Showing 81001 words to 84000 words out of 174305 words

Chapter 28 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1868

ma d'aukakin al'umman musulmai barka da sallah tareda fatan Allah ya maimaita mana🥰
Here is your sallah gift, kuyi karatu har ku gaji😂😂


```Page 26



Ai kasan dai ko banyi Allah ya isaba sai Allah ya saka mata, tunda dai ni nace taje ta gyara d'akin,
shine dan bak'in mugunta zaka kama musu yarinya kana neman kwankwashe mata kwalwa , zonan takwara in gani Allah yasa dai bai rusa miki kai ba? Ke dama gaki nan kullum kamar wata kalallab'a".

ta fad'a tana janyo Meenal din dake ta kwarara ihu tana murje² a kasan tile's kamar wacce ake yankawa zuwa jikin ta,
"Yi hakuri kinji barshi da halin shi ai tsabar mugunta ne ke damun shi to jama'a inba mugunta ba mai zai d'iba a jikin wannan lab'ub'uwar yarinyar ? in mutum tak'amar shi karfi basai ya fita cikin maza ko yaje gidan damben dake Sabon Gari ya tub'e su daku da mazan ba, shine zai huce haushin shi akan jikata, yi shiru kinji uban shi zan kira yajama d'an shi kunne ya shata layi tsakanin mu in kuma ba haka ba wallahi koni ina iya mishi kud'in jirgi in tarkata mishi kaf kayan tsiyar shi dake gidan nan in kuma had'a shi da police su rakamin keyar shi zuwa airport ya tafi can inda iyayen shi nima in huta atoh haba Jama'a ina ma dalilin wannan kwazzaba nikam."

Har ya juya da niyyar barin falon jin abinda Hajiya ta fad'a yasa shi juyowa yana mata wani irin kallon dashi ba harara ba shi kuma bai rufe idanun ba, kasa² dai yakeyin kallon.

"Hajiya!
Hajiya!!
Hajiya kin san dai bako yaushe nike son ana shiga gonata ba koh, kuma kud'in jirgin da zakimin ki tsakura a ciki ki siyama jikar ki paracetamol"

Yana gama fad'in hakan yasa kafa ya fice ko waigen su bai karayi ba,

Astagfirullahi ya Allah kasa inga annabi jama'a me nike shirin gani yau ni Aminatu?
Ke takwara kinga abinda ya faru a falon nan nawa yau kuwa? Nagode Allah a gaban ki akai komai kema kin isheni shaida dan babu abunda zai hana ni kiran uwar shi dan dolenta ta baro Saudi tazo ta dauki takadirin d'an ta dan wannan shara'ar tafi karfin ayita a cikin waya sai ido da ido, dan in ban mike tsayeba zuwa gaba yaron nan yana iya shigomin har falon nan ya kashemin fuska da mari"

Hajiya duba min kaina Allah kuwa ya rotsamin kai! "
gyale da hular dake kanta dama tuni suka kama gaban su,

"Ke da Allah ba wani fa shafewar da kanki yayi ni banason haya gaga irin naki, tashi maza ki shirya ki koma gidan ku Allah ya bada ladan zumunci ameen"

Diff kukan Meenal ya dauke a yayin da ta tsaya tana kallon Hajiya cike da mamaki,

"Hajiya"

Ba wani Hajiya zoki wuce ai tun d'azun nike fama dake kikayi kunnen uwar shegu dani, kinga yanzun ai kya nemi inda dare yayi miki"

sai da ta turo baki gaba tana mutsts tsuke idanu
sannan tace
"Hajiya kaina!"
Ita kuma hajiya tace

"to ina ce dai nayi miki sannu? naga dai shi mugun ko kallo baki isheshi ba ya fice bayan ya gama kwashemin albarka"

"To aini maganin ciwon kai zaki bani inba haka ba kaina rabewa biyu zaiyi"

"Ah ah wallahi ba'a gidana ba, bari in ma tarwatsewa zaiyi ya tarwatse d'in bayan kin koma gidan ku kafin kisa a farayi dani a radio cewa jika tazo gidan kaka kanta ya tarwatse a'ah wallahi badani ba,

maganin ciwon kai dai ai bazan rasa shi a gidan nan ba jirani in d'auko miki"
ta fadi hakan a yayin da take mikewa zuwa ciki.

"Nidai kud'in zaki bani idan na fita in siya maganin"

"Me naji kin ambata? Kamar kud'i naji kin kira yarnan! Oh kice fashi zakimin da ranar Allah to kama gaban ki yarinya,dan banci nanin ba nanin bata cina ke tsaya ma!
Wai mema kika aikata mishi a cikin d'akin daya harzuka shi haka? "

"Ni banyi komai ba"
Inma kinyi ai jikin ki dai ya gyaya miki"

Ciki Hajiya ta wuce bata jima ba ta dawo da maganin ciwon kan, saboda yanda take jin ciwon kan yasa batayi jayayya da Hajiyar ba ta amshi maganin tasha,

"Muje wajen in ma daya daga cikin samarin nan magana su kaimin ke gida"

"Ni bana so bazan hau motar kowa ba, zan je bakin titi in samu mota"
"Kedai kika sani mutum na miki abun arziki kina gwasale shi"

Shiru Meenal ta mata ganin Hajiyar ta koma Ciki da niyyar dauko mayafine yasa ta ficewa a falon da sauri ta karasa wajen fulawoyin nan da ta ajiye shower gel d'in data kwamuso a d'akin shi ta dauke su ta cusa a cikin ledar kayan da Billy ta bata can kasa ta yanda babu mai gane cewar akwai shi a ciki,

yanzun nan fisabilillahi da ace batayi sama da fad'i da turaren shi da wannan shower gel d'inba dashi kenan fa ya rankwashi banza kenan? "Kut ai wallahi bai isa ba koba dad'e koba jima saina rama"

ta fad'i hakan a bayyane,
Hajiya ce ta karaso wajen tana mita,
"ke kuma daga in shiga in dauko mayafi shine kikayi fitowar ki? Nayi zaton kin wuce ne ai?

"To aini na fad'a miki ni bazan hau motar suba tafiya na zanyi tunda basu suka kawoni ba dama"

"Kyadai ji dashi!"
Hajiya ta bata amsa.
Koda suka fito kofar gidan Yusuf wase da Mai Jama'a ne kad'ai a majalisar sai kuma wasu bakin fuska.

"Kai Abdul taso ka mikamin yarinyar nan gidan su in samu mu rabu lafiya da ita! "

"Dama ni na kawota ne dazan mai data? tunda ta kawo kanta ai tasan hanyar komawa, kuma ni ko man petroleum ma babu a motana"
Baki bude Hajiya ke kallon shi,
"Kai Abdul Khareemu ashe bakajin tsoron kwanciyar kabari cikin duhu? da girman ka da komai kake kallon tsabar idona kana shekamin karya, ince kazo ka maida musu Y'a gida kacemin motar ka ba mai, to ai da hakan gara ka fito gaba gid'i kace min ke Amina bazan kaita ba kiyi abinda zakiyi"

Bai gama sauraren abunda take cewa ba ya mike ya wuce zuwa cikin Restaurant d'in dake wajen.

"Kai kai kai Abdul ina kuma zakaje me zakayi anan , karfa kamai dani wata shashasha, in tashi tunda farar safiya in had'a abinci shine saboda baka tausayi na kake neman zuwa wajen matar nan mai shafe² wai can zaka cin abinci to wallahi Allah dai yana kallon ka atoh dan bazaka mai dani wahalalla ba, aiko dan wahalar da nayi ka dawo kaci dambun nan, mutane da yawa ke son shi amma na hanasu na aje maka shine dan iskanci kake neman kwance min zane a kasuwa"

Juyowa yayi ba tareda yace mata komai ba ya kama hannun Wase suka wuce cikin gidan.
"To ya daifi kam ke kuma Takwara ki jira ya fito da motar saiya mik'aki gida"

Sai dai me?
Koda ta juya wayam babu Aminatu ba alamarta domin ko dama tun fitowar su ta kama hanya tayi tafiyarta tabar Hajiyar na b'ab'atu ita da bakin ta baya gajiya da surutu.

Wannan rankwashi shi yayi sanadiyyar da sai da Meenal ta kwana da ciwon kai dalilin hakan yasa basu samu damar zuwa gidan su Zulaihat d'in da sukaci alwashiba,

To kuma dan Allah shine saboda tsabar rashin imani yau ya wani biyota har gadon asibity ya mintsileta, tab ai wallahi su zuba shida ita hege ka fasa dan halak sai yanka,

Kwana hud'u Meenal tayi a asibiti suka sallameta a kwana 4 nan kuwa tab'ara sai kalar data manta, sannan kullum Malam da Hajiya sai sunzo asibitin suma da nasu kalar wasan kwaikwayon dan Malam dai zuwa dubiyar ta haka ya maidashi kamar biyan bashi akan kowa, tsaf yake lissafe da wadanda basuzo sun duba mishi uwaba.
Itako Hajiya innah nata idon akan masu zuwa dubiya babu kayan dubiya yake haka dai akayi ta fama har sanda akayi sallama kowa ya koma kan harkokin shi.


*****

Dalilin ciwon laulayin cikin da Teemah keyi a wannan karan yasa dole Sarki ya zauna da ita,abunda take da bukata kenan dama domin koh sosai ta tubure mishi akan cewa rashin sone yasa yanzun bai damu da damuwarta ba, dan haka ita bazata iya wahala ba domin a gaskiya sosai takejin jiki dalilin hakan yasa duk abubuwan ta suka tsaya tadai fada mishi in bai zauna da itaba to hakika zuwa zatayi ta cire cikin dan bata iya wahala da cikin da uban cikin bai damu da itaba,
To kun san dai dama can sai ya ciza da kyar yake iya daure zuciyar shi ya mata babu dad'i balle kuma yanzun da take shirin bashi sabon Baby dan haka dole ya d'auki hutu dan ya samu ya shawo kanta to dai suna can suna ba fulawa ruwa.

Bayan wani lokaci........

Abubuwa da dama sun faru wasu sun tafi dai² bisa tsarin da yayi dai² da zuciyoyi wasu kuma sun kasance akasin hakan ,

A yanzun haka dai saura yan watan ni su Meenal su zana jarabawar gama secondary sunfa zama yan mata sosai Masha Allah komai yaji,
Dan haka nema wasa² dai samari suka fara rububi a kanta sai dai da yike ta iya takunta da kuma kasancewar akwai waya a hannun ta yasa babu wanda ya fahimci halin da take ciki, domin dai duk kwakwar nacin mutum bata tab'a yarda yasan unguwar suma balle kuma gidan su saboda tsabar gudun tonuwar asirinta komai a cikin tsari take binshi,

Alfarma daya dai takema wadanda take ji dasu a cikin samarin shine idan suka matsa da son ganin ta zataje can Tudun wada gidan Hajiya su had'u acan kuma ko hajiyar bata san da hakan ba, wato dai duk yanda zata raina ma mutune hankali ta b'atar musu da tunani a kanta ta sanshi, domin dai kullum a gida ikirarin ta shine likita zata zama dan haka babu batun wani soyayya da aure, hakan yasa babu wanda zai zargeta cewar tana kula samari.

Sai dai bata san cewa tana shuka a idon makarwa bane, domin ko duk halin da take ciki na janyo samarin ta zuwa gidan Hajiya Mai Jama'a tuni yake ankare da hakan domin har farfajiyar gidan na Hajiya take shigo da samarin su zauna suyi hira,
Shi mamakin shi a kullum shine, su samarin da suke biyon tan mahaukatan wani kasa ne? Su basa ganin kankantar tane dahar suke iya tsayawa da ita da sunan zance? ,
Kome ma suke cewa in suna zancen oho, dan yasan shirme da yarinta dai shi zatayi ta musu kala² dan rawan kanta yayi yawa. Jama'a fisabilillahi in soyayyar cema ka nemi cikakkiyar mace mai hankali mana ba wannan yar birin wasan ba.

Kuma zai same tane wallahi in bata dena kawo musu maza gidan suba saiya had'a ita da samarin yacicci musu mutunci tunda ita bata da kunya wallahi,
Dan shifa sosai abun yake bashi takaici dan cikin samarin nata inka duba zakaga bawai irin yan kuca kucan yaran nan bane, ah ah cikakkun samari take samu wayayyu dan alama ya nuna saita darje kafin ta baka damar zuwa inda take,
Barin ma wani sakarai daya lura da cewa yafi sauran dake zuwa rawar k'afa a kanta, kuma yasan gayen Lukman Dan gidan Master ne, sosai yaron suke da arziki a gidan su to zaija mishi kunne ne kar yayi amfani da arzikin shi yama yarinyar mutane wayau.
yadai tsaya sosai yayi nazarin cewa saboda taga ta fara zama budurwa shi yasa kullum take k'ara raina shi,domin da gaskefa ta maidashi abokin wasan nata dan ko bai takaleta ba ita sai ta takaleshi, domin dai har yanzun kullum babu shiri a tsakanin su sai dai in bata zo gidan ba, inshi yaje gidan su wajen Mommy Hauwa tofa bata da katabus, domin yafi samun damar cin zalin d'inta acan da kyau dan datayi wani motsi da niyyar ramawa Jidda ke taka mata burki akan bata son raini aishi yayan ta ne, amma in a gidan Hajiya ne yana mata itama take huce haushi a d'akin shi dan dai shi baya buguwa, kuma ita dai bazata mishi Allah ya isa ba sannan ba zata yafe ba wallahi,

dan tuni saida tayi yanda tasan inda Hajiya ke ajiye key din d'akin shi, dazarar ya mata ba dai² ba take sace key din taje d'akin ta huce haushin ta akan kayan shi.

Tsaf yasan cewa ita ke daukar mishi turare da sauran abubuwan dan kullum a jikinta yakejin kamshin da ba irin turaren shi su Sadeeq ke amfani dashi ba, sai dai yana nan yana dakunta duk ranar daya kamata a hannu dumu² zata gyawa aya zakin ta.

Gefen Meelat da Musty ko soyayya suke zubawa ruwa² domin tuni aka san da zaman shi a gidan su Meelat d'in duk da akan soyayyar nasu har fad'a saida sukayi da Ak a cewar Ak din shi Musty yana haukane duk cikin Nigeria ya rasa yarinyar dazai nema sai wannan yar jaririyar, wato ashe shi yasa yaran nan suke mishi gani gani dan haka wallahi duk ranar da giyar soyayya ta kwashe shi yaje zance wajen yarinyar nan inhar ya sake ya kira sunan shi a wajen to bai yafe ba.

Maryam dai itama irin na Meenal take duk samarin ta a iya waya hirarsu take karewa dan ita dai tasan a gidan su koda wasa ma a kasan tana kula wani jikinta ne zai fad'a mata.
Su Moon da Aisha ma ko wacce tana inda take sai dai kullum Moon ta kira Meenal saita tambayeta ya labarin mai gidan yan gayu dafatan yana lafiya, tofa daman da zarar ta ambato shi hirar su ta wannan rana ta kare sai kuma wani lokacin, da alama dai Moon fa ta kamu 🤔 yarinya keda Teemah dan wannan fadar yafi karfina.

Batun ciwon marar ta kuwa Alhamdulillah duk da cewar badai ta warke bane amma in ya tashi mata yanzun akwai wani taimako da Malam ya amso mata wanda da zarar ciwon ya taso in tasha bacci zai dauke ta, hakan yasa wahalar nata ya ragu.

A gefen Malam kuma kullum cikin istikhara yake akan maneman Aminatun da zuwa yanzun suke ta kara yawa, domin a yanzun haka wadanda sukayi mashi magana akanta a da din su ya haura mutum goma sannan dukan su babu wanda inda hali bazai iya hanashi bashi auren Aminatun ba, dan haka dole yaci gaba dayi mata Addu'a domin neman zabin Allah a cikin al'amarin dan ya yanke hukuncin gara ya aurar da ita d'in kawai kodan samun lafiyar jikin ta itama, in yaso karatun nata tayi shi bayan aure.

************


A gefen Masoya biyu kuwa wato Sarki da Sarauniyar shi zamu iya cewa duniyace sabuwa ta bud'e musu domin dai tuni mutuniyar tashi ta tashi tsaya wajen ganin ta shiga ta fita ta gyara tsakanin ta da mijin ta kuma sosai yanzun kam ta samo kanshi take kuma juyashi yanda take so harma fiye da shekarun baya,
Firrr yanzun kam ta hanashi zuwa zaria komai akeyi bai zuwa sai dai aike hatta da yaran shi dake hannun uwar gida yanzun bai wani damuwa da al'amarin su ta uwar su kadai yakeyi.
Ita ko Teemah duniya tayi mata dad'i domin dama tuni abunda take so kenan taga Sarki yazama mata mijin kan tace, gashi kam ta samu dan yanzun dai sunan kawai yana aiki a KD ne amma duk sati yana Lagos bayan haihuwar ta kuwa hutu tasa shi d'auka na musamman dole ya koma Lagos sukayi jegon tare, ganin cewa yanzun shi kanshi da komai daya shafeshi yana karkashin ikon tane yasa gaba daya harta da yaran ta dake Zaria bata tunawa dasu balle kuma acewar ta yanzun ta haihu tunda ta haifo Namiji.

Al'amarin Sarki wannan karan ba uwar gida kad'ai ya dama ba hatta da ubanshi mahaifi dama sauran yan uwan shi kwarai abun ya damesu, domin dai suma sunata nasu kokarin bakin gwargwadon nason ganin ya dawo hayyacin shi sai dai ina, domin sosai Teemah ta rike wuta wannan karan.

Daga karshe dai sun tsaya akan matsaya d'aya cewa dole dai su k'arayi mai aure a wannan lokacin domin indai yana da wata matar anan Zaria dole ko baizo garin dan iyayen shi da yaran ba ya zo kodan matar shi.

Hhhhhh naku wasa ne, wanda bai tuna da uwar shi bane zai tuna da wata mata.

A hakan dai sosai uwar gida ta matsama Malam Sulaiman akan maganar cewa yaje ma Malam dan Susan wani mataki suke kai yanzun duba da cewa su Meenal din na gab da kammala makaranta,

Gaskiya Malam yana cikin halin k'ak'ani kayi, domin dai sosai abubuwa suka rikice mishi domin dai tsayin lokaci daya d'auka yana Addu'a akan nemawa Aminatu zab'i mafi alkhairi bai tab'ajin kin had'in aure tsakanin ta da Sarki ba, sai dai shi abunda yake hangowa idan yabada ta aure ma Sarki meye zai iya biyowa baya? Domin dai tsaf yana sane da chakwakiyar da ake ciki hatta shi da kanshi sosai yake tsaye wajen yin ma Sufyan d'in Addu'a dan ganin ya dawo hayyacin shi domin a bayyane take cewar a yanzun kam Fateemah tasha kan Sufyan, to amma in yak'i auren yaba ma wani Aminatun ba lallai Malam Sulaiman da Uwar gida su mishi uzuri ba, dan haka yana ganin gara ayi auren in yaso sai su bisu da Addu'a kawai,

To amma Aminatu fa?
Hakuri zatayi koba komai ai Sufyan d'an uwanta ne koba komai yasan bazata k'ishi ba tunda ba wasu samarin take kulawa ba dama balle har tasan abinda take so.......

Hhhhhhhhh akwai gwarama fa. Domin ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login