Showing 168001 words to 171000 words out of 174305 words
Chapter 57 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
kadai hanyar da zan samu kusanci tsakanina da d'ana,
Na manta cewa d'iya mace itace kadai ake iya tilastawa auren dole ta kuma yi biyayya ta zauna tsayin rayuwa koda ko batajin dadin kasancewa da Mijin da aka aura mata,
sab'anin d'a namiji da yake da hanyoyi da dama na kuntata ma matar da aka tisalta mishi ya aura koda ko babu duka ba zagi, sai dai kuma ganin kusancin dake tsakanin su hakan yasa nayi tunanin cewa koda yak'ita a farko akwai yuwuwar cewa zuwa gaba zaiso ta harma yayi alfaharin auren damu muka mishi, sai dai kuma ashe duk hasashe nakeyi "
Dago kanta tayi tana kallon shi fuska a raunane taci gaba da cewa,
"Nayi dana sani kwarai na dagewar da nayi har akayi auren yaran nan,ni ban san gaibu ba da ace Allah yana bamu sani akan abunda zamu riska a gaba da banja tunga na tsaya wajen ganin tabbatuwar auren ba yanzun da wani idon zan kalli jama'a?"
Kamo hannunta yayi ya zaunar a gefen shi,
"Maiya faru har hakan ya kasance bani da labari, kafin ki aikata komai daya shafeki ko yaranki, nine mutum na farko da kike fara tuntub'a don neman shawara, mai ya shiga kanki kai tsaye kikayi saurin yanke hukuncin raba auren da kika sa na shige gaba wajen neman shi,
ki fad'amin komai, dan kinsan ko ban furta ba ina cikin bakin ciki mara misaltuwa na abunda ya faru, kedai kin san komai dan gane da jelen dana dungayi wajen Malam kafin ya amsa batun auren nan,
Babu irin nacin da ban mishi ba kafin ya amsa mana,
ba kuma dan komai ba na tabbar abunda ka iya biyo baya shima yake dubawa a lokacin amma a hakan ya daure zuciyar shi badan yarinyar nan taso ba ya d'auke ta ya bamu,
yanzun kuma fisabilillahi bayan shekaru 6 sai in d'auki takardar sakin ta in tun kare shi dashi!
Da wani idon ma zan kalleshi? ,
karki manta fa wannan shine aure na farko da muka fara d'aurawa a cikin ahalin mu a matsayin *AUREN DANGI* sai gashi ya zama aure na farko da sakama kon shi ya zama mafi muni a garemu,
Sakin aure fa ake magana abinda ya zama bak'o a garemu domin bamu saba jin saki ba kaf a ahalin mu,
A duk cikin yaran da muka aurar babu wacce kaddarar aurenta ya kaita ga batun saki,
ya kike tunanin zanji da kuma wani idon zan kalli yan uwana, cewa d'an dana haifa ne ya saki yar da suka aura mishi a karon farko da zamu samu bazawara a cikin *DANGINA* kuma ta silar auren *DANGI*"
Saida ta k'arayin k'asa da kanta dan sosai take jin nauyin abunda zata fad'a mishi a yanzun, dan sosai take ganin laifin kanta ayau na jajircewan da tayi na tabbatuwar auren a shekarun baya,
"Aminatu bata amsa sunan bazawara ba domin tsayin shekarun nan Mijin da muka aura mata bai tab'a kallonta a matsayin matar shi na aure ba balle har yayi tunanin sauke hakkin ta dake kanshi a shimfid'ar auren su matsayin ta na matar shi"
"Mai kike son cewa ne?"
Ya tambaya.
"Eh Sarki bai kusanci Aminatu ba ko sau d'aya a zaman da sukayi"
"Kin san da hakan kuma kikayi shiru baki tab'a fad'amin ba tsayin lokacin nan sai yanzun kike zuwa min da takardar saki dan kun raina min wayau dake da d'anki?"
Ya k'arasa fad'a fusace.
"Kayi hakuri nima kaina banda masaniyar komai akan hakan,
dan daga ita harshi babu wanda ya nuna cewar akwai wata matsala a cikin zaman auren su, shi yana zaune da itane kawai a matsayin matar da muka bashi umarnin aure badan yana soba, dan haka yaci gaba da zama da ita yana kallon ta a matsayin kanwa ko kuma wani abun daban wanda shima bai san dalili ba,
Ita kuma a matsayin ta na mace budurwa da aka sani mai kunya taji nauyin yanda zata kawo maganar garemu ne shi yasa tayi shiru take ci gaba da zama dashi duk kuwa da irin maganganu da cin fuskan da yaran gidan nan ke mata akan tak'i haihuwa,
Ni bazan d'auki laifin in d'aura shi duka akan shaidaniyar matar shi ba domin na tabbata asiri ma yana cimma hali, in ma matar shi tayi nata siddabarun dan ta shiga tsakanin su tofa shima baya son Meenal d'in domin da ace akwai so bazai zuba mata ido yayi ta kallo tsayin shekarun nan ba,
Sai dai ita kakar yarinyar ta hango matsalar a shekarun baya, ta kuma yi kokarin d'aukar mataki sai akayi rashin sa'a allah kuma ya rubuta cewa karshen abun baizo ba a wancan lokacin,
Tiryan tiryan ta karanta ma Malam Sulaiman komai daya faru tun wancan lokacin har zuwa ranar da tasa Sarki ya rubuta takardar sakin.
"Nasan wasu da yawa ba lallai su fahimce niba, sai dai kuma ni na aikata abunda na aikata ne saboda koda nice na haifi meenal bazan amince taci gaba da zama da Mijin da bata da wani matsayi a wajen shiba,
Domin dai shi namiji ne yana kuma da damar da zai auro wasu matan biyu a bayan ta, amma ita mace namiji guda ne kachal ya halatta a gareta,
sannan mutum ce ita kamar sauran mutane, na tabbatar da cewa idan a shekarun baya ta iya danne kanta a lokacin da bukatar kasancewa da abokin tarayya ya ke taso mata, tofa shekarun da zasu zo mata a yanzun ba lallai ne ta iya daurewa hakan ba, kaga kenan dai tako wani gefe itace take cutuwa domin shi dai yana da wata matar bayan ita, wannan shine babban dalilin da yasa na yanke hukuncin raba auren su, da fatan ita kuma Allah ya bata wanda yafi shi, Alhamdulillah kuma sai gashi tun ba'aje ko ina ba a sanadin ta sanadin rabuwar su d'ana ya dawo gareni,
Kayi hakuri Abban su, kayi fatan hakan ya zama hukunci mafi alkhairi da muka yanke akan su"
Shiru yayi ba tareda ya iya tankawa ba, to me zaice mata kuma bayan mai afkuwa ya riga ya afku,
"Baka ce komai ba!"
"To mai zance miki bayan kintasa k'eyar d'anki ya wuce garin arna, mai yasa tunda yayi sakin baki tasa k'eyarshi kuka kai takardar sakin zuwa inda ya dace ba?
Yanzun ni kike nufin in tunkari Malam da takardar sakin auren Yarinyar nan da kowa yasan kololuwar kaunar da yake mata, kai innalilahi wa'innah ilairir raju'un, ni yanzun fisabilillahi keda d'anki kun kyauta min kenan? To ai sai ki shirya tun karar Malam din da kanki"
Ya furta kana kuma ya koma yayi kwanciyar shi yana mai juya mata baya.
"Haba Abban su taya nida nike mace ace nice mai kai takarda kuma, kadaiyi hak'uri tunda Allah ya kaddara babu yanda zamuyi"
Gwuiwa a sanyaye ta tashi itam ta kwanta jin yayi mata banza bai k'ara kulata ba, kwanciyar dai tayi tana mai ci gaba da sake sake.
Washe gari da asuba bayan Malam Sulaiman ya fito masallaci, gaba da masallacin can ya tsaya yana jiran fitowar Baba Adamu, domin har zuwa lokacin Malam bai dawo daga tafiyar da yayi ba,
tsakani da Allah kuma ido da kunya koda ace Malam yana gari bayajin zai iya tunkaran shi da takardar sakin nan.
Bai dade da tsayuwar ba Baba Adamu da Baba Auta suka iso inda yake,
"Malam Sulaiman lafiya kuwa kake tsaye nan kai kad'ai?"
Adamu ya tambaya.
"Alhamdulillah Adamu kai nike jira wallahi,"
Gaisawa sukayi da juna kafin Baba Auta ya wuce ya barsu nan.
"Ya'ya ko zamu k'arasa cikin gidane?"
Adamu ya tambaya.
"Ah ah Adamu mudai koma cikin masallacin tunda naga jama'a sun watse,"
"Allah yasa dai lafiya!"
Adamu ya fad'a a yayin da suke komawa cikin masallacin.
Takardar ya ciro daga cikin aljuhun sa ya ajiyema Adamu a gaban shi bayan sun zauna,
"Abune mafi girman muni ya same mu Adamu,
ban san da wani idon zan iya kallo ko tun karar Baba Malam ko kuma Auta ba, shi yasa na yanke hukuncin tun karar ka,"
D'aukar takardar Adamu yayi cike da dakiyar zuciya ya bud'e takardar.
"Innalillahi wa'innah ilairir raju'unยณ me yayi zafi haka Ya'ya?"
"Kayi hak'uri Adamu amma yanda kaga takardar nan haka nima na ganta, na kuma ji d'aci sama da d'acin da kakeji a zuciyar ka a yanzun haka, Yaron nan Sufyaan ya bamu kunya domin ya aikata abunda babu wani cikin mu da yayi tsammanin zai aikata, sai kuma fushin zuciya yasa mahaifiyar shi tsare shi harya rubuta takardar sakin ba tareda sani ba,"
kaf abinda ya faru na irin zaman auren daya gudana a tsakanin Sarki da Meenal shima ya zaiyana ma Baba Adamu kamar yanda Uwar gida ta sanar dashi a daren jiya.
"To kaji halin da ake ciki, shi kuma tun d'azun nike kokarin neman shi a waya dan in bashi umarnin mai da auren amma ban same shi a wayar ba"
"Subhanallah gaskiya abu baiyi dadi ba sam, amma kuma ya muka iya kaddarar bawa bata wuce kanshi, haka Allah ya kaddara dama, shi kuma kar kace zaka mishi dole cewa sai ya maidata d'akin ta kayi hakuri mugani zuwa gaba in Allah yace akwai sauran zama a tsakanin su sai kaga shi da kanshi yazo ya nemi sulhu sun koma dan yanzun in ka matsa tofa gidan jiya za'a koma, ina fatan kuma zaka saukaka ma kanka yawan damuwa domin dukan mu munsan aure rai gareshi, maganar tun karar malam kuma ni da kaina zan tunkare shi, nasan dai dole abun bazai mishi dadi ba amma dole yayi hakuri shima dan nasan ko zaiyi fushi na d'an lokaci ne"
Sun dade suna tattaunawa kafin suka fito daga cikin masallacin kowa ya nufi gidan shi,
Baba Adamu bayan ya shigo gida wayar Baba Auta ya kira ya bashi umarnin zuwa ya same shi a sashen shi.
Bayan zuwan Baba Auta sai da suka d'an tab'a hira sukayi harda karin kumalo duka a sashen na Baba Adamu,
Takardar shima ya gabatar mishi kafin ya d'aura da mishi bayanin komai daya faru har ya kaiga afkuwan sakin,
Shi dai duk bayanin da Adamun ke mishi bai iya cewa komai ba illah "Allah ya kyauta yasa kuma hakan shine mafi alkhairi a garesu baki d'aya"
"Ameen" Baba Adamu ya amsa dashi kafin yace mishi,
"Ka turomin ita Jiddan idan ka koma"
"To" ya amsa dashi, dan gara dai shi Adamun yamata bayani da kanshi dan Wallahi shi dai bai san ta ina zai fara ba, ga kuma Malam da yake hanyar dawowa yau, ai wallahi shi kam tafiya zaiyi dama yana da zuwa Abuja gobe ne yakamata ace ya tafi amma yanzun kam ba maganar ya jira har gobe yau d'innan zai tattara nashi ya nashi shirya d'auki matar shi su tafi,
Koda ya koma ya cimma Mommy Hauwa ta gama shirinta tsaf na wucewa office, dan yara tuni sun wuce makaranta sukam.
Dole ya kama kanshi ya shanye damuwar dake kan fuskar shi,
"Kai Mommyn su yanzun da ban dawoba ficewa zakiyi ki barni?"
"Ah ah fa Abban su taya zan fice ban sallame kaba, tunda naji shiru ai nasan wani abun ne ya rik'e ka kaga ni kuma yau ina da ayyukan da zan duba kafin gobe sannan kuma ina son biyawa in dubo Hajiya kwana biyu banje gidan ba,"
"Ita uwata baza'a biya a dubo min ita ba?"
"Wai Meenal ai dan tasan cewa Baban ta baya nan shi yasa baka ganta ba, amma yana dawowa zataci gaba da zarya"
"Oh shi kenan kuma in bata zoba babu mai dubo min ita ga baki ga hanci? To ai shi kenan ni idan na shirya zan biya in ganta, ina tunanin kuma yau zamu wuce abuja, dan haka sai ki dawo da wuri dan kin san bana son tafiyar dare, kin sani"
"To amma abban su ai gobe ne tafiyar ya kama ba yauba ko ka manta lissafin ne?"
"Kedai kika manta, zan shirya maki kayan ki kafin in fita ki biya kuma ta wajen Yaya Adamu yace in turo mishi ke yanzun, kafin ki wuce"
Yana k'arasa fad'ar hakan yasa kai ya wuce sama zuwa d'akin shi,
Bayan shi tabi da kallo domin duk yanda yake kokarin boye damuwar da yake ciki ita ta hango damuwar a tattare dashi,
"Meke faruwa to?"
Ta tambaya a sarari,
ganin babu mai bata amsa hakan yasa ta fice daga sashen zuwa wajen Baba Adamu,
Bayan sun gaisane ya shiga mata nasiha,
"Mommyn yara nasa mai gidan ki ya turomin ke nan ne saboda wani al'amari mara dad'i daya same mu,
kiyi hak'uri na sani cewa tun shigowar ki cikin mu kike fuskantar abubuwa, kuma a hakan kike shanye duka bacin ran da muke sanyaki, kike kuma rike da auren ki da dad'i ba dadi,
Meenal yarkice da kika haifa da cikin ki, duk soyayyar da wani zai nuna ma d'a bayan uwace, amma a hakan kike runtse idon ki akan duk wani abunda ya shafeta, mai dad'i ko akasin hakan baki tab'a tankawa ba,
Dan haka nike rokon alfarmar ki ayau ma ina son ki k'ara hakuri akan kaddarar data afkawa Mamana domin kowa yasan cewa bawa bai isa ya gujema kaddarar shiba"
Ita dai tana zaune ne kawai shiru kamar wacce ruwa yaci, sai dai kuma a kage take da son jin mai kuma ya samu Meenal dinta a wannan karon,
Takardar ya ajiye a tebur din dake gaban shi kafin ya d'aura da cewa,
"Wannan takardar sakin aure ne tsakanin Mamana da Sufyaan, sakin auren da akayi shi tun kusan sati biyu daya wuce batareda mu mun sani ba ciki kuwa harda mahaifin Sufyan din, kuma tun lokacin ita Maman nawa ashe Hajiyar Tudun wada ta mai da ita can gidan ta,
Kiyi hak'uri ki kuma yi mata fatan allah yasa hakan ya zama alkhairi a gareta"
Turkashi......
"Innalillahi wa'innah ilairir raju'un"
Shi kawai Jidda ke ambata a cikin zuciyar ta yayin da a sarari kuma zufa ya dunga keto mata kamar wacce ke gaban kaskon wuta,
Ganin tayi shiru bata ce komai bane yasa shi kara cewa,
"Kiyi hakuri Hauwa'u, Murjaa.... "
Ya kwala kiran sunan matar shi, wacce ke cikin d'akin ta tun bayan shigowar Auta ta wuce ta basu waje dan su tattauna,
"Na'am "
ta amsa dashi tana fitowa,
"Zo dan Allah ki kama Jidda zuwa sashen ta"
Da sauri ta k'araso tana tambayar .
"Mai ya same ta ne Abban Raheenat? Mommy yara tashi mu shiga daga ciki"
Ta fad'a tana kamo Jidda din zuwa d'akin ta, ganin hakan shi kuma sai ya fice daga sashen gaba daya bayan ya d'auke takardar .
"Auren Meenal d'ina ya mutu Murja!....... Sufyan ya maida min yarinya bazawara, tun farko sai da na nuna kin auren nan amma babu wanda ya saurareni gashi ya sakomin ita,
Ina amfanin auren dole ita dake mace ta iya jure zama dashi amma shi ya gaza rikemin amanarta,
Tsayin shekarun nan yarinyar nan bata tab'a kawo min karar shiba kullum idan na tambaye ta ya suke cemin take lafiya lau,
Ki duba irin yanda yan uwan shi ke jifanta da maganganu akan shi harta ni danike uwarta basa shakkar fad'amin maganar daya shafeta ashe cutar min da ita yake, fisabilillahi nawa Meenal take da zai jeramin ita cikin sahun zawarawa,
Kaf gidan nan babu wacce aka sako daga gidan miji sai nawa y'ar wacce ko ni uwarta banyi zawarci ba sai ita k'aramar yarinya,
wani irin *DANGI NE* wannan? Indai haka auren *dangin* yake to daga kan Meenal an gama yin shi a cikin ahali na insha Allah ita da ta zama farko to itace k'arshe,"
Ta k'arasa fada cikin kuka......
Wanda kalamanta su suka karya ma Aunty Murja nata zuciyar ta rungumeta sukaci gaba da kukan tare,,,,,,
Sun dad'e suna kokawa kafin Jidda ta yunk'ura,
"Auntyn su bari inje Tudun wada ina son jin dalilin sakin nan domin Baba Adamu yace min meenal din na tare da Hajiya tun ranar da Sarki yayi rashin lafiya,"
"To zaki iya driving ko in kira cikin yaran gidan wani ya tuk'aki?"
"Kar ki damu zan iya"
Ta fad'a tana ficewa daga d'akin,
Murja batayi yunkurin binta zuwa wajen hajiya bane saboda tasan ko babu komai idan taje can zasu so su zanta akan al'amarin shi yasa ta zauna, sai dai kuma itama sosai batun sakin ya daketa, ace yarinya karama kamar Meenal itace take shirin amsa sunan bazawara fisabilillahi Allah dai ya dai dai ta al'amarin ba tareda rayuka sun baci ba,
Koda Jidda ta isa falon ta bata nemi Baba Auta ba Jakar ta dake nan falon kawai ta d'auka ta fito daga sashen ta shiga mota ta fice a gidan.
Ikon Allah da tsarewar shi ne kawai ya kaita gidan Hajiya lafiya, koda ta isa bata tsaya yin parking mai kyau ba ta kashe motar ta nufi sashen Hajiya,
Zaune ta iske su akan dinning table da alama sai a lokacin suke karyawa,
Kasancewar sallamar da tayi k'asa kasa tayi shi kuma kofar na Hajiya koda yaushe a bud'e yake shi yasa basuyi saurin an karewa da ita ba, har sai da ta shigo tsakiyar falon,
"Ke Jidda wani sabon hali kuma kika tsiro dashi na shigoma mutane gida babu sallama?"
Hajiya ta fad'a a sanda hankalin ta yakai kan Jidda,
"Oyoyo Mommy na wallahi I miss you"
Meenal ta fadi hakan tana tashi daga kujeran da take zaune da gudu ta k'arasa ta rungume Mommyn,
Ita kuma jin Meenal din a cikin jikin ta gaba d'aya sai taji rauni da tausayin Meenal din sun sauko sun lullubeta, dan haka kawai sai ta saki kukan da take ta faman rikewa,
Kuka takeyi irin na wanda abu ya b'ata mishi rai sosai, ta kuma kasa magana........
*UMMIEE ZARIA*โ๐ผ
[8/9, 2:46 PM] Zainabusmanummiee584: โ๏ธ๐ฑ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ *DANGINA!*๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ๐ฑโ๏ธ
~{{MY FAMILY}}~
*FREE BOOK*
*RUBUTAWA*
*UMMIEE ZARIA*โ๐ผ
```` *Page 50*...... *END OF BOOK 1*
Kuka takeyi sosai har zuwa lokacin kuma rungume take da Meenal d'in a jikinta ba tareda ta sake taba,
Cikin hanzari Hajiya ta taso daga kujerar da take zaune