Showing 123001 words to 126000 words out of 174305 words

Chapter 42 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1866

k'ara cikar kyau da girman jiki, ga kuma gogewa data k'ara samu ta fannin mu'amalah da jama'a dama yanda zata kula da kanta a yanzun kam ita kanta tasan bata da matsalar komai saina karatun data sa a gaban ta dan miji dai zaman nasu kullum jiya iyau ne,

cigaban dai daza ace an samu shine yanzun in yazo gari yana zama yaci abincin ta in ma bata had'a mishi takai ba yakan zo har sashen ta yaci sannan lokaci lokaci ko baya gari yakan kirata a waya yaji ya lafiyar jikin ta,
Su Meelat da suka san irin yanda auren nata ke tafiya sun sha zaunar da ita suyi mata hud'uba akan zuwa yanzun ya kamata fa ta watsar da komai ta rungumi mijinta, sai dai ita kuma tsaf ta kuduri cewar inhar bashi bane ya sauko dan ra'ayin kanshi yaga cewar ya dace su fuskanci rayuwar auren da kyau ba,
ita wallahi bazata tab'a kai mishi kanta ba.

Shi kuma a gefen shi bawai kin auren yakeyi ba, ah ah wani lalura dai yake fama dashi na d'aukewar sha'awa aduk sanda ya shigo garin bazaiji shi ya koma cikakken Namiji ba har sai yabar garin, sai dai kuma kwata² bai dauki hakan da mahim manci ba balle har yasan matakin d'auka dan shi dama a yanda ya yanke ma kanshi shine baizai tabbatar da ita a matsayin Matar shi na aure ba har sai zuwa sanda ta kammala karatun ta yasan zuwa lokacin tayi girman da zata iya dashi, amma yanzun idan ya nemeta allah yasa rabon haihuwa yana kusa ai ganin yake ya shiga hakk'in ta dame zataji?
da kulawa da buk'atun shi, rainon ciki ko kuma karatun dan haka yake ganin ai rashin sha'awan ma normal ne.

*Bari mu waiwayi uwar gida Teemah*

Tun bayan koma warta hankalin ta bai kwanta ba har saida ta shiga ta fita tayi kullin da aka tabbatar mata da cewa muddin Sarki ya taka Zaria tofa zai zauna ne a matsayin mace domin dai bazai tab'a jin sha'awar saduwa da mace ba har sai sanda yabar garin sannan zai koma yaci gaba da amsa sunan Namiji,
Ita a yanda taso, so tayi a sakamar ma Meenal zubar jini, ko warin jab'a ko kuma a cusa mummunar tsanar ta a zuciyar Sarki, sai dai shi bokan nata ya tabbatar mata da cewar hakan bazai samu ba domin dai bazasu iya cimma yarinyar ba, taso ita kuma a cusa mata kiyayyar Sarkin taji cewar bazata iya rayuwa a karkashin inuwar auren shiba sai dai shima hakan kuma shima bai samu ba, alwashin da taci na cewar babu wacce zata aure mata miji ta zauna lafiya yasa badan taso ba ta yarda da shawarar bokan ta na kashe gaban Sarki a duk sanda ya taka Zaria,ai koba komai sai yana da lafiya ne zai iya kusantar ta batayi tunanin mai ka iya faruwa ba a sanda ita Meenal din zata iya zuwa ta same shi a wani wajen daban.


*Tudun wada gidan Hajiya*

Kasan tuwar kwana biyu Hajiyar bataji dad'iba hakan yasa Meenal ta yanke zuwa dubata in ta taso daga Makaranta,
Kamar ko yaushe da gudu ta shigo unguwar domin dai tunda ta kware a driving tofa Sam bata tuk'i a hankali barin ma inta hau kan titin dake da karancin abin hawa,
Tunda ta doso kofar gidan bakin ta ya gaza shiru har sai da ta furta abunda ke ranta "Na rantse da Allah dan dai ban iya azumin kaffara na wanda yayi kisan kaine, amma da take motar nan zanyi inje in haye kan wad'an can yan zaman kashe wandon"

"Kai Meenal yanzun tsakanin ki da Allah da babu wani hukunci akan wanda yayi kisan rai sai kije ki haye kan nasu?" Maryam dake bayan motar ta tambaya tana dariya.
"Mai zai hana harma sai na nemi shawarar wata a cikin ku"
Harara Meelat ke banka mata,
"amma wallahi baki da mutunci qawata wato ke tunda kinyi aure kin shige daga ciki ni bari ki kashe min nawa mijin tun kafin aure, "

"Eh ai dole kice haka tunda da saurayin ki ake zaman majalisar kullum, wai bazaki mishi wa'azi su dena zaman wajen ba"
Cewar Maryam

"Ina ruwan ki tunda dai ba'a kanku suke zaune ba ku shafa musu lafiya Alhamdulillah kowa ma yasan ba zaman banza sukeyi ba tunda dukan su babu wanda bashi da abunyi a cikin su"

"Dallah Maryam kyaleta ai bata son laifin su kwata²"
Cewar Meenal
"Naga alama kam.

Koda suk k'arasa kofar gidan babu b'ata lokaci aka bud'e musu gate suka shige,
gidan na nan a yanda yake sai ma abunda ya k'aru na gyare gyaren da ake mishi a koda yaushe.

"Ku shiga zan biyo ku a baya, ina son k'arema fuskar future husband d'ina kallo da kyaune, kun san kwana biyu baya gari"
Cewar Meelat

"Mayya kawai yar wahalar soyyaya"
Meenal ta fad'i hakan cike da jin haushi ta bude bayan motar ta cire ledar kayan fruits d'in data kawoma Hajiya na dubiya.

Ita dai Meelat bata kulata ba, Maryam ko jakarta kawai ta d'auka tayi gaba dan dama tun a school take ce musu tanajin fitsari,

Da sallama suka shiga falon na Hajjaju Masifaffiya, su biyu suka cimma ita da jikanta na hannun damanta zaune suna hirar yaushe gamo, domin dai shima a yanzun gaba d'aya baya samun damar zama a Zaria kamar da ,
saboda tsabar son kud'in shi yasa yau bashi nan gobe bashi can.

Sallamar nasu ne yasa shi dago kai yakai duban shi kofar shigowa domin dai wannan muryar aiko a magagin mutuwa ya jiyota yasan kunnuwan shi bazasu gaza gano mishi mai mallakin muryar ba,
ilai kuwa ita d'ince kamar yanda ya tsam mata yarinyar dake neman ta d'imauta mishi rayuwa dan gaba d'aya a watannin baya kamar wani mai shafar aljannu haka ya nemi komawa, ba damar yaga mace da jallabiya sai yarinyar nan ta fad'o mishi arai yana ta jimamin wani hali take ciki a gidan mijin nata amma ita jibita wallahi inba k'arya idanuwan shi suka mishi ba girma yaga ta k'ara babu alamun damuwa ko kad'an a tare da ita, shi yana nan kullum cikin jimami.
Da kyar ya iya kwato idanuwan shi daga kallon da yake binta dashi yana korar shed'an a zuciyar shi, dan gaba d'aya sai yake jin kamar ya dauwama yana kallon ta dan wani sanyi mai cike da nutsuwa ne yaji yana lullub'e shi.

Wata irin zazzafar ajiyar zuciya ya sauke wanda har saida sautin fitar ta yasa Hajiya maida duban ta gareshi,
"Kana lafiya? "
hajiya ta tambaya.
"Yes yes yes am fine"
ya bata amsa yana mai sosa k'eyar shi da hannun shi na hagu,
Har ya yunk'ura da niyyar barin wajen kenan Meenal ta iso kujerar da yake zaune, kan hannun kujerar ta zauna ita kuma Maryam ta shige ciki dan sosai fitsarin da takeji ya matseta,

"Mai jama'a barka da war haka yaushe a gari?ashe ka dawo? Oh kar in manta...
Barka fa da arzik'i ashe wancan cingum d'in naka Nusaiba kuma lokaci yayi, gaskiya na maka murna ita kuma Allah ya bata zaman lafiya ya kuma sanya mata dangana yasa k'arshen wahalarta akan soyayya kenan, gaskiya dai na mata murna Wallahi gashi kuma ance mijin da aka bata d'in mai kud'i ne kuma sosai yake sonta,
Ni kuma nace oh Allah rashin sani yafi dare duhu dan Wallahi na tabbata da tasan tsarin da Allah ya mata na samun wannan mijin da bata tsaya b'ata shekarun nan tana dakon jiran ka amshi soyayyar taba, ups sorry fa Brother wannan dai ta samu tasha da kyar saura d'ayar guzuman itama ina fatan Allah ya bata lafiya ta warke daga halin makuwar da take ciki"

Tunda ta fara surutan ta bakin ta kawai yake kallo a zuciyar shi ko ayyana wa yake cewa, lallai ashe dai ba gaskiya bane da ake cewa in akama mutum aure yana hankali! To gashi dai yaga girman jikin ya k'aru amma fa hankalin har yanzun da saura,

"Ke wai sai yaushe zaki san kin girma ne? An miki auren ma amma har yanzun kin kasa hankali, dama munyi dake cewa zan aure tane? Ko mun tab'a zama dake nace miki akwai wacce nike so a cikin su? Tashi a wajen nan kafin in kifar dake mara kunya kawai"

Zaro ido tayi tana mai tashi daga kan hannun kujerar.

"Allah ya baka hakuri mai yayi zafi harda zaka kifar dani, tab aini yanzun mai kai hannun shi jikina tofa sai ya tabbatar ma kanshi da cewar ya shirya kwanan guardroom"

"Oh saboda kina auren soja koh? To tsaya ki gani in yaso idan na karya kin sai yazo ya d'aureni"
Ya fad'i hakan a yayin daya mike yakai mata cafka, aiko babu shiri ta kwasa sai bayan Hajiya.

"Wai takwara kinzo dubani ne ko kinzo tsokanar fad'a?"

"To Hajiya laifine dan na taya shi murnar auren macen daya nuna baya so bayan tsayin shekarun data d'auka tana nace mishi?aini gani nayi abun a taya shi murna ne, kuma wallahi in mutum baiyi hankali ba sai alhakin mata ya kama shi"

Mtsw yaja tsaki.
"Yarinya kiji da kanki Keda akama auren dole! "

"Eh irin auren dolen da aka min nima nike Addu'ar a d'auko wata y'ar daga kauye a had'aku, sai kaji yanda abun yake"

Juyawa yayi da niyyar barin falon dan yarinyar nan fa bazai zauna ta mai dashi mahaukaci ba,

"Taubashi na nace bah!
Nace turaren nan da kakan d'an ajiye min a d'aki kwana biyu na duba ban gani ba nace ko ka manta ne? "

"Kai"
ya fad'a da d'an karfi cike da mamakin k'arfin halin ta yana juyowa,

"Oh wato ga mai kud'in banza koh? Da mijin ki da komai sai in cigaba da siya miki turare kina fesawa saboda gani dan iskan da bai san zafin dukiyar shiba"

"Kai yayan mu dan Allah miye a cikin kyautar turare dai, naga su wadancan da suke zuwa maka kullum a kallah abincin nawa kake siya musu bayan ba wani lada zaka samu ba! Niko ai koba komai bayan ladan kyauta harda ma ladan zumunta zaka samu, nidai muje Allah ko gyaran d'aki ka sani yau zanyi maka shi da kyau indai zaka bani turaren"

"Hajiya kifa jama yarinyar nan kunne yasin ko a kofar d'akina na ganta sai na zane ta tom kar kice ban mata warning ba"

Banza dashi Hajiya tayi ganin hakan shi kuma yasa kai ya fice a d'akin....

"Dan Allah Hajiya ku mishi auren dole, shima yaji inda dad'i.......




Ummiee Zaria ✍🏼
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!* 👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️

*Free book ne ga masu buk'ata daga farko zaku iya magana dani kai tsaye* 08061358462

*Rubutawa*
*Ummiee~Zaria*✍🏼

Page 36.....



"Dan Allah Hajiya kuyi mishi auren dole shima yaji inda dad'i, ai ba iya mata kad'ai ake ma auren dole ba,
inba haka ba ni karamar yarinya dani haka nan fa kuka had'a kai saboda kun gaji da ganina kuka aurar dani sai shi k'aton tuzuru amma ba wanda ya matsa mishi yace sai yayi aure,
to gashi nan dai ai yan matan nashi sun fara watsewa tunda sun gaji da gafara sa basuga k'aho ba, Allah in bai wasa ba zuwa gaba a sanda zai buk'aci auren babu macen da zata saurare shi, badai dan yaga yana da kyau kuma yana da kud'i shi yasa yake wulak'anci ba"

Kyacci tayi tana hararar hanyar da yabi ya wuce.

"Ke Meenal wai me yasa ne ke in kinzo waje gaba d'aya bakya son kiga an zauna lafiya sai kin nemi wani zancen hankalin ki ke kwanciya ne? Kin dai san halin shi karkiga wai kina da aure in kika kureshi kin san jikin kine zai fad'a miki, kuma wama ya fad'a miki cewar irin su akewa auren dole? to yasin ko rantsuwa nayi nasan kaffara bazata hau kaina ba wannan in aka mishi auren dole tun a wajen taron d'aurin auren zai ma matar saki uku kwarara kuwa! "

Cewar Hajiya.

Turo baki Meenal tayi gaba sannan ta d'aura da cewa...

"aike Hajiya dama bakya tab'a ganin laifin shi komai yayi dai² ne in dai a wajen kine kamar shi kad'aine jikan ki mu kuma yan karere,
ni bama wannan ba mi kuka dafa a gidan nan dan Wallahi yunwa nikeji da safe ban samu nayi girki ba na fito koda naje makaranta kuma kame² kawai na dunga yi banci wani abincin kwarai ba,

wai Hajiya Jummai har yanzun bata dawo daga Kauru d'in bane? Lallai a gaisheta kawai taje kauye tayi zaman ta kamar wata wacce taje Abuja"

"Ke dai wallahi kin cika shegen surutu kamar aku, tunda kika shigo kike zuba uwa wata lalatacciyar famfo, ni na rasa Ina kikayo wannan mugun gadon na surutu wallahi, tunda kika shigo kike zuba tad'i kamar ana zuge zogale"

Zaro ido Meenal tayi cike da mamaki
"Hajiya wai nice mai shegen surutun? "
ta tambaya tana dariya.

"Lallai ma toni dan nayi surutu har a tsaya neman dalili ko tambayar wajen wa nayi gado bayan gaki!
Minene ya rage naki wanda banyi gado ba?
Kinga dai naci gadon sunan ki ni kad'ai a cikin *DANGI*.
Na kuma d'auko fuskar ki da hasken fatar ki,
surutu kuma ai bama sai na baki amsa ba, ga kuma farin jini masha Allah, yauwa Hajiya nace wai dan Allah su maza basa gane banbancin budurwa da kuma macen aure ne?"

Ta tambaya tana maida hankalin ta kacho kan a wajen Hajiyar dan da gaske so take taji amsa daga bakin ta,
Fitowar Maryam tana gaishe da Hajiyan ne ya d'an tsaida ta,
sai kuma ta maida idon ta kan Maryam d'in

"Besty wai kin san ko d'azun da safe da muka rabu daku sai da mutumin nan na shekaran jiya ya k'ara tsareni bayan a gaban ku shekaran jiyan na shaida mishi cewar ni matar aure ce!
Wallahi kawai Ina tafiya sai gashi nidai karfin haline kawai yasa dana ganshi ban zura da gudu ba to nasan koma na gudun aikin banza ne dan tsalle daya ne zai kamo ni,
Sai fa da na duk'a har kasa na dunga had'ashi da Allah akan ya rufa min asiri ni matar aure ce amma d'an iskan mutumin nan wai fa cewa yayi ai dama mu mata in bama son alaqa da mutum haka muke cewa bayan yasan cewa ni ba matar aure bane kawai kora da hali nike mishi,
Kin san me yasa ban d'ud'dura ma uwatai zagi a lokacin ba? Wallahi tsoro nikeji dan kamar an hana mutane bin hanyar ba kowa dagani sai shi kin san ko yasin ko yankani zaiyi yana iya gama fed'ewa wani bai biyo ba balle ya ceceni"

Dariya kawai Maryam keyi dan sosai alamun Meenal ya nuna ta tsorata.
"Dallah ke banzane wallahi Ina miki magana serious kina neman mai dani wata tababb'iya, nifa tsoro nike kar wani abunda zai shafi karatuna ya gifta kin san in da lokacin baya ne wallahi shida kafafun shi zai gudu"

Amsa Maryam d'in ta bata da cewa..
"Ai na fad'a miki ki nemi dogayen hijabai masu rufewa har suna jan k'asa ki kuma had'a da niqab amma kinkiji ba dole su biki ba tunda yan matan ma ai suna sa irin hijjaban da kike sawa, amma dai shima d'in dan iskane tunda ai mun fad'a mishi ke matar aure ce ya kamata ya yarda, in ya k'ara tareki wallahi k'arar shi zamu kai"

Juyawa tayi wajen Hajiya bayan ta gama hararar Maryam d'in dake magana tana dariya,
dan tafa bata haushi da gaske,

"Bari in debo abinci inzo ki bani amsa kinji Hajjaju, Allah kuwa Hajiya in kikayi ciwo lafiya kike k'arawa masifar duk sai mu nemeta mu rasa itama ciwo ya korata!"


"Eh amma ai a lissafin da kika gama d'azun banji kinsa harda masifar ba, kuma Kitchen d'in nan inba wani sabon girkin zaki d'aura ba tofa ba lallai ki samu abunda kike so ba dan tuwo mukayi kin san shi yafi ta'amali da abunci mai nauyi, Jummai kuma kin san taje zaman jegon jikarta ne data haihu nasan da bazaki rasa abunda zakici a can wajen taba, Larai kuma na aiketa kasuwa"

"Tuwo kuma" ta fad'a tana b'ata fuska jin an kira makiyin ta,
" kai innalillahi wai shi mutumin nan da zarar yana gari dole ne cimar gidan nan ya canza ne? Haba dan Allah shi kenan dan shi yana son tuwo kuma sai ku wani dunga biye mishi, ni wallahi in nice matar shi dole ma ya sauke ma kanshi wannan tsurfan atoh kullum tuwo, kullum tuwo kamar a prison"

"Wannan kuma ke kika jiyo in yunwan kikeji da gaske sai ki fita ki siyo anan wajen matar can mai bleaching dan suma dai girkin nasu babu laifi, inaga hakan zaifi miki sauk'i"
Hajiya ta k'arasa fad'a tana kauda kai gefe,

Yaraf Meenal ta dawo ta zauna a kujerar data tashi,
"Wallahi yunwa nikeji!" Ta fad'i hakan tana b'ata fuska da matse cikin ta daya k'ara lafewa saboda bai samu abu mai nauyi ya d'auka ba.

"Bari in fita sai in amso mana, me kike so?" Maryam ta tambaya a yayin da ta mik'e dan zuwa Restaurant d'in dake kofar gidan kamar yanda Hajiya ta basu shawara.

"Ke ni komai ma ki amso min amma banda tuwo "

"To"
ta amsa mata dashi tasa kai da niyyar barin falon.

"Ki shiga kitchen ki d'auko kulan da zaki zubo abincin a ciki mana koh!"
Cewar Hajiya
"Ki barshi kawai Hajiya zan amso a takeaway"

Bayan fitar Maryam kacokam Hajiya ta mai da hankalin ta kan Meenal,

"Dawo nan muyi magana" ta fad'a cike da bada umarni tana mata nuni da gefen kujerar da take zaune,
Babu musu koh ta tashi ta koma wajen.

"Hajiya ya jikin naki? Koda yake naga kin warware tunda mijin ki ya dawo"

Murmushi Hajiya tayi, "jiki Alhamdulillah kam naji sauk'i sosai fa, shi kuma adawa kike da dawowan nashi ko meya faru?
dan na dad'e da sanin sosai kike kishi dashi, tsakanina da Abdul Khareem ko mai shiga tsakani sai ya shirya gara ma kiyi ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login