Showing 174001 words to 174305 words out of 174305 words

Chapter 59 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1864

yin aure Bayan shekara 6 aure ya mutu an b'ata ma maman shi suna daga budurwa zuwa bazawara,
Koya ya zaiji in wannan bakin labari ya iske shi?
Wani mataki zai d'auka gudun kar hakan ya k'ara faruwa akan wata daga cikin ahalin Bayan Meenal.

Haha haha, wai ina labarin gwarzon mu Abdul Khareem Ahmad Mai Jama'a ne?
Shiru dai har yanzun bai iso zaria ba.

Shin AK zai samu cikar burin shi na auren Meenal cikin sauk'i kamar yanda yake hangowa kuwa?

Yaya soyayyar su zata kasance ne, zatayi saurin amsa mishi intama ta fada soyayyar shi ko wani ne zai zo yayi ma nata zuciyar kutse?

Yaya teemah zataji a sanda labarin mutuwar auren mijinta zai isketa?
Wani mataki zata d'auka dan hana shigowar wata gidan ta Bayan Meenal?

Shin Sarki zaije ya nemi yarinyar da Meenal ta bashi number da adireshin? Ko kuma hakura zaiyi yaci gaba da zama da Gimbiyar shi?

Wadan nan tambayoyi dama wadansu masu tarin yawa duka zaku samu amso shin sune a cikin littafin *DANGINA* kashi na biyu,
Wanda zaici gaba da zuwa muku nan bada jimawa ba insha Allah.

Ina mika godiya zuwa gareku yan uwa makaranta da kuka b'ata lokacin ku wajen karatun littafi na,
Nagode kwarai da yanda kuka dunga k'arfafa min gwuiwa da fari nayi zaton cewa bazan iya ba amma kuka tsaya a kaina wajen ganin ban dakata ba,
Nagode da soyayyar ku a gareni,

Kuna da yawan da bazai yuwu ince zan tsaya lissafo sunayen kuba,
Sai dai ako ina nike zan kasance mai alfahari daku akoda yaushe,

Son so fisabilillahi ina fatan Allah ya had'amu a littafi na biyu cikin aminci da sallama,

*Domin yin gyara shawara ko matashiya akan wani abunda na manta zaku iya magana dani kai tsaye a wannan number din 08061358462 Nagode*
*Alhamdulillahi*

*Ummiee Zaria*✍🏼

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login