Showing 90001 words to 93000 words out of 174305 words
Chapter 31 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
zai mata yawa a matsayin ta na Babbar ya'yar amare, dan ma Allah ya taimake ta sun riga sun kamala exam's din su gaba daya,
Koda bukatar Hajiya na komawarta can Tudun wada yaje kunnen Malam baiyi musu akan hakan ba domin koba komai yasan zamanta acan din shima zaifi mishi kwanciyar hankali domin tabbas intana nan sai an samu mai dogon bakin dazai furta batun auren nata a gaban ta.
Ita ko Hajiya kaf yayan ta saida ta kira takai musu karar cewa Malam ya nuna mata mulki da isa akan jikarta ya nuna mata bata da wani matsayi dan haka tana bukatar ganin su in ma bazasu samu damar zuwa ba tofa kowa ya turo da nashi gudun mawar dan tama fi bukatar kudaden da zasu turo akan zuwan nasu domin kayan yar gata takeso ta hadama jikarta dan Malam yasan cewa kullum cikin shiri take ita batayi gadon tsiya ba, to dai suma tunda Allah yasa sun san ko sunzo a lokacin ba wani tsiyar zasuyi ba domin infa Hajiya ta kafe ta kafe kenan yasa sai kudaden data bukata suka tura mata, ita kuma taci gaba da shirye shiryen ta na auren jika,
Tsaf ta shiga ta fita tabi kwakwafin wanda za'a aurama jikar tata acan ne kuma tajiyo abinda batayi tsammani ba, wato ashe kiyayyar da Malam kema Jiddan ta har ya kai ya dauki yar Jidda yaba yaron dan uwan shi da matar shi ta gagari kowa!
Yanzun da ace bata raye kenan haka za'ayi auren ba tareda an shirya Meenal din ba gayarta za'a dauka akaima kishiya wato taji dadin nakasa ta da kyau, to ai in sun san wata basu san wata ba ita kam da ranta da lafiyarta bazata sadaukar da rayuwar Takwarar ta, dan haka tuni itama ta zage damtse wajen neman ma Meenal din duk wani maganin da tasan na tsarin jiki ne sai da ta tanade shi,
Satin farko na komawar Meenal gidan bata fuskanci ko wani damuwa ba, domin dai Hajiya bata takura mata kuma duk inda suke bukatar zuwa yawon rabon anko da katin biki Dan gidan Master ne ke zuwa yana kaisu dan sosai yakeji da Meenal din a kokarin shi nason ta bashi dama ya gabatar da kanshi a gidan su tunda gashi allah yasa har za'a aurar da kannin ta yasan koya nema baza'a hanashi ba domin shi baiki ba wallahi a hada bikin ma dana kannin nata, amma yasan Hajiyar tashi ba yarda zatayi da hakan ba
sosai fa ta samu yanda take so a wajen Dan gidan Master dan sosai ya bud'e mata bakin aljihu take ta dandake kan nerori domin dai duk abunda take so jiki na rawa yake mata shi,
Gashi kuma kwanan nan ta lura ba Malam kadai ba yanzun harta da Mommy Hauwa sosai take sake mata fiyeda lokutan baya domin abun mamaki kulum cikin tambayan ta abunda take so take ga yawan daukarta da sukeyi zuwa kasuwa ita dasu Meelat zuwa siyayyar kayan da take zaton nasu Raheenat ce domin dai dama ko yayyin su maza in zasuyi auren Mommy ne ke hada musu kayan auren, dan haka sai bata damu ba a zaton tasan kila dan Mommy tasan in tace su Raheenat din suzo suje kasuwar tasan ba lallai su sake jiki su zab'i abubuwan da suke bukataba shi yasa, dan haka ta zage damtse da zuciya d'aya ta maida hankali ta dunga d'aukar duk abunda taga ya mata kyau dan tasan dai auren dole ne za'ama kannen ta to amma inta bada nata gudun mawar wajen ganin an shirya musu dakunan su da kyau tasan hakan zai rage musu damuwa,
Bawai kananan siyayya kadaiba hatta da kayan gado dasu kurjeru komai ita ta zaba musu sai dai abunda bata sani ba harda nata kayan ta zaba'a domin komai itama sai an tambayeta choice din ta, cikin sauk'i dai abubuwa sukaci gaba da tafiya,
Biki ya rage saura sati biyu Mai Jama'a ya duro Zaria domin duk wainar da ake toyawa baya gari yaje Lagos akan wasu harkokin su, ita kuma Hajiya hidindumun data sa a gaban ta sun sha mata kai dan haka ko a waya bata tuna ta bashi labarin abunda ke faruwa ba, a kuma sati biyu da bikin ne Hajiya tasama Aminatu takun kumin fita domin zuwa lokacin ta gama hada duk wani tanadi da tayi domin gyarar jikar nata, ta kuma fad'ama harta da masu gadin gidan cewa koda wasa suka kara barin Meenal din ta fita saita b'ata musu rai wallahi.
Ganin cewar Meenal ba had'in kai zata bata ba yasa ta fada mata cewar maganin ciwon marar tane ta amso mata kuma ka'idar maganin sati biyu ake shanshi kuma in an fara amfani dashi ba'a zuwa ko ina gida ake zama dalilin ma da yasa tace Jidda ta maido mata da ita nan kenan, in kuma bata bukatar ta warke ga kofa nan tana iya komawa gidan su,
Saida Meenal ta kirga kwanakin daya rage mata kafin zuwan al'adarta sai taga kwanakin duka basufi goma ba, to kenan in har tabi umarnin Hajiya ta zauna tayi amfani da maganin tana sa ran kenan wannan watan lafiya lau zatayi al'adarta kamar na sauran mata, gashi kuma dama tsoron da take ji kenan domin lokacin zuwan nashi a lissafin ta zaizo a cikin bikin ne dan Haka ba komai zata jure zama dai na kwana kin a gidan Hajiya ai mai sauki ne in aka hada da wahalar da take sha duk wata, sai dai gaskiya za'a takura mata dan bata gama rabon katin biki ba amma ba damuwa tunda gasu Moon zasu iso ga kuma su Meelat a gefe, sai dai kuma ya zatayi da yan anacen samarin ta da bata amshi kudaden data yanka musu na anko ba? Wannan ma ba damuwa tunda dai ga waya shi dai Dan Master tasan shegen kwakwa gareshi dole sai yazo inda take dan ma ta gode Allah iliya dan mai karfi bayanan balle yasa mata ido,
Ita fa gaba daya bata damu ba domin dad'inta kawai takeji cewa zatayi bikin kannen ta cikin koshin lafiya batareda mutane sun taru akanta suna faman yi mata sannu kamar mai ciwon mutuwa ba.
Bayan dawowar AK yayi mamakin ganin Meenal kwana 1&2 a gidan batareda ta koma gidan suba dan iya sanin shi yasa inba dai Moon sunzo ba tofa bata yarda ta kwana a gidan ranar dai ya gaji da ganin nata dan Allah ya sani yarinyar nan fa ba karamin takura mishi takeyi in yana waje ba, dan yanzun ma wani sabon iskanci ta tsira da zarar ta hango shi saita fara mishi wakar da in tanayi yake jin kamar ya shako wuyarta har saita daina numfashi kafin ya saketa, wai shi yarinyar nan take ma wakar.. .. .. Turun turun tuzuru wai yaushe zaka auree.
Tuzuru wai yaushe zaka aure....
Wai shi shi din nan da girman shi da mutunci da komai amma tsabar rainin da yarinyar nan ta mishine yasa har take mishi wakar tuzuru wai yaushe zaiyi aure, insha Allah duk ranar daya riketa sai ya fada mata taje gida ta tambaya shekarar Baban ta Adamu nawa yayi a duniya ba tareda mata ba in yaso sai tazo ta hada shekarun da nashi aga wayafi wani zama tuzuru a lokacin!
Suna zaune a falon Hajiya tuwo yake ci kamar yanda kowa yasan yafi son cin abinci mai nauyi, "kinyi wanka da ruwan maganin dana hada miki? " Hajiya ta tambaya Meenal wacce fitowarta kenan daga dakin da Hajiya ta sauke ta, "eh nayi"ta bata amsa tana wucewa cikin kitchen da plate din dataci abinci a hannun ta, Saida yaga kulewar ta sannan ya waigo gefen Hajiya,
"Me yarinyar nan takeyi a gidan nan wai?"
"Ban gane me takeyi a gidan ba!"
"Eh na tambaya ne saboda nasan ba zuwa takeyi haka nan ba balle kuma harta kwana gashi kuma tunda na dawo nike ganin ta a gidan kuma na tambayi bala yace min tayi kusan sati a gidan ko laifi tayi a gidan su ta gudo nan? "
"Kai dai ka sani da neman ba'asin ka, yarinya ita da gidan kakan nin ta ka kama tambayar me takeyi gaskiya dai ka canza hali wallahi"
Ta fada tana karkata dan kwalin kanta zuwa gefe a dai dai lokacin ne kuma Meenal din ta fito daga kitchen waya kare a kunnen ta amma cikin su babu mai iya jin abinda take cewa a wayar harta wuce su ta koma d'aki,
Sai da Hajiya ta tabbatar ta shige sannan ta baro kujerar da take zaune ta koma wacce mai jama'an yake kai, duk wannan kusancin da suka samu bai wadace taba sai da tayi kasa da muryar ta sosai tana kara kallon kofar dakin da Meenal ta shiga kai da ganin yanda takeyi ko ba'a fada maka ba kasan cewar irin gulmar nan dako kuda ba'a son yaji shi take Shirin yi.
"Aure fa uban ta zai mata karshen watan nan.... "
Wani irin mummunar shaka romon daya surb'a a lokacin ya mishi domin har cikin kwakwalwar shi romon ya wuce, aiko sai tari ya biyo baya domin a lokaci guda yaji kurjin shi ta dauka da wani irin radadi kamar na wanda aka watsama barkono akan ciwo, dan haka tari yace bani wajen, tari yake cikin azaba idanuwan shi har sai da suka zubda hawayen azabar da yakeji,
"Subhanallah innalillahi sannu sannu sannu Abdul sannu, haka Hajiya ta dunga jera mishi sannu ba kakkautawa sannan ta mika mishi ruwa ya samu yasha kafin ya samu tarin ya lafa mishi da kyar,
"Sannu yajine ya tsarke ka koh ai Saida na fadama takwara ta rage attarugun data zuba dan kar yayi yaji amma tace min farfesu in baiji yajiba baya dad'i wannan ai daukar Alhakine,
Kara shan ruwan zakaji ya sake ka"
Karbar ruwan yayi ya kara sha yana mai jama'a jingina kanshi a jikin kurerar, ba tareda ya iya cema hajiya komai ba duk sannun da take mishi kuwa dan so yake ya tuna abinda yaji ta furta wanda yayi silar da yasa roman nan haura mishi saman kai,
Saida yaji yadan sarara sannan ya kamo hannun hajiya guda dake kisa dashi, jajayen idanuwar shi da basu koma dai dai ba har yanzun da jansu ya zuba mata.
"Hajiya mai kikace d'azun? "
"Umm bari kai dai Mai gida ai wallahi nasan dole ka tayani jimami, kai ma kajishi wani bambara gwai koh? Wai Yar wajen Jidda fa za'ama aure karshen watan nan yau dai saura yan kwanaki"
Bai bari takai karshen zancen taba ya tari numfashin ta da cewa"wai wancan yarinyar ce za'ama aure?"
Sai da kara gyara zama ya fuskance ta da kyau sannan ya kara cewa"wai auren gaske ko na wasa kike magana akai Hajiya"
Wani kallon karfa ka raina min wayau Hajiya ta mishi sannan ta bashi amsa da cewa "dama akwai auren wasa ne Abdul Khareemu? Kuma kayi kasa da muryar ka karka tadamin balli dan ita kanta yarinyar bata san da zancen auren ba dalilin da yasa ta dawo gidan nan da zama kenan har zuwa lokacin bikin dan ba'a son ta sani,"
Sai da ta bata fuska cike da jimami ta daura da cewa "kuma kaji wani cin amana Soja fa zasu aura mata Sojan ma mai mata harda yaran shi 4 ba kuma iya nan tashin hankalin ya tsaya ba domin dai ita matar sojan in fada maka babu ubanda bai san yanda ta shanye mijin ba sai yanda taga dama taje juyashi ko iyayen shi baya tunawa dasu, amma dan cin amana aka dauki jikata aka bashi, fadamin dan Allah inba sun shirya ganin bayan jikata ba mai zai sa suyi haka yarinyar dako ruwan zafi bata iya dafawa ba, shi yasa kaga na kasa zaune na kasa tsaye ina ta faman shiga da fita wajen neman mata magungunan tsarin jiki, atoh ban nemi kowa da sharri ba duk wanda ya nufamin jika da sharri shi zaiga abunshi,
To bagashi ba daukotan da nayi yayi amfani tunda a yan kwanakin nan fa tare muke shiga kitchen ina nuna mata abubuwa dan Sam Jidda bata koya mata komai ba kuma a haka suke son aurar da ita, nayi magana iyayen ka sunce wai babu ruwana ai iyayen ta sun fini iko da ita, to fisabilillahi so suke insa ido a nakasa min rayuwar jika? "
Shidai tunda ta fara magana fuskan ta kawai ya kafe da kallo wai aure Aurefa wai za'ama waccen jinjirar wannan aure za'a mata ko raino dai za'a kaima mijin? Ga manya manyan yan mata nan ba'a aurar dasu ba sai wannan yar tatsitsitar hanci duk majina kai cike da rashin kunya, Allah ya sani ya tausaya mata ya kuma tausaya ma wanda za'a daurama auren ta dan yasan zai sha fama.
Babban abun da yake kara daure mishi kai kuma shine cewar da Hajiya tayi wai yarinyar bata san da batun auren ba, to kenan dai auren dole iyayen ta zasu mata? Shifa tsakanin shi da Allah sosai abun ya daure mishi kai domin shidai kullum yakanji ana maganar auren dole bai taba gani ba sai gashi yau a kusa dashi, haka nan kawai kuma sai ya farajin tausayin yarinyar yana shigar shi, karamar yarinya a rasa ma mijin da za'a aura mata sai soja kuma ma mai mata harda yara koya zataji duk ranar da taji batun auren?
"Lallai akwai rikici " ya fad'a a bayyane,
"Akwai shi kam sai dai muyi fatan Allah yasa auren shine mafi alkhairi a gareta"
"Ameen" ya amsa dashi yana yunkurawa da niyyar barin wajen domin a yanzun kam bayajin zai iya cin wani abu kuma dan gaba daya abincin ya fita akan shi.
"Tafiya zakayi kuma baka gama cin abincin ba? "
"Nakoshi Hajiya sai da safe" ya fad'a yana ficewa daga side din gaba daya, sai da ta kwashe kayan sannan itama ta shige.
Satin biki.
Tako ina fa kowa ya shirya ranar auren kawai ake jira,
Su Aisha Moon da iyayen su duk sun iso garin Zaria, sai dai suma komai da sukeyi cikin taka tsantsan sukeyin shi domin dai kar a fasa maganar harta koma kunnen Meenal, Hajiyar ku ko ta dage da shan magani domin duk abinda hajiya ta bata amfani take dashi a sonta na ganin anyi hidimar biki da ita lafiya, samarin ta kuma tuni ta amshi kudaden ankon data yanka musu, wasu sukan zo har nan gidan ne in sunzo takan saci jiki ta fita ko kuma ta tura Rukayya ko su Meelat su amso mata in tana bukatar wani abu a gida kuma cikin yayyen ta wani ke kawo mata domin shima dai ya sa'eed yayi busy da nashi shirin bikin,
Zuwa yanzun kam ba karamin tausayi Meenal keba AK ba domin dai shi Allah ya sani har yanzun bai fara mata kallon mace ba balle kuma wai ace matar aure, hakan nema yasa yau da ta fito daga sashen Hajiya zata sashen Hajiya jummai ya kura mata ido, Kai jama'a Allah dai ya tsine ma shedan la'anan ne inba shedan da kitsama mutum mugun abu a zuciya ba dan Allah yana zaman zaman shifa a kofar gida cikin abokan shi kirar wayar shi da wani abokin kasuwancin yayi ne hakan yasa dole ya shigo gidan dan ya samu damar amsa wayar a tsanake ya gama wayar nefa sai ya dan zauna dan akwai wani number din da abokin zai tura mishi shine fa kafin shigowar number din yarinyar nan ta fito tana waya, kuma yasan dai wayar nan bazai wuce da shegen yaron nan Bash Dan gidan master ba dan yanzun yaga yabar kofar gidan bayan ya sauke daya daga cikin kannen shi ta shigo gidan, yana mamakin ta yanda har yanzun saurayin nata bai san da batun auren da za'a mata ba, koda yake abune anatayin shi a munafunce, da farko dai yanda take ta fara'a har fararen hakoranta dake jere gwanin sha'awane ya dauki hankalin shi har yabi fuskar nata da kallo, tofa a kokarin shi na ganin ya dauke fuskar shi akanta ne yayi kasa da idon shi, shine dan wulakanci irin na sharrin shedan idanuwan shi suka wani ja burki suka tsaya akan kirjin ta doguwar rigar atamfa ce da akayi ma dinkin fitetgown ga shi kuma dinkin yayi dai² da jikin ta kuma dan iskanci haka nan ta wani fito a bunta ko lillibi babu, shi dai bai son yanda akayi daga kallon fuska ya koma karewa sauran sassan jikin ta kallo ba, Allah ma yaga zuciyar shi bai kalleta da wani manufa ba sai dai sharrin shedan yasa ya kasa dauke idon shi a kanta dan koda ta wuce shi ya zamana ta juya mishi baya haka yaci gaba da kallon ta zuwa lokacin kuma sai yaga kamar ma da gangan takeyin wani abun saboda yanda duk inta motsa shima jikinta yake motsawa gaba daya kasa katabus yayi har sai da ya dena ganin ta bayan ta kule ma ganin shi, a rayuwar zai iya rantsewa da Allah cewa yaune rana ta farko daya tsaya ya karema halittan wata diya mace kallo domin duk wadanda ke binshi baima da lokacin su balle har ya bata lokaci wajen kallon surar ta,
Inba shedana irin na shedan ba duk wannan kallon bai wadatar da shiba har Saida zuciyar shi ke raya mishi wai duk wannan abubuwan da ya gani fa a jikin yarinyar nan a hakan ma fa wai dan bata gama girma bane to in tafi haka kuma ya zata zama kenen? Haka kawai shedan ya fara hasko mishi ita a matsayin cikakkiyar budurwa, bakon al'amarin da ba kasafai yafiye samun shiba sai ga shi yau da rana tsaka sharri irin na shedan yana so yasa shi a shiga uku domin dai sai ga shi gaba daya tsigogin jikin shi da duk wata jijiyar da jini ke yawo a jikin shi ta motsa domin dai alkalim rubutun shi da koshi bayace ga ranar da