Showing 6001 words to 9000 words out of 174305 words

Chapter 3 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1848

malam ba, burin mukhtar bai wuce ya dawo gida ya gabatar ma Malam da jidda ba danya nema mishi aurenta.
Bai taba zaton neman auren Jidda zai zamo matsala tsakanin shi da malam ba domin tun tasowar shi yasan cewa malam yana son shi yana son duk abunda yake so domin shi Mukhtar kallon uba yakema yayan shi yana matukar girma mashi, Sai dai ya manta da ra'ayin riƙau irin na Malam akan yan boko, ga kuma laifi na 2 dashi Mukhtar din ya aikata nayin karatun bokon mai zurfi batareda Sanin malam ba.
Bayan da Mukhtar ya kammala karatun shi kasa dawowa yayi saida ya jira ya'yan shi Adam dan so yake suna komawa a fara maganar auren shi da Jidda dan haka tare suka dawo gida harma da sauran yaran.
Sai dai Abunda basu saniba shima malam a gefen shi ya fara nemawa dukan su biyun aure domin zuwa lokacin ya fara damuwa da rashin auren *Malam Adamu* domin kullum idan ya mashi maganar aure sai yace mishi "ba yanzun ba" dan haka ya gaji tare zai haɗasu ya aurar dan malam Adamu zuwa lokacin ya wuce a kirashi tuzuru dan ma yana da rufin asiri shi yasa girma bai nuna sosai a jikin shiba.

Shiko malam Adamu a inda yake yayi kafuwar da yake tsoron ya matsa daga wajen yabar dukiyar shine saboda rashin amana da tayi yawa a wajen al'umah da kaɗan² yake so ya kwaso arzikin daya Tara acan idan ya dawo gida gaba ɗaya sai yayi aure dan duk yarinyar da yace zai aura yanzun zai shiga hakkinta da yawa tunda yana dadewa bai waiwayi gida ba.
Ɗiyar wani babban Malami malam ya fara nemawa Mukhtar ba tare da shi ya sani ba, shi malam a wajen shi bazata ya shirya yi musu da sun dawo sai aure sai kuma gashi bayan dawowar su kafin malam ya gabatar musu da nashi bazatan su sun bashi nasu.
Domin shi mukhtar da kanshi yaje ma malam da zancen Hauwa'u a matsayin matar da yake son aura, Malam yana son Mukhtar sosai a cikin kannin shi wannan dalilin shiya hanashi kawo mishi maganar murjanatu anashi zuciyar ya kudura cewa idan aka gama maganar jidda daga baya zai bijiro ma mukhtar din da nashi zabin daya mishi koba komai ai Namiji mijin mata 4 ne dan haka ya taushi kanshi.

Abubuwa basu rikice ba sai da yasa a mishi bincike akan ita Jidda ɗin yar wasu ahali ne? Ranshi ya baci sosai ayayin da waɗan da ya wakilta akan su mishi bincike suka kawo mishi rahoto iri daya. Duk da yarinyar ta fito daga babban gida sannan sun bincika bata da wani nakasu tana da ilimin addini mai zurfi sai dai fa ita da ahalinta dukan su alhazi bokone domin binciken su ya nuna musu a kasar waje tayi karatunta na gaba da secondary saboda ilimin da Allah ya bata yanzun haka dai ta dawo kasane a matsayin likitan mata da ƙana nan yara.
Ran Malam ya baci sosai taya mukhtar zai aikata haka? Ya rasa yarinyar da zai nema sai yar boko ita nata bokon ma tafi karfin tayi shi a gaban iyayenta har sai ta ketare ƙasar waje! Koda yake ai uwa batayi gudu yarta ta rarrafa ba waye zaice bai san ubanta *ABDUL~KHAREEM* Ba? Mutumin da kowa yasan rikakken dan boko ne naƙin ƙarawa shida ahalin shi! Kai ina ai wannan zagi kawai *Mukhtar* yake so yaja mishi wajen mahassada dan haka wanna magana ma bamai yuwuwa bane kuma ba a gidan shiba!.

A wannan rana malam yayi faɗa kamar ya ari baki baiyi kasa a gwuiwa ba ya nemi ganin *Adamu* yace mishi ya taho tareda *Mukhtar* bayan sun iso duk son da yake ma *Mukhtar* ajiye shi yayi gefe ya mishi kacha² har Adamun bai shaba a wanna rana, karshe kuma ya fada mishi ya rufe maganar wata Jidda a cikin ahalin shi anan yake fada musu dama ya fara nema musu aure tun kafin dawowar su.


#Share please #
#My first novel ina fatan zaku soshi🤍

#Ummiee~Zaria

#25/4/2023
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*


*👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_



ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_# My first novel

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._

*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}

*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._
_Bazan taɓa mantawa da ku ba aminan ƙwarai,ina kuma alfahari da kasancewa ta cikinku,ko ban kira suna ba kun san kanku,mutanen Family House. Na gode³ ƙwarai da ƙarfin gwuiwar da kuka bani,wajen rubutun littafin *DANGINA* ubangiji ya biya da aljannah._
*MOM TEEMAH*
*AISHA HUMAIRA*
*JIKAR HAJIYA*
*CHIDA*



```Page 3


*Sosai hankalin *Mukhtar* ya tashi dan ba karamin so yakema *Hauwa'u Jidda* ba, tunani yake akan taya²ma zai tun kareta yanzun yace mata *ya fasa auren ta!* Kai ina gaskiya da sake.
A takaice dai ankai ruwa rana sosai kuma rayuka sun baci saida *Mukhtar* yayi kamun kafa sosai wajen sauran iyayen su da suke raye da kuma manyan Malaman da yasan Malam yanajin nauyin su sannan da kyar suka shawo kan Malam.

Sai dai kuma Malam yayi fushi sosai dan tunda yake da kannin shi bai taba kafa musu doka suka ƙetare ba, sai a wannan karan da *mukhtar* yake shirin ɗauko mashi yar boko ya kawo mishi cikin ahalin shi a matsayin suruka dan haka gaba ɗaya yaji ya baya ra'ayin ta, tun yanzun tana neman shiga tsakanin shi da kannan shi tana son raba haɗin kan dake tsakanin su *taya ma zai sota?* Ina har abada.....

Dan haka ya kafama *mukhtar* dokan cewa bazai matsa ko ina da sunan zama ba dole anan cikin gidan zai zauna, To shima dai baijaba tunda har yasamu an shawo mishi kanshi ai komai zai biyo baya mai saukine dan haka cikin kankanin lokaci saboda tsoron kar zuwa gaba Malam ya kara botsarewa aka tada ginin da Amarya zata zauna anan cikin gidan kamar yanda malam ya buƙata, anyi ma gidan gyare² sosai ta yanda ya nuna lallai anma bikin shiri na musam man, kowa na ɗaukin wannan biki amma banda Malam domin komai na neman auren ma zame kanshi yayi ya wakilta *Malam Adamu* haka dai akaci gaba da shirin biki ba yabo ba fallasa domin kowa taka tsantsan yake karyama Malam laifi.

Allah da ikon sa an daura aure lafiya amarya ta tare a dakin ta. Kowa yayi tunanin cewa bayan aure Malam zai sauko to ya sauko ɗin domin bai rage kanin nashi da komai ba, sai dai tsakanin shi da *jidda* ba wani abunda ya canza tsakanin ta da *Malam* gaisuwa ne kawai bayan shi baya shiga sabgarta bawai ƙiyayyarta yake nunawa ba amma dai gaskiya kowa yasan cewa baya wani yinta, Da farko yaso ya hanama iyalan shi shiga sashen ta saida *Mukhtar* ya nuna ɓacin ranshi sannan ya barsu suke mu'amalan tar juna, Itama tunda ta gane cewa ƴa'yan mijin nata baya yinta take taka tsan² bata shige mishi, Ko gefen matan shi bata zuwa indai yana gida sai dai su suje mata sannan rashin jituwarta da *Malam* baisa yaran gidan sun rainata ba, sai ma komawa shashen ta da wasu daga cikin su sukayi suka tare acan.

Malam yasa ido ko zaiga wani sauyi na tarbiya daga wajen yaran sai dai baiga hakan ba dan dole ya kauda idon shi akan su.
A haka rayuwa taci gaba da tafiya har zuwa sanda *Allah* yaba Jidda ciki haihuwar fari ta samu namiji aka sa mishi sunan mahaifin su Malam wato ~{{ UMAR FAROUQ }}~ haihuwarta na biyu shima Namiji ta kara samu aka sa mishi sunan Malam ~{{ MUSTAPHA }}~ na ukun shima Namiji Allah ya bata tayi zaton ko za'a mata kara a sanyawa yaron sunan Mahaifinta domin tana da cikin Allah yama Baban ta rasuwa, Tanaji tana gani haka yaro yaci sunan ~{{ ADAM }}~ taso ta nuna bacin ranta yan uwanta da mijinta suka bata hakuri, Koda ta kara samun wani cikin Allah da ikon sa wannan karon ma dai Namijin aka samu amma bana Malam yayi abun kai ya maida ma yaron sunan Baban ta yaro yaci suna ~{{ ABDUL KHAREEM}}~ ita da yan uwanta sunyi murna matuka dan haka sunyi hidima fiyeda wanda sukayi a haihuwar ta na baya.

Bayan wannan haihuwar bata kara samun wani cikin ba sai bayan shekara goma sha daya, Zuwa wannan lokacin sun samu cigabar rayuwa ta maban²ta fuskoki Allah ya kara musu budi arziki ya ha'baka an buge gidan an sake mishi fasali an mishi gini dai² da zamani,

A hankali zuwa wannan lokacin dayawa daga cikin tsauraran halayen malam sun ragu, domin da kadan² girma yana ta Kama shi sannan shima Malam Adamu ya dawo da dukiyar shi gida dan haka yanzun baya yawan yin tafiye²n da yakeyi, Da kyal dai aka shawo kan malam yaba jidda dama ta fara aikin ta na likitan ci, domin ta dade da samun aiki malam ya hana, Sai dai a gida mata suke zuwa tana dubasu kuma duk abunda ke faruwa Malam yana sane.

(Kuji karfin iko da isa irinta Malam gaskiya dai malam akwai karfin hali, kayi iko da matan ka matan kanni ma basu tsira ba, gaskiya ba kowa zai yarda da wannan mulkin mallakan ba).
Itama dai bata dagama mijinta hankali akan hakan ba domin yana tsaye akan buƙatun ta dana yaranta koda wani lokaci sannan yan uwanta ma tsaye suke akanta babu abunda ta rasa a hakan kuma itama tana taɓa kasuwanci.
Kaf ahalin mijinta bata da matsala da kowa dukansu suna girma mata da kyautata mata kamar yanda itama take tsaye akan hidimar su, dan haka rashin kulawar da malam ke nuna mata bai taɓa damunta ba, dan koba komai yana nuna kulawar shi akan yaranta dan haka tuni ta cire damuwar shi a ranta koba komai ai bashi ke auren ta ba.
Ana haka shima *Mukhtar* ya gaji da kumbiya²n da yakeyi na ɓoyema malam laifin daya dade da aikata mishi tsayin shekaru, kuma har zuwa wannan lokacin duk yaron daya kammala secondary shida Adamu suke ma yaran tsaye in an fiddasu waje don ganin sun samu ilimin boko da islama ba tareda Sanin Malam ba, Azaton su Shi malam yana nan yana hidimar shi bai san cewa tuni ahalin shi sun goge sun daɗe da zama yan boko ba.
*Malam Adamu* ne ya mishi jagora suka jema malam da maganar, Sai dai ga mamakin su Ashe malam yasan komai tsayin shekarun nan ya daiyi bakam ne yana so yaga iya gudun ruwan su dan haka ya zuba musu ido, koda wasa bai taɓa gwada cewar yasan abunda yake faruwa ba, yasha mamaki da yaga baiga wani canji a wajen yaran dashi *Mukhtar* din ba dan shi da fari kallon yan iska yakema yan boko sai gashi a hankali yagane cewan shine yama abun gurguwar fahimta, Dan haka koda suka gama mishi bayani maimakon suga ya rufesu da faɗa kamar yanda ya saba idan aka aikata mishi ba dai² ba sai sukaga ya tsatstsare su da ido yana kallon su yana murmushi, Su kansu sun tsargu dan haka suka dunga bashi hakuri suna kara wayar mishi da kai da bashi misalai akan fa'idar ilimin bokon a yanzun, kuma shima bai katse musu hanzari ba sai da ya gamajin ta bakin su kafin ya daura dayi musu nasiha kana ya fada musu duk abunda suke ciki ya sani kuma ya yafe musu boye mashin da sukayi, Sai dai ya kara da cewa har yanzun yana kan ba kanshi ɗiya mace bazatayi karatun daya haura secondary a gida, ba bazai yarda yarinya tayi ta jera kafada da iyayenta mata a cikin gidaba idan anyi magana ace karatu takeyi.


Basu kadai ba duk ahalin gidan sunyi mamakin abunda ya faru ayau, dan sunyi zaton sai ankai ruwa rana kafin a shawo kan malam dan haka suka cika da farin ciki lallai komai yanada lokaci kuma Allah yana iya canza mutum komai taurin kanshi ya koma mai sanyi.
A kuma wannan lokacin ne ciki na biyar ya bayyana a jikin *Momi Hauwa* dan haka murna da farin cikin wannan ahali ya karu duba da tsayin shekarun data dauka rabon ta da haihuwar dan *Abdul~Khareem* ya girma tuni,
basu gama wannan murnar ba wani ƙarin farin cikin ya same su domin a wannan lokacin ne shima *Baba Adamu* yayi aure da yarinyar nan *Murjanatu* da Malam ya nemar ma *Mukhtar* shekarun baya, idan baku manta ba!
Tayi aure tun wancan lokacin to Allah yama mijin nata rasuwa sannan tsayin shekarun nan allah bai bata haihuwa ba dan haka bayan gama iddarta Malam ya nema wa *Adamu* aurenta kuma an bashi anyi aure lafiya amarya itama ta tare a sabon shashen da aka ware masu.

---+++----

Haihuwar jidda na 5 cikin ikon Allah wannan karan mace aka samu kyakyawar jaririya mai Kama da uwarta domin dukan yaranta fuskar Baban su suke daukowa sai wannan ce ta biyo uwa, Wanna yarinya tazo da farin jini sosai domin an daɗe ba'a samu ƙaruwar ƴa mace a gidan na malam ba sauran yan matan kuma duk an aurar da dasu sai samari suka rage dan haka kowa yake ɗaukin haihuwar.
Allah da ikon shi sai ya ɗauki soyayyar wannan jaririya ya sanya shi cikin zuciyar Malam tunda ya kyallara idon shi akanta, duk haihuwar da jidda keyi bai ta
ɓa taka ƙafar shi zuwa shashen ta da sunan ya mata barka ba sai wannan karan, kai hatta kayan barka na musamman ya haɗama wannan ƴa tun kafin suna yake aikawa a ɗauko mishi jaririyar a kawo mishi, abunda bai tab'a kwatan tashi akan nashi yaran ba, Malam fa ya cika zukatan mutanen gidan shi da mamaki gashi kuma ba wanda ya isa ya tare shi dan Sanin dalilin wannan sauyin! Koda yake dama yan magana cewa sukayi *abun cikin kwai yafi kwan dadi! Domin kowa yasan yanda malam keson *Mukhtar* kaf a cikin kannin shi to amma uwar y'ar fa? (wannan amsar a bakin Malam kaɗai zakujita)

Bai karkare ba mutanen gidan mamaki ba har sai ranar sunan da jaririya taci Sunan Mahaifiyar su malam din wato *~{{ Aminatu }}~* manyan raguna biyu da jibgegen sa ya bada aka yanka sannan ya hada sha tara ta arziki ma jaririya Ameena,
gaskiya dai yayi abunda kowa bai tsam mata ba duba da cewa matan shi sun haifa mishi yara mata ɗai² har 8 amma cikin su ba wacce yasama sunan Mahaifiyar shi, sai wannan da kowa ya shaida baya yin uwarta dan haka masu gulma dai sunyi ita dai uwar ƴa gaba ta kaita, koba komai itama an mata kara domin sunan uwarta itama *Amina* dan haka ba kare bin damo.
An daiyi taron suna lafiya kowa ya koma gidan shi yana ma Amina fatan Allah ya raya,

A wannan lokaci rainon Aminatu wacce suke ma lakabi da *Meenal* wasu kuma suke kiranta da *Meenat* kashi 3 ya rabu, kason farko mafi girma yana hannun Malam, kaso na 2 kuma hannun jama'ar gida domin kowa kauna yake nuna mata , suma suna ma Malam kara, sai kaso na 3 wajen uwarta da idan tayi kuka ake kai mata domin ta bata nono wani lokacin ma ko dawo da ita ba'ayi sai tayi bacci.
Wannan bayya nan niyar soyayya da malam ke gwadama Meenal ya sanya duk wani halin ko in kula da malam ya nuna ma Jidda a baya gushewa a zuciyarta kun san shi mai ɗa wawane, domin abun a fili yake yanda Malam ya damu da al'amarin Meenal ko nashi ɗiyan na cikin shi basa samun kulawar shi hakan domin komai ya samo na Meenal ne shiga 10 fita 10 sai ya mata tsaraba, Itama kuma ta wayeshi sosai dan hatta Baban ta takan mishi kiwiya amma bata ma Malam, data fara wayau kuwa da zarar tayi laifi wajen Malam take gudu.

*******"""""""*******

Alhmadulillahi a haka rayuwa taci gaba da gungurawa wata rana Zuma wata ran madaci,
Bayan haihuwar *Meenal* jidda da yara ke Kira (Momi Hauwa) ta kara haihuwar yara 3 biyu mata sai namjin ɗaya yanzun dai yaranta 8 cif, Matar Baba Adamu Aunty Murja itama ta haifi yara 3 matan Malam suma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login