Showing 162001 words to 165000 words out of 174305 words
Chapter 55 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
da kallo,
"Kai amma wallahi Wase kama raina min wayau, banyi aure dan buk'atar kaina ba sai dan saboda in kazo gidan nan kaci abinci zanyi? To kenan kuku zan auro a matsayin matana in ajiye maka ko ya kake so inyi ne iyeh Abba Ahmadu?"
"Ai kai kaji tsiyar ka, sam ba zaka tsaya ayi maganar arziki da kai ba"
"Eh na tsiya na iya can nafi kwarewa, aure kuma layine idan nima yazo kaina zanyi shine koda kuwa ban shirya ba, ba kuma wani ne ke cidani ba balle yace ya gaji"
"Ai kai a duniya indai musu ne babu wanda ya kaika, ga bak'ar zurfin cikin da in bakayi wasa ba sai ya zama ajalin ka, badai ka iya tara damuwa a cikin kirjin kaba ka zauna a wajen harka rasa abinda zuciyar naka ke muradi kaga ka huta ai"
"Ohhh ashe ka fara maita ban sani ba tunda har ka iya gane cewa ina da wata damuwa, to malamin duba fad'amin ya gobe na zata kasance?"
Wayar da yayi record din d'azun ya d'auko kunno record din yayi ya ajiye a gaban Ak
"Can you explain this to me?"
Hannu ya mik'a ya d'auko wayar yana kallo,
"Miye wannan d'in?"
Ak ya tambaya.
"Kai dai zaka bani amsar akan abinda ya jefa ka cikin shauk'i haka da har na shigo cikin d'akin tsayin lokaci baka sani ba!"
Hummmm"
ya sauke doguwar ajiyar zuciya kafin ya d'aura da cewa,
"Wase yaushe ka koma dan sa ido ne bani da labari, ko kuma dai ka fara aikin binciken sirri akaina ne?"
Serious sosai Yusuf yaci kafin ya kira sunan Ak
"Abdul Khareem Ahmad, yaushe muka fara b'oye ma juna damuwar mu?, bani kad'ai ba dukan mu munsan kana da damuwa duk da kana ta kokarin boye mana, wanda kuma hakan ba sabon mu bane boye damuwar juna, a ganin ka mu bazamu iya tallafa maka bane idan har ka shaida mana halin da kake ciki? Su sauran sun sa maka idone dan suga iya gudun ruwan ka amma ni yau na gaza bazan iya barin garin nan ba har sai nasan abinda yake damun ka, in kuma ban kai matsayin da zan sani ba to, duk da jikina yana bani cewa damuwar naka tana da alak'a da mace, na kuma k'ara samun tabbacin hakan ne saboda yanda na sameka a d'azun,
Fad'amin wata mai sa'ar ce tayi nasarar samun ka, ka sani ko yar waye mu din masu tsaya maka ne har sai mun d'auko ta mun kaimaka ita cikin d'akin ka zama na din din din a matsayin mata, ina rokon ka karka b'oyemin komai"
Shiru falon ya d'auka kamar babu wani abu mai rai a cikin shi kafin zuwa can AK ya yanke shirun da cewa " wata karamar yarinya ce take shirin sa kaina ya tarwatse da tunanin ta Yusuf!"
Sai kuma yayi shiru tsayin lokaci bai kara cewa komai ba, shi ma kuma Yusuf din bai tofa ba dan so yake ya amayar da duk abinda ke cikin shi, ba tareda shi ya takura mishi da yawan tambaya ba.
"Yusuf karamar yarinya cefa ni banma san ta yanda zan iya tunkarar taba balle har kuma in gabatar mata da kaina a matsayin masoyi, kaima kasan hakan bai tab'a faruwa dani ba, ban saba tarar mace dan ingabatar mata da kaina ba a kullum matan ne ke tarana suna gabatar da kansu da bukatar su gareni dan haka ban san ta ina zan fara ba,
kawai dai ina tsintar kaina a ciki farin ciki sosai a duk sanda na ganta ko naji muryar ta, haka kuma nike kasancewa cikin kewa da kad'aici a duk sanda na nesan ta kaina da ita, ban san dalili ba amma ji nikeyi a cikin zuciya ta cewa ita kad'ai nike muradi ita din zata wadatar dani in zauna da ita kad'ai a matsayin mata a yanzun shine kadai muradi na, sai dai kuma ban san ta ya'ya hakan zai faru ba"
"Kenan dai kana so kace min har yanzun bata san cewa kana sonta ba?"
"Bata sani ba dan ban tab'a nuna mata koda alama ba, hasalima auren ta bai dade da mutuwa ba amma wallahi kullum da tsoron kar in k'ara rasata a karo na biyu nike kwana nike tashi"
"Bazawara"
Wase ya ambata cike da mamaki,
"Eh bazawara amma kuma wacce a zahiri ne ta amsa sunan a bad'ini kuwa budurwa za'a kirata"
"Kai malam karka wani yi mata kwaskwarima duk macen da akama aure indai an d'aura tofa sunan ta bazawara ne"
Katse shi AK yayi da cewa,,,
"ban damu ba Yusuf koda wani suna za'a kirata, tunda har zuciyata tana sonta ko a ya na sameta hakan zanci gaba da zama da ita balle kuma abinda na shaida maka Ina da tabbaci akan shi"
"Wacece ita? ma'ana ina nufin yar inace miye sunan ta ina ne garin su su waye iyayen ta? Duk ina son in sani!"
"Karka damu kanka ita din ai ba bak'uwar ka bace,"
"Eh amma ai in baka fad'amin ba bazan san ko wacece ba!"
"Sunan ta Amina amma Meenal suke ce mata yarinyar Aunty Jidda dake Unguwar Malamai zaria"
"Kaiii" Yusuf ya ambata,
"Kai mai jama'a badai yarinyar nan da akayi ma auren dole kwanan baya? Koba mai kiranka tuzuru ba?"
"Ita fa"
"Kai amma kun dace fa yasin kuwa ina fad'ama dan ni dama tun lokacin can naso inyi maka tsegumi amma sanin halin ka yasa na basar, to ya akayi auren nata ya mace ne?"
"Sakaran miji ta samu mana, ya kaita gida ya kafe kamar wanda yakai ajiyar kud'i a banki"
"Ahaf to ai mu Alhamdulillah indai haka ne gaba ta kaimu mai ya rage yanzun ai fad'awa kawai zakayi ayi faka faka a wuce wajen, dan wallahi yarinyar nan mai zafice da zarar kayi wasa sai dai ka fara ganin daka dakan motoci na layi alhaji,"
"Kai ban son wulakanci ya muna maganar arziki kai kuma kana sako wasa ne,"
"Ba zancen wasa ba Allah koni da ace baka ciki tofa tuni zanje inyi kamun k'afa a wajen Hajiya a bani ita in adana kogi ai baya k'in k'ari"
Mtws Mai Jama'a yaja tsaki yana yunk'urawa da shirin barin mishi wajen,
"Sorry sorry am just kidding, ni mai zanyi da k'arin wata mace kuma Allah na tuba, amma dai seriously zama bai ganka anan ba, can din dai daka guda zaka koma domin kasan yan magana sunce kula da kaya yafi ban cigiya, kar ka zauna anan ka saki baki acan kuma sai ka koma kaji ana wani zancen daban"
"To idan na koma taya zan tun kareta, sanin kanka ne cewa soyayyar nan ni bak'onta ne, ban tab'a yin so ba balle in san yanda zan sarrafa ta wajen aika sakon inda ya kamata,"
"Karkaji komai indai soyayya ne matakan ta ai ba tsaurara kamar yanda kake zato bane, mataki na farko da zaka fara takawa shine jawota a jiki,
Kaga duk wannan muzuran naka da kiran zan zane miki jiki da kakeyi, tofa duk ajiye su zakayi a gefe ka koyo tausasan kalamai wajen yin magana da ita,"
"Kai ban gane tausasan kalamai ba? D'an daudu kake son in zama a gabanta ne ko me? Kana ganin ta fa itama a taitsaye take kamar shinkafar da aka jik'a da ruwan zafi aka tsame, ita ba tafashe ba ita kuma ba dahuwa ba, yarinyar nan da zafina ma ba tsorona take ba in kuma naje mata a sanyi sanyi aishi kenan sai ta karasa maida ni mahaukaci,"
"Oh to a tsai-tsaye zaka tafiyar na naka salon soyayyar kenan, to ai yayi dama irin salon ai yafi bada citta, nidai ai mafita nike baka, indai kana son ta tofa dole ka ajiye duk wani girman kanka a gefe ka jawota a jikin ka har ta shak'u dakai, idan hakan ya kasance tofa bazaka sha wahala wajen yad'a manufofin kaba, jawo ta jikin naka kuma ya had'a harda d'aukarta kana d'an fita da ita yin siyayya haka ko kuma shan ice cream in ban manta ba tun a shekarun baya na Santa da son cin kaza, nasan ka gane mai nike nufi ta wannan gefen, amma tsakani da Allah karma kace ban fad'a maka ba zaka sha fama, dan kalarta ne kalar macen da suka kasance burin kowane cikakken namiji,
Dan haka sai ka shirya ma yak'i da wadanda zasu fito rububin neman auren ta suma, yanzun dai inaga tunda kwana biyu kai ma baka lek'a ba ai ka tashi mu wuce Zarian kawai tunda mun gama uzurin da yake nan d'in dan dama nima gobe nike son in wuce Wase amma ba kwana zanyi ba.
*Ummiee Zaria*โ๐ผ
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: โ๏ธ๐ฑ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ *DANGINA!*๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ๐ฑโ๏ธ
~{{MY FAMILY}}~
*RUBUTAWA*
*UMMIEE ZARIA*โ๐ผ
```` *Page 48*.....
*Masu ajiyemin sak'o a WhatsApp da masu kiran waya dan suji ya jikin mama ta k'araji, ina mai farin cikin sanar daku cewa Alhamdulillah jiki yayi sauki sosai wallahi nagode kwarai da gaske da kulawar ku gareni ubangiji Allah ya saka da alkhairi Allah yabar zumunci*
*********
Ba tareda wani b'ata lokaci ba Mai Jama'a ya shige ciki, cike da zumud'i domin ji yake kamar wanda yayi shekaru bai sanyata a cikin idanuwan shiba,wani bak'on al'amari yakeji a tare dashi, ada shike nesanta kanshi da kusantar duk wani abu daya shafeta, amma yanzun zuciyar shi cike take da kwad'ayin son kasancewa tare da ita aduk wani saukar numfashi nashi, a cikin zuciyar shi yake fatan Allah yasa yana zuwa ita ce zata tareshi tayi mishi maraba,sosai ya kudura a ranshi cewa zaiyi yaki da koma waye wajen samar ma zuciyar shi abinda take so bazai tab'a gazawa ba har sai ya mallaketa,
dan haka sabon wanka ya shek'a bayan ya fito kuma yad'an murza ma jikin shi mai kana kuma ya feffesawa sassan jikin shi turaren jiki, cikin kayan shi na sawa ya zakulo wani lafiyayyen yadi black blue da akama d'inki dai dai da zamani, manyan kaya ba wani burgeshi sukeyi ba dan haka nema yafi ta'amali da kananun kaya ko kuma suits, amma haka nan yau yaji yana ra'ayin sanyan kayan dan ya burgeta yana kuma fatan ta yaba koda a cikin zuciyar tane, wata bata tab'a kwalliyar daya yaba mata ba amma haka nan yake fatan ita da yayi kwalliyar domin ta ta yaba mishi.
mata ma na d'aukar wanka dan sujawo hankalin mazaje kansu to me zai hana shima ya gwada, dan batun yauba yasan mutane da yawa na tankawa aduk sanda zaiyi shiga ta manyan kaya, shima ya shaida yanda yake ma manyan kayan kyau aduk sanda ya sanya su,
yau kuma ra'ayin kanshi ne yasa zaiyi shigar dan ya burge budurwa,
Tsaye yayi a gaban mirror yana k'arema kanshi kallo fuska cike da murmushin shi daba kowa ke samun sa'ar gani ba,
Wai shi! Shidai ba wani daban ba!
Shifa Abdul Khareem Ahmad Mai Jama'a shine yau yayi shiri na musamman badan komai ba kuma sai dan ya burge budurwa,
Oh Allah shi yasa jama'a kance kar Allah ya kawo abinda bazai wuce ba, dan shima kanshi bai daina mamaki ba, to ya kuma sauran jama'a zasuji a randa komai ya fito sarari?
Shi kadai ya kyalkyale da dariya yana nuna kanshi daya ke kallo a jikin mirror,
"Ka daiji kunya AK an dai fad'i k'asa ba nauyi wallahi, wai duk wannan gayun dan mace kayi shi"
Juyawa yayi ya koma inda ya ke tara hulunan shi, shifa rabon ma daya d'aura hula akan shi inba facing cap ba yasin tun bikin Wase dan ko d'aurin aure zasu inya kama dole in su Musty sun matsa to zai d'auki hulan ne sai ya rik'eta a hannun shi inma ya d'aurata akan shi tofa na d'an kankanin lokaci ne zai cire, sai da ya b'ata lokaci wajen zab'o wacce tafi da cewa da kayan daya sanya kafin ya mata kari ya kafa ta a kanshi ya wani cakota zuwa gaban goshi,
(Hohoho jama'a ku hasko min kyau a wajen nan, kyau iya kyau wanka iya wanka, yau AK ne ke gayu dan ganin ya wafto zuciyar yarinya kota halin k'ak'a)
Yafa wanku ya kuma d'auku kaya kuma sunbi jiki sai zabgaga kamshin yan gayu kawai yake abunshi , turaren shi da yasan Meenal na matuk'ar kauna ya d'auko, feeeee feeee feeee haka ya dunga feshema jikin shi turaren nan kamar ba kud'ade masu nauyi yasa wajen siya ba, agogon ya d'auko ya d'aura sai glass din shi shima kalar kayan jikin shi takalmin shi kuma half cover ya sanya,
D'as ya fito a AK d'in shi namijin da yan mata ke marari, babu abinda ya d'auka sai mukullin mota da wayoyi da kuma jakar laptop, fitar shi daga cikin d'akin yayi dai dai da fitowar Yusuf daga cikin d'akin da yake sauka in yazo gidan shima, kamewa yayi kam kamar gunkin da aka sassaka aka ajiye a gidan tarihi idanuwa a waje baki a hangame, kallon kurillah yake bin AK dashi cike da mamakin wannan sauyi na farat d'aya da yake kan gani a tare dashi,
Lallai ya yarda so na sauya mutum dan kuwa ga tabbaci nan a gaban shi zahiri yana kallo,
girgiza kai yayi cike da mamaki yakai hannun shi guda d'aya ya mari gefen fuskar shi,
"Kai jama'a wallahi dai ashe ba mafarki nikeyi ba, Ah lallai da gaske kake mutumina wannan kalar gayu har ina eh gaskiya na yarda lamarin nan bana wasa bane, da gaske aure kake so bana kam irin wannan kamshi kamar mai shirin tada gari"
Cogewa shima AK yayi yana zabga ma Yusuf din harara cike da haushi yace....
"Amma dai kasan agwagwa tayi kad'an tace zatayi ma kwad'o gorin wanka, shiga kuma ra'ayina ne sanin kowa ne cewa tun ba yau ba dama ina sanya sutura duk kalar da nike buk'ata a sanda naso domin jin dad'in kaina, kar kayi zaton dan na fara son wata hakan zai sa in canza tsarin rayuwata ne" ya fad'i hakan yana hararar shi fuska a cunkushe,
"Ah ah yaro ina abun kisisina faso a ido, kana batun tsarin rayuwa, ai tuni tsarin rayuwar ka kam yanzun sai dai muyi fatan Allah ya dai'daita al'amura dan kai kam tunda aka fara da haka allah yasa kar zuwa gaba muga kana tafiya kana sambatu,
Ko ka manta a yanda na same ka d'azun ne? Kai kadai a gado ka wani uban matse filo uwa ka matse mace....."
AK bai bari ya gama furta abinda yake son fad'a ba ya wawuri fillow din kujeran dake kusa dashi ya jefe shi dashi,
"Kasan Allah Yusuf bana son wulakanci, kar kaga na zauna na fad'a maka damuwa na ka nemi mai dani wani d'an iska, ba gara ni ba kai ka manta ne lokacin da Saraki yayi maganar auren ka har ciwon k'arya saida kayi amma dan ubanka ana kai maka ita ko wata 9 cif bata cika ba ta haihu, kuma wallahi sirrina amana ne a gareka ko su Musty ka fad'ama Allah ya isana"
..... "Ah kwarai kam ai dole kace amana tunda kasan abun kunyar da kake guje musu shi kaima ka jajibo ma kanka, kai aini in ban ma fad'ama gayun nan wannan zazzafar labarin ba ai inaga ni kaina sai na zagi kaina wallahi, kaji ma da kyau labarin soyayyar ka labari ne mafi zafin da bazan bayar dashi ba sai an sauke min manyan kud'ade kafin in fesa ma duk wanda yake muradin saurara,
Kana daga zaune zakaga yanda zan kud'ance akan labarin soyayyar ka da yarinyar can"
Dariya harda na mugunta haka Yusuf ya duke yana kyakyatawa,
"Labarin soyayyar tawa ce zaka kasa a faranti kana sai dawa?"
AK ya tambaya cikin sanyin gwuiwa,
"Me za'a fasa Malam mutuwar ko hisabi bari ma kaji in rantse, wallahi ni Yusuf sai ma su Sadeeq sun biyani da tsada kafin in sam musu labarin soyayyar ka dan ba duka zan basu ba gutsura musu kad'an zanyi, atoh alhaki kuma waya bari Malam kazo kana ta yima mutane dad'in bakin cewa kai ka girmi kana nan yara manyan matan ma sai ka zab'a to yane yanzun fa?"
Ya karasa tambayar yana dage mishi giraren shi guda biyu,
"Allah ya isa na wallahi"
Cewar AK da bakin shi ya mace murus
"Allah kam ai isashe ne indai wannan ne nima kaina shaida ne, dan gashi ya nuna isar nashi akan ka ta yanda har ka kasa lankwasa zuciyar ka kayi saken da har ta kamu da son jaririyar yarinyar can da aka haifa a gaban idanun ka, amma dai ko bani ba kowa ya ganka yasan shigar ka ta yau tasha bam bam dana baya, ko ka mantane cewa kai din fa d'aurin aure ne kad'ai kesa kayi shigar manyan kaya haka, dan kai dai ko gaisuwar sirikai zamu ba kasafai kake sanya irin wadan nan kayan ba, dan hakama Babaa karka wani raina ma kanka wayau, to miye a ciki dan ka ma abinda kake so gayu ai ta isa ne duk da kai d'in aiko babu gayun ma mai kyaune, amma ka kira Hajiya ka fad'a mata kana hanyan zuwa kuwa?"
"Kai wai Yusuf ya kake min haka ne!"
Ya fad'a a yayin da ya coge hannayen shi duk biyun dafe da kunkumin shi,
"Gidan mufa zani miye kuma na wani sai na kira Hajiya cewa ina tafe?"
Ya karasa fad'a yana harar Yusuf din.
"Ai kaji tsiyar to ai kai dane kake da damar yima gidan shigar tsinke yanzun kam ai farauta zaka, naga kuwa zuwan ai bana Hajiya bane, kai ina fad'a maka fa indai kana son buk'atar ka ta biya cikin rufin asiri ba tareda ka kamu da hawan jini ba tofa ba iya yarinyar nan zaka lallab'a ba, yasin kai tsaye zan fad'a maka kayi takan tsantsan da lamarin Hajiya so samu ka nunnunka kulawar da kake bata fiye da lokutan baya,kasan dai Hajiya yar rashawa ce yasin kar kaga cewa kai na gida ne na tabbatar da cewa in baka damkowa da nauyi kana mik'awa tofa, abun nan da ake kira gida bai koshi ba shine zai K'ara faruwa, sannan kayi kokarin duk sanda kuka kasance tare ka dunga sako mata hirar yarinyar a wayan ce haka, ta yanda ita da