Showing 114001 words to 117000 words out of 174305 words
Chapter 39 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
ba saima umarni daya bayar akan a samu wadanda zasu zauna tare da ita su d'ebe mata kewa kar tunani ya mata yawa, a gidajen amare da yawa in kawaye sun kwana zaka samu cewa sun raya daren ne cike da farin ciki dan wasu ma kusan kwanar zaune sukeyi suna hira, sab'anin gidan Meenal daya kasance shiru babu wani kara kaina dan ita dama ganin kukanta yayi yawa yasa tun kafin su fito da Aunty Hassana ta tsareta taci abinci ta hada mata da maganin bacci dan haka koda suka iso gidan da aka mik'ata d'akin ta umarni Aunty Hassana ta bayar akan su koma falo domin zuwa lokacin bacci ya fara cin karfin Meenal din,
Su kuma kawayen waje can suka koma wajen abokanan ango suna daddalewa domin dai tunda aka fara hidimar bikin babu wanda ya nemi wani a cikin su gashi har amarya ta tare a d'akin ta koda suka nemi ganin ango uzuri abokan suka basu akan cewa shima bayajin dad'i shi yasa bai zo tare dasu ba, sai dai abokan sunyi musu sallama ta girma a matsayin su na kawayen amarya kafin suka juya suka koma masaukin su bayan kawayen sun tabbatar musu da cewa basa bukatar komai aka bar wasu daga cikin yaran Sarkin domin su kula da gidan.
*Jama'a wai ina Angon ya shige ne?*
Kwaro Sarki yaba mota ya je ya d'auko Teemah a Kaduna a wannan ranar basu shigo Zaria ba sai gabanin Magriba, kai tsaye kuma Hotel din daya kama domin ta yayi ma Kwaro umarnin wucewa da ita domin yafi son ya fara ganawa da ita kafin ta isa gidan su,
Dan haka koda Kwaro ya kaita d'akin da Sarki ya kama ya rakata da akwatin ta, bai kuma tsaya ba yayi sallama da Sarki ya koma domin shi ke kula da bak'in su dake zuwa dama duk wani zirga² na bikin.
Kasan cewar bata da wani gajiya a tareda ita hakan yasa Sarki ya fara gabatar mata da abinci, sai da taci tayi nak sannan ta fara tambayan shi "ya mai jikin ta k'araji suna gida ne ko asibitin? "
"Jiki da sauki tana gida domin a gida likitan ke zuwa yana dubata"
"Allah ya k'ara lafiya sai mu tafi yanzun ai ko inje in duba jikin nata dan shine mak'asudin zuwa na garin!"
"Yaran kifa? Bakya d'aukin son zuwa kigan su? Kin san dai sunyi kewar ki suma!"
"Hhhh ko sunyi kewata ya zasuyi tunda haka uban su ya zab'ar musu, an nuna min kaka tafi uwa mahimmanci na gode Allah dabai yoni a matsayin juyaba tunda gashi harna haifo wani d'an, kasan ko ai dama koba komai shi d'a namiji kason mata biyu yake ci dan haka ban yi fad'uwar bak'ar tasa ba"
Shareta yayi jin tana son tsokalo wani maganar daban kuma.
"Zamu tafi can d'in amma dai kafin nan ina bukatar matata, koba komai ai an san nayi kewa" ya k'arasa fad'a yana d'age mata giraren shi,
Ji tayi kamar ta waftoshi ta kikkifa mishi mari, wato ga dokin shi ta iso saura sukuwa koh? Shida ake batun aura mishi sabuwar budurwa ne dan bashi da kunya zai wani ce yayi kewarta bayan abunda yake shirin aikata mata?
Wallahi da badan akwai aikin da aka bata wanda sharad'in shi shine dole sai yayi amfani da ita da abun a jikin taba da bazata bari ya kusanci jikin ta a yanzun ba da saita hora shi har ya koma yana rokon ta allah annabi tukun na dan ta nuna mishi cewa ita ba Teemar banza da hofi bane, amma ba komai a jure zuwa rafi koba komai ai durkusa ma wada ba gajiyawa bane, hakan nema yasa ta murmusa cike da kissa ita ma tace,
"Nima nayi kewar kakkarfan jarumi kuma Sarki a fadar zuciyata, amma kafin a shiga filin wasa a dan barni in d'an gyagygyara domin bawa wasan damar samun armashi,
Shi kuma sokon gado ya koma a dole yana jiran ta shiryo a shiga filin wasa aci gaba da fafatawa,
Sai da ta d'auki kayan aikin da take bukata ta shige cikin makewayi tayi amfani dana matsawa daga gogawa harma dana feffesawa sannan ta fito,
Allah da ikon sa yau dai sab'anin sauran kwanakin da take jan ra'ayin shi harma ta mantar dashi Addu'ar da aka koyar damu na ma'aurata yayin saduwa da iyali yau dai Allah ya bashi ikon karantowa kafin su fara fafatawa.
Sunfa dambatu iya dambatuwa domin dai dama dukan su jarumai ne a wannan fagen,
Bayan komai ya kammala kamar wani soko haka Sarki ya saki baki ya dunga ratata ma Teemah zancen abun dake faruwa na batun auren da uwar shi ta bashi umarni akan dole, ya kumayi mata alkawarin Karin auren shi bazai taba sawa ya canza mata ba domin dai shi din nata ne har gaban abada, ya daiyi b'ab'atun shi duk a son shi na fahimtar da ita cewar babu laifin shi kuma bama son yarinyar yake ba, ita kuma gudun karya yi tunanin wani abun daban hakan yasa tadan nuna bacin ranta akan yanda kai tsaye zaiyi mata kishiya ba tareda sanarwa ba.
Kai jama'a yasin na gaji😰😰
Mu had'e gobe idan Allah ya kaimu da rayuwa,
Ummiee Zaria ce✍🏼
💗💗💗
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: 🔱⚜️👨👩👧👦 *DANGINA!* 👨👩👧👦⚜️🔱
*Free Book ga masu buk'ata daga farko zasu iya tuntub'ana kai tsaye 08061358462*
""""Page 33
*Masoya masu juriyar bibiyar labarina Ina mai baku hakurin rashin ganin posting kullum,I am very sorry for that abubuwan ne da yawa,masu kira da masu ajiyemin sak'o na fatan alkhairi Ina godiya matuk'a da kaunar ku a gareni,domin ku ke k'aramin kwarin gwuiwa nagode kwarai*
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*
_Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_infection_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*08089965176*
*07084653262*
******
Sosai ya zauna yayi ta aikin lallashin ta kafin ma ta nuna ta sauko daga fushinta,
ta kuma nuna mishi cewar komai ya wuce koba komai ai tunda umarnin uwar shine ita ma zata tayashi ganin yayi ma uwar na shi biyayya, hakan da tayi ba kad'an ba ya k'ara kankaro mata mutunci a idanun shi.
Shi yayi mata jagora har zuwa gidan su domin dai tace bata kwana sai taje ta duba yanda mai jiki ta k'araji,
Hak'ik'a ta shayar da mutanen gidan matuk'ar mamakin ganin ta a wannan daren,
domin dai koda wasa babu wanda yayi tsammanin zuwan nata a wannan lokacin duba da dad'ewar da tayi bata zo d'in ba , ga kuma wani sabon salon sauyi da suka gani k'arara a wajen ta domin dai tunda ta iso ta aro wata sabuwar d'abi'a na ladabi ga kula nan² da takeyi akan uwar gida dama sauran jama'ar gidan abinda ya zame ma yan gidan bak'o dan ba halin ta bane damin sun sani cewar sau tari intaga dama ko zuwan tayi har tayi zaman ta ta koma ba lallai wani ya ganta ba amma yau duka sassan gidan saida ta shiga ta gaishe su har da tsaraba abunda bata tab'ayiba tsayin shekarun aurenta da Sarki kuwa! ,
Sai dai kuma duk wannan rawar jikin nata ko kusa ko alama y'a ranta dake gidan kaf d'insu babu wacce ta kusanci inda uwar tasu take, domin dai ko d'aukin da yaro kan nuna na ganin uwar daya dad'e bai ganta ba kwata² yaran nan basu nuna hakan ba domin koda uwar gida tace suje su gaida maman su daga bakin kofa sukayi tsaye babu wacce ta matsa inda take suka mik'a mata gaisuwar kuma sukayi komawar su kan harkokin su domin ko acan baya ma fa suke hannunta babu wata shak'uwa a tsakanin su balle kuma yanzun day suke nesa da juna.
Inda ace itad'in wata mai hankali ne tun daga yanda yaran data haifa da cikin ta suka wofantar da ita bayan tsayin lokacin da suka d'auka basu ga juna domin dai har an kai matakin dako ta shigo KD bata yarda Sarki yakai mata su a cewar ta bata son damuwa,
wanda kamata yayi ace a yanzun da suka ganta su rugo da gudu cike da murnar ganin ta su rungumeta, amma ina ita shashashar ko a jikin ta dan K'annin Sarki ma da suka ma yaran magana cewar "bazaku je kuyi hira da mamar kuba, cewa tayi a barsu itama bata son suzo su dameta tana tare da gajiya,
******
Washe gari da safe kasancewar a gidan ta kwana, duk a kokarin ta na nunama Sarki cewan tana buk'atar kusanci da *Dangin shi* sannan dan ta k'ara tabbatar mishi da cewar tafa canza ba Teemar daya sani a shekarun baya bane wanna,
Dan haka koda gari ya waye ma shigewa tayi cikin mutanen gidan aka cigaba da gudanar da abubuwa tare da ita sab'anin lokutan baya dako me za'ayi bata sanya kanta koda yaushe tana d'aki uwa wata sarauniya saboda tsabar jinkai da kuma kallon rainin da takema ahalin a ganinta tafi k'arfin shiga cikinsu sai dai ita su biyota.
Sai dai kuma hakan da tayi yad'an sanyaya Uwar gida domin a yanayin yanda suka ga ta sake dasu wannan karon sai suke ganin kamar dai ba'a kyauta mata ba gashi tazo ta cimma bak'i cike da gida ana ta shirin bikin auren mijin ta wanda alamu suka nuna cewar bata da masaniya akan hakan! Domin sun san inda tasan ko taron me akeyi a gidan tofa daba wannan maganar akeyi ba a yanzun.
Koda Uwar gida ta zaunar da ita tad'anyi mata yan nasihohi kafin ta shaida mata abunda ke faruwa, bata wani tada hankalin ta ba, illah ma nunawa da tayi ita bata da wani matsala da hakan, dan hakan ma k'arin arziki ne Allah dai ya basu zaman lafiya, da ita akayi ta shagalin biki domin tayi kokari matuka wajen danne wutar kishin dake ruruwa a cikin zuciyarta sosai kuma jama'ar gidan suka yaba da namijin kokarin ta harma da yawa daga cikin wad'anda suke adawa da ita fushin ta yad'an sauka a zukatan su, tunda ta ga an fara shirye² kawo amarya bayan magrib dan an shaida mata nan gidan za'a fara kawo yarinyar kafin a wuce da ita gidan ta,
Kwarai taso ta tsaya a karb'i yarinyar da ita sai dai kuma a yanda takejin zuciyarta na yunk'urin biyowa bakinta yayo waje tasan bazata iya jure cigaba da basarwar da takeyi a cikin mutane bayan zuciyarta tana konewa a cikiba, kai bama fa lallai ta iya jure wa wajen hana kanta wafto wuyan yarinyar nan da za'a gabatar mata a matsayin kishiyarta ba, in hakan ko ya faru ai itake da fad'uwa domin ginin data fara ginawa ne zai rushe tun bata tabbatar da ingancin shiba. Dan haka ta d'auki excuse cewar bata jin dad'in jikinta ta koma Hotel d'in data sauka tsabar kishin dake nukurkusar tane yasa zazzabi ya sauko yayi mata rubdugun da dole sai da Sarki yaje ya zauna da ita domin dama koba zazzabin ta kuduri aniyar cewa Sarki bazai kwana a gidan shiba balle kuma har su samu daman keb'ewa da amaryar shi a ranar, to can dai Sarki ya lalace dan sosai suka raya daren cike da soyayya domin dai wani sabon amarci sukayi a karo na biyu aka bar Meenal da kwana da nata kawayen.
***
Washe gari kuwa duk wani abunda ake gabatar ma wad'anda suke taya amarya kwana sai da aka gabatar ma su Meelat dashi kasancewar kuma abu ya zama unguwa guda yasa tunda gari ya waye sukaci gaba da amsar bak'i yan ganin d'aki,
A gidan Malam ko bak'i na nesa kuwa tuni suka fara komawa garuruwan su,
Ganin dai babu wani abunda ya canza domin dai bayan tabbatuwar aure gashi dai har an kawota gidan da koh a mafarki aka nuna mata shi a matsayin gidan mijin da zata rayu a cikin shi tofa saima ta tub'e kafin ta tattaro k'arfin da zata daku da duk ma wanda ya gabatar mata da hakan amma gashi wai a gaske hakan dai ya faru ba mafarkin da take ta tsammanin zata iya farkawa ko wani lokaci ba hakan yasa dole ta aro jarumta ta d'aura ma zuciyarta, to me yayi saura kuma hukuncin Malam nefa da dai ace wani daban ne ya d'auki nauyin shiryawa da gabatar wa ba shiba to da ta dage kwarai wajen nuna turjiyanta akan hakan dan tasan zata samu goyon baya daga Ma'am dan haka yanzun kam kuka ai bashi da amfani kuma sai dai ta zuba ido taga yanda rayuwa zataci gaba da juyawa, dan haka tuni ta hak'a rami acan k'ark'ashin zuciyarta ta bunne damuwarta harta da wacce ke kan fuskanta tayi kokarin maidashi ta aro ma kanta jarumta.
Sai dai kuma har yanzun shiru take bakin nan nata kam ya mutu murus sai idanuwa da take bin mutane da shi ko abokan wasan ta da ta saba jansu suyi ta raha wannan karan kam ba dama,
K'arin haushin kuma shine tun jiya da yamma taga an cire mata layukan ta dake cikin wayar ta sai fankon wayar aka bar mata, ita babban tashin hankalin ta shine so take taji wani hali dan gidan master yake ciki amma tasan hakan bazai yuwu ba domin dai ita ba jahila bace tasan hakkin dake rataye akan ta na auren wani yanzun, tana dai mishi fatan alkhairi Allah ya bashi wacce ta fita, tasan dai Allah ne kad'ai zai wanke ta akan kallon dazai dunga mata a matsayin wacce ta yaudare shi.
*Bayan kwana biyu*
Tun dai Meenal na zaman d'ar d'ar na jiran tsammanin shiga wata rayuwar sabuwa yanzun kam harta saba ,
domin dai yan biki duk sun koma gida jen su, domin dai zaman ta a wannan gida zamane na babu mai takura mata bamai sawa balle hanata domin dai abunda ransu ya raya musu shi sukeyi ita da kawayen ta, su dafa abunda suke muradin ci suci duk dakoh cewar kullum ana aiko mata da abinci daga gidan su Sarki dama nasu gidan amma indai su Moon sun shigo wajenta sai sun jata kitchen sun had'a wani abun wani lokacin ma har kusan 10 na dare sukan kai a gidan suna d'ebe mata kewa gari na wayewa kuma kannin Sarki ke shigowa suna tayata tsaftace gidan, dan haka sai kewar gidan su ya zama sauk'ak'ka a gareta domin tana samun masu shigowa dubata kuma kullum sai sunyi waya da sauran.
Allah ma ya taimake ta da yike ana hutu hakan yasa gaba d'aya bata da wata damuwa miji dai ba ganin shi takeyi ba balle ta tsan gwami kanta,
Shi dai ango tunda aka d'aura aure har yau Allah bai sa sunyi ido biyu dashi ba domin dai baya shigowa gidan in ma yana da bukatar wani abun da zai d'auka sai cikin dare ko kuma ya aiko Kwaro ya d'aukar mishi abinda yake bukata yana can ya b'oye fulawar shi a d'akin Hotel suna gwangwaje wa a filin wasa, dan jama'ar gidan su Sarkin ma har sunyi zaton ko ta koma ne babu sallama kamar yanda ta saba, sai dai ita a gefenta har yanzun bata saku kwarin gwuiwar da zata iya fuskantar amaryar nata bane, kwanciyar hankalin data k'ara samu kuwa ganin cewa gaba d'aya bataga d'aukin auren a wajen Sarki ba domin ko ya'ya ta d'auko zancen amaryar sai Sarki ya nuna baya bukatar zancen.
°°°°°°°
Zaune take akan kujerar 3sitter d'in dake cikin d'akin Hotel d'in da suka maida matsayin gida a yanzun,
A yayin da ta d'aura duka kafafuwan ta dake mik'e sambal akan center table d'in data jawo zuwa gaban kujerar wayar tace a hannun ta guda 1 tana latse² yayinda d'ayar hannun nata kuma take amfani dashi wajen tausa mishi gashin kanshi, kasancewar shi kwance yayi pillow da cinyoyinta sala² dake waje sai shek'i sukeyi wanda hakan ke nuna zallar hutu da fatar ke d'auke dashi sakama kon kasancewarta sanye cikin kananun kaya wato gajeren wando da wata shed'aniyar half vest wacce an dai satane kawai amma bawai dan ta rufe wani abuba,
Irin wadan nan shigar sune mafiya soyuwa a wajen sarki a duk sanda zai kasance tare da ita dan haka ita kuma tunda ta gane lagonshi ta rike mishi wuya