Showing 15001 words to 18000 words out of 174305 words
Chapter 6 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel
sauran yan matan dake zaune a falon domin suma basu lura da shigowar su Meenal din ba hankalin su nakan d'inkunan da suke dubawa,
Sai gashi tun kafin Meenal ta karasa wajen Mommyn yan matasan yan matan dake daura da ita sun taso da azama sun rungume Meenal din suna masu murnar ganin ta suma, Dan haka gaba daya sai shagon ya dauka da hayaniyar su har ba'a tantance me suke fada dan haka mommy ne ta katsesu da cewa "bazaku sakar min yarinya ta karaso inji dumin taba? " Dariya Meenal din tayi "dallah ku sakeni inje wajen uwata kun wani dakune ni kamar kwabo a hannun kuturu "
karasawa wajen mommyn tayi.
"Mommy Yaushe kika zo?" Ta tambaya "jiya" ta bata amsa sannan ta dora da cewa "ai dazun nan nagama fada da Jidda dan naga kowa ban gankiba",
"To ai basu fadamin bane suka tafi suka barni shi yasa nace ya'yan mu ya kawo ni" Cewar Meenal din
* Mommy kunzo lafiya ya hanya?"
" Alhmadulillahi kowa lafiya Mamana" Mommy ta amsa dashi.
"Kawata zoki gaisheda Mommy na"
ta fada tana kallon Meelat, Dan haka Meelat din ta karaso cike da fara'a ta gaida mommy itama sannan suka koma inda Aisha da Maimoon suke Zaune suna cigaba da duba d'inkuna duka Meenal ta d'aka ma Maimoon a baya.
" amma wallahi kudai yan cin amana ne zakuzo shine ba wacce ta kirani a cikin ku", Dukan itama Maimoon din takai mata "kefa wallahi muguwa ce dallah ba surprise muka shirya miki ba kuma ai gashi kwalliya ta biya kudin sabulu ko bakiyi murnar ganin muba?
"Nayi wallahi sannun ku da zuwa ga kawata ku gaisa"
ta fada tana jawo Meelat tsakiyar su "sunan ta Jamila amma Meelat ake kiranta, Masoyiya ta ce ita din kuma ku tayani son ta"
ta fada tana zare musu ido, Dariya sukayi dukan su sannan ta juya wajen Meelat din "kawata wadannan yan uwana ne *DANGINA* na jini wannan sunan ta Maimoon amma Moon ake mata lakabi" ta fada tana taba maimoon din "sai Aisha shatu tsohuwa dafatan zaki so su kamar yanda suke sona? Duka suka kai mata suna dariya "wato ma ashe mu ke sonki ke bakya yin mu? Cewar Aisha suna cikin hirar wani kyakykyawan matashin ya shigo shagon dogo wankan tarwad'a mai kirar karfafa kai tsaye wajen da Mommy ke zaune ya karasa yana mai mika mata gaisuwa cikin girma mawa
"kiyi hakuri Mommy mun d'an shiga cikin gari da yaron kine" Ya fada bayan ya gaisheta, "Tare da Mai Jama'an kuka dawo? Ta tambaya "eh gashi can a Fadar shi tareda su Sadeeq, "Ba laifi ai zai zo ya sameni , nike ta kiran shi baya dauka,"
"Bai fita da wayar ba a gida ya barta shi yasa baiga kiran naki ba" ya bata amsa kai tsaye, "basu kawo miki kayan bane? Bash" ya kwalama Kira sai gashi ya fito "barka da dawowa OGA"cewar bash din,
" Ya akayi baku sallami Mommy ba? Ya tambayi bash din , "Mun sallame su Oga wasu kayan suka kawo,
"ok to jeka koma bakin aikin ka nayi tsammanin ko baka san sun shigo bane ai, Mommy kije kawai ba wani damuwa zaki same su cikin lokaci" Anty Billy ce ta fara gaishe shi kafin su Maimoon suma suka haɗa baki wajen gaishe shi, suma ya amsa musu yana tsokanar billyn da sunan Amaryar su
" Amaryar mu kema dinkin kika kawo ne?
"Eh OGA Musty nawa da nasu Meenal ne ta fada tana mashi nuni dasu Meenal din,
"Kai wa nike gani yau unguwar nan a shagona kamar takwarar Hajiya Innah jaririyar Aunty Jidda? Amma dai batan kai kikayi ne koh? Ya fada muryar shi cike da zolaya, Rufe fuska Meenal tayi da tafin hannun ta tana dariya domin tsaf ta gane shi dan suna zuwa wajen momin ta shida yayyen su Aisha. "kai dan Allah mai sunan baba Malam wai har yanzun bazaka dena cemin jaririya ba"
Ai dole kiji kunya tunda kin san baki da gaskiya, kuma ni ai har yanzun kallon jaririyar nike miki shi yasa"
"Nidai wallahi na girma" ta faɗa tana tura baki,
Mommy ne ta katsesu da cewa su tashi su wuce gida "kije mommy zamu shigo gaba daya"
Cewar Aisha, wucewa tayi ta barsu bayan Anty billy ta bada nata dinkin itama wucewa tayi tabarsu a shagon sai bayan wucewar ta sannan Meelat ta bada nasu itama kiran Bash yayi yace ya turo mishi Asiya ta dauki measurements din su "kawarki bata magana ne Meenal!? " ya tambaya yana kallon Meelat data dukar da kanta kasa saboda yanda taga ya kura mata ido, kallon Meelat din tayi sai taga kanta a kasa tana wasa da yan yatsun ta kamar wata wacce take gaban sirikin ta "kawata ya dai? Meenal din take tambaya ɗan dagowa tayi kadan ta kalli Meenal ba tareda ta iya cewa komai, "ko kunya na takeji? Cewar musty dariya Meenal tayi shi kuma ya samu waje gefen Meelat din ya zauna "An mata yane ko dai kodai²! Dariya dukan su suka fara Maimoon ne tace "Allah ya musty inaga dai kayi kasuwa ne, da gudu Meelat ta daga kanta tana hararar Moon din
"kai dan allah ni yaushe mukayi haka dake? Meelat din ta fada tana kama hanyar barin shagon dariya dukan su sukeyi.
'"To ai shikenan zokiyi zaman ki tunda ni banyi kasuwa ba ke kinyi zadai ku bani koh? Ya tambaya yana kallon su ai kamar hadin baki dan kusan a tare suka hada baki wajen cewa "da gudun besfa ma" fitowar Asiya ne ya katse su "Gani Oga" ta fada tana ajiye littafi tape da biron rubutun data fito dasu, karaso kizo ki dauki Measurements din su kun zabi style ne? "Ah ah" Meenal ta amsa mishi bari in Kira kawata ta fadi style din da za'a mana ɗin" ta fada tana mikewa zuwa waje tsaye ta samu Meelat a bakin kofar shagon tana waya dan haka ba tareda tayi mata magana ba taja hannun ta suka koma cikin shagon measurements din Meelat din Asiya ta fara dauka sannan ta dauki na Meenal sannan ta koma bakin aikinta a ciki ta barsu zaune a falon. "Me zakuci ko me zakusha? Musty ya tambaye su kallon kallo suka shigayi a tsakanin su Maimoon da Meelat sukace sudai sun koshi Meenal da Aisha kam drink suka ce suna so dan haka shida kanshi ya fita bai jimaba ya dawo da leda shake da snacks da drinks din ya damka a hannun Aisha "yanzun zaku wuce ko sai zuwa dare? Ya tambaya yana karema Meelat kallo Meenal ce ta amsa da cewa "sai zuwa anjima gidan hajiya zamu shiga yanzun" "oh baku dade da zuwaba kenan "eh" ta bashi amsa ok to nagode da ziyara to amma zaku tafi banji sunan kawar taki ba! "Jamila (Meelat) ta bashi amsa suna fita daga shagon shi kuma yayi ciki.
*Moon ce ta kamo hannun Meelat din tana dariya bayan sun fita "ke An mata kinfayi kasuwa, dan allah irin kallon da naga Ya Musty na miki nasan da wata a kasa dan yan magana sunce in kaga kare na shinshina takalmi dauka zaiyi,
ke kam ai kinyi sa'a wallahi d'inkin ki a bati style sai wanda kike so" cewar Aisha,
"Ke kibari kawai ai inaga nikam d'inki duk wata sai nayi dan naga waje" cewar Meenal, hararar ta Meelat tayi "kawata bana son haka fa ke wai baki k'are mishi kallo bane? Abu jiki duk a murmurd'e keda ganin shi kinsan yana cin karfe, gidan ubanwa zan kai wannan katon? Dan allah ku rufamin asiri kubar maganar nan".
"Anki abar maganar, ke yarinya karki raina min wayau fito fili kawai kice kin raina arzikin shi baki iya soyayya da tela inba haka ba ai wallahi ko hasidin iza hasada yasan mai sunan Malam hadaɗɗe ne karki bata min rai Ina ce a makaranta Head Boy sonki yake, koba kuɗin shi mukeci kullum ba? ta fada tana zazzarema Meelat din ido kamar zata kai mata duka,
"Ke kifa kiyayeni inba so kike mu raba hali a wajen nan ba dan iskanci kike maganar Head Boy yo shi wannan Namiji ne? Yaron da sai ubanshi ya bashi kudin breakfast yake zuwa ya kashe min uban me zanyi dashi kema ai kinsan dan dai kar a raina mu shi yasa nike kulashi,"
Suko su Maimoon tsaye sukayi suna rarraba ido kamar marasa gaskiya tsoron su Allah kar yasa wani daga cikin yayyen su suji wannan hirar yau su shiga uku Aisha ce tayi karfin halin cewa "ke Meenal muna kusa dasu Ya Mai Jama'a nefa kuyi a hankali kar yaji ku,
balla mata harara tayi "ke toni dama nace miki Ina tsoron wani ne? Dallah can ni ku daga kafa mu karasa inyi in bude ledar nan inga kayan dadin da mai sunan Malam ya siyamin, "kutmelesi ke tsaya naji kina wani cewa ya siya miki ba tare da kinyi jam'i ba in kin isa kici kayan nan ke kadai a canza mun suna daga Jamila zuwa salaha ke har kin ma isa dallah ni bani ledar ma in rike!
Ai makalewa su Aisha sukayi baki bude suna kallon ikon Allah ah lallai shi yasa ake cewa ba'a kawance sai hali yazo daya dan sun dade da Sanin halin*Aminatu* na rikicin gangan ashe itama Jamilar ba tayar baya bace su dai fatan su shine su rufa musu asiri su samu su wuce majalisar nan lafiya atoh ina dalili suna neman sasu a shiga uku. Maimoon ce taja Meelat ita kuma Aisha taja Meenal dan Allah ya sani basu shirya shiga komar Mai Jama'a a yau ba, gara su dan zuwa anjima gida zasu gudu suko dole gida ɗaya zasu kwana da shi, tun basu karasa wajen majalisar ba mutuniyar ku ta fara kana nan surutu "Ke wai ita Hajiya duk bala'inta mai yasa akan mu ya kare ne ga yan zaman banza a kofar gidan ta amma ta kasa tarwatsa su ? "To ai ba laifi In kin shiga ciki sai ki tambayeta" cewar Aishatu "Ina wunin ku"
suka hada baki wajen gaisar da matasan dake zaune a majalisar amma banda Meenal ita ko daga kai batayi ta kalli ko su waye a majalisar ba duk da tsungulin ta da Aisha keyi dan tayi gaisuwar kinyi tayi yau dai anyi sa'a ba mata mazan ne kawai, "Daga Ina kuke? Wata murya mara hayaniya a cikin ta ta doki dodon kunnen ta Aisha ce ta bada amsa da cewa "daga shagon Ya Musty muke, a dubaran ce a wayance Meenal ta dan dago idonta tana neman wanda yayi maganar hada ido sukayi dashi yana zaune hakimce akan kujera kamar sauran, wayace a hannun shi yake latsawa hararan ta yayi yana zazzare mata idanun shi da suke nan dakwa² tubar kallah ba bata lokaci itama ta bishi da katuwar harara harda alakoron murguda baki zare ido yayi yana binta da kallo cike da mamakin shine wannan jaririyar yarinyar ke harara harda murguda baki aiko sai ya fasa wannan bakin data murguda mishi, Sauri ta Kara tayi gaba tabar su Maimoon a baya dan haka nan taji kirjin ta yana bugawa kasan zuciyanta kuma tanajin kamar bata kyauta ba me yasa itama zata harare shi aida ta barshi da halin shi, abun kunya wai babba da tsokanar faɗa ai Allah ma sheda ne cewa shine nan da girman shi ya fara hararar ta, bayan ba girman ido yafita ba gaskiya dai anji kunya inda wani ne yace mata manya najan tsokana ba yarda zatayi ba, sai gashi ta gani da idon ta wato tunda yasan ya girme ta shine bari ya tsokane ta salon zuwa anjima inyaso cin zalin ta ya tare ta yace zai zane ta. Allah dai yana kallon mutum atoh
# Share fisabillahi #
#Ummiee~Zaria
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*
*👨👩👧👦DANGINA!👨👩👧👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_
ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._
*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}
*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._
_Bazan taɓa mantawa da ku ba aminan ƙwarai,ina kuma alfahari da kasancewa ta cikinku,ko ban kira suna ba kun san kanku,mutanen Family House. Na gode³ ƙwarai da ƙarfin gwuiwar da kuka bani,wajen rubutun littafin *DANGINA* ubangiji ya biya da aljannah.
```Page 6
***Ganin kanta a cikin gidan Hajiya Innah yasa tuni ta watsar da tunanin wani harara da murguɗa bakin data gamayi a waje, haka nan ta tsinci kanta cikin farin ciki domin abune da bata taɓayi ba tsayin rayuwar ta wato zuwa gidan bisa radin kanta ba tareda an aikota ko sunzo da yay'yinta ko Momi idan anayin wani abun ba.
Ita kanta bazata ce ga ainihin dalilin da yake hanata zuwa gidan a wancan lokacin ba, abu guda ta sani shine ita bamai ra'ayin shiga cikin mutanen da batayi sabo dasu bane tafijin sakewa a cikin gidan su cikin *Danginta* wannan dalilin shi yasa ba ko ina take son zuwa ba daga gida sai Makaranta. rayuwar ta mafi yawa tareda Malam tayi shi dan yanzun nema data samu Jamila da Maryam har take iya barin gidan su taje musu hira kasance warsu cikin unguwa guda shima saida sukuyi ta mata mita tukun kafin ta fara zuwa musu.
Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke gaskiya tayi kewar gidan dama mutanen dake zaune a cikin shi domin indai ba mantawa tayi ba a kallah yanzun tayi kusan rabin shekara rabonta da gidan nan, gaskiya dole Hajiya tayi ta fada kullum dan itama sai yanzun take kara tabbatar ma kanta da rashin kyauta warta na rashin zuwa gidan, dan Allah ya sani taji zafin yanda aketa abubuwa a gidan amma Momy bata taɓa sata a lissafi ba, ace hidimar gidan nan da take matsayin jika a cikin shi wai sai a bakin Raheenat takeji fisabilillahi wannan ai abun kunya ne wallahi, dan haka ta kuduri niyyar toshe duk wata kafa na rashin kusanci tsakanin ta da *danginta* na wajen uwa data bari a baya Insha Allah saita ba kowa mamaki yanzun kam dan ai itama tana son su kamar yanda a kullum suma basa gajiyawa wajen nuna mata soyayya mazan su da matan su duk da cewa da yawan su ba mazauna garin Zaria bane amma duk sanda sukazo tsarabar ta daban ne suke ware mata daga cikin na yan uwanta, kuma har kwanan gobe duk wani abu da za suma ƴaƴan su tare suke hadawa da ita basa taba ban²n tawa haka suma ƴaƴan nasu indai sunzo garin can gidan su wajen mamanta suke tarewa basu cika zaman a gidan Hajiya ba saboda jarabar faɗanta sukan gwam mace zuwa wajen Momy Hauwa har su gama hutu su koma garuruwan su,domin dai kowa yasan zama da Hajiya da daɗi ba daɗi hakan nema yasa ta shaku dasu tunda ita dai bata taba zuwa garuruwan su da girmanta ba ,
Kamar yanda kowa ke son kakar shi haka itama take son Hajiya innah domin macece mai kirki ga ta da tsafta dan har yanzun data fara tsufa kullum tsaf zaka ganta cikin gayu yar gayuce ta gasken gaske dan ita gayunta basai zata fita unguwa takeyin shiba ko gidan ta kaje tsaf zaka sameta kullum kafarta baya rabo da lalle mai mata kitso ko duk sati ne wannan kam ba fashi dan haka yasa bata shiri da kazami ko bako tayi inhar ta raina tsaftar mutum bata barin ya shiga mata babban falon ta , tana da karamin falo na ganawa da duk wanda ta raina tsaftar shi.
Hajiya tana da ilimin boko dana zamani mai zurfi domin a lokacin da mijinta yana raye ta rike manyan mukaman gomnati kashi², kasancewar mijin nata babban mutum fitacce wanda tako ina ake damawa dashi a gomnatan ce yasa sukayi fice, Hajiya nada buɗaɗɗen hannu domin ko sam bata da rowa akwaita da kyauta bata da kwauro in zata baka a wadace zata baka ga kuma san zumunci tana son yau ace ɗan uwanta ne daga waje kaza yazo mata ba karamin dadi hakan ke mata ba haka itama tana da kokarin ziyartar yan uwanta , Sai daifa duk wadan nan kyawawan halayan na Hajiya wallahi ba karamar mafadaciya bace masifaffiya ce ta gaban benci kwata² bata daukar raini gashi sam bata da hakuri bata iya ganin abu ta gyale duk wanda yayi ba dai² ba ko a inane ko waye kai tsaye zata fito ta tsage mishi domin ita yar gaskiya da