Showing 126001 words to 129000 words out of 174305 words

Chapter 43 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1905

kanki,
ya kike kema da naki ciwon marar koda yake yanzun kam banji kina yawan kuka dashi ba! D alama ya dai tafi kenan?"

"Bai tafi bafa amma dai ya rage sosai ba kamar da can baya ba"

"To ya mai gidan naki dama wajen ita kishiyar naki duk dai kowa lafiya koh?"

"Shi dai nasan Lafiya lau yake dan d'azun ma dana kira shi nace mishi zanzo duba ki banji wani alamun ciwo a tare dashi ba dan shima ya shigo garin jiya da dare"

"To shi kuma haka akeyi? Kalar nashi rayuwar kenan da bazai zo ya duba kakar matar shiba? Ko baki fad'a mishi bani da lafiya ba ai yaci ace yazo ya dubani, Rabon shi da gidan nan fa tun ana saura kwana biyu auren ku!,
Shin wai ma wani irin zama kukeyi ke da shi ne takwara? ,
ya kamata ace zuwa yanzun dai kema ki fara laulayin nan da mata keyi in sun d'auki ciki,
amma shiru nikeji har yanzun ba labari ga k'annin ki ma da ake zaton cewa basu isa auren ba duk sun haihu,
Kodai akwai wani abu a k'asane wanda bamu da masaniya akan shi?"

Shiru Meenal tayi ba amsa, to jama'a fisabilillahi wani amsa zata bata, ah ah wallah ita kam ba'ajin mutuwar Sarki a bakin ta.

"Shirun nan naki shike k'ara tabbatar min da cewa har yanzun dai baki amshi auren ba kenan?"

Da sauri ta amsa Hajiya da cewa...
"Ah ah Hajiya ni wallahi ba laifina bane, kuma da ban amshi auren ba ai bazanyi ta zama har yanzun a gidan ba shekara biyu fa da watanni yanzun.... "

Katseta Hajiya tayi da cewa
"Kenan laifin shine tunda kince ba naki ba?"
Shiru tayi bata cema Hajiyar komai ba,

"Wai shin yama tab'a neman ki a shimfid'a kuwa?"

Innalillahi jama'a wannan wani irin magana ne,
Wani irin kunya ne ya sauko daga sama ya lullubeta kai Hajiya miye kuma na zakule zakule fisabilillahi.

"Ina magana dake kina wani duddukar min da kai uwa kwarton da aka ritsa a d'akin sabuwar amaryar da ango bai kwana da ita ba,
Nace kun tab'a had'a shimfid'a tun bayan auren ko a'a? In kuma so kike in fito miki a mutum ta yanda zaki gane to!
Ina magana ne akan kwanciyar aure tsakanin miji da mata nasan kin san wannan, shi mijin naki ya tab'a neman ki kun raya sunnar ma'aiki ko a'ah? Dan ya kamata in sani.
Ina tambaya ne saboda insan ta inda zan kamo bakin zaren, kinga in ma bashi da lafiya ne mu sani dan mu d'auki mataki, koda yake Ina mara lafiya zai haife yara har Biyar,
Shin ko kuma dai kece kikayi wani siddabarun dazai hanaki d'aukar cikin dan karki haihu tun yanzun?"
Ta karashe tambayar tana tsatsare Meenal d'in da idanuwan ta.

"Ni wallahi banyi komai dan kar inyi ciki ba, to bama sai an kwanta da miji bane akeyin cikin ni kuma ai har yanzun bamu tab'a kwana d'aki daya ba, haka ma fa kwanaki Uwar gida tazo tana tambayan wai in Ina shan wani abune dan Allah in dena karya bani matsala zuwa gaba, bayan ni bana shan komai, maganin ciwon marana mafa yanzun bana shan shi kuma tunda ciwon ya ragu"

"Iyee.. "
Hajiya ta furta da k'arfi cike da mamaki tana dafe k'irjinta da duka hannayen ta,
Kafin ta koma salati da sallallami tana tafa hannuwa,
"La'ilah ha illah lahu muhammadur Rasoulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam, oh ni Ameenatu yan ninaga abunda yafi zare tsayi, Innalillahi wa'innah ilairir raju'un, "

Hannun ta ta maida kan habarta ta tallafe cike da jimami, can kuma tace,

"Anya kuwa jama'ah? Ah wallah babu lafiya a wannan harka, um umm aure shekara biyu da watan ni babu ci gaba, wani irin rashin rabone wannan a wanke maka karamar yarinya mai jini a jika a kaimaka amma ace miji ya zuba mata ido tsayin lokaci babu abunda ya shiga tsakani"

Sai kuma ta koma kan Meenal.
"Ke takwara kiji tsoron Allah ki fad'amin gaskiya, karki sa in fara tsine mishi alhalin bashi da alhaki!
Ya'ya za'a daura miki aura miki shekara biyu da yan watanni kina zaune a gidan mijin nan kuma duk bayan lokaci yana zuwa kuyi rayuwa a gida d'aya harna tsayin kwanakin dazai d'auka kafin ya koma ace babu wani abunda ya gifta a tsakanin ku. Anya kuwa fad'amin gaskiya dai hala tsoro kikeji shi yasa in ya nemeki bakya yarda? "

Ta tambaya tana tsatstsare ta da idanuwan ta,

"Wallahi Allah kuwa Hajiya ni bai tab'a nema naba balle ink'i yarda dashi, abinda ko d'akin shima baya barifa Ina shiga, kuma kullum in yazo in zan dafa abinci harda shi nikeyi kuma harma d'akin shi nike gyara mishi amma ko Ina ciki bazai shiga ba har sai na fita"

"Turk'ashi, lallai to indai haka ne akwai matsala kenan, dawa kuka tab'a yin irin hirar nan?"

"Ba kowa! Ni ban tab'a fad'ama kowa ba"

"Madallah dan ko yanzun ma shiru zakici gaba dayi da bakin ki, kin san dai kuma nace miki ki dage dayin azkar kullum safe da maraice koh?"

"Kullum ina yi ai Hajiya"

"To Allah ya k'ara tsarewa"

Rufe bakin Hajiya yayi dai² da dawowar Maryam wacce suka shigo tareda Meelat sa kuma Musty da Sadeeq na take musu baya.

Suna shigowa Hajiya ta mike zumbur,

"Yau ni naga jaraba nifa likita na cewa yayi in dunga samun isashen hutu in raba kaina da hayaniya, amma shine fisabilillahi kuka kwaso jiki wato kuga zakarun da suka biyo kaji, su suna a gaba ku kuna take musu baya, to ga falon nan dan bazan zauna ku sakamin ciwon kai ba wallahi, dan yanzun in nace ku fitar min a falo sai kuce nayi rashin kirki na koreku, to ni dai so nike in gama da kowa lafiya atoh,
Ke takwara in kingama cin abincin ki duba cikin freezer akwai kajin da mai gida ya kawo ki taimakeni ki cire biyu a ciki kimin dambun kaza kafin ki wuce"

"Babu wani dambun da zan miki tafiya zamuyi tunda kin koremu"

"Ah ah fa kiji tsoron kwanciyar ki a kabari kar kimin sharri Allah ya gani ba Koran ku nayi ba, in kuma kinfi son kullum inyi ta fama da ciwo ai sai in dawo in zauna, dama mai yayi saura ai tsufa tuni ya dad'e da buga min kofa wadanda basu kaini bama suka mutu balle kuma ni da dama kullum cikin istigfari nike Ina fatan cikawa da imani, ki dai taimaki tsufana kimin dambun nan dan jiya har mafarkin shi saida nayi,"

Mai da dubanta kan Meelat tayi,
"Sannu Jamila tare kuke ashe? Hala wannan mai d'aga karfen ne ya tsareki a waje ya hanaki shigowa ki dubani tun d'azun? To kiji dai da kyau karki wani ce aure sai kin gama makaranta in dai da gaske yakeyi gara ki bashi dama ya tura ki shige d'akin ki kema hankalin ki ya kwanta, Allah dai ya rufama Yusufu Wase asiri shi uwar shi ta nema mishi mata da yike d'an mutunci ne haka ya amsheta hannu hurhud'u su kuma suna nan har yanzun sun kasa zab'ar wacce ta dace,
To ku kuma ai mun gaisa daku d'azun koh?"
Ta tambaya tana kallon su Sadeeq.
Basu amsa mata ba sai ma wajen zama da suka nema, to Hajiya cefa waye zai fad'a musu halinta ai su sai dai suba wani labari,
Maida budanta tayi kan Maryam,
"Maryam wannan ledar da qawarki ta kawo ban dai san ko miye a ciki ba tunda bata gabatar min dashi ba ki shigar min dashi ciki"

"To Hajiya ai har dambun ma sai in miki"
Taba Hajiya amsa,

Sadeeq ne ya katseta da cewa...
"Muje kitchen din to in tayaki aikin"

Hajiya bata k'ara kulasu ba tayi hayewar ta sama abinta.

"Bestyn mu ashe ana ganin ku? Aida cewa zanyi ko Soja ya hanaki yawon ziyara ne?"

Musty ya tambaya yana kallon Meenal.

"Kai Babana taya zai hanani ziyara kawai dai kune da bakwa zama sosai yanzun shi yasa mukan dad'e bamu had'uba kuma ai Ina cema qawata ta gaishe ka"

"Gaskiya ne kam dan tasha fad'amin,"

"Ba kullum kana zuwa tad'iba amma ko sau d'aya baka tab'a neman Indan nike ba, dukan kuma"
Ta fad'i hakan tana b'ata rai alamun abunda sukayin ya k'ona mata rai,

"Tofa kai Sadeeq kaji wani batu, to ke yanzun fisabilillahi Ina kika tab'a ganin yayye sun kama zarya zuwa gidan kanwar su balle kuma ni uba guda? To amma dai tunda kinyi korafi zamu gyara insha Allah zamu zo wata rana,

Ganin Maryam ta d'auki abincin ta tayi hanyar kitchen shi kuma Sadeeq ya take mata bayane yasa ita ma ta mike ta da'auki wayarta da nata ledan takeaway d'in ta fice daga falon, tabar Meelat da Musty a falon.

Kai tsaye wajen da ta faka motar ta ta wuce ta bu'de gidan gaba ta shiga kunna motar tayi sai ta d'an kwantar da kujeran ta kunna ac da radio din motan ta rage volume, ledan abincin ta bu'de ta faraci hankali kwance, tana cikin motar a zaune taji motsin alamar ana shirin fita da motar dake gefen ta wacce ta tabbatar da motar na AK ne dan kaf gidan shike iya cire manyan kud'ade wajen siyan manyan motoci kamar wanda bai san zafin naira ba,
Ilai kuwa shi din ne a ciki kasancewar motar da take ciki gilasanta a d'age suke kuma suna da duhu sosai hakan yasa bai lura da ita ba har ya kunna motar masu gadin gate suka bud'e mishi ya fice.

"Alhamdulillah" ta furta a bayyane, dan hakan ma wani dama ne ta yanda zataje ta d'auki turare dama sauran abubuwan da take buk'ata kafin ya dawo,
Dan fa Allah ya sani bawai bata da kud'in da zata cire ta siya turaren bane, No tana dashi amma tsakani da Allah bazata iya cire makudan kud'i ta siya turaren da kud'inta ba duk da dai ba aikin wahala tayi ta samu kud'in ba hasali ma cuwa² irin na student kullum takeyi tana tara kud'ad'enta dan insha Allah in har zata siya handout ko wani abun da zata siya ko take buk'ata na fannin karatun ta tofa babu d'aga double take amsa a hannun iyayen ta, zata amsa a hannun Malam ta kuma amsa a hannun Baba Auta, Baba Adamu kai harda ma iyayen ta mata takan amsa a hannun su hakan kuma bazai sa tak'i amsa a hannun Sarki da wajen sauran yayyen ta ba dan haka maganar gaskiya bata talauci, amma tattala abinta takeyi dan so take ta kud'ance kafin ta gama makaranta ta samu aiki ta riga ta tara kud'in siyan ma Malam fili dan data fara aiki kud'in ginin zatayi tanadi, ita wallahi bata san haka ake samun kud'i da cuwa² in kana karatu ba sai da ta fara, to gadai kud'in a asusun banki amma fa ranar da sukaje kasuwa ta gwada tambayan kud'in turaren nan da sunan ta siya ma kanta wallahi da mai turaren ya kira kud'in juwa taji kamar yana neman ya d'auketa ya nana da k'asa, ashe tsadadden turarene take ma feshin ala tsine bisa rashin sani, to daga karshe dai dole turarukan cikin akwatin auren ta ta d'auko taci gaba da amfani dasu amma Sam ko kusa ko alama basu kama kafar waccen d'in ba, dan haka ta kuduri aniyar zata kwantar da kai indai AK zai cigaba da bata turaren dan lokacin data fad'ama Sarki sunan turaren wani daban mai sunan shi ya siyo mata amma kamshin su ba iri guda bane.

Barin duk abinda takeyi a cikin motar tayi ta fito, sai da ta wanke hannun ta sannan ta waige ta tabbata babu wanda ke ankare da ita sannan ta k'arasa bakin kofar inda suke ajiye key d'in ta duba, amma ga mamakin ta babu makullin a wajen, har ta fara tunanin juyawa dan jikin ta yayi sanyi da alama dai yau ba sa'a sai kuma ta karasa ta tab'a kofar wai ko Allah zai sa ya manta bai kulle ba,
Aiko tana murd'awa ta tura sai kofar ta bude,
Taji dadi matuk'a dan harda tsallen murna tayi tana jin jinama kanta,
Babu b'ata lokaci ta shige ciki sannan ta mai da kofar ta shige,
Bata tsaya wani kalle kalle a falon ba gudun b'ata lokaci kawai ta amfa cikin bedroom din dan gara ta d'auki abunda zata d'auka ta fice kafin wani cikin su Musty ya shigo ya ganta a d'akin tunda dai shi ya fice,
Kan mirror ta wuce kai tsaye kamar yanda tayi tsammani ga koh turaren nan har kwalba uku a ajiye,
D'aukar d'aya daga ciki tayi ta cire shi a kwalin shi ta mishi feshin huce haushi na kewar shi da tayi tsayin watanni tana sauke ajiyar zuciya cike da shauki,
"Kai gaskiya dai mutumin nan duk yanda akayi d'an Aljannah ne Allah kuwa, Allah dai ya k'ara arziki bari gobe tuwo zan kokarta in tuk'o in kawo mishi tukuicin turaren nan,"
Guda biyu ta d'auka tabar mishi guda d'aya can kuma kamar wacce akayi ma tuni sai ta shige cikin bathroom din shi, yau ma showel gel din ta d'auko harda wasu mayukan wanke kai dama duk wani abunda taga ya mata ta fito niki² kamar wacce tazo shopping, sai da ta zube kayan akan gadon shi da yau Allah yasa gadon a kimtse yake yaji gyara harya gaji ga d'akin sai kamshi yake zubawa, dibi dibi ta farayi tana neman leda sai dai kuma bata samu ledar ba duk binciken ta a d'akin, daga karshe dai ta yanke hukuncin cire gyalen data rufe jikinta dashi kasancewar yana da girma sai tayi rolling dashi ya rufe jikin nata da kyau, dan tana ganin hakan zaifi sauki in ya so in ta isa mota tasan bazata rasa ledar zubasu ba, ko bata samu bama ba laifi dan yanzun in tace ta barsu taje mota dubo leda tofa yana iya dawowa ya isketa. Dan haka zuciyar ta d'aya tunda dai tasan cewa daga ita sai itane a d'akin hankali kwance ta balle fin d'in data mak'ale gyalen dashi ta warware gyalen ta shimfide shi akan gadon ta fara zuba kayan akai tana gama wa ta daure shi da kyau gudun kar wani abu daga ciki ya fad'i.
"Masha Allah" ta furta a yayin data gama kullewa ta juya da niyar d'auko hulan kanta daya fad'i a gefe a yayin da take warware gyalen, sai dai mai tana dagowa daga duken da tayi kamar almara kamar a mafarki idanuwan ta suka fad'a cikin na mutumin da bata san da wani suna zata kira shiba,
Aljani zatace ko kuma fatalwa, domin dai ai mai d'akin ta tabbata ya fita a gidan da mota, kuma sanda ta shigo ta tabbatar cewa babu kowa a cikin d'akin dan haka bata tsaya wata ² ba ta fasa ihu had'ada tsalle tsalle tana kiran aljanni,

"Waiyo Allah na shiga ukuna, dan Allah dan annabi aljani kayi hak'uri, Wallahi niba barauniya bace ba sata nazo yiba, wallahi niba barauniya bace, dan Allah kayi hak'uri, waiyo Allah Hajiya, Jamila Maryam Sadeeq Musty, dan Allah kuzo d'akin Mai Jama'a ku kawo min d'auki nayi gamo da mutanen boye,
K'alu innalillahi wa innah ilaihir raju'un, Allahu la'ilah ilah huwa innahu min sulaimana wa innahu........ A uuzubillahi mina shaidanir rajeem."

Sosai fa ta firgita dan Allah ya sani gaba daya ta riga ta sadakar cewa aljannun d'akin ne suka gaji da zuwa d'akin da takeyi tana sama da fad'i da kayan mai d'akin shine yasa suke shirin hukun tata,

Tafa tsorata matuk'a dan sosai take karkarwa addu'a kam yau babu kalar wacce batayi ba, tayi rantsuwar cewa ita ba barauniya bace yafi cikin tirela marasa adadi, alqawari koh tayi ta k'ara cewa daga yau ko hanyar d'akin bazata k'ara kallo ba balle tazo da sunan d'aukar turare.

Har kasa takai idanuwan ta a runtse tana fad'in dan Allah dan annabi aljani yayi hak'uri ya barta ta tafi, wallahi tayi alkawarin ta bari daga yau bata karawa,

🤣🤣🤣🤣😂


Abinda bata sani ba shine babu wani aljani mai d'akin da take zaton ya fice a gidan ne ya dawo domin dama fitar ba mai nisa bane ya fita da motar ne yaba wani yaron shi ita dan ya wanke mishi dan kwana kin nan da baya nan motar tayi kura, jiya kuma daya kira mechanic din shi yazo ya duba motocin gidan ya manta yace su wanke motocin gashi kuma yana da wajen zuwa anjima.

Koda ya dawo gidan baiyi tunanin k'ara komawa wajen Hajiya ba, dan bai san dalilin da yasa a yan kwanakin nan ko tunowa yayi da yarinyar nan sautin zuciyar shi ke sauya bugu ba,
Dalilin hakan ne ya yanke hukuncin ya shigo ciki ko wani abun yayi wanda zai dauke mishi hankali, koda ya shigo Sam bai lura da takalman taba, har ya shigo cikin d'akin ya nemi kujera ya zauna yana yan k'ana nan tunane tunanen da bazai iya cewa ga katamai man abinda yake tunanin ba,
Tabbas yaji kamshin turare a d'akin ya k'aru ba kamar yanda ya fita yabar d'akin ba, amma ko kusa bauyi zaton wani ne ya shigo d'akin ba duba da cewa dama duk inda aka ajiye turare kamshi baya barin wajen ne yasa ya kauda tunanin daga karshe ma sai ya d'auki wayar shi ya shiga latse latse,
Babu jimawa ya fara jin motsi, sanin shi kad'ai ne a cikin d'akin yasa ya so ya share sai dai kuma yawan motsin daya k'ara karfine yasa shi dago kai ya maida duban shi inda motsin yake fitowa,
Da fari shima ya d'auka dai ko gizo ne yarinyar nan ta fara mishi, to inba ciwon hauka keson kama shiba taya zai dunga ganin ta a wurare daban daban, lallai in ya riketa zai buga mata warning in ma wani abun ta mishi gara ta karya dan shi ba wasa yakeyi da yara ba,
Sai dai kuma abun mamaki koda ya kulle ido ya bud'e ita din dai yaci gaba da gani ta jido abubuwa daga cikin bayin ta fito kamar wacce ta dawo daga shopping, sai dai da alama itama bata san da wanzuwar shi a d'akin ba hakan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login