Showing 120001 words to 123000 words out of 174305 words
Chapter 41 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
hakan ta kasance ai ba laifi bane koba komai ai kowa yasan dama son sone amma kuma son kai yafi wata ma daga waje can wata uwa duniya ta aure shi take cin arzikin shi balle kuma ni *Jinin shi DANGIN SHI* ko kin manta ne cewar wata kusan tafi wata kusan naga ai nikam dai koda aure ko babu ina iya had'a kayana in dawo gidan nan dan in dangwali arzikin Ya'yana balle kuma gashi yanzun darajojin sun k'aru, domin dai tuni na fara amsa sunan *Matar Sarki* nima"
Ta karashe fad'a tana wani marmar da ido uwa wata babbar mace,
A gefen Teemah ko kai tsaye zamu iya kiran kafewar da tayi a waje guda da mutuwar tsaye, domin sosai kalaman bakin yarinyar nan suka dake ta, duka kuma irin na mamayar da yazo mata a bazata, dan batayi zaton yarinyar tana da confident d'in da har zata iya tsayawa a gaban ta ta maida mata martani har haka ba, sai ga shi a gaban Sarki akayi komai amma ko sau d'aya baiyi yunkurin takama yarinyar burki ba sai ma waje daya nema kawai ya zauna abunshi.
Shiko ya zauna ne saboda tabbacin da yake dashi cewa infa yaci gaba da tsayuwa tofa bazaiji wahalar takawa wajen damk'o su ya gwara kawunan su waje guda ba ya sumar ko ya denajin cece kucen su, dan hakan nema yasa tun zaman nashi ya lazamci maimaita fad'in kalmar innalillahi wa'innah ilaihir raju'un, sai da yad'an lafa, sannan ya bud'e baki cike da bada umarni yace...
"In kungama cacan bakin kunemi waje ku zauna"
Zaman dukan su sukayi kowacce nama yar'uwarta kallon hadarin kaji.
Ganin sun zauna d'in shi kuma sai ya mik'e ya kufi inda dispenser ke ajiye sai da ya latsa ya cika kofi da ruwa masu sanyi ya shanye har sau biyu sannan ya k'ara d'aukar wasu kofunan suma ya tsiyayo ruwan a cikin su ya nufo inda suke zaune,
Mik'ama dukan su ruwan yayi ba tareda yace komai ba,
Koda bai furta ba sun san cewa dai yana nufin su shane, ita dai Meenal kad'an ta kurb'a dan ba wai k'ishin take ji ba, amma Teemah kam duka ta shanye har sai da ta k'ara dana hannun shi saboda yanda bama-baman kishi ke mata tashi a cikin kirjinta suna kai mata harin bazata.
Babu wanda ya k'ara ko tari a cikin su sai ma Meenal dake cin apple d'in da tun d'azun ta ciro shi daga fridges saboda yayi sanyi da yawa dama shi yasa ta ajiye shi a gefe dan ya huce, yanzun kam da ya rage sanyi hankalinta kwance ta d'auki abinta tana yankawa da yar karamar wuk'a tana ci, kamar ma ta manta da mutane a falon.
"Uhumm-uhmmm"
yayi gyaran murya yana mai k'ara gyara zaman shi, kafin ya maida kallon shi akan Teemah.
"Abinda kike bukatar yi kenan dama anan shi yasa kikace in kawo ki?"
Shiru tayi ba amsa dan sai yanzun data sha ruwan nan hankalin ta ya dawo jikin ta sannan ta tuno da gargad'in da aka mata cewar karta takale shin da sab'ani zai shiga tsakanin su,
Dan haka sai tayi k'asa da kanta cikin sassanyar murya tana kokarin boye bacin ranta tace.
"Kayi min afuwa Baban Boy sharrin shedan ne! Hakan bazai kuma faruwa ba"
Har cikin zuciyar shi yaji dad'in furucin nata amma sai ya dake bai nuna hakan ba ko a fuska,
Ita ko mutuniyar ku duk da bawai kai tsaye take kallon taba amma k'asa k'asa take faman aika mata harara jin da tayi kuma tace wai sharrin shedan ne yasa itama cikin kasa da murya sosai tace.
"ai kece shaidaniyar mai shigoma mutane gida ba sallama"
Gefen Meenal ya kaida duban shi,
"Ke kuma haka aka koya miki karb'an bak'i? Kinyi bak'uwa ko ruwa baki iya bata ba kun k'are da fad'a bayan kuma ita d'in ba tsarar ki bace, ko bakiga ita d'in ta girme kiba?"
Kyar ta daga fararen idonanuwan ta tana mishi kallon ido cikin ido ta yamutsa fuska tana mai turo bakin ta tace,
"To ai ko a musulunci babu inda akace bak'o ya shigo gidan mutane babu sallama balle kuma gidan matan aure, kuma fa har mara tarbiya ta kirani bayan kuma ai abunda yayi ka nima shi yayi ni, in tarbiya ne ita Babban ai a wajenta zan gani har in d'auka amma ta shigo gida kamar wata pastor bayan ko gidan arna ana nocking"
Ta karasa fad'a tana mai da kai gefe.
"To naji bata kyauta ba ta shigo gida ba sallama, amma kuma itama d'in ai gidan tane nan d'in tunda gidan mijinta ne! "
Ba zato ba tsamnani yaji ta bashi amsa da cewa,
"Ah ah kam gidan ta yana Lagos nan kam tuni ya amsa sunan Gidan Meenal tun ranar da aka d'aura aure aka kawoni cikin shi, in kuma mutum yana tantama zai iya fita daga waje ko yaro ya samu yana iya tara ya tambaye shi cewar gidan waye nan d'in dan ya tabbatar, koma ba wannan ba tsayin shekaru gidan nan ai kowa ya tabbatar ba'a ajiye ko wacce macen aure a cikin shiba sai yanzun, mai yasa tun wancan zamanin bata dawo gidan ta zauna ba sai yau ne za'ace min gidan mijin ta, nan gidan Mijin Aminatu ne can kuma inda take shine gidan mijin ta"
Kai innalillahi jama'a wai dama yarinyar nan haka take? Ko kuma yanzun ne ta dawo haka? Ya tambayi kanshi sai dai kuma babu wanda zai bashi amsa a tareda shi,
Ita ko Teemah yanda kuka san wata gunkiya haka ta koma domin dai ita zata iya cewa anan d'in da take zaune iya zuciyarta ne kad'ai yake bugawa amma hatta da jinin jikinta batajin yana zagawa a cikin jijiyoyin ta lallai tayi sake da yawa da har wata ke iya kiran sunan mijinta da sunan nata a kuma gaban idon ta, tana raye tun bata mace ba.
Dan haka da kyar ta iya bud'e bakin ta tace.
"baki da labarin cewa shi gidan mijin da kike ikirarin naki , shi mijin auren cushe aka mishi dake ma'ana auren dole? "
"Fateemah"
sarki ya kira sunan ta a kokarin shi na ya dakatar da ita,
"Kar kace komai ka bari in fad'a mata tasan matsayin ta cewar ba sonta kakeyi ba ka aureta ne kawai dan kayima iyayen ku biyayya"
Abun ya daki Meenal kwarai amma ta danne dan bata son ta nuna gazawarta tun yanzun,
"Ai ba mijin kine akayi ma auren dole ba face ni da nike da kananun shekaru amma aka nakashe min rayuwa wajen had'ani da tsoho,
Dan koba komai shi tsohon tunda ya samu sabon jinin da yasan zaiyi tafiyar dogon zango da ita ai dama bazaik'i ya amsa ba,
amma nifa?
Bari in miki tuni akan maganar d'azun da kikace cewar bani da tarbiya, to ki sani tarbiyyar dana samune yasa harna iya daure zuciyata na amshi tayin auren tsohon mijin ki dan in bancin biyayya ba kema kin san babu yanda za'ayi in k'are da auren tsoho kalleni da kyau ki gani"
Ta fad'i hakan a yayin da ta mike tsaye tayi taku d'aya biyu sannan ta k'ara juyowa ta bada wasu takun,gyas gyas gyas sautin yatsun babba da da d'an tsakiya data had'a ta kyasta,
"Ya kika gani ai Aminatu kowa ya gani yasan tafi k'arfin yaro sai dai baban yaro, hakan nema ya bani kwarin gwuiwar naji zan iya zama da mijin ki dan haka ki koma can inda kika fito kisa ido kisha kallon yanda zan wanke shi ya koma dai dai dani, bari in fad'a miki ita sutura in kinga tayi saurin tsufa wanki da gugane basu wadace taba"
Komawa kujerar data tashi tayi bayan ta gama karkad'a musu kayan alatu ta maida kafafuwanta ta d'aura daya kan daya.
Da kallo sarki yayi ta binta mamaki yana neman sumar dashi a zaune,
Ashe haka take?
Sai da Sarki yayi da gaske sannan suka nutsu da habaice²n da suke jifan juna dashi.
Tashi muje in mai dake masaukin ki"
"No anan zan kwana"
Ta fad'a tana mikewa zuwa inda matakalar benen dake cikin falon yake da nufin haurawa sama,
"Wani gidan? Badai gidan nan ba!"
Cewar Meenal itama tana mikewar.
"Oh bakiji abunda nace bane? Yau a gidan mijina zan kwana"
"Teemah mai yasa kikeyin haka ne wai? Ok let me make one thing clear, ki sani duk sanda zaki zo garin nan baki da masauki a gidan nan kamar yanda in itama taje inda kike bata da masauki a naki gidan, na riga na yanke hukunci dan haka ki wuce mu tafi,"
Sororo ta tsaya tana kallon shi, kujimin wani sab'o fa da Sarki yake furtawa wannan ma ai zunubin gangancine wallahi, wai gidan daya gina domin tane zaice bata da masauki a cikin shi, ko dai mutumin nan ya fara korawa ne bata da labari? Kai anya kuwa kodai asiri akai mishi? Eh gaskiya sai dai asirin ai dama ance indai asirine yan zaria sai a barsu🙄 (nidai nace k'arya ne).
😂😂😂😂😂Nace ba Hajiya fa ta iya kashedi wallah gashi dai yau kashedin ta ya kwatar ma jikarta yanci atoh da wa yasan abunda Teemah ta shirya aiwatar wa ayau,
Ummiee Zaria ✍🏼✍🏼
Share and comment please,
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱👨👩👧👦 *DANGINA!* 👨👩👧👦🔱⚜️
*Free book ne ga masu buk'ata daga farko zaku iya magana dani kai tsaye* 08061358462
*Rubutawa*
*Ummiee Zaria*✍🏼
Page 35......
A babu yanda ta iya haka ya mata jagora,
uwa wata rak'uma haka ta bishi a baya suka bar gidan,badan ranta ya so hakan ba,
Wallahi dan dai dare yayi a lokacin ne amma da babu abunda zaisa ta k'ara kwana a Zaria, sai dai ita d'in babu mafi kololuwar abunda take tsoro irin Night travel balle kuma anan da ba garinta ba.
Bayan fitar su daga gidan komawa Meenal tayi ta zauna tana jiran tsammani dan a zaton ta zai raka matar tashi zuwa mota ne ita kuma ya dawo ya zane mata jiki, sai dai ga mamakin ta sai tashin motar su ta jiyo sun bar gidan.
D'aga muryar ta tayi ta kwala ma su Meelat da suka kulle kansu a d'aki kira....
"Ku dallah can ku fito ya wuce fa"
Sif² haka suka bud'e kofar d'akin suka fito,
"Ke Meenal amma dai wallahi kina da k'arfin hali da har kika iya tsayawa a gaban matar nan tana fad'a kina bata amsa inda ta miki duka fa? "
Cewar Maryam.
" tab d'ijan duka dai lallai ma, Oh so kike inyi zaune kamar wata kujera tazo ta haye kaina ta zauna? Ai in tsoho baiji kunyar hawa jaki ba shima jakin bazaiji kunyar kayar dashi ba"
"Kunga nidai ku tashi mu tafi gaskiya karya dawo ya taddamu yace muna zuga mishi mata"
Cewar Aisha da duk cikin su tad'an fisu hankali, "ta sannu uwar iya" Meenal ta fad'a a yayin da ta mik'e tsam mutuniyar ta taje ta murzama kofar falon key ta kulle sannan ta cusa key d'in a cikin bra din ta,
"Sai inga ta kofar da zaku bi ku tafi, wallahi babu gidan ubanda zaku muna nan daku!"
Ta fad'i hakan a yayin da take shirin hayewa sama,
Haka suka dunga rok'on ta akan tayiwa girman Allah tazo ta bud'e musu kofar su kama gaban su amma tayi hayewarta sama taba banza ajiyar su koda ta shiga d'akin da take kwana ma kulle shi tayi dan karsu dameta,
*Bayan wasu kwana ki*
Zuwan da Sarki yayi gidan a waccan ranar bai canza komai ba, domin dai tun fitar da yayi da matar shi bai k'ara komawa ba can ya lalace wajen matar shi sukayi sulhu kafin su wuce Kaduna tare a washe garin ranar daga can ita kuma ta wuce Lagos shi kuma sai washe gari ya dawo,
Bayan tafiyar na Teemah dole gidan ya dawo da kwana sai dai kuma hakan babu abunda ya canza domin dai kowa harkar gaban shi yakeyi shi yana sashen shi da inba yaga dama bane har gari ya waye rana ta fad'i daga ita harshi babu mai ganin wani,
Shi bai neme inda take ba ita kuma dama bashi bane a gaban ta damuwarta dai shine Allah ya nuna mata fitowar result d'insu lafiya dan Wallahi dai ta fara gajiya da zaman gidan gashi babu damar ta fita dan Mommy ta kwad'a mata warning cewa karta yarda ta ganta a gida,
Saukin tama lokaci lokaci uwar gida kan turo K'annin Sarki ko ita da kanta tazo ta duba ta.
Malam ma yazo gidan sau d'aya dan ya duba ya take abinda bai tab'a yima sauran yaran gidan ba wato zuwa d'akunan auren su.
hutun auren da Sarki ya d'auka ya k'are dan haka tuni ya tattara ya koma bakin aikin shi duk da ba wata uwa yake tsinana ma Meenal d'inba amma dai taji kewar rashin zaman nashi a gidan domin yanzun ba kasafai take samun bak'i kamar daba dan su Moon sun koma garuruwan su ,
su Meelat ma yanzun ba kullum suke shigowa ba sai gidan ya zamana daga ita sai masu gadin dake bakin gate,
sai dai in tayi kallo ta gaji ta d'auko kujera ta dawo dashi kofar falon ta ta zauna tana kallon masu gadin dake kaida kawowa ko kuma ta koma sama ta zauna a balcony d'inta dake saman tacan takan iya ganin kaida kawon jama'ar unguwar dake zirga².
Bata da Matsala na komai a yanzun kam domin dai komai an tanadar mata, kuma shi kanshi Sarkin bai bar garin ba sai da ya sauke mata wasu yan kud'ade ko zata buk'aci wani abun, ga sakon abubuwan ci na sha'awa da ake mata daga gidajen biyu , domin dai har gobe indai Malam ya dawo daga tafiya kamar yanda ya saba zai bada tsarabar ta a kawo mata,
A watan ta na uku da aurene ta rok'i Sarki ya barta ta koma Islamiyar su wanda dama a cikin unguwan yake sannan shima ganin yanda take rayuwa cikin gidan ita d'aya yasa ya sauk'aka mata , wajen bata umarnin fita zuwa wani wajen in baya gari a duk sanda hakan ta kama dan ta d'auke ma kanta kewa, dan yasan wani abun na iya tasowa a sanda zata neme shi a waya kuma ba lallai ne ta same shiba.
Abun mamaki kuma a cikin watan nin nan ko sau d'aya batayi irin ciwon marar nan da takeyi mai tsanani ba, koda period d'in zaizo kad'an kad'an ciwon yake mata ba tareda ya takura mata kamar lokutan baya ba.
Rayuwa nata tafiya cike da tarin nasarori tako wani gefen, gefen Meenal dai a zuwa yanzun kam bata da wani damuwa tuni ta cire komai a zuciyar ta taci gaba da harkokin ta,
Sarki yakan yi kokari yazo ya ganta duk bayan wani lokaci gudun shiga hakki sai dai fa babu wani cigaba da aka samu ta fannin auratayya, in yazo dai zai kirata yaji ko tana da buk'atar wani abun, in akwai zata fad'a mishi in babu kuma in ya tashi komawa zai bata kud'ade ta rike a hannun ta,a haka suke zaman
bata k'ara jin duriyar kishiyarta ba balle ta damu kanta dan haka gaba d'aya ma wallahi mantawa take wai tana da kishiya, to mijin ma har yanzun bai amsa sunan miji ba balle kuma wata aba wai kishiya.
Jarabawar su duka biyu sun fito cike da tarin nasarori,
kamar kuma yanda Malam yayi alkawari shida kanshi ya kira Sarki ya fad'a mishi cewar Aminatun zata koma makaranta, baija da batun ba domin dai a cewar shi bashi da hujjar yin hakan sai ma fatan alkhairi da yayi, ya so ace shine ya d'auki nauyin karatun nata domin a cewar shi hakkin hakan a wuyar shi ya rataya yanzun,
sai dai Sam Malam yak'i bashi wannan daman.
Aminatu,
Maryam,
Jamila sun fara karatu cike da karsashi domin dai Malam yayi abunda ya saba naba kowa mamaki wajen gwangwaje d'iyar shi da sabuwar mota domin zirga²n zuwa makaranta, babu b'ata lokaci kam Ya Sa'eed ya shige gaba wajen koya mata motar har zuwa sanda ya tabbatar da kwarewar ta,
Alhamdulillah burin ta na farko ya cika na ganin kanta a matakin gaba da sakandire wanda shi take kallo a matsayin tsanin da zai kaita ga cika sauran burukan nata, kamar yanda suke tafiya sakandire su uku wannan karanma hakan sukeyi ita da Aminanta su Meelat wad'anda babu abinda ya canza a kawancen su sai ma abunda yayi gaba.
Rayuwa yana ta tafiya a 360 abubuwa nata faruwa a cikin shekarar farko Billyn ya sa'eed ta samu karuwar d'a Namiji watan ni kad'an baya ita ma Raheenat ta haihu wanda su Meenal sukaje suna har KD sai da suka kwana biyu suka dawo, ba'a jima sosai ba ita ma Sa'adatu ta haifo nata jaririyar,
Wannan k'aruwa da aka samu shiya fara karkato da hankalin *DANGI* akan zaman auren Meenal da Sarki domin dai har wasu sun fara yad'a cewa Mommy ne take ba Meenal maganin hana d'aukar ciki saboda karya yanke mata karatun ta a yanzun,
Sai gashi babu damar Meenal d'in tayi koda ciwon kaine sai kowa ya fara sa ran ko ciki ne, ita dai ko a jikinta.
A fannin uwar gida ko ita da kanta tasha zuwa ta amso taimako ta kawo ma Meenal d'in domin su abunda suka d'auka shine kila ciwon marar tane yasa har yanzun bata dauki cikin ba, (ko ce musu akayi a ruwa ake shan cikin oho)...
Ita dai Mommy bata tab'a zaunar da Meenal dan taji yaya take tafiyar da zaman auren taba, domin tsayin lokacin nan dai itama Meenal bata tab'a kawo karar Sarki da sunan ya mata wani abun ba, koda ta tambaye ta ya take? Amsarta kullum shine "ina lafiya, "
kai da ganin yanda ta kara mumulewa gabobin jikin ta suka k'ara budewa ma basai ka tambaya ba kasan bata da matsala sai wacce ba'a rasawa, domin dai ta