Showing 1 words to 3000 words out of 174305 words

Chapter 1 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1851

[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*


*👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_



ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_
Karku manta wannan din shine littafina na farko kumin uzuri a inda na kuskure.

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._

*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}

*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._
_Bazan taɓa mantawa da ku ba aminan ƙwarai,ina kuma alfahari da kasancewa ta cikinku,ko ban kira suna ba kun san kanku,mutanen Family House. Na gode³ ƙwarai da ƙarfin gwuiwar da kuka bani,wajen rubutun littafin *DANGINA* ubangiji ya biya da aljannah._
*MOM TEEMAH*
*AISHA HUMAIRA*
*JIKAR HAJIYA*
*CHIDA*

Happy sallah to all muslim ummah, Ubangiji Allah ya karɓi ibadun mu, Ameen


```Page 1```

***Kamar ko wacce rana yauma cike majalisar yake da samari,ba ka jin komai sai kace nace dake tashi a wajen ana musu kan ƙwallon ƙafan da aka kalla daren jiya,a ɗabi'a irin ta samari dama hakan na faruwa,musamman idan aka samu bambancin ra'ayi,ma'ana wane yana da club da yafi so shima wane haka,kuma abun takaicinma shi ne,a lokuta da yawa tare za'a je a kalla,a guri ɗaya majigi ɗaya amma idan an dawo dole sai anyi musu. Ƙarar taka burkin motar data faka daga can gefe ɗaya yasa ilahirin samarin dake gurin juya wasu na faɗin "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Allah yasa ba accident aka samu ba.." Daga cikin motar data faka matashiyar budurwar ta fito kamar an cillota ta sha gaban ɗaya budurwar dake tafiya cikin kwalliya tana kwarkwasa,sake buɗe motar akai wata budurwa ta fito tana faɗin "Hafsat don Allah kada kice za ki takaleta da faɗa a gaban maza.." Ai bata gama rufe bakinta ba,faɗa ya kacame tsakaninsu babu zato bare tsammani,cikin kumfar baki ɗaya daga cikinsu harshenta har yana sarƙewa take faɗin

"Ke har kin isa kiso saurayin da nike so? Me kike ji da shi? Me kike taƙama da shi? Wallahi in baki fita sabgar *ABDUL-KAREEM* ba sai na canza miki kamanni.."

Tana huci taci gaba da cewa "na ga batun yau ba kike bibiyar shi dan maita,duk da ko sau ɗaya bai taɓa nuna ya san kina yi ba,wane irin maita ne wannan da baza ki fita sabgar shi ba!?"

"Maitar data hana ki rabuwa da shi,duk da yanda yake yakice ki a kusa da shi,nima ita ta hana zuciyata rabuwa da shi" amsar da abokiyar faɗan nata ta bata kenan cikin haki suna ci gaba da kaiwa juna naushi,kaca² suka ci gaba da dambatuwa a filin Allah mutane na kallonsu,ganin al'amarin ya fara munana ne yasa mazan dake zaune a majalisar da abun ke faruwa tasowa suka shiga ƙoƙarin raba faɗan,suna faɗin "ku kuwa mene ne haka za ku tsaya faɗa da junanku a titi alhalin kuna mata?" Hafsat tace "ku rabu da mu yau mu fitar da raini ni da ita.. Ita har ta isa taso abunda nake so" ɗayar budurwar wani matashi ya kalla yana cewa "haba Nusaiba! Wannan ai ba girmanki bane,ina ke ina faɗa da wata a titi?" Nusaiba cikin jin zafin abunda Hafsat tayi mata tace "Sadeeq kuna dai kallo ta tare ni a hanya,bance mata ƙala ba ta nemi rufeni da duka,akan me? Ita ba uwata ba za tai min abu ban rama ba?" Haƙuri samarin ke basu duk da cewa inda sabo sun saba dan ba yaune karon farko da suka fara rabon fada na mata a majalisar tasu ba,amma kamar suna turasu,sai da ƙyal bayan sun yayyagema juna riga sannan aka rabasu,kowa ta tsaya tana kallon ƴar uwarta tana nishi kamar zakarun dambe,tabbas sun dambatu kuma sun goge raini,a wahalce dukansu suke maida ajiyar zuciya,daga mai kumburarren baki sai wacce aka naushe ma hanci.
Wani matashi cikin masu rabon faɗan ya kallesu cikin takaici yace "kun san Allah ku rufama kanku asiri ku tattara kubar unguwar nan kafin *MAI JAMA'A* ya fito, "in ba haka ba kuma kun san sauran" cewar wani daga cikin samarin da suka raba faɗan,yana gama faɗa musu haka ya juya tare da shigewa cikin gidan da yake nan daura da majalisar tasu.
Ƙawar Hafsat da tun farkon fitowarta a mota take cewa kada ta tankawa Nusaiba ce ta tallafeta bayan ta ɗauko ruwa a cikin mota tana cewa "kinga Hafsat kizo mu wuce,ni dai kin san ban son tashin hankali,ku kullum da kun haɗu ko a ina ne sai kun raba hali" tayi maganar tana zuba ruwa a hannunta tana wanke ma Hafsat ɗin fuskarta da aka fashe ma hanci jini sai zuba yake.
"Kareema ki barni in koya ma yarinyar nan hankali,wani shegen ne yace mata ta fini son Mai Jama'a? Wallahi duk yanda take jin son shi na tabbatar na fita,dan kullum da shi nike kwana nike tashi a zuciyata,kuma wallahi yanzu na fara son Mai Jama'a,dole ta barni da masoyina.." Hafsat ta faɗa cikin kumfar baki,tsaki Kareema taja,cikin tarin jin haushi tace "ai kinji abunda kullum yake haɗani dake kenan,wai ke fisabilillahi yaushe za kiyi ma kanki karatun ta nutsu? ,ke ba masoya kika rasa ba,da kyanki da komai amma kin manne ma Abdul,wai ko kunya ba kyaji? Ni fa gani nike in baki girmi Abdul ba,to za ku zo kan²kan dashi,wallahi in kika ce haka za kici gaba da zubda ajinki akan shi,kina tare da wahala kuma zakice na faɗa miki hakan wata rana, dan tabbas kema kin san gaskiya nake faɗa.
Yanzu ina amfanin abunda kuka aikata? Kuna mata ku tsaya dambe akan saurayi,kuma dan rashin kunya a ƙofar gidansu,ko kunyar tarin jama'ar dake wajen da masu wucewa baku ji ba? Yanzu duba yanda ta fasa miki hanci,faɗamin wani amsa za kiba mutanen gidanku idan suka tambayeki garin ya hakan ya faru?"
Da ƙyar Hafsat ta ɗago kanta bayan jinin ya tsaya tana kallon ƙawarta tace "Kareema dan Allah ki ƙyaleni,ba na son yawan surutu, banajin zan iya tuki a halin da nike ciki kija motar mubar unguwar nan dan bana so Abdul ya fito ya taddani a nan,raina ƙara baci zai yi.." Taɓe baki Kareema tayi,ba tare da tace komai ba ta kamata zuwa gefen mai zaman banza ita kuma ta kewaya gefen direba taima motar key suka bar unguwar,to ita ma dai Nusaibar bata tsaya ba bayan matasan sun bata ruwa ta wanke bakinta daya fashe gidan su dake nan saman layin ta karasa dan itama bazata so ya fito ya ganta a haka da kumburarren baki ba, haka dai kowaccen su ta kama gaban ta ba tare da sunga mai Jama'an da suka yi faɗan akan shiba. Bayan wucersu haka samarin dake zaune a majalisar suka ci gaba da caccakar su,suna alawadai da halin ƴan matan, da kullum suka hadu sai sun tankama juna sannan babban abin takaicin shi wanda suke faɗan a kanshi babu wacce yake kallo da gashi a cikin su, dan wallahi da yana wajen sukayi wannan haukar karamin aikin shine ya sa belt din shi ya cicci musu uwa shiba ruwan shi, suma basa fara yin har gagin su muddin yana waje.

*Mai Jama'a* kenan kullum mata ke binshi shi kuma bai gajiya da yarfa su.

Ko da Sadeeq ya shiga cikin gida,kai tsaye inda yake da tabbacin zai samu mutumin nashi ya nufa,wato sashen Hajiya Innah,kishingiɗe kan doguwar kujerar 3 seater ya sameshi yana cin soyayyar gyaɗa,ko sallamar da yayi Innah bata amsa ba sai juyowar da tayi tana sababi
"Oh ni Aminatu na ga abunda yafi zare tsayi,ace mutum ba shi da halin da zai yi ɗan abunshi na kwaɗayi yaci,sai kunzo kun baibayeshi kamar wasu sabbin mayu.. Shi wannan ɗan mai karfin ga shi yazo yamin sake² a falo,ko taya mishi gyaɗar nan banyi ba,amma kaga yanda ya wafce min kusan rabi,ga shi kaima zalo² ka biyo bayan shi,kuma yanzu dan Allah idan na hanaka gyaɗar nan baza ka koma gefe kana tsinemin a cikin zuciyarka ba?"
Sadeeq dake ma Hajiya Innah wani kallo yace "yanzu nan Hajiya dama saboda soyayyar gyaɗa ne yasa ko sallamar da nayi kika ƙi amsamin?"
Cikin jin haushi Hajiya Innah tace "ameen wa'alaikumus salam.. To na amsa sai me kuma?"
Sadeeq yace "nifa dama zuwa nayi ince kije ki raba faɗa,dan inaga zuwa gaba ƴan matan jikanki kashe juna zasu fara,saboda hauka da kishin wanda bai san suna yi ba.."
Salati Hajiya Inna ta fara tana tafe hannuwa "Muhammadur rasulullahi (S.A.W)!" Ta faɗa tana yunƙurawa har zanin ta na neman faɗuwa tace
" Kai saddeequ! Fisabilillahi ina cikin gidan nan,amma dan cin amana har akaci aka siɗe baka zo ka kirani ba sai yanzu?"

Sadeeq yace "Hajiya to ai kallo na tsaya dan in samu damar kawo miki rahoto da kyau, basai kin fita ba ai tuni suka gama dakuwa nasan yanzun sun riga sun wuce"
Hajiya Innah tace "ɗan nema me yasa baka zo ka kirani tun ɗazu in fita mu daku da su ba? inji dalilin da yasa suke neman maida min kofar gida filin dambe" tai maganar yayin da take komawa kujerar data tashi ta zauna tana gyara zanin jikinta..
"Ni dai wannan abu na ci min tuwo a ƙwarya,yanzu ace duk cikin ƴaƴa da jikokina mata babu wacce ta ɗauko farin jinina har gara² ma ƴar wajen Jidda ita kam sak kamar ni lokacin ina yarinta na, a rasa wanda za'a ba farin jinin sai wannan mutumi mai ƙirar ƴan dambe,mutum a tsaye gansansan jiki duk a mummurɗe nayi² dashi ya raba kanshi da ɗaga waɗan can tsinannun karafunan yakiji, yanzun fisabillahi in tsautsayi ya gifta wata rana ba fata dai nike ba amma in suka kutto daga hannun shi suka dakar mishi kirji ba shike nan ba,to Allah ma dai ya kiyaye atoh nidai ba fata nike mishi ba, amma wai haka mata ke binshi su ko tausayin kansu basaji.. Ni fa kullum tunani nike ina zan samo mashi mata inya tashi aure,eh mana to mutumin da matan na binshi yana guduwa ai sai dai in nagaji da ganin shi a haka insa kayo min list na ƴan matan dake mishi layi kullum ka haɗomin kan hotunan su in duba mishi, kaga in ba'a dace ba sai in fantsama cikin gari ko a dace dan nidai ba mahaukaciya bane dazan ɗauki kasadar haɗashi da ɗaya daga cikin jikoki na atoh dan so nike in darzo mishi mai irin ƙirar jikinshi,kada in ɗauko wanda zai ƙwara.. Allah kuwa! Yo inba haka ba wannan ai zuwa ɗaya zaima mace ya tasheta aiki"
Ƙyalƙyalewa da dariya Sadeeq yayi,shi ko gogan yanda kuka san ma bashi a falon,ko kallo basu isheshi ba gyaɗarshi kawai yake afawa a baki hankali kwance.
Hajiya Innah ta ci gaba da cewa "kana ji koh Saddeequ,ni fa tsoro nike saboda a zamanin ƴan matancina tsabar farin jinina dole haka aka dunga ɓoyeni ko fita ba kasafai nike yinta ba domin fita 10 sai na samu saurayin da zai biyoni cewar sona yake,to farin jini ne dani duk inda na shiga sai masoya sun biyoni.. To wallahi ko Kakan ku ma darajar ƴan uwantaka yaci ya sameni da ƙyal,dan ni a lokacin manema na duk manyan mutane ne,rabon haihuwar iyayenku ne dai ya ajiyeni a Nigeria,na san da yanzun ina can kasashen larabawa.. Ko da yake shima fa Kakan naku mun kusa zagaye duniyar nan da shi gurin yawon buɗe ido,kafin ya mutu ya barni.." Sai kuma ta fara shessheƙa tana faɗin "ai ga irinta nan ABDUL-KHAREEMU ka tafi ka barni da yaran nan sun garƙameni a cikin gida kamar ƴar fursuna,nan da Habuja idan nace zanje sai na yi da gaske suke barina zuwa" ta ƙarasa faɗa tana face majina a cikin tissue,
kamar ya samu TV haka Mai Jama'a ya gyara zama yana kallon dramar Hajiya Innah,ƙasa² ya furta "lallai matar nan" in ma ba kallon bakin shi kayi ba bai zama lallai ka gane mai ya faɗa ba.

Gefenta Sadeeq ya koma ya zauna,cike da lallashi yace "yi haƙuri Hajiyana ki share hawayenki,In ABDUL-KHAREEMU ya wuce ai ga wasu jaruman mazan yabar miki masu jini a jika ma ba irin shi daya tsufa ba yanzu ki faɗamin wani ƙasa da wanne ƙasar kike son zuwa ni zan kai ki, kina wannan maganar gama na karfen naki nan a gefen ki Hajiyata kina damu ai baki da takaici wallahi umarni zaki bayar dole a cika !"

Tunda suka fara magana bai yarda ya tsoma musu baki ba dan so yake yaga iya gudun ruwan su daga Hajiyar harshi kanshi Sadeeq ɗin da yake nema ya zama ɗan taya ɓera ɓari,to yanzun kam an kai matakin da dole sai ya tanka musu dan haka da wata irin kakkaurar murya yana juya idanunsa akan Sadeeq yace "ka kaita ina? Last month fa Hajiya ta dawo daga Dubai,kana sane da yanda ta hautsina min kai akan son zuwa dubai wai zata kaima kawarta ziyara, sannan yanzu daga dawowarta kace wai ta ƙara ƙetare ƙasa? Babu inda za taje kada ma tasa kai asarar kuɗin ticket.."

"Innalillahi wa'innah ilaihir raju'un.. *ABDUL-KHAREEMU!* Ashe kana cikin ƴan hassada na bani da masaniya? To dan ƙaniyarka naje Dubai ɗin,eh nace na je ɗin! Kuma komawa zan yi yanzuma,na ga dai iya kuɗin kuɗin jirgi ka biyamin kona shan ruwa a hanya da ake ba matafiyi baka bani sai wata shegiyar dubu 50 daka turamin wacce ko dan kenne bazata siyamin ba.. Ashe yanzu nan duk gatantaka da nike yi bita da ƙulli kakemin? To ta Allah ba taka ba,tashi maza² ka koma gidanku,dama ni na san ba zuwan Allah da Annabi kakema garin nan ba,zuwa kake saboda ɗan kayan daɗin da ƴaƴana suka taramin mu cinyesu da kai da askarawan daka tara min a kofar gida, kana nan kullum manne dani wai sunan ka gama makaranta amma kullum kana nan kamar nan ne gidan ubanka.. To tashi maza ka fice ka barmin gidan mijina,kullum haka zaka zo kana taramin jama'arka a ƙofar gida,sai kun zazzagemin buhunan abinci hankalinku yake kwanciya,idan za ka dawo kuwa haka nan kake zuwar min gida hannu na dukan cinya sai in naci sa'a ne kake ciko bayan motar ka da kayan abinci salon wani ya gani yace kai kake cidani,
Haka kawai kazo gidana kuma ka nemi yimin iskanci,to uban kuturu yayi kaɗan.. Waiga bayan ka ga ƙofa nan,ta nan ka shigo ko? To maza bita ka fice min a ɗaki kafin in targaɗaka"
Dariya Sadeeq ke yi domin indai rikici ne tsakanin Hajiya da Mai Jama'a,ba yau ne farau ba,kuma duk wanda yayi gigin shiga tsakani,tofa ya shiga ukun shi dan kanshi zata koma tace ana so a shiga tsakaninta da jikanta,dan anga duk cikin jikokinta shi ya ɗauko komai nata. Shi ko Mai Jama'a miƙewa yayi "nadai fada babu inda zaki" yana gama furta hakan ya fice kamar yanda ta buƙata,dan yau ba ya jin zai iya biye mata su raba hali da maraicen nan, Dan Hajiya bakinta baya gajiya da Masifa.

Bayan fitar shi ta ɗauko sameerar da gyaɗarta ke ciki ta dankwafar a gefen Sadeeq tana cewa
"To ga gyaɗar nan kaima kaci,karka ƙullaceni kace ina nuna bambanci.. Atoh! Ni ba ruwa na..
Yauwa! Faɗamin su waye ma kace sun yi dambe?"

Sadeeq yace "Hafsa ce fa wannan yarinyar dai data nace mishi kin dai santa da yarinyar nan ƴar saman layin nan Nusaiba.."

Hajiya tana yatsina fuska cikin takaici kamar ta ga abun ƙyama tace "tir! Yanzu su waɗannan danƙara²n ƴan mata,dan rashin daraja shi ne suka zage suna min dambe a ƙofar gida, ita dai wannan Hafsat to gaskiya dai banace uwarta tayi asarar aihuwa ba, amma ina tantama idan basuyi gadon maita a dangin suba, yarinya ta nace tuntale tale tunfa tana kwailarta take nan ta manne mashi dubi kaga yanzun yanda tayi wani uban ƙiba, nifa ranar da tazo nan tsoro naji kai anya yarinyar nan ba shaka fashe take shaba kuwa? kai bakaga yanda takoma ba? to wallahi ko wani nonon ta daya yayi girman kaina ga uban ɗuwawuka saida na kare mata kallo fes dan da fari nayi zaton ko ciko tayi, kai niko inba na koma Aminatun mahaukata ba ina zan yarda jikana ya auro min ita! wallahi irin su suke juya miji su sa yakijin maganar uwar data haifeshi ma balle kuma wata ni kakarshi, atoh nidai ko zannuwan data kawomin ranar babu wanda na ɗauka Jummai na kira nace tazo ta kwashe kaikoh kana nan zannuwa nefa duk babu wacce ta haura dubu ashirin kuma ma dai tsoro nike kar yazo kila ko tayi tsafe²n da yan mata keyi,
Kaga nifa shi yasa banyi maraba da wannan majalisar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login