Showing 141001 words to 144000 words out of 174305 words
Chapter 48 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
ka da abinda zan ce mishi"
Ganin tana k'ara ja mishi rai akan abinda baifi ya danneta ya kwata ta karfi bane yasa shi yunk'urawa da niyyar ya zafko ta sai dai kuma a dai dai lokacin cikin nashi ya k'ara mishi wani irin mugun kullin da dole sai da yakai kwance yana salati,
Ita kuma a zaton ta wayau yake mata dan ta matsa kusa dashi,
Da sand'a ta samu ta wuce inda yake kwance ta wani irin zabgaga da uban gudu ta fice a d'akin dan gara ta fita ta duba ko zata samu wanda zaizo ya fito mata dashi su kaishi asibiti,
A bakin kofar falon ta suka kusan cin karo da Hajiya dake shirin shiga falon.
"Ke kuma lafiya kike fitowa da gudu kamar wata wacce mutuwa ta biyo? "
"Hajiya sarki ya Sarki ne baida lafiya wallahi mutuwa zaiyi in ba'a kaishi asibity ba dan Allah muje ki kamo min shi mu kaishi asibiti"
Jan hannun Hajiyar ta fara da niyyar suje ciki,
"Subhanallah meke damun shi? Tun yaushe ne bashi da lafiyan Ina ce yaune kukayi gurmin to yaushe ya fara ciwon"
"Nidai Hajiya duk ban sani ba na dawo dai na same shi ya fado daga kan gado yana ta nishi kamar zai mutu"
Matsawa baya kad'an Hajiya tayi tana k'arewa Meenal din kallo...
"To ke kuma miya sameki haka naganki duk wani a yamutse kamar wacce ta kutto daga bakin kura? Kalle kifa duk kin wani yamutse"
"To ba naje d'agashi mu fito bane kuma shine na kasa shi yasa na fito in kira masu gadi ai"
"To ai ko yanzun sai mun nemo masu ceto Ina ni Ina iya d'aukar wannan mijin naki mai k'irar mutanen farko, koma daga ciki ki d'an gyara shi bari in ma Dan mai k'arfi magana yau ga ranar shi, dan nasan shi kad'ai keda zarrar d'auko shi ya fito mana dashi zuwa waje"
Komawa cikin tayi kamar yanda Hajiya ta buk'ata yana nan kamar yanda ta fita ta barshi...
"Ya'ya zamu tafi asibitin gasu Hajiya nan sun shigo"
Hannun shi kawai ya iya mik'a mata yana mata ishara da cewa ta rik'ashi ya mik'e tsaye,
"Ke takwara kuna ta inane? Ina d'akin mijin naki yake?"
"Gamu nan Hajiya"
Ta amsa ma Hajiyar tana fita daga d'akin.
Hajiya ne a gaba shi kuma AK a bayan ta, fuska d'aure da alama dai dole Hajiya tayi mishi bawai da son ranshi ya shigo gidan ba,
"To shiga daga ciki ka fito dashi ko! Ke kuma gyara mishi a hanya dan wannan aikin na maza ne ba iyawa zakiyi ba, nidai gani nayi da ace masu gadi da baku had'a komai dasu ba su shigo su gane miki sirrin gida ai gara shi koh? Naga dai ai koba komai shi d'an uwan kine, dan duniya yanzun ba gaskiya ka shigo da mutum yazo ga gama gane maka tsarin gida sai dare yayi a taho harda shi a yaye ka tass wallahi, nawa kuma akayi"
Ita dai Meenal bata tsaya sauraron Hajiya ba itama tabi bayan shi cikin d'akin,
Abunku da namiji yana zuwa haka ya d'ago shi ta gefe ya rataya hannun shi a kafad'ar shi sukaci gaba da taku sannu sannu har suka fice daga d'akin Hajiya na famar jera ma Sarki sannu da fatan Allah ya sawake,
Motar da AK yazo da ita ya nufa dan dama kafin ya shiga gidan saida ya bude kofofin motar ya barsu bud'e, dan haka suna k'arasawa ya taimaka ma Sarki ya shiga, ganin fitowar sune kuma yasa sauran ma'aikatan gidan tasowa suna tambayan Lafiya,
"Bashi da Lafiya"shine amsar da AK ya iya basu a takaice, gaban motar Hajiya ta shiga tayi ma kanta mazauni, ita kuma Meenal ta zagaya ta d'aya gefen da niyyar shigewa motar ita ma,
"Keeee!!!! Gidan ubanwa zaki bimu a haka? da wannan shegen rigar na jikin ki kai ko kallabi babu karki sake ki shigar min mota na fad'a miki, k"
Ya fad'a a matukar fusace, sai kuma ya juya inda ma'aikatan gidan sukayi cirko cirko
"Ku kuma kuna iya komawa bakin aikin ku an gode"
"To Ya AK dan Allah ka jirani in canzo kaya sai in fito mu tafi tare"
"Eh na Jiraki mana tunda ga direban gidan ku, kinga kafin ki fito shi kuma ya mutu koh! Come on jare bace min anan"
Hajiya ne tasa baki da cewa..
"Ah ah ka bari ta Sanyo ko hijabi ne sai mu tafi tare Ina zai yiwu mu barta ita d'aya"
Jin Hajiya tasa bak'ine yasa ta samu kwarin gwuiwar falfalawa da gudu zuwa ciki,
Shi kuma ya bita da kallo yana jin uwa zuciyar dake kirjin shi tana shirin fitowa, mai da duban shi yayi inda ma'aikatan gidan suke da ya tabbatar ba ita suke kallo ba sannan ya samu salama,
Kamar yanda ta shiga da gudun hakan ta k'ara fitowa,
Lokacin harya juya motar an ma bud'e mishi gate,
Tun bata gyara zamanta a cikin motar da kyau ba ya gaza daurewa sai da ya furta,
"Bana hanaki wannan yawan gudun da kikeyi ba? Ke me yasa har yanzun wai baki san kin girma bane, Abu kad'an gudu kamar wata shil shila"
"Sorry" kawai ta iya furtawa, tana maida hankalin ta kan Sarki dake rik'e da cikin shi sai dai yanzun baya wannan nishin na d'azun bata sani ba ko ciwon ya ragune ko kuma ganin idon su Hajiya ne yasa ya kama jikin shi oho.
"Wani asibity kuke zuwa?"
"Dr Mubarak"
Ta bashi amsa,
Babu b'ata lokaci suka isa asibitin, kamar yanda ya tallafo shi daga cikin d'akin shi zuwa waje haka ya k'ara tallafa mishi suka fito a cikin motan kafin ma'aikatan asibitin su kawo kujerar da aka daura shi suka shige dashi ciki,
Ganin an shige dashi ne hakan yasa Meenal nufa office din Dr Mubarak dan ta shaida mishi wanzuwar su a cikin asibitin, tunda ta mik'e yake binta da kallo ga mamakin shi sai yaga ta nufi office din da aka rubuta sunan maishi a saman kofar d'akin,
"Keee"
Ya d'aga murya yana kiranta,
Juya tayi dan rainin wayau kuma wai sai itama take tambayar shi da cewa "ni" tana nuna kanta.
"Eh kefa Ina zakije anan wajen?"
Ya fad'a shima yana nuni da office din da take shirin shiga,
"Dr zan gani"
"Ke kadai?"
Bata gane mai yake nufi ba dan haka bata iya bashi amsa ba.
"Dawo nan ki zauna!"
Kwabe fuska tayi kamar wata mai shirin yin kuka,
"Hajiya kice mishi ya barni in shiga Dr din fa abokin Ya Sarki ne zan fad'a mishi ne saboda yaje ya duba shi"
Kafin Hajiya tace wani abu sai ga Dr ya bullo da alama kiran shi akayi,
"Dr Mubarak"
Meenal ta kira shi tana k'arasawa inda yake tun bata jira ya amsa mata ba,
"Ah ah Aminatu keda waye anan? Waye ba lafiya?"
"Dr Ya Sarki ne babu lafiya yana can d'akin an shiga dashi nayi zaton ko kana cikin office din ka ne naso inje in sanar dakai sai kuma gaka"
"Subhanallah Sufyan da kanshi! Tun yaushe ne bashi da lafiyan?"
"Nima ban sani ba naje makaranta ne na dawo na sameshi a haka"
"Subhanallah to bari inje in duba shi keda waye kuka zo?"
Nuna mishi Hajiya da AK tayi,
"Kakata da Yayan mu"
Sai da ya gaisa dasu sannan ya juya zuwa duba halin da sarki ke ciki.........
Ita kuma ta koma gefe AK ta zauna,
"Ke saboda baki da kai shine zakije office din wani k'aton ke kad'ai koh?"
Yayi maganar kasa kasa dan baya son Hajiya taji shi,
"To ai shi d'in abokin mijina ne"
Kamal saukar dalma akan gyambo haka yaji saukar kalmar a zuciyar shi, lallai ma yarinyar nan abun nata ya bunk'asa har shi zata cema wai wani abokin mijinta ne,
Bayan ganin idon shi ai yaga abinda ke wahalar da mijin nata dan da taje gidan bai ganta ba amma yanda Hajiya ta dunga zabga f'ada tana ba Hajiya Jummai labari yasa ya fahimci komai tass.................
To dai Sarki bai mutu ba masu mashi fatan mutuwa sai kuyi hak'uri ku cinye gumbar da kuka daka atoh.
*ummiee Zaria*โ๐ผ[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ๐ฑโ๏ธ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ *DANGINA!*๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆโ๏ธ๐ฑ
~{{MY FAMILY}}~
*RUBUTAWA*
*UMMIEE ZARIA*
````` *Page 41*....
"To ke yar nan ai sai ki kira mutanen gidan ku kona gidan su shi mijin naki dan su san abinda yake faruwa koh?
Dan yanda muka kawo shi ranga rangan nan nasan indai likitocin nan na gaskiya ne tofa bazasu yarda su sallame shi ya koma gida ya mace a banza ba, dole rik'eshi zasuyi har jikin nashi ya dai'daita,
Wai ke tsayama ! Shin ina kike cire rigar likitancin naki kika rataye wai da baki tsaya kin duba shiba? Kin daiji kunya wallahi kina likita a gida anma kin kasa tab'uka komai"
"Uhmm nidai Hajiya dan Allah kiyi shiru asibiti mukefa ba gida ba, ke a ko ina ma sai kiyi ta surutu, kuma ni nama manta da wayata a gida ban d'aukoba da zamu taho sai dai ki bani Aron taki in kira dashi"
"Kujimin wani zancen banza wajen yar wajen Jidda fa, to wallahi kiyi ta kanki dan nidai kin san da zarar naga ba dai dai ba tofa sai na tofa, daga cewa ki kira shine zaki hayayyak'o min kice sai dai in baki wayata salon kin cinye min katin wayar, badan halin kiba dai gata ki kira iyayen mijin na ki dan gara suzo su tsaya akan d'an su dan dai nida jikana ba zaman jinya zamuyi ba taimakon musulunci ne ma yasa na matsa mishi ya shiga ya fito dashi muka kawo shi asibitin nan, taimako dai ba wata abun tsiya ba to kin dai san sha'anin asibiti kar sugan mu da k'atuwar mota su fara lissafo abubuwan da zasu mishi amfani dashi dan nidai kudin jakata uzurin da zanyi dasu daban bana hidimar asibity bane,
Atoh ina dalili za'a sani zubin adashin da babu kwasa bayan shi mijin naki ba gidana yake zuwa ba balle ince ya tab'a kawo min wani abun ko hakan zaisa yau in mishi kara, naki wasa ne yarinya bari ki gani uwarki zan kira ita tasa mayafin ta shiga gidan nasu fad'a musu"
AK dake ta danne danne a waya ne ya amsa ma Hajiyar da cewa...
"Ba sai kin kirata ba na riga na turama Sa'eed sak'o nasan zai kirani"
AK ya bata amsa yana b'ata rai dan shima surutan ta sun fara sha mishi kai, inba abun Hajiya bama waye ya tambayeta ta bada ko kwabon tane,
Kawai fa dan shi Sarki baya zuwa gidan ta balle ta samu damar more mishi aljihu shine yasa take duk wannan maganganun,
Kiran Sa'eed daya shigo cikin wayar AK ne yasa shi tashi ya barsu a wajen yana nufar hanyan wajen asibitin dan ya tarbi Sa'eed din bayan ya amsa wayar.
Dr Mubarak yad'an jima kad'an kafin ya fito daga inda Sarki yake,
"Sannun ku da zama Hajiya"
"Yauwa sannu Dr yamai jikin ya k'ara ji?"
"Jiki alhamdulillah zai samu lafiya insha Allah dan zuwa anjima in ya k'ara warware wa ma kuna iya komawa gida dashi, amma
Hajiya inba damuwa zanso mu d'an karasa daga cikin office d'ina domin akwai abinda nike so mud'an tattauna, akan ciwon nashi,"
"Ah ah dani kuma zaka tattauna? ai dai gara in ma wani abun ne ka jira har yan uwan shi su iso dan sune dolen shi, kaga nifa ba wata uwa na had'a dashi ba kawai dai ni uwar Jidda ce mahaifiyar matar shi amma bacin haka ni ban had'a komai dashi ba sai dai zumunta irin na musulunci da kuma auren shi da ke rataye a wuyan jikata, atoh Allah dai yasa ba wani abun bane ya taso, dan kaga ni dai bada shirin zuwa asibity na fito ba dan haka jakata ma yan kud'ad'en cikin ta basu taka k'ara sun karya ba,"
A zuciyar shi yace ๐ฎ wow wanga tsohuwar daga gani yar jidalice, a fili kuwa dariya ya d'anyi, sannan ya daura da cewa..
"Hajiya dama ba wani abu bane domin maganar dama da ita matar nashi ya kamata inyi to amma tunda gaki a kusa shi yasa nike so kema kisa baki dan nasan zata fi jin maganar ki fiye da nawa inke kika fad'a mata"
"Tooo subhanallah ciwon nashi kuma ya shafeta? Kai likita badai wani mugun ciwon yake dauk'e dashi daya gogama jikata ba dai koh?"
"Ah ah Hajiya ko d'aya baya dauke dako wacce cutar da zai goga mata, mu k'arasa daga ciki dai sai mu tattauna da kyau"
"Ke takwara tashi muje dan nikam gwuiwa ta ta fara sanyi kedai wannan aure naki dai toh Allah dai yasa kaffara ne, dan kina kan bautuwa"
Tare suka jera har zuwa office din sannan Dr yayi musu nuni da kujerun dake gaban teburin shi suka zauna shima ya zagaya ya zauna.
"Hajiya ko kina buk'atar wani abin a kawo miki? ruwa ko lemu wanne kike da buk'ata"
"Ah ah wallahi na gode, kaga nikam da ruwan nan gara kayi gaggawar shaidamin abinda kenan dan insan wani sabon iftila'in ne kuma yake tunkarar jikata"
Hannu ya mik'a ya zare glass din dake sanye a idon shi sannan yayi amfani da wani hankaci daya ciro daga aljihun rigar shi ya share fuskar shi,
Kafin ya gyara zaman a kujerar da yake zaune kana ya d'aura da cewa..
"Hajiya a binciken da mukayi akan ciwon nashi mun gano cewar ba komai ne yayi sanadin ciwon ba face, hali na matsanan cin sha'awar da yake ciki domin ko rashin samun biyan bukatar da zai gusar da sha'awar ne yasa har ciwon ya taso mishi haka sosai,
Abinda yasa nace ina son magana daku ba komai bane sai dan inyi ma ita matar shi nasiha, wala'allah ko sun samu sab'anin da yasa kila koda ya nemeta tak'i bashi had'in kai wanda hakan ne kila yakai shi a wannan halin da yake ciki,
Domin dai inba haka ba wannan dole yaxam abun d'aure kai duba da cewa magidanci kamar shi ace yana fama da ciwon sha'awa alhalin kowa yasan yana da mace har biyu, na aure"
Sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin yaci gaba da jawabin shi...
"Nafi ta'allaka matsalar a wajen ita Aminatu duba da cewa anan dai itace a tare dashi"
Juya gefen Meenal yayi ya fuskanceta da kyau,
Ita ko Allah ya sani da tasan abinda zai biyo bayan shigowa office din kenan wallahi da bata shigo ba, kuji min sharri kawai zai wani ce wai laifin daga ita, ita ina ruwan ta da ciwon shi tuntuni bai san bashi da lafiya ba sai da yaga matar shi tayi komawar tane zai wani kama ciwo!
"Meenal "ya kira sunan ta
Bata iya amsawa ba tadai dago kanta kad'an,
"Meenal meya had'aki da mijin ki wanda har yasa kike hanashi samun natsuwa dake?bayan kin san hakkin hakan a wuyar ki ya rataya! "
Ji tayi kamar ace tayi wani siddabarun da zata bace b'at a wajen.
To jama'a fisabilillahi wani amsa zata bashi?
Hajiya ce ta amsa mishi da cewa,
"Masha Allahu anzo inda nike so azo!
Dan nan kace ciwon sha'awa ke damun shi koh?"
"Eh Hajiya gaskiyar kenan"
Waigawa tayi inda Meenal ke zaune sai faman mutsuยฒ takeyi gaba daya ta kasa zama da kyau akan kujerar da take,
"Ke takwara fad'amin shekarun ku nawa da aure yanzun?"
Bata iya d'ago kanta ba ta amsa ma Hajiyar da cewa "shekara 6"
"To kaji shekarun su 6"
"Yauwa to fad'amin a tsayin shekarun nan sau nawa mijin ki ya nemeki a shimfid'a?"
Zumbur Meenal ta mik'e da niyyar barin office d'in jin wani sabon tonon asiri da Hajiya ke shirin mata a gaban Dr Mubarak.
"Kina dai fita a d'akin nan kin san wa zaki tarar a wajen dan haka zaifi sauk'i ki dawo ke ai Allah ne ma ya miki gata yake son warware mana komai cikin sauki"
Badan taso ba tana tura baki tana komai haka ta koma a kan kujerar data tashi ta zauna.
Shi dai Dr kallo kawai yake bin Hajiya dashi jin wani zance daban da take son kawowa.
"Uhummn bashi amsar tambayan da nayi miki"
"To Hajiya kema ba kin sani ba" ta fad'i hakan cikin turo bakin ta gaba,
"Ni idan na sani shi likitan yasan gaskiya ne? Koba a gaban ki kinaji yake neman d'aura miki laifin da ni dake mun san ba naki bane, dan haka nike son yaji komai a bakin ki ta yanda zai zama min shaida a gaban iyayen ki, dan haka fad'a mishi don ya sani"
"Ni tunda mukayi aure babu abinda ya h'adamu kowa a d'akin shi yake kwana"
"To kadaiji da kunnen ka koh? Kaji kuma daga bakin ta ba daga bakina ba balle kace ko k'arya na shek'a maka, to Alhamdulillah Dr ai nan d'in dai asibitin Kane koh? dan haka duk ranar da zaka bada sheda ya zagayo ni da kaina zansa azo a tahomin da kai ka kafamin sheda,
Yanzun kuma sai kasan maganin da zaka bashi wanda zai d'auke mishi sha'awar har ya ririta ta yaje ya sauke ma wancan matar nashi ita na k'arfen ita kuma jikata tunda Allah ya mata gata har tayi dakon igiyoyi uku na aure tsayin shekarun nan ba tareda ta tsallake sirad'in auren ba aini abun inje in siya dabino in raba sadaqa ne dan jama'a su taya mu murna, kai Jama'a! kai Jama'a!! Ke takwara wannan mijin naki tabbas kiyayyar shi gareki bayya nan niyace,
Ashe mu ya maida yan iska ni ina can ina ta kissima cewar ko kishiyace ta shiga tsakanin ku yo ashe shi kam rass yake da lafiyar shi da komai, to aiko tunda har rashin kauna takai haka ni nan zan nuna ma kowa na isa tashi mu tafi"
Ta k'arasa fad'a a fusace tana mik'ewa,
"Hajiya kiyi hak'uri ki zauna dan ban gane me yake faruwa ba?"
Tarar numfashin shi tayi da cewa,,, "kaga duk tarin tambayoyin ka gara ka nemi littafi ka rubuta in yaso inshi ya tashi sai ka jero mashi su ya baka amsa, ni kam na riga na samu amsar abinda na d'ade ina nema a wajen ka, kana iya kiran yan uwan shi suzo su zauna dashi mu mun tafi"
Cike da dumbin mamaki Dr Mubarak