Showing 36001 words to 39000 words out of 174305 words
Chapter 13 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
cikin ganin su,
Kai amma dai halan kunsan Aunty Feenah bata nan shi yasa kuka zo,bari dai in kawo muku ruwa"
Ke dallah wai miye haka sai wani rawar jiki kikeyi,kuma ai mu kinsan ko tana nan ko bata inta mela mana zuwa zamuyi gidan Ya Mashkur nefa mu ina ruwan mu da ita, kuma karki damu kanki yawon zamunci yau mukazo dan haka wallahi bamu shan ruwa domin dai ko Ya Mashkur bai bamu go ahead akan muci abunda muke soba kin san ci zamuyi balle kuma ya bamu" Bebs mai zaku sha? dan Allah ku saki jikin ku gidan Ya Mashkur mukazo ba baƙon waje ba".
Cewar Meelat,
"ke Auta nidai ku rufamin asiri kunsan in Anty ta dawo ni zatama faɗa baku ba imma wani abu zakiyi ku bari harta dawo dan Allah" cewar Sarah.
Ke wallahi bazamu jira ba bari ma ki gani wai ina Sweat heart ɗina Aslam ya shige ne ko har yanzun bai tashi a bacci bane?",ina dalili mutum yazo gidan ɗan uwan shi a wani fara kafa mishi dokoki,to ni nabi takan dokar nata na wuce asa wuƙa a yanka ni.cewar Meelat a yayin data Mike zuwa neman Aslam ɗin dan tasan sau da yawa a gida uwar ke barin shi ta fice harkokin ta.
Ai tareda maman shi suka fita" Sarah ta bata amsa tana juyawa zuwa cikin kitchen ɗin data fito,
Zazzaune sukayi akan kujerun dake falon, "keni dan Allah ki bani labarin mai gidan yan gayun can na matsu inji waye shi" cewar Moon.
" yau naga abunda yafi zare tsayi wannan wani irin jidali ne haka Maimoon ance miki mutum yana da mata amma still kin dage sai maganar shi kikeyi to in ma sonshi kike tun wuri gara ki kama kanki dan ba samun shi zakiyi ba,ke ina ke ina soja fisabilillah kifa kiyayeni"
Cewar Aisha da tuntuni mamakin Moon ɗin yasa ta kasa cewa wani abu sai yanzun.a dai² lokacin ne kuma Sarah ta fito daga kitchen hannun ta ɗauke da farantin data jero musu kayan motsa baki ta kawo ta ajiye musu,
"Ga ruwa nan kusha" ta faɗa itama tana zama a gefen Meelat "maganar me kukeyi halan?
Uhm yama sunan ki? Moon ta tambaya,
"Sarah" ita kuma ta bata amsa "dan Allah in tambayeki tsakanin ki da Allah wancan gidan mai Ash and Black ɗin penti ɗin dasai an wuce kafin azo nan ki fadamin tsakanin ki da Allah in kikazo wuceshi bakyajin ina ma ace gidan nan ya zama naki,ina nufin ki zauna matsayin mata a gidan?".
" Wai gidan Sarki kike nufi ? Wallahi³ kinji rantsuwar musulmi ko to gidan nan ko hasidin izah hasada bazai kushe shiba dan yasan bashi da makusa balle kuma irina mai addu'ar Allah ya bani makaman cin shi,ke gidan nan fa ya gama haɗewa yasin dan ma iya wajen kika gani bakiga cikin shiba dasai kinfi haka ruɗewa,bani labari mai ya faru kike tambaya akan gidan?"
Hannu Moon ɗin ta mika ma Sarah "Salamu Alaikum mu gaisa ƴar uwa, kina ji koh waifa kawai dan munzo wucewa na tsaya koɗa kyan da gidan yamin shine fa duk suka wani hayayyako suna neman cinyeni ɗanye,dan Allah kin taba ganin me gidan?",
Kai gani sosai ma gidan Sarki nefa,ga ƴar uwar shi a gefen ki kike neman wanda ya sanshi" ta faɗa tana mata nuni da Meenal dake cin doughnut da drink kamar bata san akan me suke magana ba.
"Wai da gaske ɗan uwan sune? Ah ashe ma ɗan uwan mune",
Ta faɗa tana kaima Meenal duka a cinya,
"Zan cicci miki idan kika ƙara sani a maganar nan ƴar kalan dangi kawai a gidan ubanwa ya zama ɗan uwan naki ? Kinji kunya wallahi mtwss"
Eh naji ba komai dai cigaba da bani labari Sarah,
"Toni me zance dan nima ba wani sanin shi nayi ba kawai dai nasan matar shi kawar Aunty Feenah ce kuma ita ya gina ma gidan amma tace ita bazata taɓa barin lagos ta dawo Zaria da zama ba sai dai ya mata gini a Abuja ko Kaduna,iya abunda na sani kenan dan lokacin da sukayi rikicin har Aunty Feenah saida tasa baki amma tace wallahi bata dawowa sai dai ya saida gidan ya siya mata wani a inda ta keso,shi kuma yayi alwashin bazai siyar ba sai dai tayi ta zama a lagos ɗin gashi yanzun ita tana can shi kuma ya dawo KD da aiki kunsan dai dama yanda Aiki Soja yake.
Tabdijan to ita bata tsoron ya ƙara wani auren a nan ne yasa matar a cikin gidan?
Aisha ta tambaya tana jinjina kai,
Oho mata" ta faɗa cikin rashin damuwa.
Dan Allah fadamin ya zumuncin su yake dasu Meenal? cewar Moon, "wai ba gata nan ba ki tambayeta mana" No ai kema kinsan bazata fadaba tunda batayi niyya ba.
"Ke bakiga daga gidan su Ya Sufyaan ɗin sai nasu Meenal ba to ai Dangi ɗaya suke yayan yaya da kani ne iyayen su,ina nufin kakan su Meenal da nasu Ya Sufyaan ɗin.
Ok yanzun na fahimta" cewar Moon ɗin.wai ke Meenat me yasa a komai sai kinyi zari ne kin tasa abu a gaba kamar ke kaɗai aka kawoma sai faman ci kike",
Oh to bari inƙi ci in tsaya biye muku da banzan surutun ku" kallon Sarah tayi "ke yarinya gidan nan baku da kaza ne naga sai kayan fulawa kika jibgo mana salan muci mu kunbura irin matar gidan,muje kitchen ɗin ai wallahi an bamu go ahead muci duk abunda muke muradi,
Atakaice dai a wannan gidan sukayi kusan rabin wunin su bayan sun shiga kitchen sun dafa abunda suke so sunci sunyi nak harda zuguri ma sunyi dan mai gidan ya kira ya faɗa musu bazai samu damar dawowa da wuri ba ya shiga cikin gari,gashi kuma daɗin daɗawa har sukaci suka suɗe matar gidan bata dawo ba dan dama ita haka take wuyar ta dai tasa kafa tabar gidan tofa sai sanda Allah yayi dawowar ta.basu tashi barin gidan ba saida sukayi sallar azahar sannan sukama Sarah sallama wacce ta rako su har bakin gate ɗin gidan kafin ta juya su kuma sukayi gaba.
******
Bari mu waiwaya gefen Sarki muji dalilin daya mai dashi cikin gidan shi bayan ya fito,
Bayan shigar shi cikin gidan kai tsaye falon nashi dake buɗe ya wuce ba tareda ya kula abokin shi dake zaune a falon wanda ganin shigowar nashi yasa yake tambayar shi "Sarki ya haka bakaje ɗin bane kuma? Da alama dai fitan da yayi daga gidan wani wajen yayi niyyar zuwa,
Ba tareda ya iya buɗe baki yayi magana ya amsa ma mai tambayar dakai kawai ya wuce shi yana mai haurawa zuwa sama inda ɗakunan gidan suke,a daddafe yaci gaba da haurawa hannun shi guda akan marar shi yana tallabe da ita kamar mai tsoron kar marar ta fita daga jikin shi,koda ya kai kanshi zuwa ɗakin baccin nashi wajen window ya nufa ɗan Jan labulen yayi kaɗan wanda hakan ya bashi damar kallon su Meenat kai tsaye daga nan inda yake tsaye,cigaba da kallon su yayi duk da bawai yanajin abinda suke cewa bane har sai da suka wuce kafin ya koma yayi ruf da ciki akan gadon ɗakin daga ganin shi dai kasan bayajin daɗin kwanciyar a dole yayi ta duba da yanda yaketa faman juye ² akan gadon kamar mai nakuda.
Ganin dai abun bana karau bane yasa ya mike a dudduƙe yakai kanshi bakin mirror wani magani dake ajiye a wajen haɗewa da ruwa ya ɗauka yasha sannan ya shige bayi ya samu ya watso ruwa kafin ya dawo kan gadon yaci gaba da kwanciya.
*Shin wai wanene Sufyaan inkiya Sarki Mai Zamani ma?*
Nasan kuna son sanin wanene shi kuma.
A baya munyi magana akan ahalin Malam sai dai bamuyi magana akan yan uwan shi dake kewaye dashi a cikin unguwan ba,dan in baku manta ba na faɗa muku yawancin mazauna unguwar ahali ɗaya ne,
Bari mu fara da gidan su Sufyaan Sarki sauran a hankali duk zasu fito a cikin labarin.
Gidan Malam Ladan shine inkiyar sunan da akeyiwa gidan nasu Sufyaan kasancewar Kakan su Sufyaan ɗin shine Babban ladanin masallacin unguwar tun fil'azal ,kamar kuma yanda na faɗa a baya suma dai gidan su na malamai ne Zumunci ne mai karfi tsakanin su da gidan Malam domin dai dukan su asalin su ɗaya iyayen su uwa ɗaya uba ɗaya suke dan haka ko bayan shuɗewar iyayen su sukaci gaba da rike zumuncin su har ya zuwa yanzun,shima nan ɗin babban gidan ne sai dai sabanin gidan Malam nan ɗin mazajen gidan daga mai mace biyu ne sai sama da haka domin ko shi Mahaifin Sufyaan ɗin mai suna Sulaiman matan shi hudu ne kuma Sufyaan ɗin shine Babban ɗan shi namiji kafin shi akwai mata amma tunda matayen suna gidajen auren su hakan yasa gaba ɗaya girman ya koma kanshi,
Sai dai kuma matan gidan saɓanin gidan Malam sukam sun kasance wasu irin mata masu zafin kishi ko wacce a cikin su cike take da kishin ƴar uwarta idan ka cire uwar gidan Malam ɗin Mai suna Hajara wacce ahalin gidan ke kira da uwar gida,dan tana bakin kokarin ta wajen ganin kishin matan gidan bai raba tsakanin yaran gidan ba kuma duk yanda kishiyoyi dama facalolin nata ke haukar su bata taɓa daga kai ta kalle su dan bata lokacin su,to suma dai iskancin nasu a gefe sukeyi basu fiye yin mata hawan ƙawara ba.
Sufyaan ya taso ne a matsayin natsatstsen yaro ta yanda har wasu iyayen sukan bama nasu yaran misali dashi,yaro ne mai tarin ilimin boko dana addini saboda hakan yasa baban shi jawo shi a jikin shi sosai ya cusa shi cikin har kokin kasuwan cin shi Allah da ikon shi kuma sai gashi ya zama mai nasibi domin bayan shigar dashi cikin harkokin nasu sai sukayi ta samun cigaba sosai kasancewar dama harkar kasuwan cin ya karanta kuma yana son kasuwancin sosai,wannan cigaba daya samu yasan ya Baban shi akoda yaushe yake ƙara alfahari dashi sai dai abunda bai saniba shine matan shi guda biyu ba karamin bakin ciki sukeji da faruwar hakan ba, domin duk cikin su babu wacce Allah yama arzikin samun ɗa namiji sai mace, dan haka suka haɗa hannu wajen lallai sai sunga bayan Sufyaan dama mahaifiyar shi data zame musu ciwon ido dan batun yauba suke ta Neman yanda zasuyi da ita sai dai tako ina tafi karfin su kasancewar ta fito daga cikin gidan sarauta kuma sunan Baban ta aka sanyama Sufyaan ɗin dan haka suke kiran shi da Sarki.
Kun san yan magana na cewa tsafi gaskiyar mai shi domin dai da kaɗan² abubuwa suka fara kwabewa ta fannin Sufyaan da farko gaba daya suka cire zuciyar shi akan harkokin Mahaifin nashi dama nashin gaba daya,dan kwata² ya dena zuwa kasuwa zai shirya ya fice daga gidan amma kuma ba can ɗin ya nufa ba,da wannan damar sukayi amfani suka dunga kai sukar shi a wajen Mahaifin shi, Mahaifiyar shice ta fara lura da canjin da yayi dan ba haka ta saba ganin ɗan nata ba dan haka ta Mike tsaye wajen sanya shi cikin addu'o'in ta,Allah kuma yaji kanta dan abun bai daɗe yana tasiri a jikin shiba ya sake shi dan har ya koma kan kasuwancin shi,ganin cewa basu dace ta wannan fannin bane yasa suka canza shiri wannan karan so suke bama iyayen shi kadai ba harta sauran jama'ar dake bama yaran su misali dashi su tsine mishi.a hankali sai ga Sufyaan ya fara shaye² tun yanayi a boye har Allah yasa ranar Mahaifiyar shi ta ganshi,tsabar tashin hankali suma ne kawai ya rage batayi ba dan wallahi da wani ne ya faɗa mata cewa zatayi sharri akema Sarki dan iya sanin ta tasan ɗanta ko warin sigari baya so balle kuma azo ga batun shanta sai gashi yau Sarki ne da shan kayan maye Innalillahi wa'ainnah ilaihir'raju'un me yake shirin faruwa da ahalin ta,shine abunda bakinta ya iya furtawa dan haka ko Mahaifin shi bata bari ya sani ba ta kira ɗan uwanta ta zayyana mishi abunda yake faruwa,washe gari yasata ta tura mishi Sufyaan ɗin can inda yake zaune a Abuja sukayi ta neman taimako da kuma addu'ar uwa Allah yasa wannan karan ma suka karya kadarin ba wanda yaji koya gani,bayan komai ya lafane ɗan uwan nata ya bata shawara a kan yana ganin gara Sarki yabar garin dan yana tsoron abinda zai faru zuwa gaba kuma dan in wadanda suke mishi hakan sunga basuga abunda suke tsammani ba yana tsoron mugun abunda zasu aikata mishi a gaba,kuma shi kawun Sufyaan ɗin shine yama Baban Sufyaan ɗin bayani akan halin da ake ciki da kuma shawarar daya kawo na barin Sufyaan ɗin garin gaba ɗaya,babu bata lokaci ya amince domin koba komai bazai so rayuwar ɗanshi babba ta lalace ba.dan haka daga wannan lokacin rayuwar Sufyaan ta koma Abuja inda yaci gaba da karatun shi daga bayane da taimakon kawu yusif ya nemi aikin soja Allah kuma yasa ya samu a yanzun haka shiɗin sojan ruwa ne,
yanayin aikin shine ya kaishi Lagos inda Allah ya haɗa shi da uban gida mai mutunci Brig,Gen,Abubakar ya rike Sufyaan kamar ɗanshi saboda kwazon shi a wajen aiki wannan dalilin ne yasa Sufyaan komawa gidan Brig da zama ,ya taka matakan nasara da dama sanadiyyar General dan yanda ya ɗauke shi kamar ɗa haka shima yake mishi kallon uba,
Yaran Brig su hudu Allah ya bashi 3 mata 1 namiji wanda shine karamin cikin su babbar ƴar shi mace ba a 9ja take karatu ba dan haka bata san Sufyaan ba sai dai kullum tana jin sunan shi sai kuma a hoto,sai dai kuma Allah da ikon shi tun ranar farko da taga hoton shi taji bata da gwani sai shi,dan haka tun tana can tasa baban ta ya tura mata Number ɗin shi ta fara yaɗa manufofin ta akan shi,kunsan yan magana na cewa da zafi² akan daki karfe to hakika kusan hakan ne ya faru domin dai saida tayi duk yanda tayi wajen ganin ta yaɗa manufofin ta akan shi ya zamana harta da iyayen ta sun san ra'ayin ta akan Sufyaan ɗin,duk da ilimin addinin da Sufyaan ke dashi shiɗin mutum ne mai son wayayyar mace ƴar gayun data san kanta wacce bazaiji nauyin nunata a duk inda hakan ta kama ba,sai gashi a ganin shi hakan yazo mishi cikin sauki dan haka bazancen Jan aji tuni ya bada kai sukaci gaba daba fulawa ruwa har zuwa sanda Fatima ta dawo, ba'a dauki wani dogon lokaci ba aka fara maganar auren su.
Zuwa wannan lokacin shima Sufyaan ɗin a hankali ya fara taka manyan matsayi ta fannin aikin shi ga kuma kasuwancin shi da yake gudanarwa a gefe guda dan haka ba ƙaramin shiri yama bikin nashi ba,sanin da yama Teemah na rashin son zaman cikin barikin nasu yasa dole ya nemi wani gida a wajen barikin mai kyau madai'daici na zaman mace ɗaya ya siya dan su zauna a can subar barikin saboda tsabar yanda yasan Rabin ran nashi ta tsani zaman barikin ne yasa ta bijire wajen yin karatu a 9ja,
sosai ya gyara gidan nashi a kokarin shi na ganin ya faranta ran masoyiyar nashi dan gaskiya ba so na wasa yake mata ba sosai ya sanyata a zuciyar shi da alama dai inba Teemah ba sai rijiya.
A can gidan su a Zaria kuma duniya sabuwa wajen kishiyoyin uwar shi domin su rashin shi a gari gaba ta kaisu koba komai bazasuci gaba da ganin shi rayukan su tana ɓaci ba,dan su a zaton su aikin sune yaci shi yasa gudun abun kunya yasa uwar shi tasa shi barin garin dan haka suka koma wajen da suke zuwa akan a dan kwafar musu dashi acan karma ya ƙara marmarin dawowa gidan ma,
rashin dawowar nashi yasa suke zaton aikin sune yaci dan haka sukaci gaba da sha'anin su,
Sai dai abunda basu sani ba shine a yanzun yafi jin daɗin rayuwar shi a inda yake fiye da c
nan ɗin sannan duk sanda iyayen shi suka so ganin shi sukan kai mishi ziyara haka shima duk sanda aiki ya kawo shi arewa yakan zo yaga iyayen nashi sai dai maimakon yazo ido na ganin ido sai ya maida zuwan nashi na dare,har sai yazo ma yayi abunda zaiyi ya wuce wani bai san shine ba,
Iyayen shi maza sun san meke faruwa sai dai Malam Babba ya kwabi kowa akan yin maganar da mai ɗakin shi,
Sai gashi kwatsam bayan wasu shekaru maganar auren Sufyaan ɗin ya taso da yike bikin a can lagos ɗin za'ayi ba anan ba dan haka basu san wacece zai aura ba shi yasa ba wacce ta damu,
a ganin su ai gara yayi auren ma ya dauwa ma acan ko ba komai sun san abinda sukayi na kafeshi a can,(a zaton su fa).
Su Malam ne suka niƙa gari har lagos wajen Neman aure da duk wani al'adar da ake gabatarwa na neman aure,
Wata ɗaya akasa yayin da Mahaifiyar shi da yan uwanta sukayi tsaye wajen ganin sun haɗa mishi kayan aure na fita kunya,sai dai matsala na farko daya fara kunno kai kafin auren shine batun kayan lefe duk da yan uwanta sun yaba kwarai amma fa kawayen Teemahn yan gayu kuma yan karya irin ta suna zuwa suka fara kushe kayan a cewar su kayan ba ajinta bane a kokarin su nason ganin sun kaskantar da Sufyaan ɗin dan tun abun bai bata haushi ba har saida ranta ya bacci ,dan batun yau ba suke kokarin nuna mata cewar tafi karfin Sufyaan ɗin ita matar manya ce ina laifin