Showing 33001 words to 36000 words out of 174305 words
Chapter 12 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
***
Kira Anty kiji ko Ya Mashkur yazo gida"
cewar Meenat tana kallon Meelat, "kuma fa haka ne Allah yasa ma ya fita dan wallahi bana son muje gidan nan mu sameshi, dan wallahi yau duk abinda Nafi tamin ramawa zanyi" ta faɗa tana ciro wayar ta a jaka ta danna ma Aunty kira, wayar bata daɗe tana ringin ba Auntyn ta ɗauka, "Autar Aunty badai har kinyi kowata ba? ta fada muryarta cike da kewar ɗiyar tata, dariya Meelat ɗin tayi "Anty ina kwana"
Lafiya lau, ya kwanan mutanen gidan?
"Kowa lafiya lau Aunty dama na kirane in tambaya ko Ya mashkur ya shigo dan kinsan Meenat tace zamuje gidan yau"
To bai dai riga ya zo nan ɗinba, kardai kuje gidan ku zauna kinji koh Auta dakun gaisheta kubar mata gidan ta, ni dan ma kunki jin ta nawane da bazakuje ba"
Allah kuwa Anty bazamu daɗe ba zamu dawo bye" ta faɗa tana kashe wayar, hahaha tayi dariya tana kallon Meenat kinji Anty Allah bata son muje gidan nan kuma yau dai saidai tayi hakuri in mun dawo ma bata labarin yanda ta kaya.
"Ai wallahi Nafisan nan munafuka ce inta ganka a cikin mutane sai tayi ta maka fara'a kamar da gaske ta dunga fadin wai bama son zuwa gidanta bayan daka taka kafarka a gidan take canza fuska to yau dai gamu nan tafe gareki uwar Aslam kuma wallahi yau sai munci mun ture koya kukace? "
Ah kwarai kuwa Rabin rai fadi ki kara muda gidan Ya'yan mu ai dole mu sarara, duk wannan hirar da sukeyi suna kan tafiya ne sukeyin shi.
Wow tubarkhallah masha Allah gaskiya gidan nan ya wuce da kwatar zuciyata," Moon ta fada tana ɗaura hannun ta a kirji idanuwan ta a waje tana mai karema gidan kallo,
Gaskiya ba hassada nidai gidan nan yamin kyau ko a kasar waje sai haka,
Gaskiya indai irin gidan nan za'a kaini wallahi na shirya ayimini aure na hakura da karatun bokon"
Ta fada tana rungume Meenat cike da shauƙi, sororo Aishat ta tsaya tana kallon ikon Allah "ke Maimoon yaushe kika zama yar iska bani da labari dan ubanki daga ganin gida tun baki san meshi ba zaki wani ce kin shirya a miki aure! To shi mai gidan zaki aura kowa! "
Tafaɗa cike da takaicin Moon ɗin,
Inda kasan Meenat ta rufeta da duka haka takeji dan haka tayi kicin² da fuska dan abun yakai mata ko ina, ita ko Meelat inta kalli Moon saita koma ta maida kallon ta ga Moon sai kuma ta kyalkyale da dariya,
"Ke wai wani dariyar iskanci ne wannan kikeyi kamar wata taɓaɓɓiya ke kuma in baki rufemin baki da batun gidan nan ba kuka wuce muka tafi duk sai na muku rashin mutunci wallahi mtws koba gida ba kawai daga ganin gida dan hauka sai ki fara warwarewa kina sambatu"
Katseta Moon ɗin tayi da cewa "ke Meenat kiji tsoron Allah wallahi komin hassadar mutum yasan gidan nan ya gama haɗuwa, kinga fa yasin ko rantsuwa bazanyi ba nasan ginin mace gudane wannan gidan oh allah Allahumma Arzugni ya Allah" ta karasa addu'ar tana shafawa a fuskarta.
Ganin haukar na Moon da Meelat ba karewa zaiyi ba yasa fuuuu tayi gaba cike da takaici karo taci da mutum shi ya fito daga gidan cikin hanzari ita kuma adai dai lokacin burinta shine taga tabar kofar gidan, kanta ne ya bugi kirjin shi a take wayar hannun shi ta faɗi sai akan kafarta, "waiyi Allah Baba Malam za'a fasa maka kaina ta faɗa tana dafe goshin ta daya daki kirjin shi tana shirin yin kuka chak yayi tsaye yana binta da kallo dan gaba daya gabban jikin shi yaji sun sake.
"Ke karki sake kimin kuka a wajen nan" ya faɗa cikin muryar shi mai amo sosai ganin yanda tasa hannu tana mutsutsuka ido alamar gab take da fashewa da kuka.
"To bakai bane kawai ina tafiya na kashiga gabana ba waya sani ma ko goshina ya fashe"ta fada tana turo baki, "ai da yike kinsan da dutse kikayi karo dazai fasa miki goshin koh, come on duƙa ki mikomin wayata da kika yar min kuma tana fashewa sai kin biyani"
Dukawa tayi badan taso ba ta dauko wayar dake gefen kafarta ta mika mishi ba tareda ta ɗaga kai ta kalle shiba, karbar wayar yayi ya dudduba ta cikin sa'a dai wayar bata fashe ba, "Allah yasoki da sai kin koma gida kin faso asusunki kin gyaramin wayata, ba tareda tace komai ba ta ɗaga kafarta da niyyar tafiya cikin zuciyarta koh ba kalar kunkunin da batayi ba, daga kafarta yayi dai² da buɗe makeken gate ɗin gidan da akayi wata motar hilux ta fito daga cikin gidan ashe ba iya motar bane kadai harda waɗan nan sheggun karnukan nashi masu kama da zakuna a bayan motar fit haka karnukan nan da gudu kamar an korosu suna haushin su na rashin dalili,
Lura da fitowar karnukan da yayi yasa shi juyawa cikin zafin nama da niyyar ya kamota dan yasan yanda take jin tsoron su, aiko juyawar da zaiyi sai jinta yayi a cikin jikin shi ta wani irin rukun kume shi kamar wacce ke shirin komawa cikin jikin shi tama kasa ihun data saba na neman ceto duk sanda ta gansu sai ma numfashin ta da take wani irin jan shi da kyar, jikin ta ko babu inda baya rawa sai faman kara kankame shi take, ga kuma karnukan da suka kewaye su sukayi tsaitaye suna dararo harshen su ganin uban gidan su tsaye a kofar gidan,
Zuwan da tayi ta faɗa cikin jikin shi ba tareda tsammani ba yasa harta da fatar bakin shi yaji sun mishi wani irin nauyin daya kasa motsa su,
Sai ma runtse idon shi da yayi yana jin yanda take kara shigewa jikin shi tana gogga mishi abubuwan dake kirjin ta waɗanda suke karasa jinin shi yana kara daskarewa, duk yanda yaso ya cireta a cikin jikin shi abun ya faskara dan gani take da zarar ya cireta a jikin shin to karnukan shi zai mikama ita suyi kalacin hantsi dan haka taki yarda ta fita a jikin shi,
Da kyar ya samu ya buɗe bakin shi "ki nutsu mana baki ganin suma sun nutsu, sakeni ki gani bazasu miki komai ba"
Girgiza kanta tayi alamun bazata sake shi ɗin ba karamin murmushi yayi "oh dadin kwanciyar kikeji a jikin nawa kenan da kike ta wani kara kankame ni"
Dan ɗago kanta kaɗan tayi domin ta tantance shin wai a jikin nashi taken kamar yanda yace ɗin?
wani irin kunya neya kamata dayasa fita daga cikin jikin nashi babu shiri tana duddukar dakai gefen shi ta koma bayan ta kama hannun shi ta rike gam,
To kace musu su koma ciki nidai tsoron su nikeji ance suna cin naman mutane"
Kur yama fuskarta yana kallon yanda take motsa labban ta tana magana a shagwaban ce,
"Kaji" tace ganin yayi shiru kuma bai kora karnukan nashi zuwa gidan kamar yanda ta bukata ba sai ma zagaye su da karnukan sukeyi suna kaɗa bindi, kara manne wa da jikin shi tayi a sanda wata karya tazo dab da kafarta tayi kwance, "waiyo Allah dan Allah ka koreta ai kaga dai wallahi bada gangan nayi karo dakai har wayar ka ta faɗi ba Allah da nasan ma kana gidan nan da bance mu biyo tanan ba"
Alama yayi ma karnukan dasu wuce cikin gidan ganin yanda har yanzun jikinta bai daina rawa ba, "ki natsu nace wai me yasa kin cika tsoro ne Ameenatu"
Dago kanta tayi cike da mamaki take kallon shi dan tsawon rayuwarta bata taɓa sanin wai yasan sunan ta ba dan koda wasa bata taɓa jin ya kira sunan taba sai yau,
"Kibar kallo na Malama"
"To kaima ba tun ɗazun kaketa kallona kuma bance komai ba ta faɗa tana juyar da kanta gefe "ina su Moon? Ta fada a bayyane tana juyawa dan sai yanzun take tuna cewa ba ita kadai ta fito gida ba, can ta hango su a baya sunyi carko² duk da halin tsoron itama ba gama sakin ta yayi ba amma wallahi sun bata dariyar yanda sukayi tsamo² kamar waɗanda ruwa ya daka aiko sai ta kyalkyale da dariya, daga kai yayi shima yabi inda take kallo da ido dan yaga dalilin dariyar nata, ɗan murmushi yayi dan shima sun bashi dariyar saima girziza kai da yayi yana ci gaba da binta da kallon "Ya Sufyaan kalle su kagani dan Allah matsorata dasu kawai"
"Ai garasu tunda nasu tsoron baisa sun rungume wani sun tada mishi tarxoma ba"
Na'am tace tana kallon shi, shareta yayi "ina zaku ne ma wai?
Ku me yasa bakwa gajiya da yawo ne? "
Bafa yawo zamu ba gidan Ya Mashkur ɗin su Meelat zamuje'
Kara sowa su Maimoon sukayi "Ina kwana" suka hada baki wajen mika gaisuwar su gareshi "lafiya" yace a takaice juyawa cikin gidan yayi ya fasa fitar da yayi niyya dan yarinyar nan ta rusa mishi tsari kuma.
#karku manta dan Allah kusa Sister ɗina a addu'a, Allah ya baki lafiya Fauzy
#Share and Comment
#Ummiee~Zaria[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*
*👨👩👧👦DANGINA!👨👩👧👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_
ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._
*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}
*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne gareku mutanen gidan uwata Mai Dambu, most especially Oum Khadija💙, NAgode sosai da comment
*Surayyahms*
*Binta Umar Abbale*
Nagode da kulawa.
```Page11
Ba ita ta dena binshi da kallo ba har sai sanda ya kulle ta dena ganin shi tukun,doguwar ajiyar zuciya ta sauke tana mai maida dubanta zuwaga su Moon katuwar hararar tabi dukan su dashi tana mai cewa "ai wallahi kulli yaci amanar koko daga yau daga yanzun ɗin nan nasan zamana daku, shine dan cin amana kuka barni a gaba wato ashe ma tsayuwa kukaci gaba dayi kuna gulma,yanzun fisabilillah da Ya Sarki baya wajen nan fa haka karnukan nan zasuyi partyn kalacin hantsi da nama a wajen nan,gaskiya dai Allah ya isana,"
Meelat na danne dariyar da takeyi kasa² gudun kar Meenal ta gani ta dangwalo ma kanta wani jangwal ɗin tace "haba kawata kema kinsan bazamu miki haka ba,kuma ma waye a cikin mu yayi zaton karnukan suna gidan nan tunda mun san ba anan ake ajiye suba,kuma karon ki da Sarki ai naga laifin kine tunda ke kika kai mishi karo kika gaure shi koh? ta karasa faɗa tana kallon su Aisha "eh wallahi mu bamu san kinyi nisa bama",
" Yauwa kinji koh kuma ba gashi yauma Sarki ya kara cecenki a hannun karnukan shiba".
"Dallah yimin shiru ai wallahi nasan dake ce sai kinyi fitsari a wando da shegen tsoron kin nan,"
cigaba da tafiya sukayi ba tareda wata a cikin su ta kara cewa komai ba dan sunga alamar mutuniyar nasu fa ta shaƙa da yawa.
can dai Moon ta kasa daurewa tace "Bebs tsakanin ku da Allah gayen nan bai burgeku ba? kuma fa kamar mutumin da yasa aka rakamu gida jiya koh? duk da dai jiyan ba wani ƙare mishi kallo nayi ba dan Allah shike da gidan nan koh? Oh ya rabbi yau dai inga a sa'a na tashi shi yasa nike ta gane² nidai wallahi ya burgeni,ku baku gani ba duk tsayin Meenal fa wallahi nidai gani nayi kamar a iya kugun shi ta tsaya,oh Allah yau she za'a aurar damu ne kar maza masu kyau su gama karewa a barmu da kwarababbu masu kama da mata"
Takalmin dake kafar Meenal ta cire ta fara bin Moon ɗin dashi tana son lallai saita bugeta,faɗi take cewa "badai kin zama yar iskaba zaman lagos ya lalata ki kema kin iskance,to yasin duk ki gama iskancin ki ki ɗauka cewa kinyi shuka a idon makarwa ne domin kamar a kunnen Hajiya maganar nan"
ta karasa faɗa tana dafa Aisha da yau mamakin Moon itama yake ta neman kasheta wai Moon ce take ta maganganu haka kamar wata wacce tasha kwaya, so take tajawo musu bala'in daba iya kanta zai tsayaba dan dukan su zai shafa in yayyen su maza sukaji batun nan karma Iliya ɗan mai karfi yaji labari tasan shi kenan su kuma sun tashi aiki.
Cike da nishaɗi Moon tace" wai ke ƴar Malam miye matsalar ki shikenan mutum inyaga abu ya burgeshi bazai faɗa ba,to wallahi nikam na fada na kara gidan damai gidan duk sun burgeni,Allah da ace na isa aurema cewa zanyi ina son shi to miye a ciki".
Itafa tsakanin ta da Allah bata ɗauki hakan a bakin komai ba.
"Innalillahi wa'ainnah ilaihir'raju'un kai jama'a yau kuma boyayyun aljannu ne ke shirin bayyana a jikin yarinyar nan ne koya?
" Ke yana da mata fa" cewar Meelat dan ita Meenal ai nihin yau ne taga abunda ya isheta dan haka da ido kawai take bin Moon ɗin,.
"And so sai me dan yana da mata sai inƙi son shi kome?ko akwai inda aka rubuta kar aso mai mata ne?
Na rantse da Allah in bazaku zo mu tafi ba zanyi komawa ta gida ban son iskanci,ke dan makiyin ubanki har kike wani cewa miye dan kince kina son shi,to ai baida damuwa ko yanzun kina iya shiga ki faɗa mishi cewa kina son nashi,ai da nasan cewa iskancin Lagos jinin mutane yake bi dako ke bazan dunga sakar miki fuska ba iskancin banza mutumin dako dariya baya yi kullum fuskar shi a ɗaure shine zaki wani ce kina so tirr wallahi kin dai faɗi kasa ba nauyi wallahi,duk inda zai shiga fa haka zakiga yaran shi na binshi shine zaki wani ce kina so to sai kije kiyi ta kaya ai,shin zakuzo ku wuce ne ko tsayawa zakuci gaba dayi kuna kallon bakina".
Easy mana Meenal wannan zafin da kika ɗauka ai yayi yawa miye laifin ta dan ta faɗi abunda ke cikin zuciyar ta,ke shike nan dan baya burgeki sai kice kar wata ta gani ta yaba kuma"cewar Meelat bayan ta rike hannun Meenal suna cigaba da tafiya.
Wai halan ya kuke dashi ne Meenal? Aisha ta tambaya.
Hahaha yan mata ai inda Meenal ce bata faɗa miki, bari dai mu karasa gidan ya Mashkur sai in baku labarin ko waye shi Sarki kenan Mai Zamani kuma shi ɗin ɗan adawar Kawata ne shi yasa nima baya burgeni,
Ah ah wallahi bamu musha tun dazafin shi,dan daga ganin gidan nan kowa yasan bana karamin mutum bane gida kamar a turai aka kerashi aka ɗauko aka kawo nan aka ajiye,
"wallahi nayi mamaki da naji wai shike da gidan nan ashe dai warrgajejen mai kuɗi ne"cewar Aisha.
"Eh wallahi nima nayi mamaki" itama Moon ta faɗa,"to ai mun kawo gidan ku bari dai mu shiga ciki mu zauna kusha labari.
A farfajiyar gidan suka haɗe da Ya Mashkur yana shirin shiga cikin motar shi cikin shirin fita,"ah ah yan matan Aunty ai nayi zaton ko kun fasa zuwa ne shi yasa nace bari in fice kunsan Aunty na jirana,karasawa kusa dashi sukayi suna gaidashi bayan ya amsa ne ya kara cewa "zaku jirani in dawo kafin ku wuce koh? Dan matar gidan ma bata nan amma nasan itama bazata jima ba,ku shiga daga ciki mana"
Ya Mashkur meka ajiye mana? cewar Meelat.
"Ai kunsan nidai ba mace bace balle kusa ran in shiga kitchen in muku girki kamar wani ɗan daudu Sarah na nan a ciki taji daku komai kuke bukata akwai a store you can serve your self."
Ya karasa fada yana shigewa cikin motar shi gamida bata wuta yayin da mai gadin shi ya buɗe mishi gate ya fice,
Huhhuu lallai yau zamuci karen mu babu babbaka a gidan nan tunda matar gidan bata nan"cewar Meelat cikin farin ciki dan ba karamin daɗin hakan taji ba dan tasan in matar gidan nanan bazata barsu su wala yanda suke soba dan karamin aikin tane ko ruwan gidan taga damar ta hanasu in sunyi magana tace fita unguwa zatayi.
To yane Bebs let's get inside" ta faɗa tana musu jagora zuwa cikin gidan ko iso basu nema ba kai tsaye sunayin sallama suka shige cikin falon gidan.
Sarah!
Sarah!!
Sarah kina ina yau gamu a gidan ku" da hanzari wacce Meenal ta kira da suna Sarah ta fito tana washe baki cike da jin daɗi tace "wai wasa ko gaske dan Allah ku ɗin ne dai nike gani kai gaskiya kun min bazata,ku zauna mana sannun ku da zuwa kai gaskiya naji dadin zuwan ku wallahi" haka ta dunga nan nan dasu cike da farin