Showing 57001 words to 60000 words out of 174305 words

Chapter 20 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1867

karamin yaro ya muku kuka kaishi police station da sunan tsintuwa alhalin ba hakan bane?"
Ya Kara jefo musu tambayar,

"Mufa tsintar shi mukayi"
Meenal ta bashi amsa,

"Karya kukeyi, ku fadamin me yasa kuka aikata abinda kuka aikata din? In ba haka ba jikin ku zai fada muku, "

"Kayi hakuri dan Allah wallahi mun dena daga yau bazamu karaba"
Cewar Meelat dan itafa a duniya bata kaunar abinda zai tabi lafiyar jikin ta wallah,

"Ni ai ba hakurin ku na nema ba dalilin dayasa kukayi hakan nike son sani"

Meenal ce ta amsa mishi da cewa,
"Aini dama koda na kai yaron can nayi hakan ne saboda in Baban shi ya amso shi gobe koda bacci Maman yaron keyi in yaron na kuka bazai tsallake su ya fice a gidan ya barta da dawainiyar yaron ita kadai ba, kuma ai dan ma mu ne taba yaron fisabilillahi da ace masu Satan yarane taba shi bashi kenan ba, kawai daga ganin mu zamu wuce ta kofar gidan ta saita dauki danta ta bamu, yanzun ai sai suje su sulhunta yanda zasuci gaba da rainon yaron atoh, gobe ai bazata Kara bama wasu shiba ko kukan me yake kuwa shima Uban kuma dole ya koyi raino daga yau"
Ta karasa fada tana kauda kanta gefe,
Ba Kwaro ne kadai ya cika da zallar mamakin karfin halin yarinyar ba harda Meelat ma kallon mamaki take mata.

"Me yake faruwa anan? "

Cewar Sarki daya maido hankalin shi kansu bayan tashin dayan mutumin,

"Ku sai yanzun kuke dawowa tun fitar safe da kukayi? "
Ya Kara tambaya,

"To ai ya Mashkur ne yace mu jirashi ya dawo sai mu wuce gida kuma ko yanzun ma bai dawo ba muka taho,"

Meelat ta bashi amsa, ita ko Meenal a dubarance take ma Kwaro magiya akan ya rufa musu asiri karya fadama Sarki abinda suka aikata.

Kuje har gida zuwa gobe kuba matar hakuri, kuma in bakuje ba nida kune wallahi"
Cewar Kwaro, a yayin da ya amsa Meenal da kai cewar bazai fadama Sarki ba,

Ku tashi ku wuce gida" Sarki ya basu umarni,
Kamar wadanda suke kan kaya haka suka zabura ba tareda bata lokaci ba suka bace awajen Wai Allah ansha da kyar.

Koda suka shiga gida kuwa koda wasa basu tada maganar ba,

Abubuwa da yawa sun faru a wannan kwanakin ciki su harda zuwa gidan Zainab din Bala uwar yaro bada hakuri duk da basuje a ranar da Kwaro yace ba,


Sannan ba fashi kullum sai sunje tudun wada,
dasu aketa hidimar biki sai dai boyewa suke da sunga an fara taso su gaba da yawan aike,

Tsakanin Meelat da Musty kuwa kullum ko basuga juna ba sukan zanta ta waya ko sakon text albarkhacin shi yasa duk wani program da aka shirya na biki sai da suka samu halarta kamar yanda suka tsara.

An gama hidimar biki lafiya su Maimoon sun koma garuruwan su sai dai koda yaushe sukan zanta a waya, sukanji nishadi a sa'ilin da suka tuna irin shirmen da suka shuka na zuwan su wannan biki da bashi goguwa a cikin tarihin rayuwar su, wanda ya kasance biki na farko da Meenal ta taba shiga ciki akayi komai da ita ba kamar lokacin baya da takeyi kamar me tsoro mutane ba,
babban abinda in suka tuna suke kara sadaqarwa da iya shegen Meenal shine ranar yinin bikin da tasa ma yan matan da sukazo ma Mai Jama'a biki maganin amai a cikin Lemun 5alive suka sha suka dunga competition din amai gwanin tausayi daga karshe sai cewa akayi wai lemun ne yayi expired bayan ba hakan bane.


Ana daurewa ana comment da sharing please.

#Ameenatu. 🧕🏻
#Team Sarki. 🤴🏼
#Team Mai Jama'a. 🤵🏻‍
#Sheikh Naseer.👨🏻‍💻
#Ummiee~Zaria
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*


*👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_



ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._

*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}

*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._
*Ga masu tambayar littafin daga farko zaku iya tuntuɓata kai tsaye da wannan number ɗin 08061358462,*
Karku manta littafina kyauta ne banyi shi dan in siyar ba dan haka karkuji ɗar kuba duk wanda kuke so.

Free book ne yan bati a dage da karatu a daure a dunga comment atoh.



```Page 19


........... Zaune take akan kujerar daya kasance mazaunin ta na din-din-din a cikin ajin nasu yayin da ta yada kanta akan tebur din dake gaban ta sai faman ciccije bakin ta take sakama koh mararta data kejin tana ta kara daure mata kamar yanda ta saba mata aduk sanda lokacin yin hailarta yazo, kwata² batayi zaton zuwan nashi a wannan lokacin ba domin a lissafin ta ko zaizo mata sai sati na gaba dan haka bata fito da shiri kamar yanda ta saba shirya ma zuwan bakon nata ba, dan hatta da pad da take yawo dashi aduk sa'ilin datake tsammatan zuwan period din nata yawancin lokuta a cikin jakanta domin yin kunzugu yau bata da koh daya a cikin jakar nata, gashi a hankali mai makon ciwon ya ragu sai karuwa takejin yanayi alhalin lafiya lau ta fito daga gida, agogon hannun ta takallah sai dai har yanzun akwai sauran lokaci akallah kusan awa uku kafin lokacin tashin su zuwa gida,
Tasani sarai cewa ba lallai ta iya jure zafin ciwon zuwa anjima gashi kuma daga Jamila har Maryam basa ajin dan a cikin su ita ce kadai ke science,
"Amina Mukhtar"
Malamin chemistry din nasu ya kira sunan ta,
Bata iya amsawa ba illah dago kanta da tayi ta kalleshi da idanuwan ta da suka farayin ja alamun dake tabbatar da cewa akwai abinda ke damunta.
"Are You alright? "
Ya tambaya.
Bata iya bashi amsa da baki ba illah girgiza kanta da tayi kawai ta Kara maida kan nata,
To shima dai ganin cewa in ma ciwo take ai tasan inda zataje ta amshi magani yasa bai Kara bi takanta ba har ya gama koyarwar shi ya fita a cikin class din,

Sakina ce ta baro sit dinta zuwa na Meenal dan tun tuni take lura da ita ta tabbatar da wuya inba ciwon cikin ta na fama bane ya tashi mata ba.

"Meenal ya kamata ki tashi kije gida fa tun kafin ki galabaita muje in raka ki ki dauki permission dan nasan bazaki iya jurewa har a tashi ba" cewar Sakina,

"Kira min su Maryam" inji Meenal din,

"Ah-ah tashi dai ki gani in kamaki"
Ta furta hakan a yayin da ta mika hannu ta dauko jakar Meenal din na makaranta dake gefe, sauran yan ajin ne suka taso kowa na tambayan meya samu Meenal din, ita dai Sakina bata da lafiya kawai ta iya ce musu,
"to mu kaita clinic mana"
cewar daya daga cikin daliban yayin da sauran sai faman Sannu suke mata da addu'ar samun lafiya,
Da kyar ta samu ta iya mikewa bayan sakina da wata yarinya sun tallabo ta,
"karku kaini clinic gida zanje" ta samu ta iya furtawa da kyar dan zuwa lokacin dauriya kawai take amma gaba daya ji take kamar ana sanya igiya ana daure mata marar nata tsabagen yanda take jin ciwon,
bafa karamin dauriya takeyi ba wajen hana kanta kuka a halin da take ciki, dauriya na duniya ta aro ta daura ma kanta gudun kar tayi kuka da ihu a gaban yan ajin su su rainata illah dai matsar hawaye kawai da takeyi su kuma suna Kara mata sannun a haka har suka samu suka karasa Staff room domin daukar permission, Aunty Hajara daya daga cikin Malaman su mata kawai su ka samu a wajen tanayin marking din wasu littafai,
Da kulawa ta dago tana kallon su ganin kusan gaba daya yan ajin ne suka rako Meenal din "lafiya meya sameta? " ta tambaya a yayin da tabar abinda takeyi ta taso zuwa inda suke rirrike da Aminatun da take ta kokarin dukewa zuwa kasa,
"Lukman Kira Malam Sa'idu yazo ya wuce da ita gida"
A tsinke su Maryam suka shigo cikin office din "Meenal meya sameki? Ciwon cikin ne ya tashi?"suke tambaya duk sun gigice dan su ganau ne ba jiyau ba na irin yanda take wahala da ciwon marar ta duk wata,
"Aunty Hajara kin Kira Mommy ne? "
Maryam ta tambaya,
"Ban Kira kowa ba nadai tura Lukman ya Kira Malam Sa'idu sai ya kaita gida"
Wayarta dake gefe ta dauko dan ya kamata ta tambayi Maman Aminan taji ko za'a wuce da Aminan asibiti ne sai dai kuma Kira uku ta mata amma duk kiran basu jeba,
"Ban samu Maman ta a waya ba"

Maryam ce tace to tunda ba'a sameta ba akai Meenal din gida kawai,
Lukman ne ya shigo Malam Sa'idu biye dashi a baya.

"Ku fito da ita ku kuma ku koma class" yace a yayin da ya juya zuwa inda motar shi ke ajiye,
Fita sauran student din sukayi bayan sun mata fatan samun lafiya su kuma su Jamila da Aunty Hajara suka kama Meenal din da zuwa yanzun ko iya mikewa batayi balle harta tsaya akan kafafun ta, haka dai suka tallabeta zuwa cikin Motan,

Aiko dai uwar Malam kamar jira take a shigar da ita cikin motar dan tun basu bar cikin makarantar ba ta fara ihun kuka tana tumurmusa a jikin su Maryam kamar wata mai nakuda,

Fadi take tana karawa cikin ihun kuka...
waiyo Allah cikin ta tun tana kiran ciki har ta koma fadin waiyo Allah mararta zai balle shike nan mutuwa zatayi,
haka dai ta dunga sambatu barkatai dan dama hakan yake mata gaba daya in ciwonya taso saita fice a hayyacin ta tayi ta surutai marasa kan gado,
tun su Meelat na mata sannu har suma dai ganin wahalar da take sha yasa suka fashe da kuka suna kwantar mata da hankalin cewa bazata mutu ba zataji sauki ne,

gaba daya haka suka cika motar da ihun kukan su yanda kasan duka su ukun ne masu ciwon,


"Dan Allah ni kumin shiru yan rainin wayau kawai ku barni inyi kuka na kunzo kuna ta cikamin kunne da naku ihun kukan,
Ko ubanwa yace muku naku kukan zai ragemin ciwon ne,
Waiyo Allah Baba Malam dan Allah driver ka tuka motar nan da sauri kafin mala'ikun mutuwa su karaso"

tana damke da marar nata fa amma sai gashi tana bude kofofin hancin ta tana shin shine shin shine,

"Bakuji kamshin turaren al miski ba? Allah kuwa suna kusa da motar nan, ni kayi sauri ka kaini gida direba Ina jin ina kusa gab da suma, saura fa kadan in some karku barni in suma wallahi suma kanin mutuwa ne, ka kara gudu karsu Kara so su dauki raina ban roki yan gidan mu gafara ba, kunga fa kana nan yaran dake gidan mu dukan su nikeyi in sunmin laifi kar fa yazo ace wata rana sun min Allah ya isa a bayan idona."

Kara fashewa tayi da kuka,
"Waiyo Allah ni Aminatu Ashe mutuwa na a kusa yake shi yasa kwana biyu niketa mafarkan koraye da fararen furanni,"
cikin kuka sosai sakama kon marar nata data Kara murda mata taci gaba da cewa.
"Allah sarki ni Ashe mutuwa zanyi tun ban gama sakandire ba, jama'a in na mutu wazai ginama Baba Malam gida a Abuja? Waiyo Allah zan mutu ko saudiya banje ba,banje hajji ba balle umara, banje na ziyarci ka'aba ba balle har in taka madina,
Hajiya innah ke kikace wannan shekarar dani zaki inyo umara in zaki duba Abba Ahmad, waiyo Allah sarkar zinare ta dana aje sai da sallah zansa"

(Kai jama'a, ku matsofa inga rabon gado uwar Malam zata yi karta manta damu a lissafi 🥳)

Cikin sheshshekar kuka Maryam tace "Meenal kiyi shiru dan Allah kince mu daina kuka dan bazai rage miki ciwo ba, amma ke kuma baki dena naki kukan ba bayan kuma kin san naki kukan ke jawo wa muma muyi kuka dan Allah ki dena surutan nan babu kyau kiyi Addu'a"

Sai da taja majina sannan ta maida kallon ta inda Meelat da itama fuskarta yayi jagab da hawaye tana kwabe fuska tace,

"Besty kina jinta koh zagina fa take son yi da wayau,
So take tace na fiye raki kuma wallahi ba raki bane sosai marar kemin ciwo fa, sa hannun ki kiji yanda fatar wajen tayi Zafi waya sani ma ko gobarace ta kama a ciki"

Kamo hannun Meelat din tayi ta kai kan marar nata ta matse,
"Ki danna min dan Allah karya fashe"

Kafin su isa gida gaba daya ta riga ta gama fita hayyacin ta, har cikin farfajiyar gidan Malam Sa'idu ya shigar da motar shi da yike ranar aiki ne kuma gaba daya yaran gidan suna makaranta hakan yasa ba yaro ko daya a harabar gidan,
Kashe motar yayi bayan ya faka sannan ya juyo yana tambayan su Maryam cewa wanne ne sasan su Aminan?

"Wajen Baba Malam zamu shiga da ita dan dazun da safe tace min Mommy taje Kaduna kuma nasan bai isa ace ta dawo ba"

Allah da ikon shi suna cikin maganar saiga shigowar Sarki cikin gidan da alama yazoma Malam sallama zai koma bakin aikine domin ko shirye yake tsaf cikin kakin shi na aiki, baima lura dasu ba har sai da ya nemi gifta su dan koda ya shigo dama wayace a kunnen shi,

"Assalamu Alaikum bawan Allah nace ko zaka taimaka naga kamar cikin gidan zaka shiga, Amina Mukhtar ce bata da lafiya ni din Malamin makarantar sune"

Ya karashe fada A yayin da ya mikama Sarki hannu domin suyi musabaha.

Duk yanda su Meelat ke tsoron shi yau ba wannan batu domin suna an Karewa dashi a wajen tauni sukayi azamar fitowa daga motar,

"Ya Sarki dan Allah ka taimake mu Meenal zata mutu zoka gani ta dena motsi"
Jan hannun shi Meelat tayi suka zagaya ta daya gefen inda Maryam ke rungume da Meenal din data dena motsi zuwa lokacin sai faman jijjigata takeyi tana fadin ta tashi karta mutu ta barsu,

ita ko Aunty Hajara tsabar rudewa yasa gaba daya ta kasa aiwatar da komai zaune kawai take a cikin motar itama tana hawaye, dan tsayin rayuwarta bata taba ganin inda ciwon mara ke galabaitar da mace irin haka ba, Ashe haka wasu mata ke faman shan wahala, lallai duk mace da period ke zuwa mata ba tareda ko wani kalar laulayi ba to taci gaba da mika godiyarta zuwaga ubangijin al'arshi.

"Ibrahim!
Ibrahim!!
Kai Kwaro!!!!!!
Wai kana cikin rijiyane da baka jin Kira"
da gudu kwaro ya shigo gidan,
"A fuwan Sarki "
Bai tsaya sauraron abinda kwaro zaice ba yace ya kunna mota yanzun nan, shi kuma ya zura hannayen shi cikin motar ya dauko Meenal da batama san wainar da ake toya waba yanzun kam.
Sai gata wata yar tsurut a hannun shi

Kwala kiran sunan Kwaro da yayi da muryar shi da dama koya yayi magana da ita na nesa dashi ma yana iyaji balle kuma yau daya budeta masha Allah,

Wannan dalili yasa tuni hankalin mutanen gidan ya dawo zuwa farfajiyar gidan domin ko ba'a fada musu ba sun san muryar waye amon muryar tashi kuma karara ta nuna cewa ba lafiya ba,

Malam ne ya fara fitowa kafin sauran jama'ar gidan a dai dai sanda Sarki ya ciro Meenal daga cikin motar Malam Sa'idu,
ba tareda ya tsaya yinma kowa bayani ba yayi waje abinshi cike da zafin naman da akasan sojiji dashi, su Meelat suka rufa mishi baya suna kuka,

Aunty Hajara ce ta fito daga cikin motar tana mai gabatar musu da kanta a matsayin Malamar makarantar su Meenal din da kuma abinda ya samu Meenal sannan ta mikama yan gidan jakan Meenal din a sa'ilin da suke masu fatan Allah yaba Meenal din lafiya su kuma suka juya,

"Innalillahi wa'innah ilaihir raju'un" Malam ya fada a yayin da yakai zaune a wata kujera, Allah kadai yasan yanda yakeji a lokacin nan.

"Malam ai ba zama zakayi ba kamata yayi mubi bayan su, bakaga yanda Sarki ya fita da ita bane ko motsi fa batayi, kai innalillahi jama'a yaushe yarinyar nan zata huta da ciwon nan da yake neman zaman mata tamkar mahadin rayuwa? Ace duk wata babu fashi sai tayi shi"
Ta karasa fada tana matsan kwalla, dan wallahi ji take da tana da halin da zata raba Aminatu da ciwon nan da tuni tayi.

Dagowa Malam yayi a zafafe yana mata wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login