Showing 108001 words to 111000 words out of 174305 words
Chapter 37 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
sanyaye,
A hankali kuma sai kiran da su Baba Usman sukayi mata a safiyar jiya da maganganun da suka fad'a mata da kuma yanda tun shigowar su unguwan mutanen gidan da sukayi ta kiranta da suna amarya harda ma zuwan su falon Malam dama komai daya faru ya dawo mata tsaf cikin kanta,
Aiko babu shiri ta kwalla wata uwar kara wanda da ace d'akin da suke ciki ba irin ginin nan bane dake rike sauti babu abunda zai hana sauran jama'ar cikin gidan jiyo karar data yi.
"Innalillahi da gaske ne! da gaske ne!! da gaskene aure za'amin yau,
Waiyo Allah na shiga uku za'amin auren dole
*Bari muje a gurguje*⚜️🔱👨👩👧👦 *DANGINA! * 🔱⚜️👨👩👧👦
''''''Page 31
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*
_Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_nfection_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*08089965176*
*07084653262*
**************31
Farouq Malam ya kira ya d'auke ta zuwa wajen Mommy Hauwa, yasani daman cewar bazasu kwasa ta dad'iba hakan nema yasa yayi ma Dr Mubarak magana, shi ya bashi maganin baccin daya zuba mata a cikin ruwa tasha domin in har ba hakan yayi ba yasan ba lallai bane ta iya kwantar da hankalin ta balle harta samu yin bacci ayau, yasan koda Allah yakai rai gobe ba zatayi bori sosai ba.
A ranar da Meenal ta baro Gidan Hajiya shi kuma Sarki da Abokan shi suka isa gidan domin ganawa da ita, kamar yanda Uwar gida ta bashi umarnin zuwa ya gana da ita, Sanin cewar har zuwa wannan lokacin bata san da zancen auren ba kuma zuwan nashi na iya haifar da wani abun hakan ne yasa Hajiya ta ha'da Meenal d'in da iyayen ta mata suka wuce da wuri domin sosai Hajiya ta shirya tarban angon Takwarar nata a cewar ta dole ta gindaya mishi dokar da mudun ya takata zata wanke kafafuwar ta taje har inda yake ta karta mishi rashin daraja, dan karma yaga an d'auki jikarta an bashi yayi zaton ko sun gaji da ita ne.
Misalin karfe 1 saura su Sarki suka isa kofar gidan koda suka isa an fara kiran Sallah a masallacin dake kofar gidan dan haka basu shiga ciki ba har saida suka gabatar da farali tukun,
Bayan sun idar da sallah a kofar gidan bakin gate sukaja burki domin neman wanda zai musu iso zuwa cikin gidan kasancewar su na bak'i bazai yuwu su wuce ciki kai tsaye ba.
Fitowar Yusuf wase daga masallaci kenan yazo da niyyar shiga ciki Kwaro ya mishi sallama.
"Bawan Allah kamar cikin gidan nan zaka shiga koh? " ya tambaya bayan sun gama gaisawa dasu Sarki.
"Eh ciki zan shiga"
"Alhamdulillah tazo mana gidan sauk'i kenan, mu bak'ine ko kuma a tak'aice dai ince sirikin gidan ne yazo gaisuwa, inba damuwa zamu so kayi mana iso zuwa ciki duk da dai an san da zuwan namu amma kaga ai bai kyautu mu shiga kai tsaye ba! "
"Ba damuwa kuna iya shigowa ai"
Rufa mishi baya sukayi zuwa farfajiyar gidan, ganin cewa sunce su sirikan gidan ne yasa shi yanke shawarar kai su falon Hajiya tunda itace uwar kowa a gidan. Sai da suka karasa gab da falon sannan ya juyo garesu "bari in shiga in isar musu da sak'on isowar naku koh? "
"Ba damuwa muna jira anan" suka bashi amsa shi kuma yasa kai cikin falon.
Da sallama ya shiga, ya kumayi sa'ar samun Hajiya da iyalanta maza dukan su zaune a falon,
"Karaso daga ciki mana yusufa, ga wajen zama ai kadai zauna koh? ga kuma abinci duka in kana da bukata"
"Nagode Hajiya dama bak'i ne akayi suka buk'aci inyi musu iso, sunce sirikan gidan ne gasu a nan bakin kofa"
"To Allah ya musu isowa kenan barkan su da zuwa to ai ce musu su shigo kawai dan dama zaman nan daka gani zaman jiran zuwan su akeyi"
Ta fad'a tana jawo mayafin ta dake gefen ta ta rufe jikinta dashi,
"Larai! Ke larai!! Waini anya Larai basai na dangana ki da asibitin kurame ba kuwa? Jama'a kayi ta ihu kana kiran sunan mutum kamar wanda yake cikin rijiya nan da kitchen ace mutum baiji kira ba, ah ² wallahi wankin kunne zan kaiki a miki waya sani ko dattin kunne ne yasa bakijin magana sai anyi ta miki ihu duk kisa makwogoron mutum ya tsatsage wajen d'aga murya"
"Ayi hakuri hajiya ina ta baya ne" Larai ta fad'i hakan a yayin da ta iso falon, "to ai sanin hali yafi sanin kama yar'nan yanzun dai fito da abubuwan da aka tanadar na taron bak'i domin gasu nan sun iso atoh kar suce sunzo gidan surukai ba'atare su da komai ba"
Tana rufe bakin ta bak'in suka fara sallama su uku ne sai Sarki angon cikon na hud'un su.
Bayan gaisuwa da yan tambayoyi dasu Baba Usman sukayi ma Sarki duk Hajiya na zaune tana karema Sarki kallo dan tunda abokanan shi suka gabatar dashi a matsayin Mijin takwarar ta take mishi kallon ciki da waje.
Jin sun fara sallama zasu wuce yasata dakatar dasu da cewa "Nace ba! "
Juyowa sukayi suna sauraron ta.
"Ku d'an bani Aron abokin naku na yan mintoci",
Ba damuwa Hajiya suka amsa dashi a yayin da suke ficewa, maida kallon ta kan su Baba Usman tayi "kuma ku bani waje sirri nike son yi da mijin takwara ta"
"To Hajiya" suka had'a baki wajen fad'a duk da basu so hakan ba dan suna gudun kartayi wani maganar daba ita kenan ba domin dai ko d'azun nan babu abunda ta mance bata fad'a ba akan shiga hakkin jikarta da akayi wajen yi mata auren wuri, amma haka nan dukan su suka fice suka bar mata falon ta suna fatan Allah yasa kartayi katobara.
"Kace sunan ka Sufyan ko? "
"Eh Hajiya Sunan kenan Sufyan Sulaiman Ladan"
"Masha Allah, sunce min matar ka d'aya da yara 4 koh? "
"Eh haka ne"
"To dama so nike in tambaye ka inji ya zaman naku zai kasance duba da cewar aikin ka a KD yake ita kuma uwar gidan ka ance tana can Lagos itama yanayin aikin tane ya hanata dawowa nan ta zauna a kusa da kai koh? "
"Eh Hajiya a Kaduna aikina yake a yanzun duk da dai yanayin aikin yakan d'aukeni zuwa wasu state d'in inje inyi kwanaki ko wata ma haka, kuma itama iyalin nawa kamar yanda aka fad'a miki yanayin aikin tane yasa bata dawo nan d'in ba amma in ta samu hutu takan zo nan d'in nima kuma duk karshen wata a can nike yin shi"
"Da kyau to dama abunda yasa na tambaya dan inji ainihin inda zaka ajiyemin jikane, anan Zaria ne ko a Kaduna inda kake aiki? "
" anan zata zauna Hajiya saboda a can d'in cikin barracks nike zaune kuma gaskiya ni bana da ra'ayin ajiye iyalina a cikin bariki dan haka nan zata zauna ni kuma zanyi kokarin in ringa zuwa dubata duk sanda na samu lokaci"
"To hakan ma ba laifi, Sai dai kuma gashi gidan ka na nan d'in daka ce jikata zata zauna naga gidan ginin zaman mace guda ne gashi kuma kace ita uwar gidan naka takan zo maka hutu nan, to yanzun daka ke shirin auren jikata ita kuma matar taka idan tazo a ina zaka sauketa kenan? Dan dai rashin adalcine kace zaka sauke ta a gidan da jikata take ciki! "
Sai da ya nisa dan Wallahi wadan nan tambayoyin da tsohuwar nan ke mishi sun fara hawa mishi kai, to fisabilillahi ina ruwanta da sha'anin gidan shi, inace dai gidan nan nashi ne koba matar shi ta aure ba yana da damar da zai sauke duk wanda yake so a gidan balle kuma matar shi da daman saboda ita ya gina gidan, amma dai dan su rabu lafiya sai ya amsa mata da cewa.
"Eh ai da yike ita Fateemah ko tazo a KD can tare dani take zama kota shigo nan d'in ba zama takeyi ba"
"Eh ba shakka to aini dai daman saboda gudun abunda ka iya tada wani fitinar a gaba nikeyi, koba komai dai kaga ita takwara ta bata da iko da gidan ka dake can lagos, na kaduna kuma tunda ka nuna baka bukatar matan ka su zauna a wajen nasan ba zaka d'auketa ka kai can ba, shine dama yasa nake so ince tunda abun haka ne karfa wata rana ita uwar gidan ka tazo nan kace zaka sauke ta anan inda jikata gudun wani abun ya biyo baya kaga ai gara ayima kowa adalci koh? Saboda a samu zaman lafiya kaga dai ita wannan karamar yarinya ce domin dai a haife wallahi tsaf nasan ka haife wacce ta fita, in ma banda had'in dangi ai nasan ko kai ido da kunya ma ka kalleta kace kana so balle ayi zancen aure, to karamar yarinya ce fa wacce dai dududu bata wuce 17 ba Inma fa takai kenan, sai kuma abu na gaba"
Ta fada tana mai mashi kallon ido cikin ido duk dashi d'in yana ta k'ok'arin yanda zai cire nashi idon a cikin nata a matsayin ta na kakar matar da ake shirin aura mishi.
"To dai rokon ka zanyi ko kuma ince alfarma zan nema, wato kaga dai ita yarinya nan wallahi kankanuwar yarinya ce in ma dai banda cewa yaran yanzun suna da kufan jiki wama zai kalleta yace ya kalli mace! To nidai dan Allah karkaga tayi saurin girman nan ko ina a ciccike kayi zaton wata uwar mata ne wallahi ba iyawa zatayi dakai ba, dalilin hakan nema yasa nace bari in roki arziki dan Allah ka daure ka d'auke idanuwan ka akan ta ka bari harta k'ara girma tayi kwarin da zata iya d'aukar dawainiyar ka kafin kace zaka haike mata dan nasan ku maza baku iya kawaici ta wannan gefen ba, ita kuma kaga yarinya ce karama zuwa d'aya zaka mata ka tasheta a aiki,karshen ta in an sab'a number kaji ana fad'in wacce ai auren wuri ne yayi sanadin data kamu da yoyon fitsari, to kaga to tunda har Allah ma yasa kana da wata matar inaga Ai komai zaizo da sauki ko? Ina fatan ka fahimci abunda nike magana akai domin dai magana na gaskiya bari in maka b'aro² yarinyar nan fa bason auren nan take ba ubanta Malam shine ya shirya ya kuma gabatar da komai ba tareda yayi shawara da kowa ba, harta ninan dana haifi uwar ta dama ita kanta uwar nata bamu samu labari ba saida ya riga ya zartar da komai in fad'a maka karewa ma hatta dai ita amaryar taka yanzun haka da nike magana dakai a matsayin gobe za'a daura mata aure tofa labarin auren bai kaiga isa kunnen taba, dalilin ma da yasa baka sameta a gidan nan ba kenan dan zuwan naka na iya sanyawa ta hasaso wani abun"
Yau dai Sarki shi yake ganin ikon Allah jama'a to wai ita matar nan bata san cewa ba iya jikarta ce kad'ai akama dole a batun auren nan ba harta shi da girman shi da komai biyayya kawai zaiyi ma uwar shi domin yaga sun rabu lafiya yasa dole ya amshi auren badan yana bukata ba!
Shine tun ba'a daura ba har an fara kafa mishi dokoki, shi aiko shaye shaye yakeyi to ba kana nan kayan maye zaisha wanda har zai iya kaishi ga kusantar yarinyar nan ba, balle kuma shi rabon shi da zuke² ai tun lokacin da bai san ciwon kan shiba, dan Allah jama'a Inma yace zaijema yarinyar nan a matsayin miji ai zalinta kawai zaici hakan kuma ai shi gani yake bama karamin zunubi bane, yarinyar dakoh autar su ta girme mata sosai, yaso ya d'aga ido ya kalli Hajiya yace mata ke Hajiya nima fa auren nan ba dan ina so ake shirin daura min shiba, kamar dai jikar ki nima auren biyayya zanyi, amma ina bazai iyaba dan sa'insa da babba ba dabi'ar shi bace balle kuma su Sojoji da aka san su da biyayya komai sai dai suce *yes sir*
Dan haka sai ya k'ara dukar dakan shi kasa yana mai amsa mata da cewa.
"Hajiya insha Allah zanyi kokarin kula da ita bazan cutar da itaba koba komai ita d'in kanwata ce dan haka zan kula da ita kamar yanda zan kula da kannena ko kuma yarana na cikina"
"Kai madallah madallah kaji Allah dai yasanya Albarkha da alkhairi a wannan aure ya kuma baku zaman lafiya, to abu na karshe da banyi magana akan shiba shine batun karatun ta nasan ba lallai iyayen ta su tada maganar ba, amma ka sani tana da burin ganin ta zama likita kamar mahaifiyarta, kuma ni nayi mata alkawarin dafa mata wajen ganin cikar burin ta, nagode Allah kuma da yasa kaima mijin nata ba mazauni bane kaga hakan zai bata damar da zatayi karatun ta a tsanake cikin kwanciyar hankali, dan haka da zarar jarabawar su ta fito za'anema mata admission taci gaba da karatun ta ina fatan bazaka hana ba"
Ta karasa fad'a tana kallon shi dan so take ta fahimci shin zai amince ko k'ak'a,
"Ba damuwa insha Allah domin nima nasan dad'in karatu dan haka bazan tauyeta wajen hanata cikar burin taba".
"To Alhamdulillah yanzun kam kana iya zuwa ka samu abokan ka ku wuce Allah yasa ayi taron biki lafiya, a kuma daure a gunda yin Addu'a da yawan sadaka maganin bala'i dan makiya da mahassada ako ina suna nan wasu ma tare ake bacci dasu ayi tayin azkar ba gajiyawa kaji"
"Insha Allah za'a kiyaye Hajiya Nagode Allah ya kara lafiya da nisan kwana"
"Ameen ameen Allah ya muku albarkha muje in taka maka dan dama zuwan kune yasa ban fita ba nima aminyata ke aurar da jikanta matar da kanin ka Sa'eed dan wajen Malam zai aura kasan jikar Aminiya ta ce can nike son lekawa tunda nidai nan ba taron komai zanyi ba duk matan gidan suna can sun kwasa sun tafi unguwar naku"
A bakin kofa tayi karo da kwalayen su drinks da buhu nan kayan abinci, Larai ta kwalama kira tana tambayan wannan kayan kuma daga ina ya fito aka ajiye mata su a bakin kofa?
"Bak'inne suka kawo Hajiya" Larai ta bata amsa, "shine tun tuni baki sanar dani ba har saida suke shirin tafiya, fisabilillahi ai sai ki sanar dani inyi musu godiya koh, irin wannan dawainiya haka"
Ita dai Larai komawa ciki tayi tabar ta.
*WASHE GARI*
Meenal bata samu damar tashi ba har sai zuwa karfe 12 na rana kasancewar Mommy Hauwa tasan tana al'adah hakan yasa bata damu kanta wajen ganin ta tashin ba sai dai lokaci lokaci takan duba yanayin numfashin ta,
A yayinda ta farka abubuwan da suka faru a daren jiyane suka fara dawo mata amma sai take ganin inah wannan ai sharrin mafarki ne dan a mafarki ne kawai kake ganin abubuwan da kaima kasan ba lallai bane su auku a zahiri ba,ta ina ma wai ita za'ace za'ayi auren ta har a gama komai bata da labari bayan kullum cikin lallab'a d'an gidan master daya damu kanshi dason turo iyayen shi gidan su take yi akan ya bari tukun har sai zuwa gaba, shine kawai shirmen mafarki zaice wai za'a mata aure da wani. dan haka ma ta watsar da tunanin ta tashi ta shige cikin bayi domin dai a jikin ta takejin yanda pad din dake jikin ta ya jike sosai.
Lekowar da mommy Hauwa ta k'arayi a karo na ba adadi ne ganin bata a gadon da take kwance kamar ko yaushe hakan yasa tasan ta farka kenan,
Kayan data ware domin Meenal din tayi amfani dashi ayau ta d'auko ta ajiye mata shi akan gadon dama duk wani abunda tasan zata buk'ata,
Babu jimawa Meenal ta fito,
"Mommy ina kwana" "lafiya lau Meenal kin tashi lafiya?"
"Lafiya lau " ta amsa dashi tana karasowa inda mommy ke zaune sai da ta jingina kanta da jikin Momin sannan tace "yunwa nikeji wallahi kamar wacce tayi sati bataci komai ba"
"Tashi kisa kaya to sai in had'o miki abun karin"
Harta