube tana kallon su itama tana nata matsar kwallan,
"Jeki kiramin Hajiya Jummai yanzun nan"
"To" ta amsa dashi ta wuce,

"Kiyi hakuri kiyi shiru haka, kukan ya isa, baki san duniyar nan a lokacin da wani yak'ika shi kuma lokacin wani yakejin cewa ko ranshi ne zai iya badawa dan ya faranta miki ba, me yasa zakiyi kuka dan kin rabu da mutumin daya nuna ma duniya cewar baya sonki, bayan dubu sau dubu a bayan shi kullum mafarkin son suyi rayuwa tare dake suke?"

"Saki na yayifa kuma yanzun ai kowa kallon bazawara zai min"

"To sai me dan an miki kallon bazawara? Iyeh baki san wata macen nata auren bai tashi mutuwa ba har sai sanda tsufa ya fara cimmata, kuma a hakan zakiga maza na rububinta har sai mai rantsatstsan rabone zai d'auka balle kuma ke,
Kiyi shiru kukan ya isa haka dan in kika sa kanki a damuwa muma zamu shiga damuwar shiko Kinga ai can wajen d'aya matar shi zai koma ya manta dake"

Kuka ta k'ara fashewa dashi,

A haka hajiya Jummai ta shigo ta same su,
"Mai ke faruwa anan?"



*Ummiee Zaria*โœ๐Ÿผ
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA!*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆโšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ
~{{MY FAMILY}}~

*FREE BOOK*

*RUBUTAWA*
*UMMIEE ZARIA*โœ๐Ÿผ


````` *Page 45*.....

"Me yake faruwa anan?"
Hajiya Jummai ta tambaya tana binsu da kallo,
Kamar mai jiran iso warta haka Meenal taje da gudu ta shige jikinta, tana ci gaba da rusa ihun kuka.

"Hajiya aure! Yau aurena ya mutu, Ya Sarki ya shigo har gidan nan ya kawo min takarda ta, ashe da gaske ne baya sona, hajiya ya sarki bai tab'a sona ba, ya dai zauna danine kawai dan babu yanda zaiyi waiyo Allah na shike nan na zama bazawara"
Take fad'a cikin kuka mai tsuma zuciya,

"Innalillahi wa innah ilaihir raju'unยณ ubangiji Allah kai mana maganin abinda kasan bazamu iyaba,"
Ta fad'i hakan tana mai dan dukan gadon bayan Meenal din alamun lallashi cike da jimami.

"Kiyi shiru Meenal kukan ya isa haka, ai bake ce ya kamata kiyi kuka ba shi da yayi rashin mace kamar ki shi kamata ya shige cikin d'aki yayi kuka, ke ai abun ki d'aga hannu ne ki gode Allah tunda har shi da kanshi ya sallame ki salin alin, kwana nawa ne zakiyi a gidan kafin wasu mazajen su fara tururuwar kawo miki cafka,"

Wannan kalmar nata kamar fitar kibiya haka taje kai tsaye ta caki zuciyar AK wanda dole ya daga kanshi yana mata wani kalar kallo mai kama da shi kenan so take ta kasheni,

Ita ko ba tareda damuwa ba a kokarin ta shawo kan kukan da meenal din keyi ne taci gaba da cewa
"share hawayen nan naki ni bana son ganin su,indai kukane akan namiji insha Allah kiyi d'aya bazaki k'arayin na biyun shiba, inba ma kaddara ba ai dama shi din ba sa'an auren ki bane dan yayi miki tsufa me ma zakiyi da mijin wata?
Kai kuma tashi ka d'auko min ruwa masu sanyi in bata tasha ko ta samu sanyin zuciya, ka wani zo ka zauna ka tasata a gaban ka kamar ka samu TV ita kuma saboda rashin sanin ciwon kai ta wani dage da kuka akan mutumin daba kaunar ta yake ba amma ka kasa hanata"

Zaunar da Meenal din tayi sannan ta yago tissue paper ta shiga goge mata hawayen ta dake ta faman shatata uwa ana korosu,

"Kinga nifa in baki kama kanki kin dena kukan nan ba to a gaskiya ba zamu shirya ba da wuri zamu raba jaha dan nidai banga dalilin da zaki tsaya kuka akan mutumin da bai san darajar kiba, in kuma kina ganin kamar baki iya rayuwa ne dole sai tare dashi to ai sai ki mik'e muje ni da kaina zan mai dake d'akin ki in duk'a har kass in roke shi ya mai dake d'akin ki tunda naga kamar son shi kike da yawa ta yanda sai dashi zakiyi numfashi dole"

"Aini dai bance zan koma ba!,
amma ni ai ban san me zan fad'a a gida ba,shi yasa nike kukan kinga fa ban mishi laifin komai ba ya biyoni har gidan nan ya kawo min takarda ta, fisabilillahi kaf cikin *Dangina* wacece auren ta ya tab'a mutuwa idan bani ba?, aini wallahi kunya zanji a dunga nunani ana cewa aurena ya mutu"

"Mtwsw"

AK yaja wata irin doguwar tsaki mai shegen k'ara, dungure musu ruwan yayi cike da fusata, ya fara nuna ta da yatsa,
"Na rantse da Allah in baki rufama mutane baki da wannan kukan iskancin da kikeyi tun d'azun ana lallashin ki kina ci gaba da iskanci ba saina zane miki jiki tass wallahi, kujimin wani sabon gulma da munafunci, oh dama kin san kina son nashi kika biyema Hajiya kika taho nan gidan, mai yasa tun jiya da nasa baki baki bijire mata kinyi zaman ki a gidan kiba? In bama hauka ba mijinki na kwance a gadon asibiti yana jinya kika tsallake shi kikayi tafiyar ki sai yau dan ya biyoki da takarda ne zaki samu a gaba kina mana kukan iskanci da rainin wayau, Larai"
Ya kwala ma kira da karfi, sai ko gata a falon tsulum dan dama tsaye take daga bakin kofar kitchen tun d'azun tana jimamin wannan mutuwa na auren Meenal din.

"Haura sama ki d'auko min akwatin kayan yarinyar nan ni nan nida kaina zan maidata gidan mijinta, tunda tana son shi taje can ta k'arata,"
Hajiya Jummai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login