Showing 30001 words to 33000 words out of 174305 words

Chapter 11 - Dangina Complete Book 1 Complete Hausa Novel

29 Sep 2025

1857

da ledar tsarabar da suka kawo mata zazzage kayan tayi kusa da inda Antyn ke zaune cike da jindaɗi tace "Anty kinga tsarabar da suka kawo min, kuma fa yau muka san juna dasu",
Kai Masha Allah sannun ku da ɗawainiya kunji angode,
Meenat ce ta rike ƙugu tana hararar Meelat ɗin "ke wai wannan godiyar da kike tun ɗazun na miye? nifa bana son haka duk kinsa naji wani iri, to nima ku tayani godiya aina faɗa muku kayan ɗazun Anty ce ta siya mana koh? ta karasa faɗa tana kallon su Moon, su kuma kamar wasu masu jiran umarni suka haɗa baki wajen cewa "angode Anty ubangiji Allah ya kara arziki" Ameen,
Sai da Anty ta rako su har bakin gate bayan ta sa Meelat ta ɗauki kayan da zasu kaima Momi Hauwa sannan ta koma cikin gida.


Sai bayan sun fito sannan tabi bayan kiran Ya Sa'ad, "ina kika ajiye wayar ne? " ya tambaya bayan ya ɗauka, sallah nikeyi Ƴa'ya ta bashi amsa tana istigfari a cikin zuciya na ƙaryar data sharara mishi "ok to ya maganar kazar a siyo ko kin koshi?"
Kai ya'yan mu bafa ni kaɗai nasa raiba harda su Aisha ma sunsa rai ga kuma Jamilata itama yau a gidan mu zata kwana dan Allah ka siyo mana kaga sai ya tayamu hira wallahi Allah ne kaɗai yasan ladar da zaka samu in kai wannan taimakon yau kaji Angon Anty Billy" bata kara sauraran jin me zaice ba ta yanke wayar a dai² kofar wani shago dake cikin layin nasu ta hango shi zaune gefen shi dama da hagu waɗansu irin ɗika ɗikan karnuka ne sunci sun koshi gwanin firgitarwa gamai kallon su gefe guda kuma yaran shine suke dafa shayi a cikin irin kananun butocin nan na buzaye,
Meenal ga ɗan gidan kinan fa, cewar Meelat data matso kusa da ita, "yaushe ya dawo kuma ni Amina? " oho in kin matsa kusa kya tambaye shi.
Ganin suna kara matsawa inda suke yasa karnukan fara haushi, wani irin haushi suke mai bada tsoro, tsukuikuye juna sukayi tsabar tsoro, suko samarin dake gefe me zasuyi ba dariya ba,
"Shutup" ya daka ma karnukan tsawa sai gasu duk sunyi kwance sunyi shiru sun natsu, ku kuma miye na dariya anan" ya faɗa yana kallon samarin fuska ɗaure, ayi hakuri Sarki" suka haɗa baki wajen faɗa,
Daga ina kuke da daren nan? Ya tambaya babu alamun fara'a a fuskar shi, Meelat ce ta iya bashi amsa da cewa "daga gidan mu muke".
Kuma sai baku iya gaisuwa ba koh? Ya tambaya "mun iya" suka haɗa baki wajen faɗa kamar wasu gaulaye,
"oho to ina wunin ku"
Kayi hakuri Ya'ya Sufyaan ina wuni ka dawo lafiya ya aiki barka da zuwa" haka suka dunga jero gaisuwa domin duk sun riga sun gama ruɗewa, "lafiya lau" ya amsa musu dashi a takaice yana kauda kai.

"Kuzo ku wuce kai kwaro zoka rakasu, yace cikin wata irin buɗaɗɗiyar muryar shi da sam bata rikuwa duk sanda yaso ya rageta da niyyar yayi magana a tsanake baya iyawa dan muryar nashi tana da amo sosai da zarar yay magana harna nesa dashi sai yaji.


Huhuhu gafa Sarki ya bayyana🤕
ina fatan kun shirya tsaf dan yanzun zamu shiga cikin labarin kaain da naain.


#Share and Comment


#Ummiee~Zaria
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*


*👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_



ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._

*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}

*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._
_Bazan taɓa mantawa da ku ba aminan ƙwarai,ina kuma alfahari da kasancewa ta cikinku,ko ban kira suna ba kun san kanku,mutanen Family House. Na gode³ ƙwarai da ƙarfin gwuiwar da kuka bani,wajen rubutun littafin *DANGINA* ubangiji ya biya da aljannah._



```Page 10

#No editing


"Angama Sarki" wanda ya kira da sunan kwaro ya amsa dashi yana tasowa shima ɗin saurayine cikakke yana sanye da plain ɗin white shirt sai gajeren wandon sojoji a jikin shi, "muje ko yan mata" ya faɗa yana mai nuna musu hanya, haka sukaci gaba da tafiya har saida suka kusa isa gidan Malam sannan ya buɗe baki yace "ku dunga kiyaye fita gida da dare fa tunda sarki ya dawo kunsan zai dunga sakin karnukan shi, yauma kunyi sa'a ne da kunkai karfe 9 da kun zama nama" ya faɗa fuskar shi ba fara'a sam, waiyo Allah kinji ko Meenat wallahi dama nasha faɗa miki karnukan nan da wuya inba naman mutane ake basu suna ciba, yanzun shikenan yaufa da sun cinyemu" Meelat take faɗa a tsorace dan ita dama shegen tsoro gareta abu kankani ke firgita ta, shiko ya faɗa musu hakan ne dan su kiyaye fitan dare.
Gab da kofar gidan ya dakata "na kawo ku gida koh? " eh Malam mun gode, cewar Meenat "to ku karasa ina hangen ku daga nan"
ai gudu² sauri² suka wuce shi kuma bai wuce ba har saida yaga shigar su cikin gidan sannan ya juya.

Dukan su kamar waɗanda sukayi gudu haka suka dunga sauke ajiyar zuciya bamai iyama wani magana a cikin su har suka ƙarasa cikin farfajiyar gidan, karar da wayar Meenat dake cikin jakarta tayi ne ya sanya Meenat ɗin kallon parking lot ɗin gidan aiko sai idonta ya sauka akan motar Momi Hauwa, "waiyo Momi ta dawo tun ɗazun kenan " ta faɗa a baiyane "ku ƙarasa ciki please zanje in duba Baba Malam ko zakuje? Ta tambaya "No kije zamu shiga da safe Insha Allah ",
Ok to ga wayata Meelat in Ƴa'Sa'ad ya kira ki ɗauka kuce ma Momi na shiga wajen Baba" ta faɗa tana mikama Meelat ɗin wayar da jakarta su sukayi gaba ita kuma ta juya akalarta zuwa sashen Malam dan tasan yanzun yana gabda tashin magidan tan da suke karatun dare a wajen shi, kamar ta shige ciki wajen matan shi sai kuma dai ta wuce falon shi kai tsaye, kamar yanda ta zata ɗin haka ta tarar ba kowa a falon dan haka guri ta samu ta zauna hango kulolin abincin da aka jera mishi a gefe ya sanyata mikewa ta karasa inda suke saida ta buɗe ko wacce kula taga abinda aka shirya mishi kamar yanda ta saba duk sanda ta shigo bata tarda shi ba takan ɗibi abincin iya wanda zata iya cinyewa taci, in kuma ta sameshi to tare suke cin abincin ko kuma in bataci ba zaici yabar mata saura dan yasan dai inhar lafiya lau take ba shakka sai tazo tayashi hirar dare, da zarar bai gantaba shima hankalin shi baya kwanciya yasan ba kalau take ba, dan haka ta ɗibi abinda take muradi duk da tana da koshi ta koma kan kujerar data tashi taci gaba da cin abincin ta hankali a kwance tana yi tana kallon Agogo, zuwa can ta fara jin mitsi da gyarar muryar Malam ɗin da yake nan kamar ƙa'idah domin inhar yazo waje kafin sallama sai yayi gyaran murya, plate din abincin ta ajiye a gefe sannan ta mike tsaye domin nuna girma mawa, da sallama ɗauke a bakin shi ya shigo fuskar shi cike da annuri, karasawa inda yake tayi tana amsa sallamar da yayi,
"Uwata idon ki kenan? " ya faɗa a yayin da take amsar littafan dake ɗauke a hannun shi, juyawa tayi tana rufe fuska da littafan alamun jin kunya, "to aini har saura kaɗan in bada cigiya naji shiru² banji ɗuriyar ki ba, harna fara cewa to ko Hajiya Amina tayimin garkuwa dake ne so take in kai mata ƴan kuɗaɗe kafin ta sakomin ke? ",
Baba ai mun dawo tun ɗazun mun shiga gidan su Jameelata ne mun karɓoma Momi saƙo yanzun ma saida Ƴa sufyaan yasa wani ya rakomu kofar gida, ni ban san ya dawo ba ai da bamu daɗe a gidan ba" ta karasa faɗa tana tura baki,
"Too haka akayi? To lallai Malam Sufyan ya kyauta tunda yasa aka rakomin uwata gida Allah dai ya saka mishi da alkhairi dan nima dai hankalina bai kwanta ba dan nasan karfe 9 ake sakin karnukan gashi banga uwata ta dawo ba, to barka tunda Allah ya dawomin dake lafiya" karasawa kan kujerar shi dake gefe yayi ya zauna "kinci abincin kuwa? dan kinga yau mun ɗan kara lokacin tashin karatun namu nasan kila kinji yunwa",
eh gashi na ɗiba ina kanci nema" karasowa tayi kusa dashi ta zauna a kasa gabda kafafun shi bayan ta adana littafan data amsa a cikin ma'ajiyar su,
Ina wuni Baba, ka dawo lafiya, ya gajiyar hanya ya mutanen Zuntun? Kun ɗaura auren lafiya? Ubangiji Allah ya basu zaman lafiya!.
Lafiya kalau na wuni uwata, kuma na dawo lafiya dan harda tsaraba ma nayi miki, mutanen zuntu suna nan kalau duk sunce suna gaisheda Uwar Malam, Alhamdulillah kuma mun ɗaura aure lafiya dan har an wuce da Amarya gidan ta tuni sai fatan zaman lafiya kamar yanda kikayi.
In kawo maka abincin nan ne ko saika huta zakaci?
To da yake ma dai bani da wani yunwa sosai inaga kiɗan ɗibomin kaɗan dai haka a faranti sai in gani ko zai shiga" to ta amsa dashi tana mikewa zuwa inda abincin yake saida ta tsatsatsakuri duk wani abunda tasan zaiso sannan ta haɗo da ruwa da zoɓo drink ta kawo,
Saukowa kasa yayi ya zauna da kyau sannan ya fara cin abincin,
Baba ashe karnukan Ƴa Sufyan suna cin naman mutum? ta jefo mishi tambaya dan abinda yake ta cizon ranta kenan tun ɗazun,
Tofa uwata ke waya faɗa miki?
"Toba wannan da yasa ya rakomu bane yace wai yau da mun kara lokaci har aka saki karnukan da sunci nama, wai karnukan ne zasuci naman mu, kaji shifa.
"Ah³ babbar magana to kinji koh ai shi yasa bana son kuna fitar daren nan yanzun da sun cizamin uwa yake nan? Kai lallai to uwata ki kiyaye fitan nan kin san ance hanyar lafiya a bita da shekara kinsan dai ko banza sojoji ba kirki ke garesu ba balle kuma karnukan su da suka sha training suka koshi,
To Baba haka za'a bar karen su dunga cizon mutane baza'ace su mai dasu can inda suka ɗauko suba? "
Ina Za'ayi haka uwata bakiga su karnukan sunayi mana gadi a unguwa bane? Aisu waɗan nan karnukan sune maganin yaran nan marasa kunya yan sara suka masu sa babba zabgawa da gudu ko bai shirya ba inya gansu, ko kin manta yanda kwanan baya suka so su fara shigo mana unguwa da sunan shara, kai ubangiji Allah dai ya shirya mana zuri'a kana nan yara su dunga ɗaukar makami suna shiga unguwan ni haka kawai duk wanda suka gani yaro ko babba tsoho ko tsohuwa mace ko namiji sai subi su sassare sai dai in ka hango su kafarka ta kwace ka, dan rashin hankali da sharrin kwayoyin da suke sha in an kamasu sai kaji suna cewa wai ai su sunje shara ne,
To saboda sune yasa ai Malam Sufyan yayi Magana a kawo mana sojijin da zasu dunga mana gadi su kuma waɗan nan karnukan ai nashi ne in yazo unguwar ne yakan sallami waɗancan sojojin suje su huta nashi yaran sojojin da karnukan suke kwana gadin mu ai mu muna cikin gidajen mu muna bacci, kinga ko ai abun a yaba mishi ne koh? Allah dai ya saka mishi da Alkhairi, "
Ciki² ta iya daurewa ta amsa mashi da ameen badan taso ba, dan ita bata san me yasa Malam yake son mutumin nan ba ko kaɗan baya son laifi ko tace Ƴa Sufyan yayi kaza sai ya nemo wani abunda zai wanke shi dashi, ita dai Allah ya sani ta tsani karnukan can masu shigen kama da zakuna, shegun karnuka dako gefen gidan kaje wucewa indai sunji motsin ka sai kukan su ya firgita ka, kawai su dai ana ɗaukar alhakin su duk sonta da zuwa tsinko mangwaro da gwaiba a gidan na Malam Ladan ɗin yanzun ba hali sabida sheggun karnukan nan insha Allah sai ta nemo poison ta basu sunci sun mutu.
Uwata ya dai tunanin me kike kuma? Malam ya katse mata tunanin ta, kafin ta bashi amsa uwar gidan shi ta shigo da sallama.

Bayan ta shigo tun kafin takai zaune tal farama Meenal ɗin tsiya da cewa " gaskiya fa gidan nan karara ake nunamin ban²ci ashe kin dawo tun dazun wato Baban ki kaɗai kika nema niko oho, to ai ba komai bari lokacin aure yayi mugani ko shi Malam ɗin binki zaiyi ku tare acan, "
Taran numfashin ta tayi da cewa
" barka da dare Innan mu, so nike fa in natashi daga nan dama in shigo, ai kinsan ban iya bacci saina ganki ko Baba"
"Kwarai kuwa uwata"cewar malam.
Ah² Malam ai kai daman kullum goyon bayan mai sunan manya kakeyi to barka da dawowa ya kika baro kakar naku da sauran mutanen gidan? "
Dukan su suna lafiya kuma sunce a gaishe ku tare muka dawo dasu Aisha ma," ta karasa fada a yayinda take mikewa bayan ta gama cin abincin datake ci,
"Badai har kingama yima Baban naki hirar ba? Naga kin mike alamun tafiya! "
Eh Innan mu akwai saƙon da zanba Momi ne kinsan ita da wuri take bacci shi yasa"
Malam ne yayi gyaran murya hakan ya maida hankalin su a kanshi Kayataccen murmushine kwance a fuskar shi a yayin da yake cewa "Innan su inaga fa maganar ki keson ya zama gaskiya, yau wacce rana kinga fa uwata ta shigo har tana shirin wucewa batayi tambaya akan tsarabar ta kamar yanda ta saba ba"
Dariya tayi tana mai amsa mishi da cewa aina faɗa maka ƴata ta girma,
Tsumewa Meenal tayi a tsaye ita kanta mamakin kanta takeyi,
"Allah Baba karnukan can na Ya Sufyaan ne duk suka firgitani" ta fadi hakan a yayin da take komawa ta zauna a kusa da Malam tana leke²n inda zata hango ledar tsarabar nata, "ina yake tsarabar nawa?"
Gefen shi ya mika hannu ya yawo wata leda bag "gashi ta nan asha lafiya jeki huta kuma sai da safe"
Haba malam ka mika mata kuma duka baka bani na ɗibi kasona a ciki ba shi yasa fa nace kuna wareni gashi kuwa! " ta faɗa tana juyar dakai gefe alamar tayi fushi,
Dariya Meenal takeyi tana mai cewa "Allah innan mu ke wai sai kice muna wani wareki, nidai ba ruwa na inma duka kike so gashi in kuma ɗiba zakiyi duka dai" mika mata ledar tayi ita kuma Innar tasa hannu ta ɗauki apple guda ɗaya a cikin ledan "nagode wannan ma ya isa yi maza kije nasan suna nan suna jiran ki"
Ficewa tayi tana musu saida safe.
A wannan rana dai kusan kwanan zaune su Meenal sukayi suna hira, domin koda ta koma ta samu Ya Sa'ad ya siyo musu kazar har biyu dakwa² ya kawo musu harda su ice cream kamar yanda yayi alkawari, basu suka rintsa ba har saida Momi Hauwa ta gaji dajin motsin su tazo ta sanya su baccin dole.

**washe gari ma da wuri Momi Hauwa tabar gidan dan ta samu kira na gaggawa daga asibity dan haka ta wuce bayan ta rarraba ma su Meelat ɗin aiki sannan ta doka musu warning cewar karsu yarda ta dawo ta cimma sun mata ɓarna a kitchen dan tana sane da abunda ya faru tsakanin su da hajiya,
To suma dai basu damu ba domin tun jiyan sun gama tsara cewa yau ɗin gidan Ya Mashkur zasu in sungama da can kuma zasu wuce gidan su Maryam dan ta kirasu da safen akan tana kan hanyar dawowa daga KD.
Da wurwuri suka gama gyaran gidan tsaf sannan sukayi wanka suka shirya da niyyar ficewa, saida suka fara shiga sashen Anty Murja suka gaisheta ita da Baba Adamu kafin suka wuce sasan Matan Malam suma suka miƙa musu nasu gaisuwar haka sauran sassan sirikan gidan saida suka zaga ko ina kafin suka yada zangon su a falon Baba Malam, to anan ɗin ma basu wani daɗe ba Meenat ɗin ta nemi izinin fita a wajen Malam kamar yanda ta saba akoda yaushe indai yana gida, to shima tunda yasan bawai yawon fitan ta cika ba shi yasa duk sanda ta nemi izinin fitan bai fiye hanata ba, dan haka yaudin ma fatan dawowa lafiya yayi musu da kuma gargaɗin su kula da kansu #2k ya cire ya basu da sunan ko zasuga wani abin a hanya.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login